fuska uku complete hausa novels by arewaacademy.com.ng

[12/9, 11:24 AM] ‪+234 810 044 6653‬: *FUSKA UKU*🏮 *01* *©Sameena Aleeyou... ✍🏽* *Bismillahir Rahmanir Raheem* _*Garin Misau Jihar Bauchi*_ Zaune take saman k'aramar kujera irin wanda mata ke amfani dashi a madafi... Yanda ta rafka uban tagumi ga buta ijiye gabanta zai tabbatar maka cewa cikin damuwa take, da alama alwala take shirin yi amma ko gizau da butan gabanta bata yi ba, tayi nisa matuk'a cikin duniyar tunani.... A haka ya fito daga makewayi ya kuwa hangeta yanda ya barta nan duk'ufe gaban buta... Girgiza kansa kurum yayi ba tareda ya furta koda kalma kafin ya k'arasa gaban k'aramar randar da kansa ya d'ibi ruwa ya tada nasa alwalan... Abin mamaki har yakai ga ida alwalansa wannan baiwar Allah sam batako motsa daga tagumin da tayi ba... Cikin tsanaki ya warware hannun rigarsa kafin ya d'au karan goge bakinsa ya saka cikin bakinsa, lokaci guda ya k'araso yanda take a zaune.... "Bilkisu..!" Shiru bata amsa ba... D'an bud'e muryarsa ya kuma yi a karo na biyu "Bilkisu..!" Sai a sannan taji kiran nata da yake yi.... Saida ta sauk'e nannauyan ajiyan zuciya had'i da muskutawa kana tace "Malam wai har an sauk'o daga masallacin ne...?" Yanda ta masa tambayar yaso basa dariya amma ya d'an gimste yace "Kiyi alwala kiyi sallah idan na dawo sai muyi maganar kinji koh... Amma wllhi wllhi kinji na rantse maki ban yarda ki tafi bariki neman d'anki ba, wannan shine rayuwar da ya zab'ar ma kansa tunda shi bamu da daraja bamuda mutunci a idanunsa, na tabbata akwai ranar da zai nememu da kansa basai kin tafi nemansa ba,..." Baikai aya ba murya na rawa ta katse sa da fad'in "Malam wllhi ni nasan ba laifin d'ana bane tsinanniyar matar nan tasa ita ta shiga tsakaninmu dashi, wllhi nasan yana son zuwa gida amma bazai iya ba sabida ta jik'a ta basa yasha, kasan matan bariki sunfi maciji guba... Malam don Allah ka min izini na fita na nemo shi, yau fah kusan shekara kenan tim rabonmu dashi...." Shiru Malam yayi tamkar mai nazari had'i da yin gajeren murmushi kafin ya girgiza kai yace "Mata kenan, akan 'ya'yayenku zakuyi komai kuma zaku d'aura laifi kan 'ya'yan wasu ku wanke naku 'ya'yan... Shin kin tab'a sanin kalan matar tasa? Kinsan yaya akayi aka nema auren, kinsan wanda ya tura a matsayin wakili....? Duk baki sani ba, rana guda ya shigo tsakar gidan nan ya sanar damu yayi aure kuma bai buk'aci albarkan ko guda daga cikin mu ba... Sanin kanki ne tunda muka gama d'awainiyar karatunsa ya girma ya zama mutum ya tsallake k'afafu ya rabu damu,... Toh ina mai tabbatar maki kada ki kuskura ki d'aura laifi kan koma wacece ita matar nasa, wannan shine rayuwar da ya zab'ar ma kansa.. Laifina guda gata da na nuna masa da yawa, cikin sa'anninsa da suka taso tare a garin nan shi kad'ai ne ya tafi makarantar kwana na yaran hamshak'ai, kai tun daga alimantari d'insa karatu mai inganci na basa, idan baki mance ba har gona ta da shanayena na gado duk na sayar a dalilin na inganta rayuwar yaron nan amma ga sakayyan da yayi min, kar dai ki mance mahimmacin shanayen gado wajen bafillace.... Tabbas sai yanzu nake hango maganganun su Malam Dalha, shi yaro ba'a masa haka, yanda ka tarbiyartar dashi toh kuwa haka nan zai tashi maka, baisan babu ba tun tasowarsa shiyasa ya girma yana jin nauyin ya nunamu yace ga iyayen sa, na masa mai wuya tunda na turasa har k'asar waje yayi karatu ya sami abin yi.... Babu komai yajesa duniya ce tafi gabaruwa iya jima, bazan masa baki ba sannan bazan saka damuwarsa cikin zuciyata ya dameni ba, kuma kema ina shawartar ki da ki cire tunaninsa cikin zuciyarki domin hakan ne kurum zaifi maki sauk'i, mu zuba wa sarautar Allah idanu, rayuwarsa ce yayi yanda yaso da ita, duk yanda yaje yazo nan dai shine cibiyarsa kuma mahaifarsa.... Na wuce masallaci kinji liman har ya tada ik'ama, maza kema kar na dawo na sameki wajen nan...." Bai jira cewarta ba ya fice cikin sassarfa... Ta jima tana nan zaune a wajen tana sak'e sak'en hukuncin da zata yanke gameda al'amrin, har saida taji masallaci suna raka'a na uku kafin ta murmurs tana mai jin dad'in mafitan data samo, don bazata biye Malam ba ta zauna ta zuba idanu tanaji tana gani ta haifo tilon d'anta guda ma bariki ba..... *** *Abuja* Cikin sanyin muryarta taci gaba da buga k'ofar tana kuka take fad'in "NANA H please open the door, please listen to me sis.... Don't shut me out again please.... Dan Allah ki saurareni....." Daga cikin d'akin kana iya jiyo sautin k'aran fashe-fashe... Cikin kukan itama take fad'in "Just go away NANA A I hate you, I don't wanna see you ever again.... Ki fice min daga gida kuma kada ki sake zuwa yanda nake.... Burinki ya cika Ammah da Uncle SIRAJ suna fushi dani... Ki tafi bana son ganinki..." Hannu tasa tana share hawayen da suka wanke mata fuska kafin tace "Sis I'm sorry.... I.... I didn't mean to upset you, please let me explain.. Wllhi zanyi duk abinda kika umarceni kiyi hak'uri dan Allah...." Jin kalamanta na k'arshe ya sanyata sakin wani shu'umin murmushi tana mai duban kanta jikin dressing mirror kana tace "I you sure zakiyi duk abinda na umarceki..." Cikin sauri ta bakin k'ofar ta shiga jinjina kai tana fad'in "Wllhi zanyi kinji pls open the door....." Saida ta mik'e tsaye tayi rawa saman gadon tamkar mai tab'in hankali kafin ta dirk'o daga saman gadon ta nufo k'ofa.... Kallo d'aya tayi mata sanda ta bud'e k'ofar nan ta lura da yanda fuskar 'yar uwartata ta kod'e sosai alamun taci kuka, lokaci guda tayi rau-rau tana fad'in "Oh Sis ki daina kuka pls... Kinji I'm sorry, bazan sake sakaki kuka ba kinji koh...." Lokaci guda suka rungume juna kafin suka koma cikin d'akin hannayensu rik'e cikin na juna,... Yanda suka jeru suka zauna bakin gado zaka gane tsan-tsan kamannin da suke, basai ance maka tagwaye bane sabida tsananin kamanni da suke, saidai d'aya 'yar gayu ce ta k'arshe yayinda d'ayan gayun sam bai shalleta ba, hasalima bata iya ba.... "NANA ASMA'U....!" Cewar 'yar gayun tana mai duban 'yar uwar tata wacce itama ita take kallo.... "Kina jina, bawai bana son Uncle Siraj yayi aure bane, kinsan 'yan matan yanzu wllhi idan yayi aure shikenan mun sallamawa matar da danginta shi, kuma sanin kanki ne bayan shida Ammah bamuda kowa, gwara ni ma nayi aure inada miji, but what about you, wa kike dashi? Waye zai tsaya maki a rayuwa namiji idan buk'atar hakan ta taso,... A kullum ina nusar dake hanya but baki ganewa, nifa idan ta ni ne Uncle Siraj zai iya zuwa yayi aurensa, but wllhi har ga Allah ke nake jiyewa Sis, kinga dai irin lalurar da kike fama dashi ta rashin k'afa guda, shin kina jin a haka zaki sami wanda zai k'aunaceki tsakani da Allah... Kema kinsan saidai ya aureki kawai don babban kaso na dukiya da mahaifinmu ya mutu ya bar mana, na sani kinada kyau Nana A amma duk yanda kyaunki yake baikai na lafiyayyayar mace ba maras nakasa a tattareda ita... Nana ki auna magana na ki gani, this world is something else now,..." Tunda ta soma magana jikinta yayi sanyi dama hakan ne yake faruwa da ita duk sanda 'yar uwar tata tazo mata da wani zance ko shawari.... A hankali ta shiga jinjina kai tana mai auna kalaman 'yar uwar tata kana tace "Na fahimceki NANA HAFSAT, kuma duk abinda kika fad'a hakan take, amma wannan dalili sam baiki yasa mu hana k'anin mahaifinmu jin dad'in rayuwarsa ba, Nana H sam nakasata bata dameni ba, kuma nasan shi aure lokaci ne kuma abincin wani guban wani, nasan Allah zai kawo min wanda zai soni ya k'aunace dukda cewa yana sane da nakasan dake tattare dani, don haka ki daina saka ma ranki damuwa sabida lalurata... Sannan Uncle Siraj went through alot, yaga iftila'i daban-daban a rayuwa, kar ki manta a baya duk macen da ya nema toh fah mutuwa takeyi, sannan kar ki mance Aunty Zulfah a daren aurensu 'yan fashi suka shigo har cikin gidan suka kasheta, daga wancan lokaci ya shafe shekaru kusan uku cikin tsananin tashin hankali da alhini, uwa uba sanin kanki ne babu abinda Ammah take so kaman taga autanta yayi aure.... Nana H nidai a gani na mu bar Uncle Siraj yayi aure idan har Allah ya tabbatar da hakan....." Tunda ta soma magana take binta da wulak'ancaccen kallo tana huci, lokaci guda ta mik'e tsaye tana nuna mata k'ofa take fad'in "Fita.. Fita nace idan ke baza'ayi shawarin arziki dake ba...." Bata mik'e d'inba bata fice ba sai gyara zama data kuma yi..... Lokaci guda tamkar ta tuna wani abin ta komo ta zauna a mazauninta kafin ta sauk'e ajiyan zuciya tace "Gaskiyanki ne Sis, Uncle Siraj deserve to be happy... Babu damuwa zanje har gidansu Nadiya na bata hak'uri, amma nasan yana fushi dani..." Lokaci guda idanunta sukayi rau-rau ta kuma damk'o hannun 'yar uwar tata tana fad'in "Dan Allah Sis ki basa hak'uri kinji, make sure ya hak'ura pls kinji dan Allah...." Ta k'arashe kaman zata kurma ihu... Lokaci guda tausayin 'yar uwar tata ya shigeta.... *** Driver na ida parking ta hangi Ayiya tsaye farfajiyan gidan hannu hard'e da k'irji tana bin motar da kallo, ga dukkan alamu dawowarta take jira, ta kuwa sha mur.... Sosai tasha jinin jikinta don babu wanda yasan sanda ta fice a gidan, bayan tasan ya zamto tamkar doka duk yanda zataje tofah tareda Ayiya ne , Dattijuwa mai kimanin shekaru 66 a duniya... Cikin takunta na d'ingishi ta nufo yanda take... Sam bama ta kanta Ayiya take ba tukuna, Sule dreba kawai take kallo yanda yayi parking motar cikin tsoro don yasan zai iya kwasan nasa buhun bala'in tunda ta sa masa doka bataso 'Yar Albarka tana fita ita kad'ai sabida lalurin dake tattareda ita.... "Ayiya barka da yammaci...." Kallonta kawai tayi ba tareda ta amsa ba kafin ta k'arasa ta nufi yanda Sule ya ida parking.... Kafin ta soma magana Sule ya tari numfashinta da fad'in "Wllhi wllhi Ayiya ba laifina bane, kindaiga yanda Nana Hafsat ta fice a gidan nan cikin fushi da b'acin rai, ni kuma wllhi magiyan da Nana Asma'u tayita min shiyasa na kaita..." Baikai aya ba ta katsesa da fad'in "Ka kaita a muzanta ta a wulak'anta ta a fad'a mata kalamai marassa dad'in ji koh... Kadai san Hafsatu ba mutunci bane da ita wulak'anci sam bai mata wahala, ni kuma ina numfashi k'aryan mutum ya muzanta 'yar albarka ko ya wulak'anta ta... Kai billahillazi sai mu tafi har kotun Buhari da duk mahaluk'in da ya hana 'yar Albarka rawan gaban hantsi...." Sule dai dubanta yake cikeda mamaki yanda yaga bilhakk'i laifinsa kawai Ayiya take gani sam bataga laifin Asma'u ba..... "Ayiya bafa ni na kar zomon ba rataya aka bani....." "Kai tafi can rufe min baki, da wani abin ya sameta yau da ka gane kurenka...." Ta wuce fuuu tana ci gaba da sababi.... Nana A ta bita da kallon mamaki yanda sam fad'a bai mata wuya musamman idan akanta ne.... Ko tankata batayi ba ta janyo hannunta suka nufi cikin gidan.. Sum-sum Nana A ta take mata baya... A parlor suka tarar da Ammah ta rapka uban tagumi, don duk ranar da Siraj da Nana H suka b'ata sam gidan haka zai zamto babu walwala domin gaba d'aya basu gane kan Siraj har sai ya shirya da niece d'in tasa wacce yake matuk'ar k'aunarta da kuma jida ita.... **** Bakin zaninta ta kamo tana kuma goge hawayen da suka mak'ale cikin idanunta take ci gaba da fad'n "JUNAID ka tabbata zaku iya zama ku biyu rak, ka tabbata komawa wancan gari mai bak'in tarihi shine jin dad'inku..... Junaid I'm afraid... Ina tsoron kada su sake ganinka don na tabbata a iya tunaninsu ka mutu tuntuni...." Matashi ne wanda a k'iyasce bazai gaza shekaru 32 ba zaune saman wheelchair aka kirada JUNAID, dukda cewa a ido k'afafunsa lafiya lau suke saidai a zahiri ko motsasu bai iya yi, yau kusan shekaru hud'u kenan da faruwan Al'amarin.... Cikin tsanaki ya soma tura tayan keken guragun nasa har ya iso gaban middle aged woman d'in da ke ci gaba da matsan k'walla... Cikin muryarsa wanda yake tamkar ana hura sarewa ya soma magana... "Umma Marie thank you for everything.... Thank you for taking care of us.. Nida Azeeza, na gode da jinyata da kikayi, na tabbata banida abinda zan biyaki dashi... Kuma na gode da b'oyeni da kikayi a lokacin da ake farautar rayuwata.... Umma Marie I don't have a choice than to face those three..... Nayi alk'awarin d'aid'aita FUSKA UKUN nan ta ko wani irin yanayi, kiyi hak'uri Umma Marie dole ce tasa nayi hakan..." Cikin rawar murya Umma Marie tace "Toh Junaid baka tsoron ka jefa rayuwar Azeeza cikin had'ari, meyasa bazaka tafi kai kad'ai ba ka barmin Azeeza, kar wani abin ya taso kai kuma ba k'afafu gareka ba....." Murmusawa yayi had'i da sunkuyar da kai ya k'urama k'afafunsa idanu kafin ya d'ago ya dubi Umma Marie yace "Kar ki damu Umma I can protect her and provide for her... Bazan tab'a bari wani abu ya sameta ba, ki kwantar da hankalinki kinji....." Jigum tayi tana dubansa kafin tace "Shikenan, Allah ya tsareku gaba d'aya, amma Junaid muddin naji wani mummunar labari gamedaku zan baro Yobe na taddaku a can Abujan...." Murmusawa ya kumayi kana yace "Umman mu kar ki damu, na rigada na shirya, kawai taimako guda da zaki sake min shine ki shawo kan Azeeza ta yarda ta biyoni, and please kar ki sanar da ita komai gameda k'udirina..." *SameenaAleeyou...📚**FUSKA UKU*🏮 *02* *©Sameena Aleeyou...✍🏽* _*Tambuwal* _Sokoto_ Zaune suke baje-baje a tsakar gidan ko wacce hannunta rik'eda kananan beads irin wanda ake had'a sark'a na amare dasu.... Budurwa ta tsakiyar mai kimanin shekaru 24 itace ke fama zira na hannunta tana yi tana taunar chewing gum ga d'aurinta a gaban goshi irin wanda hausawa ke cema ture kaga bala'i, itako wacce ke zaune daga k'arshen tabarman sai faman 'yan wak'e-wak'enta take tana had'a nata 'yankunnen Wata dattijiwar mace ce wacce bazata gaza shekaru 58 ba ta fito hannunta rik'e da langa tana duban 'yanmatan wanda yanzu sun k'ware sosai a sana'ar tasu, har cikin ranta take jin dad'in yanda suka rik'i sana'arsu babu ruwansu da abin hannun saurayi, shiyasa take matuk'ar son k'awancen d'iyarta da Zaliha don ya fiye mata k'awance da yaran lungun nasu don duk bawai tayi na'am da tarbiyarsu bace.... Sai sannan 'yan matan suka lura da ita, har suna had'e baki wajen cewa "Dadda barkada fitowa...." Fuskarta d'aukeda murmushi tace "Sannunku da k'ok'ari 'ya'yana Allah dai ya dafa maku...." Gaba d'aya suka murmusa itako mai taunar chewing gum d'in harda wani yin k'araras dashi kana tace "Ameen Daddata abin alfaharita, da kud'in beads zan kaiki Makka na sai maki hak'orin gwal...." Nan fah Dadda ta washe baki tace "Allahumma ameen d'iyata...." Ana cikin haka wani almajiri yayi sallama ya soma gaida Dadda da tuni ta gimtse fuska don tasan yaron bazai wuce aike yazo ba.... Aiko kaman jira yaron yake nan ya soma fad'in "Wai ana sallama da MAIRO a waje...." Ai bai ida maganar ba Dadda ta dasa butar ta a k'asa kana tace "Jekace bazatazo ba dan uwarka...." Yaro kuwa jin haka ya fice a guje har yana cin karo da k'yaure... Dadda taci gaba da sababi tana fad'in "Inyi ai kaji irinta, dagaji sune irin samari masu lalata yaran mutane, toh dan ubanka bazata zo ba, salon ya matseta a lungu koh... Ni d'iyata sai na darje mata miji kafin na aura mata ehe, babu shegen da zai wanko b'aragurbin k'afafunsa ya nemi auren d'iyata na basa....." Bata ida magana ba sai ganin saurayin sukayi har cikin gidan, don tsaf yana jiyo zage-zage da masifar da Dadda ke faman yi... Saurayin nan yana shigowa 'yan matan nan suka bar abinda suke suka mik'e tsaitsaye babu shiri suna kallon ikon Allah... Dadda na ganinsa ta shiga gyara bakin zaninta tana fad'in "Toh jarabebbe d'an naci, ni dama nasan kaine fitinannen da bazaka d'auke idanu kan d'iyata ba... Toh duk maitanka haka zaka ganta ka barta dan uwarka, shege d'an bakin uwa...." Batakai aya ba saurayin ya shek'e da dariya kana yace "Gwara ni ko uwata ta min baki inada uba, shegiyar 'yar taki da kike b'oyeta uwa gwal ki sanar damu ubanta, aikin banza aikin wofi ashema yawon garuruwa da kuke ba haka kurum bane, idan ba tsoro ba ki sanar da d'iyar taki ubanta mana ko kuma ki sanar da ita ga garinta mahaifarta...." Yayi wata murmushi kafin yaci gaba da fad'in "Bakuda gari yawon duniya kawai kuke, ki jik'a 'yar taki ki sha babu abinda zamuyi da shegiya maras asali, kuma kinji na rantse idan baku bar mana gari ba sai mun kwance maki zani a kasuwa....." Baikai aya ba yaji sauk'ar lafiyayyar mari a k'uncinsa... Shaye da mamaki yake rik'e da fuskarsa yana duban wacce ta maresa gata a gabansa baifi yayi wurgi da ita ba... "MAIRO ni kika mara....?" "An mareka d'in maras mutunci wanda baisan darajan tsofaffinsa ba, kaji na rantse maka idan baka fice a gidan nan ba sai mu lallasa maka na jaki...." Ta k'arashe tana kwance d'aurin kwalinta had'i da shan d'amara dashi... A tamanin d'aya budurwar ta fad'a kitchen ta rarumo wuk'a ta shiga wasawa yayinda Mairo ta sunkuya ta wawuso k'afafunsa ji kake timmm ta kadasa k'asa babu ko gizau a tattareda ita.. Fad'i take "Zaliha yi maza ki kawo wuk'ar kafin ya tashi...." Jin haka yasa Saurayin kukan kura zai tashi don bai zaci Mario nada k'arfi har haka ba, saidai kafin ya mik'e Dadda ta zaune akansa tana fad'in "Dan uwarka koma babu yanda zakaje..." Ai tuni ya bud'e murya ya soma neman d'auki... Basu k'yalesa ba saida suka masa lilis, bai t'aba yarda da hausan da akace b'aro a hannun mata ba sai yau, shikam ya shaida dukda ba sata ya shiga ba... Saurayin nan yana ficewa a guje Dadda tasha jinin jikinta don tasan yau an d'agowa Mairo gyambon dake zuciyarta, akasarin garuruwan da suka baro wannan dalili shikesa su baro, sannan wannan na d'aya daga cikin da yasa Mairo batada tak'amemmen manemi, da zaran sunji batada asali sai su gudu ko iyauensu suk'i yarda, idan ma baka gudu don rashin asalinta ba zaka gudu don bala'in uwarta Dadda.... Dadda zatayi magana Mairo ta d'ago mata hannu alamun dakatarwa, ta kuwa cika tayi fam sabida b'acin rai, cikin tsananin fushi ta wuce uwar d'aki ta kulle, don duk masifa irinta Dadda tana tsoron masifa da fushin Mairo... **** *LAUSHI GROUP* Tafe suke cikin tampatsetsen kamfanin wanda ya tsaru iyaka tsaruwa, yaji landscaping.... Matasa ne wanda a k'iyasce bazasu gaza shekaru 35 zuwa 36 ba, sannan da gani zasu iya kasancewa sa'anni ko kuma subawa juna ratan shekara d'aya zuwa biyu... Wanda yake daga tsakiya shi ne yafisu haske gaba d'aya sannan sanye yake cikin business suit d'insa wanda ya amshi jikinsa sosai ya dad'a fito da kyaun halittarsa... Shi kuwa d'ayan wanda yake daga b'arin dama sanye yake cikin kaki irinta Nigerian police force, shima kakin ta 'yansanda ta amshesa sosai saidai shi baida haske kaman na mai sanye da suit d'in amma kallo guda zaka masa ka fahimci tsan-tsan bafillace ne ga sumarsa da suke a nannad'e irinta fulben usul... Shi kuwa d'aya na b'angaren hagu sanye yake cikin wata lallausar yadi ruwan toka d'inkin half jampa, shi yafisu duhu gaba d'aya saidai Allah ya masa kyaun jiki da cikan zati, wanda hakan yasa yakeda gizo sosai a idanun jama'a... A wata 'yar k'aramar rumfa ta shak'atawa suka zauna suna ci gaba da tattaunawarsu lokaci guda wata mace sanye da farin uniform ta ajiye k'aramar tray a gabansu wanda ke d'auke da cups basai ance maka Champaign bane cikin cups d'in..... Saida ya sipping Champaign d'in kafin ya kuma duban saurayin dake sanye cikin business suit yace "You've been an ass.... Ka sani ko?" D'ago idanunsa guda d'aya yayi had'i da kanne d'ayan kana "Na sani.... Kuma bazan bata hak'uri akan abinda Nana H tayi mata ba, wannan ita ya shafa bani ba.... Kai nifa tunda na rasa Zeenatu bana tunanin akwai macen da zan kuma rasata ya dameni ba.... Banida lokacinta ma..." Da gefen bakinsa yake murmusawa yana duban abokin nasa kafin ya d'ago cup d'insa alamun toast yana mik'awa d'aya abokin nasu yake fad'in "To Siraj Laushi's pain in the ass behavior.... May he stay as forever bastard ...." Kallonsa kawai Siraj yake had'i da girgiza kai kana yace "LAMID'O idan kana son Nadiya ce fah you can have her, wllhi I dont care....." Sai sannan mai sanye da kakin ya murmusa had'i da ajiye cup d'in hanninsa saman k'aramar table d'in kana yace "Wannan shi ake kira fad'an gauraye.... Ya kamata ku ajiye iyali tsufa kuke kun sani koh...." "Fad'a masa Detective ya ajiye Iyali dai don shine mai manyan d'iyoyi 'yanmata... Nikam I'm still young yanzu ma na soma cin tawa duniyar....." Siraj yayi k'wafa yana watsawa Lamid'o mugun kallo kafin ya dubi matashin dake sanye cikin kakin yace "AHIDJO tashi muje naga Hafsat, I'm worried about her...." Kallonsa sukayi gaba d'aya yanda ya mik'e a birkice kafin Lamido yace "Wannan SHAK'UWA taku tayi yawa, a dai dinga ragewa ake tunawa Hafsat ta girma ba k'aramar baby bace infact tama fika samun experience na rayuwa tunda tayi aure kai kuwa bakayi ba...." Banda watsa wa Lamido mugun kallo babu abinda Siraj keyi... Baida lokacin tsayawa amsa masa gajeren tsaki kawai yayi had'i da d'aukan car keys d'insa ya fice daga cikin rumfar... A tare Ahidjo da Lamid'o suka mik'e suka take bayan abokin nasu..... Suna tafe wayar Ahidjo ta soma vibrating daga wajen aikinsu ake kiransa dole ya wuce ofishin nasu yayinda Lamido da kuma Siraj suka nufi gidan Ahidjon domin duba Nana H, 'yar gaban goshin Uncle Siraj wanda a kullum kafawa abokinsa Ahidjo sharad'ai yake akanta, ba'a b'ata ranta, donma shi kansa Ahidjon bawai lokacinta yake dashi ba yafi baiwa aikinsa mahimmanci, sam basuma faye zama tare ba sunan anyi auren ne kawai... *** *Misau* A guje yauma ta shigo gidan tagajan bagajan... Innah Balki tana lafiya meke faruwa... Ai kafin ta ida fitowa daga d'aki ta hangi mutum saman rijiya sai tsalle take tana kururwa... Babu shiri zani a hannu ta fito burut daga d'akin tana sallalami... Iya Gaje ce ta shigo cikin gidan itama a d'ari tana fad'in "'Yar k'wal uba yau yankaki zanyi shegiya mai kamada mayu...." Aiko Gaje tayi wajen rijiyan nan da d'aurin k'irji haka nan ta fito tun daga gidan nata... Innah Balki banda salati bata komai sai rawa da jikinta keyi kaman an d'ana mata shokin ganin yanda Gaje ta biye k'aramar yarinyar da batafi sha hud'u ba suna kokawa jikin rijiya.... Innah Balki ta maza tayi ta rik'o yarinyar ta b'oyeta a bayanta yayinda Gaje taci gaba da sababi... "Yau zaki bar min gida ehe, munafuka mai halin uwarta, tambad'add'iya kawai...." A hasale Innah Balki ta soma fad'in "Ke Gaje ki sauk'ak'a harshenki kan 'yar marainiyar nan, ke ko tausayi bakiji... Shin wai bakida imani ne....?" Bata kai aya ba Gaje dake binta da kallon wulak'anci tace "Toh uwar shisshigi da iyayi, banida ita, nace banida imanin anyi rabonta ina bacci.... Yo dole ma kice d'a na kowa ne mana sabida naki d'an ya fantama bariki... Ayyiriri ni Gaje naga salo... Toh wllhi Balki ki fice a hidiman gidana idan ba haka ba billahillazi zan maidaki abin kwatance a garin nan....." Tunda ta soma magana Innah Bilki ke kallonta, girgiza kai kurum tayi tana mai bin Gaje da addu'o'i na shiriya.... Gaje ta gyara d'aurin k'irjinta ta dubi yarinyar tace "Dan ubanki zaki dawo gidan ki sameni ne...." Daga haka fuuu tayi ficewarta daga gidan.... Innah ta maido da dubnta ga yarinyar wacce har lokacin shan zuciya take kana ta dafa kanta tace "DEEJO mai kika mata yau kuma? Ba na hanaki rashinji ba..?" Bakin d'amaranta ta kamo tana sharen hawayenta take fad'in "Innah waifa kawai don wannan Ladon mai kid'a a dandali yace na kai mai fura d'akinsa ya saya ban kaiba shine fah tayita dukata wai na mata asara..." Innah ta shiga sallalami tana tafe hannaye cikeda mamakin bak'in zuciya irinta Gaje, Allah sarki tausayi Deejo ya kuma cika zuciyarta, Deejo k'aramar yarinya ce wacce kamata yayi ace tana makaranta bama tallaba, amma gaba d'aya Gaje ta tauye rayuwar wannan yarinya, sannan nema ma take ta d'aurata kan wata mummunar rayuwa, tabbas d'a na kowa ne idan ta taimaki Deejo watak'ila Allah yaji k'anta ya karkato mata da hankalin nata d'an zuwa gida...... *** Sosai Nadiya taji manikin ganin Nana H a gidansu, don irin d'iban albarkan da tayi mata a while ago kan Kawunta bata tsammaci zata kuma iya mata koda kallon mutunci bane, sai gashi kuma wai hak'uri tazo bata har tana neman su zamto k'awaye.... "I'm sorry for being bit emotional.... Aunty Nadynmu kiyi hak'uri da Nana H, kowa da kika gani a gidanmu wllhi hak'uri suke dani, kinsan ina son Uncle Siraj sosai kuma inaji dashi, so duk wata mace sai naga kaman rabamu dashi zatayi....." Ta k'arashe tana sipping laccasera juice d'in da aka serving d'inta a cup, k'afafun nan kuwa d'aya bisa d'aya.... Ga wani tayani gantalin gyale wanda ake kira kafi rariya shi ta d'aura bisa kafad'anta, yatsunta kuwa kama daga na hannun zuwa na k'afa duk sunsha kwalliya da faratan roba, tamkar ba d'iyar musulmai ba balle kayi tunani wai har aure gareta.... Nadiya ta d'an murmusa kana tace "Babu komai Nana Hafsat na fahimceki kuma na hak'ura komai ya wuce insha Allah...." Murmushi Nana H tayi had'i da matsowa kusan Nadiya tayi hugging d'inta tana mai bayyana murnanta... Daga haka hira sosai ya b'arke tsakanin Nadiya da Nana H har saida taga kiran Uncle d'inta Siraj na shigo mata, nan ta nunawa Nadiya fuskar wayar taga mai kiran nata yanda aka rubuta _Uncle luv_ Da murnanta ta d'aga don ta sanar dashi gata gidansu Nadiya kuma ta fixing komai.... Siraj yaji dad'in hakan sosai, don yasan yanda baison b'acin ran Nana H haka itama bata k'aunar b'acin ransa.... Lamido da ya kanne idanu had'i da kafe Siraj dashi sai faman sak'awa da warwarewa yake... Suna rabuwa da Siraj gidansa ya wuce yanda ya jera wasu pictures wanda akayi crossing d'insu da jan marker alamun an gama dasu... Had'e kansa yayi waje guda yana wasa da zoben hannunsa saman hotunan....... *** Ayiya da Nana A ne zaune a parlorn suna kallon tashan abin dariya cikin raha da jin dad'i.... Kaman daga sama sai ganin Hafsat da Siraj sukayi sun shigo cikin gidan mak'ale da juna... Nan da nan Ayiya ta had'e fuskar nan tamau don itakam tak'i jinin wannan Shak'uwa mai k'arfi dake tsakanin Siraj da Nana Hafsat.... Ammah dake sauk'owa daga bene murmushi ta sakar masu sanda ta hangi Siraj da Nana H na shigowa cikin parlorn kana tace "Inyye kaga 'yar gidan Kawu an shirya kenan...." Nana H ta kuma shigewa cikin k'irjin Siraj tana wani murmushi take fad'in "Ammah kinsan bani son fushin Uncle luv yanzu ma daga gidansu Nadiya muke mun warware komai, tama riga ta zama k'awata..." Ammah ta fad'ad'a murmushinta kana tace "Da kyau 'yar gidan Uncle haka nake son ji maza ku k'araso nayi serving d'inku dinner...." Ko takan Ayiya da Nana Asma'u basu bi ba suka nufi wargajejen dining area d'in... Asma'u ta d'ago idanunta da suka d'anyi rau-rau tana duban Ayiya, domin har cikin ranta wani sa'in takanji zafin banbanci da Kakarta da kuma Kawunta da suke nuna mata k'arara tsakaninta da 'yar uwarta..... Cikin sauri Ayiya ta kamo hannunta tana girgiza mata kai alamun kada tayi kuka... A hankali Ayiya ta kamo hannunta tace "Tashi muje lokacin hutawarki tayi, a cire k'afar nan ki huta koh...." Babu musu Asma'u ta shiga jinjina kai tana k'ok'arin dafa kujera domin mik'ewa.... Haka suka taho zasu wuce saman bene sai sannan Siraj ya kula dasu ya d'an bud'e murya yace "Nana A , sweetheart zo mana muci abinci...." Daga yanda yayi maganan cikin nuna kulawa har cikin ranta Nana H bata so ba, amma gimtsewa kawai tayi tana ci gaba da cakalan fruits d'in dake gabanta... Cikin sanyin muryarta had'i da murmushi saman fuskarta ta d'an kaikaito tana dubansu kana tace "A'a Uncle na riga naci abinci... You go ahead..." "Come on sweetheart, zo ki zauna cikin 'yan uwanki mana, kar ki koma d'aki ke kad'ai..." Caraf kaman jira take ta tari zancen da fad'in "Uncle luv ka k'yaleta kasan ta saba da zaman d'aki, ko tazo nan ma bazata saki jikinta ba....." Ayiya data cika tayi fam kaman jira take nan ta soma sillesu tas... "Toh bazata zaunan ba, data zauna yanda za'a muzanta ta a b'ata ranta gwara ta zauna ita kad'ai a d'aki... Ank'i ta zauna d'in.... Wuce mu tafi 'yar Albarka...." Ko amsarsu bata tsaya sauraro ba ta janyo hannun Nana A suka wuce.. Nana H ta rakasu da hara had'i da jan tsaki.... *** Sunfi minti talatin suna zaune a train station d'in babu alamun jirgi ga yunwa da sanyi dake azalzalanta "Ya Junaid nifa yunwa nakeji..." Ta fad'i tana kuma kwantar da kanta saman luggage d'insu... D'an dubanta yayi yanda take hamma babu ko k'akk'autawa cikeda tausayinta... Hoodie d'in dake bisa kansa ya kuma janyowa ya rufe fuskarsa sosai kafin ya nufi kujeran da ya hangi dangin snacks ajiye saman kujerun..... *SameenaAleeyou... 📚* [12/10, 10:06 PM] ‪+234 810 044 6653‬: *FUSKA UKU*🏮 *03* *©Sameena Aleeyou...✍🏽* Yaran sam basu kula dashi ba har ya isa yanda snacks d'in suke ajiye bisa dogon kujeran, sai faman tsalle-tsallen su suke a wajen.... Ya jima yana duban yaran kafin ya janyo hoodie d'insa ya kuma rufe fuskar shi da shi.... Cikin azama ya kwashi snacks d'in dake nannad'e cikin tissue paper ya zura cikin rigar sanyin nasa.... Har ya soma waina tayar kekensa cikin sauri don barin wajen, kaman wanda aka ce ya tsaya, cak yayi birki ya tsaya tamkar wanda ya tuna wani abin, cikin sauri ya kuma juyo kan keken ya nufi yanda ya d'au abincin, kaman yanda ya d'auka haka ya bud'e rigarsa ya maidasu ma'ajinsu... Duk abinda Junaid keyi akan idon yarannan ne... Sosai Junaid ya basu tausayi musamman da sukaga halin da yake ciki a haka har mahaifinsu ya k'araso ya taddasu, nan suke nuna masa abinda suke kalla, d'an babban cikin yace "Daddy yunwa yakeji." Mutumin da ya ambata da Daddy shiru yayi tamkar mai nazari basu ankara ba sai gani sukayi babu Daddyn su a wajen, suka ci gaba da kallon Junaid yanda ya komawa Azeeza babu abinci sai faman kuka take masa yana lallashi.... Yaran har suna rige-rige wajen d'aukan sauran abincinsu suka kaiwa Azeeza, ta macen wacce bazatafi shekara biyar ba harda gogewa Azeeza hawaye tana fad'in "Aunty ki daina kuka you can eat our food kinji, tunda Momy ta tafi ta barmu Daddy ya hanamu kuka yace mai kuka tears d'insa zai k'are...." Daga Azeeza har Junaid cikeda mamaki suke duban yarinyar, d'ago kai da zasuyi suka Kalli mutum tsaye akansu hannunsa rik'eda farin takarda wanda yake a nad'e basai ance maka snacks bane ciki... Jikin mutumin yayi sanyi sosai jin abinda 'yar tasa take fad'i Shiko namijin mai kimanin shekaru 6 kallon mahaifinsa yayi yaga yanda yayi sakare yana duban k'anwarsa sannan ya dubi su Junaid da Azeeza yaga yanda suma suke kallon mahaifinsa da k'anwarsa cikin wani irin yanayi... Cikin sauri yaron ya k'arasa ya shiga janyo k'anwarsa daga jikin Azeeza yana fad'in "Taheera what do you think you're doing, unhand her... Didn't Dad warn us about strangers?.." Cikeda damuwa yarinyar tace "But Hammad look she's crying and hungry... I only want to help..." Cikin sauri mahaifin nasu ya durk'usa had'i da dafa kan yaran kana yace "Hey kids go back to your seat now okay...." Babu musu yaran suka jinjina kai , Taheera ganin abinci hannun mahaifinta harda d'anyin tsallen murna kana ta juyo da dubanta ga Azeeza tace "Aunty Daddy bought some.... Ki daina kuka kinji....." Azeeza da murmushi ya cika fuskarta don sosai yarinyar ta burgeta batasan sanda ta shiga jinjina mata kai ba tana share hawayenta... Bayan su Taheera sun koma wajen zamansu sai kuma aka shiga kallon-kallo takanin mutumin dasu Junaid..... Saurin saita kansa mutumin yayi kana ya mik'awa Junaid hannu donyin musabaha.... Junaid bai mik'a masa hannu ba sai kallon da ya bisa dashi... K'ak'aro murmushi mutumin yayi yana d'an satan kallon gefen da Azeeza take kana yace "Am.... am.... Kuyi hak'uri da surutun Taheera, haka yarinyar take da son taimako,...." Ya maido da dubansa ga Azeeza wacce ta kafesa da idanu uwa ta sami TV... Gaba ya d'aya ya tsargu da kallon da take masa, cikin sauri ya ajiye abinda ke hannunsa a gefenta kana yace "If you don't mind miss...." "Bazataci ba..." Kalaman da ya jiyo kenan tana fitowa daga bakin Junaid.... Mutumin ya bisa da kallo cikeda mamaki... Azeeza da tuni har tasa hannu zata d'auka Junaid ya finciko takardan yayi wurgi da ita... Cikeda mamaki mutumin ke kallon Junaid sai sannan ya tuna yayi shisshigi ta yuwu wannan yarinya matan gurgun nan ne dole abin ya zafesa idan yayi mata kyauta... Saida ya daidaita tsayuwansa had'i da gyaran murya kafin yace "Kayi hak'uri bawan Allah taimako nayi niyyan yi kaman yanda naga yarana sun buk'aci hakan, sannan ni ba mugu bane bazan cutar daku ba kuma ni d'an uwanku musulmi ne....." "Malam naci bazataci ba... Bamu sanka ba bamusan daga ina kake ba kawai ka baiwa 'yar uwata abinci.. A ina ka tab'ajin anyi haka...?" Saida ya sauk'e nannauyan ajiyan zuciya jin Azeeza ba matar Junaid bace kafin ya d'an murmusa yace "Toh ni sunana Barrister Nasaar Gumau, kuma ni d'an asalin garin Gumau ne dake jihar Bauchi sannan mazauni garin Abuja.... wad'ancan yarana ne Hammad and Taheera, yanzu haka mun fito garin Maiduguri ne domin duba dangin mahaifiyarsu..... Kuyi hak'uri nayi abinda baku umarceni ba, a yanayin aikina kullum ina zama ne cikin shirin had'uwa da sabbin mutane...." Tunda ya soma magana suke dubansa cikeda mamakin yanda ya zak'e sai basu labari yake uwa wanda suka tambaya.... A dai-dai lokacin jirgi ta iso ba tareda sun sami zarafin amsa masa maganganun tasa ba, iyakaci abinda suka fahimta shine gari d'aya suka nufa.... Junaid bai kuma cewa komai ba sai tura wheelchair d'insa da ya shigayi had'i da tura jakan kayansu... Azeeza kuwa tuni ta d'au snacks d'inta ta soma ci tana alamu wa Barr Nasaar da hannu alamun godiya.... Kallonta ya dingayi yana murmushi har yaransa suka k'araso suka rik'e hannayensa, cikin sauri ya isa yanda luggage d'insu yake shima ya shiga janyowa suka nufi jirgin..... *** *Misau* A k'ofar makarantar allonsu ta hangi Lado ya kasa ya tsare hasken farin wata tal ya haske mata d'an duk'uninin fuskarsa..... Jikinta ya d'auki kyarma don duk yanda taga Lado haka takeji, Lado ya zame mata kaman dodo a garin... Sunkuyar da kanta tayi had'i da damk'e allonta sosai ta soma tafiya tamkar wacce zata auka k'asa.... Tana isowa yanda suke shida abokansa bugun k'irjinta ya k'aru ga uwar warin kayan maye da ya gauraye wajen, musamman suka maida wajen dabansu sabida hanyar wucewar Deejo ne.... Aiko kaman jira suke ta k'araso suka mik'e suka nufota, bata ankaraba duk saurin da take sai ganin Lado tayi tsaye k'ik'am a gabanta yana hura hayak'in sigari... K'iris ya rage Deejo bata saki fitsari a wando ba sabida tsoro, ta yunk'ura zata sa gudu tayi d'aya hanyar sai ganin Tanimu tayi a wannan gefen, d'aya gefen ma Muntala ya tsare..... Deejo ta soma kuka tana k'ok'arin duk'awa take fad'in "Dan Allah kuji k'aina kumin rai wllhi makarantar Allo na nufa...." Bud'an bakin Muntala sai cewa yayi "Allah yasa tawada kika nufa gaba d'aya, banza kucaka ke kin tab'a ganin Lado ya kira budurwa d'akinsa a garin nan tak'i zuwa... Ke wacece??" "Kaima ka tsaya kake tambayanta wllhi tunda nayi niyya ko babu kaji sai na d'ana shegiya ku nad'o min ita....." Lado ya fad'i cikeda umarni wa sauran abokan nasa... Deejo ko dukda k'arancin shekarunta ta fahimci cutar da ita suke sonyi, tana ganin Muntala ya kai mata sura ta saita allonta ta sauk'e masa a gefen kunnensa saida yaji jinsa ya d'auke ya saki k'aran azaba.... Bata jira ba tasa gudu, zaninta sai filfilawa kake, 'yan k'afafun kawai kake hangowa.... Lado da Tanimu suka bi bayanta a guje, abinka da wad'anda suke buge sai gani suke tana zille masu, idan wannan yakai mata wawusa sai ta zille ta k'asan k'afarsa har saida ta had'asu gware, ta dumbuzi k'asa ta watsa masu aiko nan suka soma ihu suna lalumen hanya.... Ai Deejo tunda ta samu hanya take gudu bata zarce ko ina ba sai gidan Innah Balki... Innah da Malam na zaune tsakar gida suna sauraren radio abokin hiransu zab'en dare kawai sai ji sukayi an banko k'ofa an shigo... Ai a tamanin suka mik'e suna salati, k'afafuwan Deejo kawai suka hango ta d'age labulen Innah Bilki tana fad'in "Baffah a kule k'yauren zasu shigo...." "Ke Deejo lafiyarki? Su waye zasu shigon....." Innah ta tambaya cikeda tashin hankali, Baffah kuwa cikin sauri ya fice ya nufi wajen gidan ganin su waye suka biyo Deejo amma wayam baiga kowa ba.... *** Wajajen 12am suka iso Abuja, kowa sai watsewa ake amma su Junaid basu san yanda suka nufa ba, Allah yasa Barr da yaransa basu tafi ba don dama Azeeza da yaran sosai suka sha hiransu cikin jirgin, Taheera kam ma jikin Azeeza tayi bacci... Barr baiji d'ar d'in tambayansu unguwar da suka nufa ba, ganin Junaid bai basa k'wakk'waran amsa ba yasa ya nemi alfarman da su wuce gidansa gaba d'aya, da farko Junaid k'in amimcewa yayi saida Azeeza tayita masa magiya don lokaci guda soyayyan Taheera ya shiga zuciyarta... Ba don Junaid yaso ba suka d'unguma gaba d'aya suka nufi gidan Barrister Nasaar **** Belt d'insa ya ida d'aurawa had'i da karkata hularsa ta 'yansanda ya zauna cif akansa kafin ya feshe jikinsa da turaruka masu k'amshi... Sai faman binsa da kallo take daga yanda take zaune saman gadon k'afafu d'aya bisa d'aya har lokacin cikin kayan baccinta take.... "Sweet kayi kyau....." Ta fad'i tana juya idanu.... Gajeren murmushi yayi kafin ya k'araso ya manna mata peck gefen kumatunta yace "I'm off to work.... Idan bak'uwar taki tazo ki gaisheta...." Ta kuma murmusawa tanai masa wasu salo da yasan k'arshe sai yayi lattin fita, cikin dabara ya zame ya fice ko breakfast baiyi ba, idan da sabo fita babu breakfast yabi jikinsa.... Yana ficewa ta koma gado tayi kwanciyarta... Kwanciyarta da kaman minti ashirin taji doorbell na k'ara..... Saurin mik'ewa tayi tana mamakin har Nadiya ta iso.... Abinka da jik'ekk'iyar 'yar bariki d'an mayanin rigar baccin nata kawai ta yafa ta nufi k'ofan.... Da murmushinta ta hangame k'ofar tana fad'in "Thanks for accepting my invitation in such a short ti....." Had'iye maganar nata tayi ganin wanda ke tsaye gabanta..... Tun daga sama har k'asa yake faman binta da kallo shu'umar murmushi kwance saman fuskar sa.... Tsaki tayi had'i da juyawa cikin gidan tana fad'in "So tell me, what the hell brought you here.... Bance maka ina expecting bak'uwa ba...." "Come on darling, no even good morning kisses sai masifa....." Ya k'arashe yana rik'ota lokaci guda ta fad'o cikin jikinsa.... K'ok'arin turesa take duk yanda yake sumbatan ta tana fad'in "Lamid'o stop all this, and kindly get yourself outta here.... You can't be seen here.... Dan Allah ka tafi kafin Nadiya tazo...." "Oh really darling, korata kike... So tell me mai kike shiryawa akan Nadiya....?" Ya k'arashe yana k'ek'ashe idanu.... Shu'umin murmushi tayi had'i da dafa bayan kujera kana ta soma fad'in "I'll win her trust and then.... Move to the next step, besides no need to rush things...." Murmushi Lamid'o yayi had'i da shafa sumarsa data sha low-cut kana yace "I trust you darling... So tell me, do you need my help....?" Murmushi ta kumayi kana tace "Not really..... Ka gane kawai ka tafi we talk later...." "Haka zan tafi babu komai...." "Ka tafi before I hate you....." Ware hannayensa yayi alamun surrender kana yace "Alright fine, zan tafi.... If you need anything just call or text OK...." Gira kawai ta d'aga masa had'i da binsa da kallo har ya isa k'ofa.... Saida yakai dai-dai k'ofa kafin ya juyo had'i da huro mata kiss saman hannunsa sannan ya fice... Yana ficewa ta ruf'e k'ofar ta fad'a wanka..... *SameenaAleeyou....📚* [12/11, 11:14 AM] ‪+234 810 044 6653‬: *FUSKA UKU*🏮 *04* *©Sameena Aleeyou...✍🏽* Zaune suke itada Ayiya a parlorn suna kallon tashan _Discovery Family_ a DSTV da gani zaka gane Asma'u najin dad'in shirin da ake nunawa, Ayiya kam sai kallonta take tana mamakin ina abin kallo a nan domin kuwa wani bature ake nunawa cikin daji babu kalan abincin da baici, dangin su k'wari da sauransu.... Asma'u na sipping tea d'inta tana d'an k'ek'ata dariya take fad'in "Ayiya look zaici d'anyen snail... Ya Rabb ewww!" Ayiya dai murmushi kawai tayi domin har cikin ranta take jin dad'in taga Nana Asma'u cikin farin ciki... "Ki canza wannan tasha kafin ki kasa cin abinci...." Ta fad'i tana bud'e mata 'yar k'aramar plate d'in dinner set dake ajiye bisa table... Sallaman da suka jiyo daga bakin k'ofa ya sanyasu maida hankulansu can... Murmushin Ayiya ya fad'ad'a domin kuwa sosai take ji da Lamid'o mutum ne da yasan darajan 'yan Adam ba kaman abokinsa Siraj ba.... "A'ah lale-lale da takwaran Sarki, kaine tafe...." Ta k'arashe tana gyara masa kushin... Murmushi fal saman fuskarsa, fuska a duk'e ya k'araso ya durk'usa saman carpet d'in kana ya soma gaida Ayiya... Cikin jin dad'i taketa amsawa yayinda bugun k'irjin Nana A ya k'aru don duk sanda taga Uncle Lamid'o hakan ce ke faruwa da ita, gaba d'aya sai ta kasa ci gaba da cin abincin nata... "Zauna bara na kawo maka karin kummallo ko...." Ayiya tace sanda take k'ok'arin mik'ewa... "A'a Ayiya wllhi da kin barshi na gode, a k'oshe nake daga gida nake ban wuce Company ba nima, na tsaya ne ko zan iske Siraj bai fita ba...." Ya k'arashe yana duba agogon hannunsa daga durk'ushen da yake... "A'a Sarki zaka saka wani abin a cikinsa, yau kuma girkin Ayiyar taka, haba kardai muyi haka, jirani minti biyu kacal..." Bata jira cewarsa ba ta shige cikin d'an sassarfa tana ci gaba da fad'in "Gauro kamanka nasan bakaci komai ba....." Murmushi kawai Lamid'o keyi lokaci guda ya gyara zamansa sosai saman carpet d'in, sai sannan ya kulada Nana A dake faman juya fork da knife cikin plate.. Saida ya murmusa had'i da d'anyin gyaran murya kana yace "Nana ashe kina nan a wajen shine babu ko gaisuwa, toh ni bara na gaisheki good morning..." Tunda ya soma magana ta sinne kanta sosai tana murmushi... A hankali ta d'an saita kanta had'i da ajiye plate d'inta saman k'aton wooden center table dake gabanta kana tace "Kayi hak'uri Uncle Lamid'o dama zan gaisheka, Ina kwana....?" Tayi maganar tamkar wata k'aramar yarinya... "Murmusawa yayi yana studying d'inta kana yace "Gaskiya ki rik'e gaisuwarki saidama na rok'a..." D'an fito da idanu waje tayi kana tace "Laa Uncle Lamido wllhi ba haka bane dan Allah kayi hak'uri..." D'an murmusawa yayi kana yace "Toh shikenan na hak'ura.... Da fatan kina lafiya...." Fuska cikeda murmushi take jinjina masa kana tace "Lafiya lou, ya aiki...." Ya amsa mata da lafiya angode Allah sannan ya d'aurada "Ya batun bud'e foundation d'in naki....?" Saida ta d'an muskuta don idan ta jima a zaune k'afarta nayi mata d'an tsami kana tace "Ana kai Uncle.... Jiya munyi magana da Uncle Siraj yace akwai wani business trip da zaiyi cikin 'yan kwanakin nan so da zaran ya dawo za'ayi bikin bud'ewa...." Lamid'o ya murmusa kana yace "Da kyau.... Da fatan dai za'a gayyacemu....".. Saida ta d'an dubesa kafin tayi murmushi mai bayyan hak'wara wanda ya sanya kamaninta da 'yar uwarta Nana H ya kuma fitowa sosai kana tace "Kai Uncle ai kune organizers ma saidai ku gayyata...." Ya kuma murmusawa yana binta da kallo kana yace "Toh shikenan naji dad'in wannan karamci da aka bani.... Allah ya sanya alkhairi ma cibiyan...." Kai a k'asa ta amsa da "Ameen...." Dai-dai lokacin Ayiya ta k'araso wajen hannunta d'auke da tray.... Cikin sauri Lamid'o ya mik'e ya amshe tray d'in yana fad'in "Haba Ayiyarmu ai da kirata kawai kikayi na d'auka...." Ayiya na murmushi take fad'in "Kai haba Sarki kar ka damu kasan shi gauro lallab'asa ake....." Sosa k'eya ya soma yana murmushi don yasan Ayiya babu b'oyo abindake cikin ranta take fad'i "Ayiyarmu na dai kusan kawo maki ita insha Allah..." Ya fad'i sanda yake bud'e plate d'in... "Kai tafi can sai an laluma aji wayam ko budurwar bakada ita..." Ta basa amsa sanda take k'ok'arin had'a masa ruwan shayi.... Sam bata son zancen Ayiya da Lamid'o domin jinta take wani iri haka nan.... K'ok'arin mik'ewa ta soma tana fad'in "Ayiya I'll be upstairs .... Uncle Lamid'o sai anjima..." Kallo ya bita dashi yanda take dafa kujera kana yace "Okay Nana A.. Ki kula da kanki...." Bata sami zarafin amsa sa ba sabida wani irin bugu da zuciyarta tayi jin kalamansa na k'arshe, mai yake nufi ta kula da kanta, kenan ya damu da ita...? Batasan yanda zata samo amsar wannan tambaya tata ba, tana cikin tunanin taji hannun Ayiya na taimaka mata, A dai-dai stirs suka had'u da Ammah da Uncle Siraj suna sauk'owa.... *** *Tambuwal* Yanda tayi d'aurin kallabin gefen fuskarta ga chewing gum da take faman taunawa uwa uba ga hudin hanci na kunne kuwa kusan huji hurhud'u ne, a ido zakayi tunani kilakice ta k'arshe amma duk d'an iskan da ya nemi tab'a mata mutunci ubansa takeci ta kwana lafiya, yawan kwalliya da takeyi yasa kyaunta ya kuma fitowa sosai samari da manyan mutane da dama sukan kawo mata k'ok'on baransu, amma fa bata isa tayi fira da saurayi ba sai a b'oye domin Daddanta ba bari zatayi ba... Mairo kukeji d'iyar Dadda mai dambe da k'arti.... Yauma mayafinta a kafad'a d'aurin kallabin a sama harda d'amaranta tasha ko a jikinta d'aurin zanin kuwa da kad'an ya d'an wuce k'anjinta harda su sark'an k'afa yau ta saka, Zulai na gefenta tana take mata baya... Duk yanda suka wuce sai kaji an ambacesu... Mairo ko kan nan a sama take tafiya tana taunar chewing gum har suka iso k'ofar makarantar Malam Balarabe.... Yauma kaman kullum ya kasa ya tsare a k'ofar makarantar tasa sai muzurai yake idanunsa bisa kwalta... Su Mairo suna isowa Malam yayi gyaran murya ya soma tsine ma karuwai yana la'anta, yana fad'in siffofin shigar da Mairo tayi.... Mairo ta janyo Zulai ta mata rad'a a kunne Zulai ta Shek'e da dariya tace "Hakan za'ayi...." Zulai ta cire d'ankwalinta tayi wurgi dashi had'i da barbaza suma tamkar mai tab'in hankali ta fad'a ajin islamiyan Malam Balarabe tana tsalle.... Ai a d'ari yara suka soma arcewa wasu ta window wasu ta osin Malam Balarabe... Malam yayi kan yara yana "Subhanallah... Kai ku dawo, ku tsaya nace...." Inaa ai babu yaro ko guda da ya tsaya.... Malam bai ankara ba saiji yayi an dank'wafo 'yar hularsa tashi ka faye naci.... Malam ya yar da karan hannunsa yana "Subhanallah a kawo d'auki...." Ai kafin ya ankare Mairo ta danna kansa cikin ajin yaran Zulai ta saka sakata ta rufe.... Malam ya gansa a hannun mata, Mairo ta tsaya cak gabansa rik'eda dorinar da yake dukan d'alibai... Jiki na karkarwa Malam Balarabe yake fad'in "Wa'azi nake Mairoruwa wllhi ban kama suna ba, kumin rai....." "Mairo ta kuma gyara tsayuwa kana tace "Haka ake wa'azin a gidan uwarka.... Kullum kana bisa kwalta idanunka kan mata ka bar aikin da iyayen yara suka biyaka kayi kana yin wanda ba'a aikeka ba koh... A gidan uwar wa kaga muna karuwancin? Ko kuma ka tab'a ganinmu cikin babbar mota a layin nan... Gacan wad'anda suke saka rigar musulunci suna aikata bad'alansu a gansu sun fito daga gida da shiga ta kamala ashe ciki panko ne babu sitira baka bisu ka la'ancesu ba sai mu koh....? Toh yau la'antar da kake mana zata koma kanka ubanka zakaci gobe zaka koyi yanda ake nasiha da wa'azin, kasan baka biyo hanyar data kamata ba...." Malam tun na magiya har ya koma fad'in "Wllhi na tuba, Mairo ki rufa min asiri Malami ne ni.... Wayyo wllhi na bar sa ido har abada.... Kuyi hak'uri dan Allah.... Na yarda ban biyo hanya mai kyau ba, wllhi wllhi zan gyara halina, kumin rai kada ku dakeni dan Allah..." Yanda yake magiya har yaso basu dariya.... Zulai tace "Yo ba dashi kake dukan d'iyoyin jama'a ba, tsoro na me kuma zakaji...." "Wllhi na tuba....." Ya kuma fad'i yana duk'e gabansu sai faman tattamke hular hannunsa yake.... Zulai ta bud'e masa k'ofa tace "Maza ka fita a guje....." Ai kaman jira yake suna bud'e k'ofar burut ya fice a guje ko waigowa bayayi... Mai zasuyi banda dariya sun san har abada sunyi maganin sa idon Malam Balarabe... *** Barr Nasaar ya kuma kai dubansa ga Azeeza wacce keta faman shirya Taheera cikin uniform d'inta don yau Daddy ya huta tunda ga Aunty nan ta samu.... Sauk'e ajiyan zuciya yayi kafin ya maido da dubansa ga Junaid wanda ke rik'eda mug na tea tururi na tashi ciki, daga yanda suke tsaye cikin balcony d'in ya k'urawa garin Abuja idanu motoci da mutane sai safa da marwa suke, sai abinda ya k'aru bayan shekaru kusan hud'u da ya bar garin ba tareda ya kuma lek'owa ba.... Komai ya shiga dawowa kwanyarsa daki-daki.... Muryarta ya shiga yawo a dodon kunnuwarsa sanda take sanar dashi an tilasta mata auren waninsa.... Ya shiga tuna sanda yaji k'aran bindiga alamun an harbeta, sautin k'aranta na k'arshe bai daina yawo cikin kunnuwarsa ba..... Ya tuna lokacin da ya bud'e idanunsa ya tarar k'afafunsa sun zama tarihi A DUNIYAR SA..... A hankali ya lumshe idanunsa zuciyarsa da kwanyarsa na barazanar tarwatsewa.... Wani k'ara ya saki had'i da jifa da Mug d'in dake hannunsa...... Cikin sauri Barr ya tura k'ofar balcony d'in don baiso yaran su fahimci abinda ke faruwa... Mamaki bai gama cikasa ba saida yaji muryar Junaid cikin kuka yana fad'in they killed her.... Those three killed her.... Wllhi bazan huta ba sai na d'aid'aitasu gaba d'aya, sai na gansu a situation d'in da nake a yanzu.... Wllhi duk sai sun d'and'ana...." Ya k'arashe jijiyar goshinsa da take koriyar shar tana kuma fitowa.... Jin k'aran horn d'in school bus d'insu Hammad alamun ta iso yasa Barr saurin fitowa nan kuwa ya tarar Azeeza tana ratayawa yaran school bags d'insu had'i da lunch packs d'insu.... Da gudu suka k'araso suka rungumesa sunai masa waving.. Saida ya bisu da sunba had'i da addu'a kafin suka fice suna waving new Aunt d'insu Azeeza... Har suka fice Azeeza murmushi take yayinda Barr ke faman binta da kallo... Jikinta ne ya bata ana kallonta, aiko tana d'ago kai suka had'a idanu.... D'an sunne kanta tayi kana tace "Am... Am ina Yaya na....?" Murmushi yayi yana jinjina yarintarta kana yace "Muna d'an magana dashi.... Idan bazaki damu ba ki k'arasa kitchen kiyi breakfast kafin mu gama koh...." Jinjina masa kai tayi kana ta nufi kitchen d'in tana wasa da 'yan yatsunta... Har ta kai k'ofa ta jiyo muryarsa yana fad'in "Aunty Zee...." ta juyo tana dubansa cikeda mamaki ashe har yaji yanda Taheera ke kiranta... Murmushi ya sakar mata kana yace "Thank you...." Bata iya amsa sa ba sai sa kai da tayi ta shige kitchen d'in murmushi saman fuskarta.... *** Nana H ta kuma duban Nadiya a karo na biyu kana ta d'an sauk'e ajiyan zuciya tace "Nadiya ki sani jinki nake tamkar 'yar uwa ta jini a gareni, kuma na yarda dake hundred percent, nasan idan kinga abinda zai cutar dani bazaki bari na auka masa ba. Shin ke kin yarda dani kin yarda bazan cutar dake ba...?" A hankali Nadiya ta jinjina kanta kana tace "Nana Hafsat wllhi na yarda dake d'ari bisa d'ari kuma nasan bazaki cutar dani ba..." Nana H ta murmusa kana tace "Alhamdulillah da kika yarda dani..... Kuma insha Allah zaki sameni da rik'on amana...." Nadiya ta murmusa cikeda jin dad'i.... Nana H ta kuma muskutawa kana tace "Nadiya nasan baku jima da dawowa garin nan ba, kuma nasan bakuyi k'wakk'waran bincike kan Siraj Laushi ba, koda shike koda kunyi bincike Uncle Siraj nada kyawawan d'abi'a tsakaninsa da Al'umma... Saidai abu guda tak da nake ji maki tsoro kuma mutane basa fad'i sabida gani da ake he's rich, handsome and famous.... and above all d'an babban gida.." Nadiya ta kuma gyara zama had'i da ajiye fork d'in dake hannunta cikin plate tanai ma Nana H kallon ban fahimceki ba... Nana H ta murmusa had'i da kuma lank'wasa k'afafu kana tace "Uncle Siraj Uncle d'ina ne wanda nafi k'auna fiyeda kowa a family na harma da 'yar uwata da muka zauna mahaifa guda..... Nadiya shin kinsan cewa duk macen data rab'i Uncle Siraj mutuwa take? Shin kinsan adadin matan da suka rasa rayuwansu ta dalilin soyayya da Uncle Siraj....? Kina so ki zama next victim.... Do you want to die at your young age....?" Dukan tara-tara kawai k'irjin Nadiya keyi tana kallon Nana H cikeda tsoro da mamaki... Babu alamun wasa a fuskarta taci gaba da fad'in "Nasan zakiji tsoro da mamaki toh ki sani wannan itace iyakacin gaskiyar, har yau babu wanda yasan dalilin da yasa 'yanmatan da Uncle ke nema suke mutuwa, na tabbata badon yanada dukiya ba da tunin an kullesa ko kuma an fatattakesa daga garin nan.... Amma idan baki yarda dani ba kina iya tambayan one of his friends mijina Ahidjo ko kuma Lamid'o da suke aiki company guda...." Tana kaiwa aya ta d'au coffee mug d'inta tana sipping lokaci guda take karantar Nadiya da ta koma tamkar mutum mutumi.... *SameenaAleeyou...📚* [12/12, 6:45 PM] ‪+234 810 044 6653‬: *FUSKA UKU*🏮 *05* *©Sameena Aleeyou....✍🏽* A hankali Barr ya durk'usa gaban wheelchair d'in Junaid yana dubansa cikeda tsananin tausayi, yana gani cikin idanunsa tsananin zalunci da aka masa, yasha gamuwa da masu case shigen na Junaid dukda baiji cikekken tarihinsa ba, amma tabbas yasan anyi masa zalunci mafi muni A DUNIYAR SA.... "Hannu yakai ya dafe na Junaid dake zube saman cinyoyinsa... Lokaci guda Junaid ya d'ago rinannun idanunsa yana duban Barr Nasaar..... Barr yaci gaba da fad'in "Junaid let it out.. Kayi kuka domin zai rage maka zogi da rad'ad'i..." Junaid ya murmusa wacce tafi kama da ta takaici kana yace "Barr yau shekaru hud'u kenan ina rayuwa cikin k'unci da burin d'aukan fansa, kuma banzo nan ba saida na shafe shekaru biyu ina karantar duk wani motsi nasu...." Shiru yayi ba tareda ya ci gaba da maganar ba.... Barr ya gyara tsugunonsa had'i da yima Junaid k'uri kana yace "Junaid su waye wad'annan mutane, sannan wacece suka kashe and meye dalilin kasancewarka saman wheelchair....?" Ya k'arashe fuskarsa cikeda alamun tambaya... Sararin samaniya Junaid ya k'urama idanu kaman bazai kuma cewa komai ba domin har Barr yacire ran cewa Junaid bazai amsa masa tambayoyinsa ba.... A hankali ya saka hannunsa bayan kekensa ta d'an k'asa kad'an ya ciro wata 'yar kati kana ya shiga warwarewa.... Barr dai k'uri ya masa yana kallon ikon Allah har ya ida warware katin dake hannunsa sai sannan Barr ya lura cewa hoto ne a hannun Junaid wanda aka duk'unk'une waje guda.... A fuskar Barr ya manna hoton wanda da gani jikin news paper aka cire.... "Kasan wad'annan FUSKOKIN...?" Ya tambayi Barr sanda yake kuma ware hoton tarr idanun Barr... Da mamaki Barr ya kuma gyara tsugunonsa yana kuma kallon hoton wanda da gani jikin news paper aka cire, k'irjinsa naci gaba da bugu.... Tabbas yasan mutanen dake cikin hoton kuma yasan exact ranan da aka d'auki hoton.... Hoton Boss d'insa ne da aminansa, lokaci guda yaji bakinsa ya masa nauyi ya kasa furta koda kalma guda..... Ganin yanayinsa yasa Junaid kafesa sosai da idanu kana ya sauk'o da fuskarsa dab da na Barr yace "Ka sansu ne.....?" Kallonsa kawai Barr keyi kafin yace "Kana nufin wad'annan sune FUSKA UKU da kake shirin d'aukan Fansa akansu....?" Shiru Junaid yayi yana nazarinsa kana yace "Ka amsa min tambayata first.. Ka sansu ne.....?" A hankali ya shiga jinjina kai k'irjinsa naci gaba da bugu..... "K'warai na sansu sannan na san ranar da aka d'auki hoton,.... The photo was taken a ranar aurensa sa'ilin da 'yan jarida suka masa chaa domin jin ta bakinsa da aminansa irin farin cikin da suke ciki....." Shiru yayi ya kasa ci gaba da magana yayinda k'irjin Junaid taci gaba da tafarfasa.... Hannu yasa ya damk'o kwalan Barrister yana mai ci gaba da wani irin huci yake fad'in "Tell me everything.... I mean every.....thing u know about 'em......" Barr ya d'ago yana duban Junaid yanda fatarsa ta koma ja gaba d'aya.... A hankali yake furta "Let me go....." "No sai ka gaya min komai ko na fara daga kanka na murmuk'usheka a nan....." Junaid ya basa amsa yana kuma shak'e masa wuya.... "Ka sake min wuya sai na sami damar sanar dakai komai...." Cewar Barr dayaji damk'a sosai.... A hankali Junaid ya soma sakar masa wuya yana watsa masa wani irin mugun kallo had'i da huci Saida Barr ya koma ya zauna gijif had'i da zubewa jikin garu yana kuma sosa wuyarsa kafin ya d'ago yana duban Junaid da babu alamun rahama a fuskarsa.... A hankali ya soma fad'in "Siraj..... Ahidjo.... Lamid'o....." Ya kuma duban Junaid dake faman ci gaba da tururi lokaci guda Junaid ya jinjina kai kana yace "The three Bastards... Tell me. ... who are you to them....?" Barr ya jinjina kai yana duban Junaid kana ya soma fad'in "Ni d'aya ne daga cikin Attorneys na Laushi Group, Companyn marigayi mahaifin Siraj wanda a yanzu haka Siraj yake running..... Kaji alak'ata dasu, sannan naji mamaki matuk'a da suka kasance sanadin K'uncinka sabida a iya sani na sunada alak'a mai kyau tsakaninsu da mutane...." Murmushi Junaid yayi sabida har cikin ransa yaji dad'in samun wanda zaiyi linking d'insa da three devils d'innan cikin ruwan sanyi kafin ya turo kekensa ya k'araso dab da Barr yace "Haka suke a Fuska, amma a bad'ini sunfi kumurcin maciji guba... A yau zan sanar dakai da su waye kake aiki, da wasu irin azzalumai ka aminta har kake aiki k'ark'ashinsu...." Barr ya kuma gyara zamansa dirshan a k'asa yana duban Junaid da tuni ya d'aga kai sama yana kallon sararin samaniya dai-dai sanda ya soma fad'in..... **** *Misau* Kasa tura k'yauren tayi sabida wani irin k'ugi da cikinta keyi, ba ta yunwa bace saidai koh ta tsoro domin yau karin kummalo maiji da lafiya Innah Balki ta bata.... Tsayuwa tayi tana kuma tsuru-tsuru da idanu tana tuna yau shikenan kashinta ya bushe batasan yanda zasu kwashe da Iya Gaje ba tasan yau rai kad'an zata rage mata..... "Wayyo Allah na... Wayyo Allah ka ceceni kasa kar Iya ta jibgeni...." Tayi addu'ar a hankali idanunta na k'ok'arin ciko k'walla.... Har zata shiga gidan taja burki ta tsaya jin yanda Gaje take salle mahaifinta uwa ta sami yaronta, dama hakan take masa bashida fad'i a gidansa sai abinda Iya Gaje tace.... "Deejo dani take wasan nan, yau zata sanar dani gidan uwar wa taje ta kwana, shegiyar yarinya hatsabibiya ta iya bajewa d'akin saurayi tayi kwana amma batasan ta kawo min sisin kwabo ba sai anyi magana tace ita saliha batasan zancen ba koh....? Kai kuma sullutu gaula da anyi magana sai kace nice zan lalatata koh, toh yanzu sai ka sanar dani a gidan uwar na lalata maka d'iya....?" Ta k'arashe tana nuni da ludayi saman fuskar sa.... Kaman daga sama suka jiyo ana bugun k'yauren gidan, ko izinin shigowa ba'a basu ba suka tokari k'ofar suka shigo... Ba kowa bane illa Lado da muk'arrabansa... Yana hura taban wiwi yake fad'iwasu Muntala.. Ku shiga lungu da sak'o na gidan ku fito min da ita....." Jikin Gaje ya d'auki kyarma ta nufi Lado tana fad'in "Lado mai asharalle wai lafiya... Ina Dijon ba'a wajenka ta kwana bane...." Marin da Lado ya sauk'e mata ya sanyata had'iye kalamanta tana kururuwa.... Lado yaci gaba da fad'in "Ke har kin isa kici kud'ina a dad'in rai, saida mukayi dake kan cewa na jirata hanyar islamiyarsu ashe kinsan 'yar taki 'yar akuya ce baki bata irin tarbiyar da ya kamata ki bata ba, ga abokina nan Tanimu bayansa sai an masa d'auri sabida allon makarantar ta ta dinga rabza masa yanzu haka gashi nan d'ingishi yake, bata tsaya a nan ba ta dinga lailayamu cikin garin nan har saida ta cika mana yashin k'ofar kurmi cikin idanu muka kuma nemeta muka rasa kaman aljana ta b'ace... Toh wllhi kinji na rantse ko ki nemota ko na fanshe kud'ina akanki...." Lado ya k'arashe yana k'ok'arin cazgo kallabinta... A d'ari Gaje tayi bayan Malam Ard'o mahaifin Deejo tana kururuwa take fad'in "Malam ka agajeni kada su min fyad'e... Malam zasu tona mana asiri.... Wayyo Deejo kin cuceni babu abinda zai hanani yankaki cikin gidan nan....." Tsam ta d'ale bayan Malam Ard'o dukda ta fisa a tsaye da kuma jiki sai kururwa take.... Dai-dai lokacin Malam Sada da mai d'akinsa Innah Balki suka shigo had'i da wasu 'yan unguwa Deejo kuwa na mak'ale da Innah Balki.... Mamaki ya cika mutane jin abinda Gaje tayi akan marainiyar 'yar mijinta Deejo... Lallai duniya abin tsoro, gashi ta shanye mijin nata gaba d'aya bai iya um balle um-um.... Innah Balki kam batasan sanda k'walla suka shiga zarya a idanunta ba sam batayi zaton rashin imanin Gaje yakai nan ba, Malam Sanda kuwa sai faman girgiza kai yake cikeda mamakin yanda wasu mutanen basu san girman amanan d'a a wajensu ba.... Tabbas barin Deejo hannun wannan azzalumar mata babban had'ari ne gwara yasan yanda zaiyi ko gaban Mai gari suje idan abu ya gagara su dangana gaban sarki a canzawa Deejo uwar rik'o koda wajen dangin mahaifiyarta ne a maidata tunda yasan bazata rasa ba.... Da k'yar aka samu aka fatattaki su Lado a gidan, Gaje ta baje a k'asa kallabi a hannu tana maida numfashi, tabbas yau taga tashin hankali.... Innah Balki ta girgiza kai cikeda takaici kana tace "Toh Gaje shidai kukan kurciya jawabi ne amma fah mai hankali ne ke fahimta, kuma ki sani Deejo bata kwana d'akin ko wani gardi ba sai d'akina, gashi k'ulleliyar da kike shirin yi mata ya tasamma juyewa kanki, toh wllhi kiji tsoron Allah, dan ke Allah bai baki ba bawai ya k'iki bane sannan fad'owar Deejo hannunki alamun Allah ya baki kenan koda ba ke kika haifa ba, shin godiyar da zakiyiwa mahallicinki kenan.... Ki sake tunani Gaje ki kuma gyara halayanki tun kafin lokaci ya k'ure maki... Kuma bazan gushe ba ina sanar dake shidai d'a na kowa ne ba'a musguna masa sabida son zuciya bakisan waye zaki mora ba nan gaba, bakisan mai Allah ya ajiye tattareda wannan 'yar marainiyar Allahn ba...." Tunda ta fara magana Gaje ke watsa mata mugun kallo.... Mik'ewa tayi had'ida shan d'amara da kallabinta kana tace "Toh kanwa uwar gami... Sai ki dake ni kawai nasan kin haifeni, banda felek'e kin wani sakani gaba uwa 'yarki kina silleni sabida makirci da munafunci irin taki... Toh sai ki gaya min idan kina kawo kwabo cikin kud'in tufatar da Deejo koko ci da ita.... Wllhi wllhi kinji na rantse ki fita daga hidiman gidana...." Ta k'arashe tana finciko hannun Deejo take fad'in "Saketa tinda ba 'yarki bace, yo ke wa ya kaiki asara kin haifawa bariki tuk'ek'en saurayi... Ahayyye abin kunya na tattare dake wllhi gwamma ni dama ban haifa ba ke kuwa kin haifa wa karuwai ya tafi ya barki...." Ihun da Deejo ta saki tana k'ok'arin k'wace hannunta daga rik'on da Gaje tai mata ya sanya Gaje dasa aya tana kuma janyo Deejo take fad'in "Nan ne gidan ubanki dan uwarki babu yanda zakije, nan ne dolenki...." Deejo ihu take tana tsalle take fad'in "Nidai wllhi gidan Innah zan koma, ni wllhi bana son nan gidan...." Gwab'e mata baki Gaje tayi tana fad'in "Uwarkice baki so bamu ba shegiya annoba...." Innah Balki ta yunk'ura zata janyo Deejo Malam Sada ya rik'eta had'i da girgiza mata kai... "Malam kagafa abinda take mata... Malam wllhi ina son Deejo...." Innah ta k'arashe cikin kuka... Malam Sanda durk'usawa yayi gaban Malam Ard'o kana ya soma fad'in "Malam Ard'o zan rok'i alfarmanka guda d'aya.... Dan Allah kayimin ita..." Malam Ard'o da tuni k'walla sun gama ciko idanunsa kallon Malam Sanda kawai yayi had'i da jinjina masa kai.... Malam Sanda ya d'an sami k'warin gwiwa kana yace "Dan Allah ka min izini na tafi da Deejo gidana, ba ina nufin ka bani ita ba, a'a ina nufin rik'onta ya dawo hannu na da iyalina..." Ai bai kai aya ba Gaje ta malmalo ashariya ta watsa cikin azama ta hankad'a Deejo d'aki wacce ke faman ihu da bori.... Gaje bata fasa fad'in "Toh tsinannu munafukai annamimai baza'a baku ba kuce neman 'ya'ya kuke kota halin k'ak'a toh kace a baka auren Deejon mana kaga tinda da jini a jikinta zata haifo maka abinda matarka ta kasa baka... Kadai ga yarinya mai jini a jika kana so a baka ka dinga bin dare ko... Toh baza'a bayar....." Bata kai aya ba Innah dake faman huci ta d'aga hannu zata kwad'a mata mari Baffah ya rik'e hannun cikin sauri.... Tabbas ya yarda yanda kunya yabi toh fah Gaje bata bisa ba, dole abin abun a lallama.... "Ahayye da ka barta ta mareni yau datasan ta d'abo Gaje mai jigidan masifa da bala'i... Ku fice mana a gida kafin ranku gaba d'aya ya b'aci...." Ta k'arashe tana hankad'e Innah Balki dake kuka shar-shar don tana jiyo sautin kukan Deejo tana fad'in "Innah dan Allah kar ki tafi ki barni... Baffah dan Allah ku d'aukeni daga gidan nan.. Innah ta dan Allah ki d'aukeni...." Cikin sauri Malam Sanda da zauciyarsa ta karye gaba d'aya ya janyo matarsa suka fice daga gidan.... Suna jiyo Gaje yanda taci gaba da ashariya tana surfa masifa wa mijinta.... Har suka isa gida Innah bata daina kuka ba tana fad'in "Malam yanzu haka zamu barta, yanzu babu abinda zamuyi.. Malam kace min wani abu dan Allah...." Ta k'arashe cikin kuka sosai... Baffah ya sauk'e ajiyan zuciya kana yace "Balkisu kiyi hak'uri insha Allah zamu kub'utar da Deejo daga makircin kishiyar uwarta bi iznillahi, kuma babu abinda zai cutar da ita, ki bani zuwa d'an wani lokaci...." Jinjina masa kai kurum tayi hawaye naci gaba da ambaliya a fuskarta.... *** Junaid yaci gaba da fad'in "Kamar yanda na fad'a maka asalinmu 'yan k'asar Cameroon ne, mahaifanmu gaba d'ayansu 'yan asalin k'asar Cameroon ne birnin Yawundi.... Iyayenmu mu biyu suka haifa tak daga ni sai k'anwata Azeeza, a lokacin da muka dawo k'asar Nigeria inada kimanin shekaru 8 a lokacin Azeeza bata wuce shekara d'aya tak ba, kaga akwai ratan kusan shekaru bakwai tsakaninmu.... Lokacin da muka dawo nan k'asar Nigeria mahaifina sai ya samu aiki da wata k'aramar Company a nan birnin Abuja, ya fara aiki gadan-gadan babu kama k'afan yaro... Abinka da k'aramin ma'aikaci wanda kuma tsananin matsi yasa ya baro k'asarsa ta ainihi sai mukaji rayuwar ta mana dad'i, dai-dai gwargwado munajin dad'i muna samun duk abinda mukeso wanda baifi k'arfin mahaifinmu ba...." Sauk'e ajiyan zuciya yayi had'i da sakin murmushi sabida tunowa da yayi da mahaifansa kana yaci gaba da fad'in "A companyn da mahaifina yake aiki, shi mutumin wanda mahaifina ke aiki a k'ark'ashinsa ya kasance yanada wata d'iya ZEENATU... Zeenatu zan girme mata da shekara biyu zuwa uku, toh a lokacin makaranta d'aya mahaifinta ya sakamu, komai tare yake mana, Shak'uwa mai tsanani ya shiga tsakanina da Zeenatu wanda ta kasance ko dawowa mukayi daga makaranta toh idan banje gidansu ba ita zatzo namu...." Murmushinsa ya k'aru wanda har takai ya kasa ci gaba da baiwa Barr labari... Barr kuwa ya k'agu yaji ci gaban labarin... "Umhum ina jinka mai ya sanyaka dariya haka....?" Junaid ya kuma murmusawa kumatunsa suka lotse kana yaci gaba da fad'in "Kawai na tuna idan Momma mahaifiyata ta had'amu abinci plate guda ne toh sai anyi fad'a kafin a ida cin abincin, kuma da zaran anyi fad'an toh za'a shirya bayan an gama cin abincin... Barr na k'are maka nida Zeenatu rakiyar kura muke ma junanmu tamkar bazamu rabu ba... A haka rayuwa taci gaba da tafiya mana, har zuwa lokacin dasu Zeenatu suka bar inguwarmu amma bata daina zuwa yanda nake ba nima kuma ban daina zuwa yanda take ba, aminci tsakanin iyayenmu ya k'ara k'ulluwa, har takaiga sun k'ulla alk'awarin aure a tsakanin mu dukda cewa mu a lokacin bamu fahimci soyayya muke ba, a lokacin shekaruna bazasu wuce sha tara zuwa ashirin ba, Azeeza kuwa bata wuce Sha biyu ba.." Shiru ya d'anyi idanunsa suka cika da ruwa.... A hankali yaci gaba da fad'in "Wata rana mahaifanmu sun tafi ziyara k'asar Cameroon suka barmu ni da k'anwata hannun Mai taimakawa mahaifiyata da aikace-aikace na cikin gida mai suna Umma Marie... Iyayenmu sunso tafiya damu saidai lokacin muna tsaka da makaranta dagani har k'anwata....." Hawaye suka soma zubowa daga idanunsa sanda yaci gaba da fad'in "Dawowar da basuyiba ta har abada, kallo na k'arshe da muka masu sanda muka rakasu airport.... A hanyarsu ta dawowa Nigeria sukayi had'arin jirgin sama wanda ko d'aya a cikinsu babu wanda ya rayu......" Kukan Junaid ya tsananta... Lokaci guda Barr yasa hannu yana k'ok'arin maida nasa k'wallan... Bai tak'urawa Junaid yaci gaba da basa labari ba har saida Junaid d'in yayi kuka mai isarsa had'i da addu'o'i wa mahaifansa Barr na amsawa da ameen kafin ya daidaita kansa yaci gaba da fad'in "Mun rasa mahaifanmu a wannnan lokacin, daga ni har Azeeza rasa mai k'arfin zuciya akayi cikinmu har saida Baba Datti mahaifin Zeenatu yayita nusar dani nine babba dole na koyi hak'uri ko don k'anwata Azeeza, haka Umma Marie wacce ta zamto tamkar uwa a garemu taci gaba da bamu baki.... A haka har abin ya soma barin jikinmu kullum Zeenatu tana gidanmu tana d'ebe mana kewa.... A lokacin ina jami'a Baba Datti ya buk'aci na soma aiki da DATTI INVESTMENT Companyn sa tinda yaga kalan k'wazona da himma na, sannan sunyi zama na amana da mahaifina marigayi Alhussain..... A haka na soma aiki da Datti Investment na maye gurbin mahaifina, ina karatuna ina aiki na soyayyarmu da Zeenatu na k'aruwa, kowa yasan muna soyayya I zuwa lokacin..... Wata rana Companyn mu ta soma samin barazanar fad'awa matsalan kariyar arziki wato bankruptcy, a lokacin Zeenat ta soma aiki itama da Comapanyn sai ya zamana mun hutar da Baba Datti nida Zeenat mune akan Compnayn muketa k'ok'arin shawo matsalar da muke k'ok'arin aukawa ciki... Kwatsam ana haka cikin k'ok'arin tallata hannun jari na kampaninmu da mukeyi Zeenatu ta had'u da SIRAJ LAUSHI President na LAUSHI GROUP....... *SameenaAleeyou...📚* [12/13, 5:14 PM] ‪+234 810 044 6653‬: *FUSKA UKU*🏮 *06* *©Sameena Aleeyou...✍🏽* Junaid yaci gaba da fad'in "Siraj....!" Shiru ya d'an biyo baya..... Hannu yasa ya shafe fuskarsa gaba d'aya d'an sauran hawayen duk suka tafi kana yaci gaba da fad'in "Tun lokacin da ya d'aura idanunsa kan Zeenatu ya aukawa soyayyarta.... Bugu d'aya Laushi Group ta amince da had'akar kasuwanci da Datti Investment, nasan zaka iya sanin lokacin tunda kaima kana k'ark'ashin Companyn....?" Ya k'arashe yana duban Barr cikin idanu... A hankali Barr ya girgiza masa kai kana yace "A lokacin ban fara aiki da Laushi Group ba domin lokacin da na soma aiki dasu lokacin auren Siraj ne....." Junaid yayi shiru tamkar mai nazari kana ya gyara zamansa saman wheelchair d'insa... "Baka sanar dani mai ya rabaka da matarka, meyasa kake zaune daga kai sai 'ya'yanka... Shin kaima iftila'i ce ta rayuwa ta auka maka....?" Shiru Barr yayi yana dubansa kafin ya d'an murmusa ya d'an shafi nape d'insa kana yace "Bai kamata ana bada labari a katse a shiga wani ba idan da mai saurarenmu zai shiga rud'ani...." Ya k'arashe murmushi kwance saman fuskar sa..... Junaid d'inma murmusawa yayi yana mai karantar Barr kana yaci gaba da fad'in "Kace wani abu.... A ina na tsaya maka ma?" Tambayar saida yaso baiwa Barr dariya ya kuwa d'an murmusa kana yace "Had'uwar Siraj da Zeenatu..." Junaid ya murmusa yace "Haka kuwa...." Saida ya kuma saita kansa kana yace "Murmushi ba d'abi'ata bace tun bayan rasa farin ciki na sai gashi yau ka sa sai yinta nake a arha... Da ace Umma Marie da Zeeza zasuga fuskata da murmushi da sai sun maka kyauta....." Barr ya kuma murmusawa kana yace "Ni fatata ka dawamma cikin murmushi domin sosai take k'arawa fuskarka annuri da kamala...." Junaid ya shafi k'asunbin sa wanda bai jima da tarawa ba kana yaci gaba da fad'in "Sabo sosai Siraj da Zeenatu sukayi duk a tunaninta sabida kasuwancin da ya had'asu ne sam bata kawo Siraj nada wata nufi na soyayyarta cikin zuciyarsa ba... Wasu lokutan haka kawai zai buk'aci suyi confidential meeting da Zeenat su biyunsu, su fita tare joints parks da sauransu duk akan ana tattauna business ne... A lokacin sai na fara zargin wani abu sam banason keb'ewanta da young tycoon d'in.... Toh sai na fara nuna mata rashin amincewata gashi lokacin Datti Investment ta soma hab'akowa da taimakon Laushi group, a lokacin Zeenat sai ta d'auki abun kishi ne kawai irin nawa, wani sa'in har ta nuna rashin jin dad'inta tunda gashi har mahaifinta na alfahari da ita, you know how business men are... Kasuwancinsu ya fiye masu komai... Ana haka abu ya soma bayyana da gaske dai Siraj soyayyar Zeenatu ne tam cikin zuciyarsa, ni kuma a lokacin sai na soma jin Zeenatu taci amanar soyayyar da nake mata, duk da banso zuciyata ta aminta da zarginta na cin amana amma na kasa... Wasu irin manyan kyauta Siraj yake mata wanda har ita kanta ta soma tsorata da lamarin nasa, koda tazo ta sameni ta sanar dani halin da ake ciki banza na mata, Mahaifiyarta kanta bataso saka Zeenatu da Alhaji Haruna Datti yayi kan hark'ok'in kasuwancinsa ba tinda ita mace ce gashi ita kad'ai Allah ya basu... Shiko Alh Datti ganin kasuwancinsa na hab'aka sai ya mance da komai, sai ya zamana Alh Siraj Laushi bashida wajen hira sai wajen mahaifin Zeenat, wanda shi kansa mahaifin Zeenat gani yake wannan babban nasara ce a gareshi tinda Alh Siraj ya tsallake k'anan Kamfanunuka da dama ya tunk'ari nasa... A haka Siraj ya soma sanar da mahaifin Zeenatu buk'atarsa..." Aya ya d'an saka ya d'ago yana duban Barr kana yaci gaba da fad'in "Kasan meye abin mamakin...?" Nasaar ya girgiza kai alamun a'a bai sani ba... Junaid yaci gaba da fad'in "Mahaifin Zeenat ya amince da buk'atan Siraj wanda bani kawai ba harta mahaifiyar Zeenatu da ita kanta Zeenatun saida muka shiga rud'ani.... Ranar wata alhamis Baba Datti ya kirani har parlornsa yake sanar dani _Junaid kayi hak'uri ka amshi soyayyarka da Zeenat a matsayin k'addarar rayuwarka, sannan ka nemo wata yarinyar ko a ina take ni zan tsaya maka a matsayin mahaifi har ka mallaketa, Junaid na riga na amshi kud'in auren 'yar uwarka Zeenatu nanda wani lokaci kad'an za'ayi auren...._ "A lokacin sumewane kawai banyi ba domin duniyar juyamin ta soma yi.. I was like.... Ta yaya Baba zaimin haka, bayan duk mafarkan da mukashayi wajen gina gidanmu da Zeenatu, tare muka girma tare muka gina rayuwarmu da mafarkanmu da komai da komai, bamusan soyayyar kowa ba sai na junanmu, rana d'aya tak ace na rabu da ita... How could that be possible....? Muryata tana rawa nake fad'in Baba lafiya wani abin nayi.. Baba ko baka aminta da tarbiyata bane... Baba dan Allah kar ka rabani da Zeenatu wllhi bansan yaya rayuwata zata kasance ba... Baba please don't do this na rok'eka... Baba ya kalle ni da idanun tausayi kana ya duk'ar da kansa yana girgizawa ya d'ago ya dubeni da k'yar yace _Junaid I'm sorry, ka yafe min d'ana wllhi banida zab'i kasan akan kasuwancina babu abinda bazanyi ba muddin inada halin yi d'in, rayuwata gaba d'aya nayisa ne cikin k'ok'arin gina kasuwanci na.. Kayi hak'uri Junaid kayi hak'uri d'ana..._ A lokacin bansan sanda na mik'e na soma tafiya hanya na hard'e min ba sai ganin Zeenatu nayi gabana cikin shesshek'ar kuka ta rik'eni tana fad'in _Junaid dan Allah kar ka bar Abbah yayi haka... Junaid dan Allah kace ya aura mana juna, please don't let him do this.... Junaid kar ka bari a aura min wanda banaso, ka manta mafarkanamu da burikanmu.... Junaid ka amsa min mai Abbah yace maka....._ Tamkar mutum mutumi haka Zeenat ke jijjigani ina kallon kyawawan idanunta masu zuban ruwa, kasa ganewa nayi zafin kukanta nakeji kokuwa zafin abinda Baba Datti yamin nakeji.... Ban iya ce mata komai ba sai b'anb'are hannayenta da nayi daga jikina... Ina jiyo sautin kukanta yanda na barta a durk'ushe tana rok'ona na dawo amma ban iya juyawaba sabida tsoron kar na zube a wajen nima..." Shiru yayi idanunsa suka kad'a sukayi jazir yayinda idanun Barr ya kawo ruwa sosai wani irin tausayin Junaid yakeji.... Junaid yaci gaba da fad'in "Da fari Siraj yayi kaman ya janye neman auren Zeenatu sabida sam bata sonsa dukda dukiya da kyau da Allah ya masa, amma abokansa guda biyu sukayita ingizasa don bana mancewa a k'ofar Datti Investment wani rana abokinsa Lamid'o yake fad'in _Yanzu duk dukiyar da ka kashe zai tashi a banza, shikenan kan wani k'aramin talaka saika zuba idanu wa macen da kake k'auna. Haba Siraj kada ka badamu, mai amfanin dukiya da Allah ya maka a d'an k'ank'anin shekarunka, ka taka wanda kake so kayi abinda kaga dama babu wanda ya isa ya had'a nema dakai amma fah idan kabi shawarina...._ Iyaka abinda na iya jiyowa kenan suka shige luxurious cars d'insu suka bar k'ofar kmfanin.... Bayan kaman sati guda da faruwan haka saiji nayi ana d'aura auren Zeenat da Siraj.... Na ga kira bila adadi da sak'onni da layinta ban d'aga ba ban mata reply ba,... A ranar auren kaman bazan d'agaba sai kuma na d'aga kiran cikin tsananin kuka naji muryarta tana magana k'asa-k'asa tana fad'in _Junaid zasu kasheni dan Allah kazo ka cecni ka cireni daga gidan nan... A toilet na kulle kaina amma wllhi ina jiyo muryarsa nemata suke zasu kasheni...._ Hankalina sosai ya tashi na mik'e tsaye ina tambayarta wani gida su waye zasu kasheta?... Cikin kuka da k'ank'an da murya taci gaba da fad'in _Junaid kasheni zasuyi dan Allah kazo kazo yanzun nan zanyi iya k'ok'arina yanda bazasu ganni ba har ka iso....._ Cikin tashin hankali nace ta min texting address cikin k'ank'anin mintuna kuwa adreshin gidan ya bayyana jikin screen d'in wayata... Umma Marie da Zeeza suna parlor suna kallo sai ganina sukayi na fice nida gaba d'aya ko aiki na daina zuwa ba tareda na sanar dasu daliliba amma sai ganina sukayi na fice cikin sauri.... Umma Marie ta mik'e tana fad'in _Junaidu lafiya ina zaka da mangariban nan....?_ Ina ko amsata banyi ba na fice a gigice, ina fita na sami mai babur na d'ale.... Ina isa gidan na fad'a cikin gidan kai tsaye saidai dai-dai sanda na isa na jiyo sautin k'aranta tana ambato sunana tana fad'in nazo na taimaketa.... Da k'arfin gaske na kira sunanta na shiga bud'e k'ofofin Mansion d'in ina neman ta ina take...... Kafin na ankara saijin k'aran harbi nayi tauuuu.... Daga wannan lokacin ban kuma jin ihunta ba.... Jikina ya d'auki rawa na fad'a cikin gidan sosai ina neman ta ina zan ganta..... A k'ofan bathroom d'in dake d'akin tsakiya na hangeta jini na b'ulb'ulowa daga k'irjinta yanda aka d'ana mata harsashi tana mik'o hannu tana yunk'urin yin magana amma ta kasa.... Da rarrafe na k'arasa gabanta cikin sark'ewar murya na shiga jijjigata ina tambayarta waye yayi mata haka, su waye suka mata haka.... A dai-dai lokacin Siraj, Ahidjo da kuma Lamid'o suka shigo a birkice bindiga rik'e hannun d'ansandan cikinsu wato Ahidjo... Cak suka tsaya suna kallonmu yanda na rungumeta ina kuka... Hannu take k'ok'arin d'agawa sama amma ta kasa lokaci guda Zeenatu ta daina motsi.... Na saki k'ara ina kuma k'ank'ameta.... Siraj da k'irjinsa bai daina bugu ba kukan kura yayi yayo kaina yana fad'in mai nayi wa matarsa wllhi shima sai ya kasheni.... Nima d'in damk'o shi nayi ina fad'in mai sukayi ma Zeenatu wllhi sai na kashesu gaba d'aya... Kafin na ankara saiji nayi sun had'u gaba d'aya su duka uku suna dukana kaman zasu aikani lahira, shi d'ansandan da boot d'insa ya dinga takani abokansa suna tayasa... K'afafuwana kuwa dandatsasu suka dinga yi wanda tun ina iya kallonsu har na daina.... K'arshe da sukayi tunanin na mutu suka sa securities d'insu suka kwasheni suka tafi dani can wajen gari suka watsar dani wajen gari, wani mutumi shi ya tsinceni gefen gonarsa bayan sunmin magani na gida har na soma magana sannan ne nake sanar dasu ga daga yanda nake ma'ana gidanmu.... Sosai Umma Marie da Azeeza sukayi kuka babu kaman Azeeza wacce takega tamkar ta kuma rasa wani jigo na rayuwarta... Ban sanar da Azeeza gaskiyar abinda ya faru ba sai Umma Marie wacce bayan na sanar da ita bata barmu garin Abuja ba tsoron daga su san cewa ban mutu ba su biyoni har gida su k'arasani... Tuni Umma Marie ta d'aukemu muka koma can garinsu Yobe cikin garin Damaturu, toh a nan ne aka soma jinyar k'afata har aka min aiki a babban asibitin Damaturu, saidai ba'ayu nasara a aikin ba likitoci sun tabbatar mana akwai jijiyoyi da suka daina aiki a k'afata..... Na wayi gari na bud'e idanu na tsinci kaina gurgu.... A cripple..... Bazan kuma tafiya ba for the rest of my life kaman yanda suka tabbatar mana.... Zan k'are rayuwata saman wannan keke da kake gani......." Sauk'e ajiyan zuciya yayi kana yace "Wannan shine labarin Junaid, wannan shine babban illa da FUSKA UKU sukayiwa rayuwar Junaid..." Ya k'arashe yana duban Barr wanda jikinsa ya gama yin sanyi gaba d'aya da rayuwar Duniya...... Barr ya zaro handkerchief daga suit pocket d'insa ya goge hawayen da yaji suna taruwa cikin idanunsa sabida tsananin tausayin Junaid da rayuwar da suka fuskanta kana yace "Tabbas kaga rayuwa sannan dole kayi tunanin d'aukan fansa, amma kanaga anya sune suka kashe Zeenatu kodai rashin sa'a akayi kuka isa wajen a tare...?" Junaid ya d'ago ya dubesa kana ya girgiza yana mai fad'in "Kai kasan Siraj Laushi ka kuma san duk budurwar da ya nema da sunan aure mutuwa take, a matsayinka na lauya shin ka tab'a tunanin mai yasa matan suke mutuwa? Shin mai yasa babu mahaluk'in da ya tab'a tunk'arar Siraj Laushi...? Sabida yanada k'arfin dukiya, ko kuma meye dalili...? Idanma Siraj Laushi dukiyarsa na tsafi da mata ne toh bazai sha jinin Zeenatu ya zauna lafiya ba, wllhi wllhi jinin Zeenatu sai ya tsaya masa a mak'ogoronsa.... Banzo nan ba saida na shirya...." Barr ya sauk'e ajiyan zuciya kana yace "Kenan shigar da k'ara zakayi... Ko menene shirinka...?" Junaid yayi wata murmushi don sam baiji mamakin tambayoyin da Barr Nasaar ke masa ba tunda yasan fanninsa ne.. "Ka tab'ajin anyi defeating mai dukiya a shari'a a wannan duniyar tamu.... Ko kuwa ka tab'ajin anyi fad'a da hukuma.... Kasan abokinsa d'an sanda ne mai license na harbi... Toh koma ba wannan ba ta ina shaida d'aya tak zaifi shaidu uku.... Ba wahalar da kaina nazo yiba doka nazo d'auka da hannayena Barr dan haka kada ka soma tunanin irin taimakon da zaka min kenan..." Barr yayi shiru yana dubansa, muryar Junaid ya katsesa da fad'in "Naji dad'i da ya kasance kanada babban alak'a da Laushi Group... Taimakon da nake so babba guda d'aya ka soma min shine ka samarwa Azeeza aiki a kamfaninku sannan aikin ya kasance ta zamto Sakatariya ga SIRAJ LAUSHI..... Ba Azeeza dake bakin k'ofa ta gama jiyo komai ba hawaye na faman ambaliya a idanunta harta Barr Nasaar saida k'irjinsa yayi wani bugawa..... **** Ta jima tana zaune saman kujeran tana faman fiffincike cotton wool dake cikin k'aton teddy bear d'in dake hannunta, sam bata zaci Nadiya bazata aminta da buk'atanta ba... Lokaci guda ta matse teddy bear d'in jikin kujera tana masa magana tamkar mai tab'in hankali... "So tell me uncle why? Meyasa sai kayi aure? Meyasa bazaka zauna da family d'inka kawai ba sai ka auro wata... Uncle bakasan rabamu dakai zatayi ba? Bakaga yanda Ahidjo bai damu da nasa family d'inba sai na matarsa,... Uncle haka kaimafa zaka zama idan kayi aure... Haka zata rabamu dakai ka koma sai ita kad'ai da danginta.... Uncle bazan tab'a bari wata ta rabamu ba... Kaji wllhi bazan bari ba..." Ta k'arashe tana duban yanda ta lalata teddy d'in lokaci guda ta rungume teddy d'in tana fad'in "Oh I'm sorry... I'm sorry luv... I didn't mean to hurt you... I'm sorry kaji..." Ta k'arashe tana cuccusa cotton wool d'in cikin rigar teddy d'in.. lokaci guda ta mik'e ta kaisa ma'ajiyansa ta ajiye... Cikin sauri ta zari car keys d'inta daga gidan ta fice.... *** Wani map suke kan kalla suna tattaunawa akai shida abokin nasa suna ganin tsarin da ya kamata a maida kamfanin, k'aran da wayarsa tayi ne ya sanyasa excusing kansa ya fice saida ya sami keb'ebb'en waje kafin ya soma amsa wayar... Daga d'aya b'angaren mutumin yace "Lamid'o wai shin mai ka tsayayi har yanzu, kwana biyu fah bana gane maka..." Lamid'o ya shafi k'eyarsa kana yace "Sir k'ok'arin da nakeyi yanzu kenan insha Allah bazan baka kunya ba, komai zai tafi kaman yanda muka tsara is just a matter of time... Komai ya kusa zuwa k'arshe... I'm sorry sir muna tsaka da meeting zan kiraka in the next 15 minutes... I don't want him to be suspicious ...." Daga d'aya b'angarwn mutumin ya amsa masa kafin ya katse kiran... Saida ya fuzar da iska had'i da shafa kansa kafin ya fito daga elevator d'in ya koma office d'in Siraj.. *SameenaAleeyou📚* [12/13, 9:44 PM] ‪+234 810 044 6653‬: *FUSKA UKU*🏮 *07* *©Sameena Aleeyou...✍🏽* Girgiza kai kurum Barr Nasaar yake kana yace "Amma baka tsoro ka jefa k'anwarka cikin wannan tashin hankali.... Azeeza k'aramar yarinya drag her into this please...." Ya k'arashe tsananin damuwa ya nuna sosai a fuskarsa... Junaid ya matso dabda Nasaar kana yace "Da taimakon Azeeza zan cimma wani b'angare na burina ka gane.... Kar ka damu bazanyi abinda zai cutar da ita ba nasan mai nakeyi...." Barr ya jinjina kai kana yace "Ko baka tsare Azeeza ba wllhi zan tsareta kuma a shirye nake na tayaku d'aukan fansa.... Amma ina labarin mahaifan Zeenat su kuma mai ya faru dasu...?" Junaid ya girgiza kai yana mai fad'in "I don't know ban sani ba... Ban k'arabi takansu ba, FUSKA UKUN nan ne kurum na maida hankalina akansu su nake karantar duk wani motsi nasu tsawon shekaru...." Barr ya kuma jinjina kai yana mai duban agogon hannunsa sai jiyo muryar Junaid yayi yana fad'i "Nasaar na aminta dakai lokaci guda ba kasafai nakeyin hakan ba amma kai bansan dalilin da yasa na aminta da kai cikin k'ankanin lokaci ba.... If there's one thing I hate is betrayal.... Nasaar wllhi wllhi kayi tunanin cin amanata zan zame maka sanadin k'unci na biyu A DUNIYARKA bayan matarka.... Nasaar ka rik'e min amanata..." Ganin yanda jijiyar goshinsa ta fito sosai ya sanya k'irjin Barr bugu, k'ak'aro murmushi yayi kana yace "Kana tareda yardata Junaid bazan ci amanarka ba da yardar Allah...." Junaid ya jinjina masa kai dai-dai lokacin da Azeeza ta shigo hawaye na safara a fuskarta... Kallo take kan faman binsu dashi yayinda Junaid ya soma k'ok'arin saita kansa donyima k'anwar tasa magana... Girgiza masa kai ta soma tana fad'in "Yaya u don't have to explain..... I've heard everything, so that was the reason.... Yaya why? Meyasa... Haba Yaya Junaid shin Fansa ya kamace ka, shin A DUNIYARKA babu hak'uri.... Yaya I can't bazan iya ba... And I'm going back to Damaturu immediately.... Bana cikin burin Fansarka....." Tana kaiwa nan tasa kai zata juya cikin tsananin huci... Saidai kafin takai k'ofa Junaid ya isa ya rik'o hannunta... Juyowa tayi suna kallon juna hawaye na ci gaba da ambaliya a fuskarta.... "Azeeza you must.... You must help me.... Babu komawa da baya sabida na riga na fara....." Tsugunawa tayi suna fuskantar juna su duka biyun.... Kasa magana tayi sai wani sabon kukan da ya b'alle mata... Cikin sauri Junaid ya rungumeta cikin jikinsa shima hawayen na neman ciko idanunsa.... Barr ya bisu da kallo cikeda tausayawa.... **** *Tambuwal* Kaman kullum suna zaune tsakar gidan suna sana'arsu ta sark'an beads itada Zaliha da k'awarsu Hanne yayinda Dadda ke bayi tana wanka da shike hantsi ta sako kai sanyi ya d'anyi sauk'i...Abinka da Dadda tana bayin tana wankan tana 'yan wak'e-wak'en ta.... Tun daga bayin taji ana bugun k'ofar gidan ana k'wantara sallama.... Uwar tsaki taja don tasan yanzu haka bazai wuce masu karb'an sark'an amarya bane gashi su Mairo sun sake kid'an Barmani Mai Choge a tsakar gidan tasan bazasu saurari bugun k'ofarba.... Tsaki taja tana goga soso take fad'in "Wai wayene mai bugun k'ofar nan ne....?" da shike bayin ba wani ratar kirki bane garu ne ya raba tsakaninsa da wajen gidan.... Daga yanda suke tsaye sai jiyo muryoyinsu tayi suna fad'in "Daga ofishin Hisbah ne...." Ai a d'ari Dadda ta wanke sabulun dake idanunta tana fad'in "Na'am... His mene...?" D'ayan ya k'ara cewa "Hizbah..." Cikin sauri ta janyo zaninta saman garu ta d'aura a k'irjinta tana fad'in "Toh lafiya dai koh, ko kunyi zaton nan d'in gidan Magajiya ne...?" "Ko mu shigo ne....?" d'ayan ya kuma tambaya... "Kai gani nan zuwa ku jirani, ina tafe..." Ta k'arashe tana d'aukan kwandon wankarta.... A filin tsakar gidan ta tarar dasu Mairo an sha kallabi a gefen kai jai rangaji da kai ake ana zura beads jikin d'an robar tsark'ar da gani suna jin dad'in sana'ar tasu... Batabi takansu ba sai hijabinta data d'auka saman igiya ta nufi k'ofar gida... Aiko tana bud'ewa taga mutum biyu da Uniform jikinsu da dorinai ga kuma Malam Balarabe a gefensu yana muzurai yana hura hanci.... "Toh lafiya dai ko...?" Ta tambaya tana yarfe sauran ruwan fuskarta... "Hajiya kin gane wannan.? " Guda d'aya ya tambaya yana nuna mata Malam Balarabe da dorinar hannunsa.. Yatsina fuska kurum Dadda tayi kana tace "Yo na ganesa mana, ba yaron nan ba d'an gidan Tale d'an bana sauk'e kawai ya soma malamta ko ba shine ba....?" "Hajiya toh a gidan nan naki munji labarin akwai karuwai kina tara 'yanmata da sunan kina koya masu sana'a ashe kawalci kike., kuma tabbas gashi muna jiyo sautin gurmi daga cikin gidanki na tashi don haka yanzu zamu shiga muyi kame..." "Bantan uba...." Ta furta tana tattaro hijabinta, kafin ta ankara sai gani tayi sun shige gidan Malam Balarabe yana fad'in "Ku dai shiga suna ciki watsatsun amma ku rintse idanu...." A d'ari Dadda ta take masu baya tana ruwan bala'i had'i da tafe hannaye.... Su Mairo kam zumbur suka mik'e ganin maza cikin gidansu rik'e da dorina... Dadda fad'i take "Wata doka ce ta baku dama ku shigo min kan iyalai na 'yan mata... Toh wllhi sai munyi shari'a daku...." Malam Balarabe suna had'a idanu da Mairo yayi bayan jami'in hizbah guda d'aya yana fad'in "Ka gansu nan suna asharalle dama na fad'a maku koda na masu wa'azi mutunci na sukaci harda cewa zasu bugeni...." Jami'in Hizbah ya d'aga dorina yana fad'in " Ya subihanallah.. Ku wuce muje... Muje nace, baku iya komai ba sai bad'ala da cin mutuncin Malamai...." Abinda ya basa mamaki shine babu wanda ya motsa daga Mairo har k'awayenta... Kallo d'aya kurum tayi wa k'awayen suka fahimci mai take nufi.... Kafin su ankare tuni Hanne ta gark'ame k'ofa itako Zulai tuni ta rarumo igiyan guga ganin haka yasa Dadda murmusawa don tasan mai suke shirin yi... Tuni ta yaye hujabinta daga ita sai d'aurin k'irji... 'yan hizbah suka soma rintse idanu suna a'uzubillahi Hajiya kanki d'aya.... Ai mai maganar bai ankara ba sai ji yayi an sharb'osa k'asa... Malam Balarabe na ganin haka ya nufi katanga a d'ari lawurje har tana neman kwancewa ya haye katangar... Ko waigowa bayayi fatansa kurum ya tsira... Tuni Dadda ta zaune d'ayan tana fad'in "Hanne bani muciya a kitchen..." Hanne ta tafi a guje d'auko muciya Mario da Zulai kuwa dorinar 'yan hizban suka amsa suka shiga kewayasu bakajin komai sai ihun k'artai..... Sai suka masu lilis da k'yar suka tsira hannun su Mairo... "Gobe ku sake shiga gidan wasu babu bincike sai an maku fin haka, su saka rigar addini kuna tsiyarku, baku tafi bayan gari kama karuwai ba sai cikin gari tsakiyar unguwa gidan wasu... Gobe ma ku dawo..." Ta k'arashe tana jifa masu dorinar su... Hula a hannu suka tsere suna tsinewa abokinsu Malam Balarabe, da alwashin sai sun kira ogansu na Hisbah wannan cin zarafi da aka masu bazai tafi a banza ba..... *** *Misau* Innah Balki tayi shiru tana duban k'awar tata Larai kana tace "Toh yanzu Larai kinaga naje gidan Malami nace amin kiranye Malam bazaice nayi shirka ba... Anya Larai kinaga babu komai.... Gaskiya ina tsoro nidai a ganina kawai muci gaba da addu'a kuna tayani har Allah yaji k'aina ya karkato da hankalinsa ya dawo gida, nidai duk turasa karatu k'asar Arna da Malam yayi shi ya jawo mana wannan musiba sam Hidjo na bai sami ishesshen karatun addini ba...." Larai ta kuma duban Innah Balki kana tace "Balki nifa taimaka maki nakeda niyyanyi... Idan kuma baki son taimakon kinga tafiyata bariki kuma yanzu d'anki ya soma zama cikinta k'adangarun bariki na lashesa muddin bazakiyi wani hobb'asa ba.... " Ta k'arashe tana yafa mayafinta take fad'in "Ni kinga tafiyata tunda ke 'yar dad'i miji ne komai sai kin sanar dashi baki san ki tashi ki taimaki kanki ba, toh wayema yace maki kiranye shirka ne, addu'a kawai da sadaka Malam zaiyi cikin yardar Allah d'anki ya dawo amma tunda baki son taimakon ni kinga tafiyata...." Cikin sauri Innah Balki ma ta mik'e don A DUNIYARTA babu abinda take muradi tamkar ta sami hankalin d'anta da kulawarsa.... "Larai muje kiyi hak'uri kada ki tafi...." Larai ta kad'a kai tace "Ah toh duniyar nan kowa da kika gani na buk'atar addu'a .. Yanzu Sunusi d'an gidan Iya Dumba da yabi makiyaya da masu farauta yak'i gida ba Malam d'in bane ya masa kiranye ya dawo gida, gashi yanzu yayi aure harda 'ya'yansa, nake baiwa Malam labarinki ya tausaya maki sosai yace zai taimaka shine ke zakice baki so ko...." Cikin sauri Innah Balki ta kuma girgiza kai tana fad'in "A'a wllhi ai nace muje, Ubangiji dai yasa mu dace.... Bara kiga na shiga d'aki na d'auko mayafi....." Ta k'arashe tana shigewa uwar d'akin **** Zaune take saman k'aton gadon nata cikin yalwataccen d'akinta wanda ya k'unshi kayan more rayuwa da dama... Hannunta rik'eda wani k'aton hoto wanda ya k'unshi kusan mutane biyar.... Wad'anda suke daga tsaye Mace ce da kuma namiji wanda basai ance maka mata da miji bane, na zaune saman kujera kuwa 'yan mata ne yara guda uku masu fuskoki iri guda, kamanninsu d'aya tamkar an tsaga kara, a hoton yaran bazasu gaza shekaru biyu zuwa uku ba, kyawawa dasu ko wacce an kame mata sumarta da ribbon kana ganin yaran kasan sunji hutu sun gaji, ba sai ance maka 'yan uku bane ma'ana triplets ne... Har Ayiya ta fito daga bathroom Nana A bata daina murmushi tana shafa hoton ba. A haka Ayiya ta k'araso ta sameta itama murmishi kwance saman fuskarta.... Nana A ta d'ago tana duban Ayiya da zamanta kenan gefenta, cikin sanyin muryarta tace "Ayiya insha Allah suna Aljannah..... Mummy Daddy da kuma NANA K.... Ayiya sometimes nakanji cewa da ace 'yar uwata Nana K tana raye k'ila da tayi kama irin tamu nida Nana H k'ila da yanzu FUSKA UKU iri guda ne a gidan nan.... Ina son Nana K kuma bazan tab'a kyautar da toys d'inta ba har abada ina ganin 'yar uwata a jiki......" Tana kaiwa nan ta lumshe idanunta had'ida rungume hoton... Ayiya da tausayin Nana A ya ratsa zuciyarta batasan sanda ta rungumota ba tana share mata hawaye... Bata jima da shigowa gidanba daga bakin k'ofar d'akin ta tsaya tana kallonsu makirin murmushi kwance saman fuskarta.... Cikin zuciyarta take fad'in _Ohh my poor crippled sis.. I wish you too didn't survive the accident so that bazan sharing Uncle Luv d'ina dake ba, na sami soyayyarsa ni kad'ai .. Daga shi har Ammah... But.... Anyways You still lost your leg... Ta d'an tab'e fuska had'i da furta "Oh oh oh What a pity ,..... I'm still the queen don munada FUSKA iri guda doesn't mean munada kyau iri guda.... and yes I still love you baby sis sabida Momy da Daddy sun tafi sun barmu saura mu biyu....._ Ta k'arashe tunanin nata tana watsawa Ayiya kallo lokaci guda ta saita kanta taci gaba da tafiya mai k'wark'wasa saman bene tana k'wallawa Ammahnta kira.... *SameenaAleeyou📚* [12/15, 5:59 AM] ‪+234 806 231 4322‬: *FUSKA UKU*🏮 *08* *©Sameena Aleeyou...✍🏽* Tunda suka dawo daga gidan Malam Tsalha ta rapka uban tagumi tana tunanin ta yanda zata soma b'ullowa lamarin, Malam yace saidai ayiwa Ahidjo aure a garin muddin tana so kiranyen da za'a masa yayi tasiri, amma idandai ba aure aka masa ba kwanaki kad'an zaiyi yayi tafiyarsa.... Ko motsawa daga kujeran da take bisa Innah Balki ta kasa balle tayi tunanin d'aura sanwar miyan dare.... A haka Baffah ya shigo gidan ya taddata, abin duk ya damesa da ganin yanayin da ta shiga duk a zatonsa tunanin halin da Deejo ke ciki take, yasan halin Balkisu da saka abu a ranta yanzu haka wannan tunani shi ya hanata sukuni... Bayan sallan isha suna zaune saman tabarmarsu ta azara suna cin tuwonsu ta surfeffiyar masara miyar busheshiyar kub'iya sai k'anshin manshanu ke tashi ga radio d'insu gefe suna sauraren zab'en dare, abinda zai baka sha'awa da wad'annan ma'aurata shine tsananin soyayyar juna da kulada juna da suke, Allah sarki saidai nasu jarabawan kan d'ansu ne, dama kowa da yanda Allah zai jarrabesa A DUNIYAR SA.... Innah ta musk tana duban Baffah dake faman santin tuwonsa tace "Nikam Malam nace ba...." D'agowa yayi yana dubanta kana yace "Kika ce mene Inna wuro....?" Abin duniya duk ya dami Innah gani take batabi hanyar da ya dace ba amma batada zab'i domin Ahidjo shine mata d'anga guda tak komai zata iya yi domin ta sami soyayyarsa.... Baffah ya katseta da fad'in "Ina jinki badai tunani Deejo kike ba.... Allah sarki yarinyar abin tausayi ne d'azu da zan wuce sallan magariba saida na jiyo kukan yarinyar nan, abin tausayi, na rasa ta yanda zanyi na amso yarinyar nan ta dawo hannunmu Gaje bazata tab'a bari ba... Ko gidan Mai Unguwa zan tafi gobe da sassafe...." Ya k'arashe yana duban Innah wacce damuwa ya kuma nunawa sosai a fuskarta lokaci guda wani tunani ke shigowa zuciyarta, toh kodai hakan zatayi ne...? Bata ida tunanin nataba ta kuma jiyo muryar Baffah yana fad'in "Balkisu wai lafiyarki bakiji abinda nake fad'i ba... Wai meke damunki ne ki fad'a min Bilki na....." Innah ta gyara zama sosai kana ta soma fad'in "Malam ina tausayin Deejo sosai ina jinta tamkar d'iyar da na haifa ta cikina, yanzu cewa da kayi ka jiyo kukanta har cikin raina naji ciwon hakan, ina fata mu cireta cikin wannan k'angi da k'unci da take ciki.... Malam nikam nace ba mai zai hana mu nema wa Yaron nan auren Deej....." Kafin ta dasa aya Baffah ya cire hannunsa daga cikin tuwon yana dubanta cikeda mamaki da gaske take maganar abinta.... "Bilki lafiyarki kuwa? Kanki d'aya...? Ta ina wannan Al'amari zai soma yuwuwa.... Deejo ta wahala a rayuwarta zata buk'aci jin dad'i a rayuwarta, bata cancanci miji irin d'anki ba... Yaron da baisan mutuncinmu ba balle na wacce za'a aura masa? ..... Ko kin mance acan barikin yanda ya tareda rayuwarsa yanada aurensa... Kawai mu d'auki Deejo don son zuciya irin tamu mu aura masa.... Haba Bilki wannan magana bata kamaceki ba...." Ya k'arashe yana jawo kwanun sha dake cikeda ruwa... Innah ta d'an b'ata fuska had'i da yin rau-rau da idanu kana tace "Amma Malam....." Baffah yayi saurin dakatar da ita da fad'in "Bana son jin komai, wannan magana bamai yuwuwa bane ALIYU bazai auri yarinyar nan ba...." Cikin sauri Innah ta d'ago tana dubansa domin a iya saninta rabon Malam da ya kira Ahidjo da asalin sunansa idan bata b'ata tunani ba tun sanda ya masa rad'in suna sai gashi yau ya ambato sunan b'aro-b'aro lallai tunda kaga haka tura ta kai bango.... Bata k'ara cewa komai ba har Malam ya mik'e daga saman tabarman, hankalin Innah ya kuma tashi matuk'a ta shiga tunanin wani hanyar da zata kuma bi, domin ita a ganinta dama ce ta sameta.... *** Gaba d'aya suke zaune a wargajejen dining table d'in mai k'unshe da kujeru goma sha biyu, Nana H 'yar gaban goshin Uncle Siraj hannun su mak'ale cikin na juna sai zuba masa shagwab'a da sangarta take Ammah na kuma riritata.... "Haba Uncle Luv wllhi har kunya nakeji na shiga cikin k'awaye da motata wllhi ta tsufa sosai yau fah shekara tim baka canza min ba ai k'awayena sai su rainani....." Ta k'arashe tana kuma turo baki gaba.... Daga yanda Lamid'o ke zaune ya kafeta da idanu sihirtaccen murmushi kwance saman fuskar sa. Siraj ya ajiye fork d'in dake cakalan abincin dashi ya kaikaito sosai yana dubanta kana ya soma fad'in "Baby I'm sorry okay... You know I've been very busy kwanakin nan, nasan ya kamata a canza maki mota kiyi hak'uri please akwai noticing da za'a shigo dasu k'arshen December d'in nan sai ki d'auke wacce ta maki kinji..." Ya k'arashe yana shafa kanta kaman k'aramar Baby.... Turo baki ta kuma yi cikin da shagwab'a tace "Uncle nidai naka nake so please...." Siraj ya dubeta cikeda mamaki kana yace "Baby nawa fah kika ce...." Kai tsaye ta shiga gyad'a masa kai alamun eh ta k'arada idan kuma bazaka bani ba shikenan bana so...." Siraj ya matso da kujeransa kusan nata sosai kana ya rik'e hannayenta alamun lallashi ya soma fad'in "Sweetheart bawai banason baki mota ta bace akwai important documents da na adanasu cikin different safes a cikin motar and....." Baikai aya ba sai gani yayi ta mik'e daga table d'in tana fad'in "You know Uncle I just lost my appetite..... And bana son motar ka rik'e abinka....." Cikin fushi ta soma tafiya Ammah na kiranta... Excusing kansa yayi yabi bayanta.... Ayiya da isowarta wajen kenan hannunta rik'eda bowl da alama wani abin zata serving d'insu baki sake take dubansu kafin ta shiga tafe hannaye take fad'in "Oh ni Bintu naga salo wannan shi ake kira SHAK'UWA SABON SALO.... Toh Allah shi kyauta ya yaye maku...." Ta k'arashe tana duban Nana A dake faman juya spoon cikin plate kana tace "'Yar Albarka na zuba maki 'ya'yan itaciyan ko...." D'an k'ak'aro murmushi Nana A tayi had'i da girgiza kai kana tace "A'a Ayiya na riga na k'oshi....." Bata kai aya ba ta jiyo muryar Lamid'o yana fad'in "Fruit is good to your health especially da dare ki sha ko kad'an ne...." Ya k'arashe murmushi kwance saman fuskar sa.... Batasan dalilin da ya sanyata amimcewa ba lokaci guda ta shiga murmusawa had'i da jinjina masa kai tana fad'in "Toh Uncle zan sha....." Ayiya taji dad'in hakan tana lura da irin sadda kai da Nana A keyi da kuma kallon da Lamid'o ke mata murmushi mai kyau kwance saman fuskarta, itakam Allah sa hasashenta ya tabbata sai tafi kowa farin ciki domin Sarki da 'yar Albarka ba k'aramin dacewa zasuyi ba.... Ana haka Ammah da tuntuni hankalinta bai wajen tana tunanin fushin da Nana H tayi, k'ok'arin mik'ewa ta soma yi tana fad'in "Shima dai Siraj son neman fitane dashi, yanzu idan tayi fushi ta tafi sai mu shafe sati bamu ganta ba a gidan nan mai akayi akayi mota da zai hana d'iyarsa inyi.. Haba ni banason irin haka..." Gaba d'aya kallo suka bita dashi jin irin fad'an rashin gaskiyar da take faman yi akan Nana H.... Kafin Ammah ta k'arasa mik'ewa Siraj da _Hetch_ (in Shawty's voice😂) suka dawo parlorn tana mak'ale cikin jikinsa alamun sun shirya, tuni annuri ya cika fuskar Ammah fad'i take "Hafsatu na ki kwantar da hankalinki mota ce dole ya baki...." Murmusawa Siraj kawai yayi yana mai k'ok'arin gyarawa Nana H kujera domin zama yake fad'in "Ammah ai kinsan Baby idan ba'ayi abinda take so ba toh babu zaman lafiya...." Nana H kuwa jin haka yasa kanta sai kuma fashewa yake, toh ta yaya ma zata bari Uncle luv yayi aure, duk wannan kulawar da yake bata wa matarsa zaike bayawarwa sannan idan yayi aure na nufin zai sami nasa 'ya'yan kenan da suka fito daga asalin tsatsonsa dole kenan duk wannan soyayya da yake mata ya tashi ya koma kan 'ya'yansa.... Wayar Ammah ne yayi k'ara ta soma yunk'urin mik'ewa Ayiya tayi sauri tace "Hajiya ki bari na kawo maki..." Ammah tace "A'a barshi kawai Ayiya dama ina son mik'ewa..." Ammah na barin wajen Ayiya tayi caraf ta sako zance don bataso Siraj da Nana H suci gaba da k'untatawa 'yar Albarka... "Sarki ya kamata ka kawo min matar nan taka na saka mata albarka, don na tabbata mai hankali zaka kawo wacce ta iya zama a gida ta kula da miji ba mai gantali a saman kwalta ba kullum...." Ai Ayiya tana kaiwa aya Nana H ta shak'a tasan ko ba'ace ba Ayiya da ita take, tak'i jinin wannan tsinanniyar mata mai suffan mayu, gashi dai tun mutuwar iyayensu take rainonsu amma ta tsaneta kaman ta fatattaketa daga gidan haka kullum takeji, bacin kinibibin Nana A da tuni ta koreta koda tsiya koda arziki, itace mutum guda dake neman tak'ura rayuwarta tun tana yarinya.... Lamid'o murmusawa kawai yayi yana shafa wuya yake fad'in "Ayiya na kusa insha Allah...." Ayiya ta watsa wa Siraj harara kana tace "Yauwa ai ya fiye maka kada kabi na wannan abokin naka wanda aljana ta auresa ta hanasa ajiye iyali... Idan nace a kamashi aje a masa karatu shida mahaifiyarsa ba yarda zasuyi ba... Ai sai ka zauna a haka, ita wacce ka lik'e matan naga dai babu aure tsakaninku ehe, kuma dole ranar daka ajiye naka iyalin ta sarara maka dun babu macen da zata d'auki wannan iskancin... K'atuwar mata god'e-god'e da ita kullum tana mak'ale jikinka wai kai Ankul loof koh.. Toh Allah yasa wata da Zara ne ku maga ta k'arya randa kayi aure....." Tunda ta soma magana suke dubanta, Siraj daina abinda yakeyi cikin waya yayi yana duban Ayiya yanda ta zak'e sai tsefesu take, Nana H kuwa ta kumbura sosai tamkar ta fashe, ji take kaman ta tashi ta rufe Ayiya da duka.... Burin Ayiya ya cika ta k'untata masu kaman yanda suka k'untatawa 'yar Albarka... Ganin Nana H na shirin magana yasa Nana A saurin mik'ewa tana fad'in "Ayiya zan tafi d'aki..." Don tasan k'arshe abin bazaiyi kyau ba muddin suka ci gaba da zama wajen don Nana H ba hak'uro zatayi ba yanzu zata wawwatsa wa Ayiya rashin kunya son ranta babu mai k'wabarta, ta kuma san sabida ita Ayiya tayi hakan.... "Uncle wllhi idan ba'a kori matar nan daga gidan nan ba wllhi sai ta cusawa Nana A tsanarmu kasan sakaryace batasan mai k'aunarta ba.. Uncle kaji irin maganganun da take, kaida Ammah ne kuke cewa a barta sabida Nana A wllhi da tani ce da tuni bata gidan nan tunda babu gadonta ciki...." Ai haurawan da basuyiba kenan Ayiya ta dawo da baya ta nufi Nana H tana fad'in "Maimaita abinda kika ce dan uwarki... Fitsararriya shashasha wacce batasan darajan aure ba...." Cikin sauri Nana A ta k'araso tana janye Ayiya yayinda Siraj ya mik'e cikeda b'acin rai yake duban Lamid'o kana yace "Na fad'a maka ka daina shiga sabgan wannan matar she's lunatic batada hankali....." Baikai aya ba Ayiya ta katsesa da fad'in "Uwarka ce mahaukaciya ba niba kaji na fad'a maka, kuma na zame maku k'arfen k'afa a gidan nan zama dani dole, kuma ina numfashi baku isa k'untata 'yar Albarka ba... Asararru kawai...." Tana kaiwa aya ta janyo Nana A dake zuban hawaye suka nufi sama... Lamid'o dai shafa sumarsa yayi yana kallon show d'in lokaci guda yake zancen zuci shi kad'ai.... *** Suna shiga d'aki Nana A ta fincike hannunta cikin kuka take fad'in "Haba Ayiya haba meyasa zakiyi haka, kinsan banason a miki rashin kunya dan Allah idan don ni kike shiga hidiman Uncle da Nana H.. Dan Allah ki daina daga yau I beg of you please...." Ta k'arashe tana had'e hannayenta biyu waje guda alamun rok'o.... Banda harara babu abinda Ayiya ke aika mata, itakam tasha koyawa Nana A k'watan 'yanci tun tana k'arama amma abu ya faskara ta rasa wannan sanyin zuciya na Nana A tai yawa shiyasa 'yar uwar ke cutar da ita tun suna yara.... Bata tankata ba sai ficewa da tayi ta bar mata d'akin alamun itama tayi fushi..... *** *Tambuwal* Jin bugun k'ofa ya sanyasu tsame hannaye daga cin tuwon da suke a yanda suke d'in baje a tsakar gida.... Dadda ta mik'e tana tand'e hannu take fad'in "Kuyi zamanku barin duba wasu 'yan biyan bashin ne ke k'ok'arin karya mana k'yauren...." *SameenaAleeyou📚* [12/15, 12:10 PM] ‪+234 810 044 6653‬: *FUSKA UKU*🏮 *09* *©Sameena Aleeyou...✍🏽* "Waye...? Waye.... Waye mai buga mana k'ofa haka....?" Ta k'arashe tana tand'e ragowar miyar hannunta... Tana bud'e k'ofar tayi arba dasu kusan biyar motarsu na pake gefe.... Baki sake Dadda ke dubansu kafin tace "Tohhhh! Ikon Allah bayin Allah lafiya...?" Ta tambaya tana gyara tsayuwarta jikin k'yauren... "Baiwar Allah kin gane wad'annan..?" guda daga ciki ya tambaya yana nuna mata jami'ansu guda biyu wanda sukaji d'auri da bandage a jikinsu, ko ba'ace ba ta shaidasu jami'an hizbah ne da suka jibga bada jimawa ba.... Kafin Dadda tayi magana su Mairo da sukaji shiru suka k'araso d'aurin kallabi a gefen goshi suna fad'in "Wai yaya ne su waye ne....?" Ai su Mairo suna isowa jami'an hizban nan suka b'oye bayan guda biyun.... Jami'i yace "Aiho wato kune hatsabiban kenan...." "A'a a'a iya bakinka yaro kada ka kuma cema d'iyoyina hatsabibai ko a kotu ansan k'watan 'yanci ehe..... Dan haka kada ka kuma ce masu hatsabibai...." Dadda tace tana mai murje sauran miyar kukan hannunta da duka hannayenta biyu.... Kafin jami'in ya sami zarafin magana suka hango Oga da Mai Unguwa suna k'arasowa mai unguwa yana fad'in "Wllhi rankashi dad'e ni kaina.. Ni kaina na gaji da fitinan wad'annan mutane, ba'a sati bakaji sunyi fad'a da wani ba tun ina rabo har dai na gaji na daina nace kar wanda ya sake kawo min k'ararsu...." Oga yace "Assha ai kaga tsiyan rik'on d'iya hannun mace kenan, haka nan zata tashi babu kwab'a...." Oga bai kai aya ba Dadda ta katsesa da fad'in "K'aryarka wllhi ni nan da kake gani nafi maza dubu iya kula da d'iya, yo wasu shegun mazan masu guduwa su bar matan da d'awainiyar yaransu nawa ankayi hakan... Inyi..? Kawai don anga mutum na rufawa kansa asiri bai tambayi kowa a unguwa ba sai a nemi a saka masa idanu... Toh wllhi bazan d'auka ba ehe...." Ta k'arashe tana girgiza... Mai Unguwa ya Kalli Ogan hizbah yana girgiza kai kurum alamun ka gani koh.... Oga kam tunda ya d'aura idanu kan kyakkyawar Fuskar Mairo wanda k'wan wuta ya haske ta kuma yin haske gaba d'aya ya kasa d'aga idanunsa daga kan Mairo, gaba d'aya jikin Oga sai yayi sanyi... Mairo na girgiza take fad'in "Idan fah bazasu watse a nan ba wllhi Baba Mai Unguwa saidai kayi hak'uri don zamu watsar dasu..." Ta k'arashe tana kuma turo kallabinta gaban goshi... Mai Unguwa zai soma masifa Oga yayi saurin dakatar dashi da fad'in "A'a a'a rankashi dad'e wato abi abun nan a sannu... Na lura akwai rashin fahimta a lamarin, kuma tunda nan ba gidan magajiya bace tabbas bai kamata a shigar masu huruminsu ba tareda sun bada izini ba, su Munkaila sune masu laifi da basuyi bincike ba kan lamarin...." Tunda ya soma magana Dadda ke dubansa baki sake tana mamakin yanda ya d'auki b'angarensu lokaci guda.... Oga yaci gaba da fad'in "Wato ainihin Hajiya kuyi hak'uri da abinda ya faru, kuma insha Allah zamu hukunta jami'anmu sabida ni a tunanina da gaske gidan karuwai ne kuma tabbas ko Mai Unguwa da kansa yayi shaidan ba'a ganin maza a gidanki toh kinga kuwa tabbas an shiga huruminki... Kiyi hak'uri, idan nasiha sukayi niyyan maku ba ta nan zasu soma ba, tabbas anyi kuskure kiyi hak'uri Hajiya..." Dadda ta yatsina fuska kana tace "Yauwa gara da Allah yasa kakeda fahimta, kuma kai Mai Unguwa tunda na hanaka auren d'iyata shikenan kaima ka saka mana karan tsana... Ko ba haka bane....?" Ta k'arashe tana duban Mai Unguwa da ya daburce lokaci guda yana fad'in "A'a nidai... Ni kuma....." "Rufe mana baki har zaka wani ce goyon d'iya mace hannun mace had'ari ne... Toh Mairamu k'walelenka nan gani nan bari akwatin maye Dutsen Arfa sha kallo ehe....." Ta k'arashe tana gyara d'aurin zaninta... Oga dai hak'uri ya kuma baiwasu Dadda sannan yace za'a d'au mataki kansu Malam Balarabe da jami'ansu da suka taka doka wacce shari'a ta kafa shiga hurumin da ba'a aikesu ba.... **** Sai wajajen 11:00pm ta dawo gidan babu ko mayafi a jikinta sai wani matsettsen skirt wanda yasha tsagu tun daga gwiwarta har k'asa, sam bazakace matar aure bace, ga uwar dogon takalmi tamkar ta kifa k'asa.. Da fallinta ta shigo gidan tana k'walla masa kira take fad'in "Sweet are you home....?" Birki tayi ganinsa zaune a parlor ya had'e hannayensa biyu k'asar hab'arsa laptop ajiye gabansa..... K'uri ya mata yana kallon ikon Allah sam kaman ba matar aure ba tabbas abin nata ya soma damun sa.... K'arasowa tayi bayan ta kwab'e dogon takalmin nata ta zauna saman cinyarsa ta shiga zuba masa shagwab'a tana fad'in "Sweet I thought zaka joining d'inmu Dinner a gidan Ammah, ko baga text d'ina ba... And you know what...?" Ta d'anyi shiru tana dubansa yanda ya kanne idanu had'i da d'aga gira kurum sama yana dubanta.... Rungumesa tayi sosai had'i da d'ago masa car keys tana fad'in "Uncle luv ya bani motar sa.... Ka tayani godiya please...." Ga mamakinta Ahidjo tureta yayi daga jikinsa bai tab'a mata hakan ba.... Nana H ta d'ago tana dubansa shaye da tsananin mamaki... Babu alamun wasa a fuskarsa yake fad'in "A haka kika fita, a wannan shigar taki...?" Girgiza kai take cikin rashin yarda da abinda kunnuwarta ke jiyo mata kana tace "Ban gane ba. Mai kake nufi....?" Kallonta ya kuma yi had'i da tura laptop d'in dake bisa wooden table d'in gefe kana yace "No one ever told you how to dress up as a married woman.... Huh?" Yatsina fuska tayi tana dubansa daga yanda yake zaune kafin ta sakar masa wata shu'uman murmushi tace "Oh Darling you should know by now that I don't follow rules.... Besides what's wrong with my clothes......?" Ta k'arashe tana dudduba jikinta tana juyi gabansa... Ahidjo da abin ya kuma basa haushi mik'ewa tsaye yayi shima yana dubanta cikin b'acin rai yace "Oh really Hafsat... Are you asking me what's wrong with your clothes?... Take a look of your self.... Ki Kalli kanki wai ke matar aure a haka kika fita, mai yasa bazaki rink'a koyi da 'yar uwarki ba, itada batada aure ta fiki shiga irinta mutunci, ya kamata ki farga kisan mai kike ciki....." Tunda ya soma magana take dubansa shaye da tsananin mamaki.... Cikin tsananin fushi itama take fad'in "Ka daina min shouting akai and yes this is me Ahidjo and therefore you have to accept me for what I am.... I don't particularly care what....." Tsawan da ya daka mata ya sanyata had'iye maganarta..... "Let me tell you this.... nan gidan auren ki ne ba gidanku da kika saba sangarci son ranki ba, for almost two years kin kasa banbance zamanin da bakida aure da kuma yanzun da kikeda aure, bazan kuma d'aukan iskancinki ba na fad'a maki... And you must.... You must obey my rules kin fahimta, sannan daga yau ban yarda ki kuma fita ba sai kin sanar dani.... Wawiya kawai wacce batasan meye aure ba...." Yana ida fad'in haka ya sungumi laptop d'insa ya haye sama yana watsa mata mugun aure.... Har ya haura sama Nana H bata rufe baki ba bata daina mamakin canzawan Ahidjo ba, shida a baya sabida wayewa irin nata na d'aya daga cikin abinda yasa ya fad'a soyayyarta amma wai shike cewa tayi lullub'i harma yana dangantata da wannan nakashesshiyar 'yar uwar tata,... Toh waima ta ina zata soma saka mayafi ai sai a kasa shaidata a mistaken d'inta da masakiyar 'yar uwarta... Kai ina never.. Tasan Ahidjo na masifan k'aunarta kurari kawai yake, kuma dole ta basa space na tsawon lokaci a gidan ta yanda sai ya gane kurensa ya bata hak'uri.... Ta kad'a kai had'i da d'aukan handbag d'inta ta nufi upstairs saida ta watsawa k'ofar d'akinsa harara kafin tayi shigewarta d'aki tana fad''i cikin zuciyarta... Kaine kad'aici zai kashe nikam inada irinka masu d'eben kewa.... Wani makirin dariya ta saki kafin ta turo k'ofar d'akin da k'arfin gaske ta rufe.... *** Safiyar ranar talata zaune suke cikin parlorn suna jiran fitowar Azeeza domin yauce ranar da Barr zai tafi da ita Laushi group domin nema mata gurbin aiki..... Bugun k'irjin Barr ya k'aru sanda yayi tozali da Azeeza ta fito cikin doguwar riga 'yar Dubai kalan ruwan k'asa wanda ya amshi kalan fatarta ba fara ba sannan ba bak'a ba.... Tayi kyau har ta gaji, bai tab'a zaton Azeeza nada irin wannan kyau d'in ba sai yau.... A haka ta k'arasa ga Yayanta Junaid ta durk'usa dab jikin wheelchair d'insa.... Idanuwanta da suka ciko da k'walla ta d'ago tana dubansa dasu lokaci guda Junaid yasa hannayensa duka biyu ya kamo fuskar k'anwar tasa had'i da girgiza mata kai alamun kada tayi kuka.... Murya na rawa Azeeza ta soma fad'in "Yaya... I'm doing this for you..... And I promise I won't let you down.... Yaya bazan failing d'inka ba..... Yaya Junaid zanyi iyaka abinda ka sakani kuma na maka alk'awari the young tycoon will fall for me....and Zan kawo maka shi har yanda kake a zaune...." Tana k'arashewa hawaye ya zubo daga idanunta... Barr kuwa kasa jure sauraro yayi cikin sauri ya mik'e yana fad'in "I'll be outside.... " Daga haka ya fice cikin sauri yana k'ok'arin nitsa zuciyarsa.... Junaid da tuni shima hawaye suka ciko idanunsa sharema Azeeza nata hawayen yayi kana yace "You go with my blessings little sis.... Bazan iya gode maki ba Azeeza sabida nasan ba'a son ranki zakiyi ba... Amma ki sani ni Junaid bazan tab'a barinki ke kad'ai ba tare zamuyi..... I promise...." Ya k'arashe yana k'ak'aro murmushi saman fuskar sa... Lokaci guda Azeeza ta rungumeshi tana kuka sosai... Saida tayi mai isarta kafin Junaid ya kuma gyara mata fuskarta ya rakota har yanda Barr yayi parking motarsa... Da kansa ya bud'e mata marfin motar ta shige... Bai bar wajen ba har saida yaga ficewarsu daga gidan.... *SameenaAleeyou📚* [12/16, 1:12 PM] ‪+234 810 044 6653‬: *FUSKA UKU*🏮 *10* *©Sameena Aleeyou...✍🏽* Ajiye coffee mug d'in dake hannunsa yayi saman k'araman plate yana duban Barr Nasaar.... Saida ya d'an murmusa kafin ya mik'e ya shiga tafiya cikin wargajejen office d'in nasa wanda yasha wooden floor a maimakon tile..... A dai-dai jikin aquarium ya tsaya yana kallon kifayen ciki kana ya maido da dubansa ga Barr wanda shima tuni ya kaikaito yana duban Siraj d'in... Saida Siraj ya d'anyi gyaran murya kana yace "Attorney maiyasa kake so na canza Janet bayan I'm ok with her, she does everything on time, she knows her obligations...." Nasaar ya mik'e tsaye yana takowa gaban Siraj kana yace "Sir as I told you, the girl really need the job... Yarinyar nan k'anwar Matata ce da ta taho daga Maiduguri... Sir kasan yanda yak'i ya maida yankinsu abin tausayi... I'm pretty sure the job will help, zata rink'a tura kud'in gida.... Yanzu haka sabida kulada yarana ta baro Maiduguri don ta zauna taredasu tunda babu mahaifiyarsu, ina fita aiki kuma su Hammad suna zuwa sch zaman nata a gidan ita kad'ai zaisa tunanin yak'in da ta gani iri da kala ya kasa barin kwanyarta... Inaso ta sami experience... Wannan na d'aya daga cikin dalilin da yasa 'yan uwan suka dage ta sami change of environment.... Sir offer her the job... Na rok'eka dan Allah...." Tunda ya soma magana Siraj yayi shiru yana saurarensa jikinsa ya d'anyi sanyi.... Mug d'in coffee d'insa ya d'auka ya shiga kurb'a a hankali yana tunanin maganganun Barr Nasaar... Saida ya koma mazauninsa ya zauna kana ya kuma duban Nasaar yace "Attorney kazo da Cv d'inta nan ne...?" Gaban Nasaar ya d'an buga kafin ya saita kansa tuni wasu dabaru suka shigo kwanyarsa abinka da lawyer.... Gyara zamansa yayi had'ida daidaita suit d'insa kana ya soma fad'in "Sir Azeeza k'aramar yarinyace she's just 19 secondary school kawai ta gama sannan naso sakata a makarantar gaba da secondary saidai unfortunately takardunta sun watse dalilin tashin tashinan hanakali da suka fuskanta, shiyasa naso ta soma aikin kafin zagayowar wata shekara sai ta sake jarabawa ta koma makaranta... Sir I'm pretty sure you'll enjoy working with her... Yarinya ce mai hankali sannan a ganina Sir tafi kayita aiki da mai d'angallalen skirt kullum tana kwarkwasa gabanka, zaka iya kai Janet wani department...." Yana kaiwa aya yayiwa Siraj k'uri sabida yasan ya gama siyesa da kalamai.... A hankali Siraj yake jinjina kai kana yace "But do you think she's that literate da har zata iya aiki damu....?" Ya k'arashe fuskarsa cikeda alamun tambaya... Cikeda jin dad'in nasarar da ya samu kan Siraj lokaci guda ya shiga jinjina kai yana fad'in "Sir kana iya interviewing d'inta and see for yourself...." Siraj ya jinjina kai kana yace "Fine.... Babu damuwa... Skedules d'ina na yau a cike suke da na ganta a yau amma maybe a cikin week d'in nan...." Da sauri Nasaar yace "But sir... She's here already... Please sir if possible ta shigo ka mata gwajin...." Kallonsa Siraj yayi kana ya d'an murmusa da gefen bakinsa yace "Seems you're desperate Attorney.... Kar ka damu ni nace zan mata gwajin kuma zan mata...." Mik'ewa yayi yana duba agogon hannunsa yake fad'in "I have to attend to some clients... Kar ka damu zamuyi maganan Attorney...." Daga haka wayarsa dake faman ruri ya k'ara a kunnensa yana amsawa ya nufi private elevator d'insa wanda shi kad'ai ke bi ta cikinta a Kampanin.... D'an fuzar da iska Nasaar yayi had'i da d'an ware hannaye alamun babu matsala tinda ya amince zai d'auketa, kuma baima yi zaton zai iya shawo kan Siraj lokaci guda ba tunda yasan yanayin yanda Business men irin Siraj suke, lokacin kansu basuda shi..... Nasaar na fitowa ya hangeta zaune tana jiransa sai d'aga kai sama take tana kalle-kallen tapkeken ginin wanda bene ne a k'alla mai hawa kusan ashirin.... A hankali Nasaar ya murmusa komai nata na birgesa musamman son yaransa da takeyi ga dukkan alamu Azeeza zata k'aunaci d'iyoyinta idan Allah ya nufa zata samu gaba idan tayi aure... Allah sarki ba kamar matarsa ba wacce tasa k'afafu ta tafi ta bar nata yaran ko oho, bikon duniya yayi tak'i amincewa ta dawo k'arshe har cewa tayi zata maka sa kotu idan bai fita hanyarta ba.... Saurin kawar da tunanin yayi ganin hankalinsa na k'ok'arin tashi... A haka ya k'araso ya tadda Azeeza tana ganinsa ta sakar masa murmushi... K'irjinta na bugu take tambayarsa feedback... D'an k'ak'aro murmushi Nasaar yayi kana yace "Kar ki damu kin sami aikin an gama cikin satin nan Boss d'in naki zai maki interview, badon rata sosai dake tsakanin nan da gida ba da na maidaki yanzu saidai ko zaki d'anyi hak'uri tunda lokacin d'auko su Taheera a makaranta ya kusa idan yaso da zaran mun d'aukesu sai na wuce daku gida tunda nima lokacin break d'ina kenan...." Jin zata school d'in su Taheera ya sanyata jin dad'i sosai har ta kasa b'oye farin cikinta..... Nasaar ya bita da kallo fuskarsa cikeda murmushi don baiyi zaton zata amince ba kai tsaye office d'insa suka wuce ta kuwa shiga tayasa aiki.... Sosai Nasaar yaji dad'in hakan har lokaci yayi saurin masa, d'an zamansa da Azeeza yau ya kuma haifar da sabo tsakaninsu... K'arfe d'aya dai-dai suka nufi school d'in su Hammad don d'aukosu... Tunda Taheera taga yau harda Aunty Zee akazo d'aukansu sai murna take hakan sai ya tuna mata sanda take k'arama sosai farkon shigarta school da Momynta Daddy ke zuwa d'aukansu watarana.... Shiko Hammad tunda ya gansu a tare ya b'ata rai sosai koma kula Azeezar baiyi ba, ya fara tsanarta baisonta kusa da Babansa bai son ganinta a gidansu, wajen Daddyn sa kawai ya nufa yayinda Taheera ta nufi wajen Azeeza sai zuba mata surutu take ita kuma Azeezar na biyeta, Nasaar na hankalce dasu sai jin dad'in shak'uwar da sukayi da juna yake..... **** Keys d'in ta mik'a masa tana mai wasa dasu a fuskarsa.... Lokaci guda ya saki murmushi had'ida amsar keys d'in yana jujjuyawa kana yace "Wow 'yar gidan Uncle baki hawa motar k'anan mutane.... Dole Uncle yayi abinda kikeso a lokacin da kike so....." Murmushi take kanta na kuma fashewa kana tace "Lamid'o kenan a lokacin da na fad'a wllhi Uncle Siraj zai bani motarsa a ranar ai ka zaci wasa nake amma yanzu na tabbatar maka babu abinda Uncle luv bazai min ba.... Lamid'o wllhi wllhi duk wanda ya nemi ya datse tsakanina da Uncle Luv wllhi sai naga bayansa ko shi waye....." Lamid'o ya murmusa yana mai shafa hab'arsa yake fad'in "Kin wuce duk yanda nake tunani Nana H kuma na yarda zakiyi komai akan Siraj.... Toh yanzu mai kike ciki da batun alak'arsa da Nadiya don naga yarinyar ta dage tana son Siraj kaman ta mutu, takan masa waya a rana bila adadi.... She's into him totally..." Yayi wata murmushi kana yaci gaba da fad'in "My guy ya had'u ta yanda babu budurwar da zaice yanaso tak'isa ke kinsan da haka... And you know ina mugun tausaya maki duk randa yarinyar nan Nadiya ta auri Siraj wllhi wllhi kaman yanda kika contributing wajen datse Ahidjo da iyayensa haka itama zata datse Siraj da familyn sa ke Laushi group sai ya gagareki shiga idan bakiyi wasa ba....." Kallonsa kawai take k'irjinta na tafarfasa tana imagining abin a gaske... Lokaci guda tayi wata murmushi kana tace "Delusional.... Kai kuma kana tunanin haka zai tab'a faruwa.... Toh ka jira kaga mai zai faru...." Ta kuma matsowa dab dashi tana shafa fuskarsa take fad'in "Just trust me sweetheart.... And remember no one messes with Nana Hafsat Laushi, the one and only Queen in the Laushi's family...." Ta k'arashe murmushi fal saman fuskarta... Murmushi Lamid'o ma yayi kana yace "I trust you darling.... Nasan zaki iya so now za'a ara min motar ne na d'ana ko kuwa....." Juyawa tayi ta soma tafiya ta nufi cikin gidan nasu da suka saba had'uwa.. Tana tafe ba tareda ta juyo ta kallesa ba take fad'in "Don't take too long...." Tana fad'i tana karkad'a masa yatsa cikin tafiyarta wanda tamkar da jikinta take yinsa..... Murmushin cin nasara Lamid'o yayi kana yace "I won't darling...." Cikin sauri ya nufi motar ya kunnata ya bar wajen..... Tafiya kad'an yayi ya d'an kutsa dajin dake gefensa kad'an ya shiga bincike a motar, duk yanda yake tunanin zai sami takardun ya bud'e bai samu ba, yasan Siraj shegen kaya ne bazai tab'a wasa da wad'annan takardu ba... Wato har ya ciresu.... Wani mugun tsaki ya buga ya shiga dukan tayun motar yana furta " Damn it.! Damn it.....!" Lokaci guda wayarsa ta shiga ruri ganin mai kiran ya sanyasa sakin wani tsaki kana ya nutsa kansa had'i da d'aga wayar.... Yana d'aga wayar daga d'aya b'angaren mai maganar yace "Ka sanar dani an sami improvement...." Shafa bayan wuyarsa yayi cikeda damuwa kana yace "I.... I... I'm sorry sir, wllhi ya cire documents d'in....." Baikai aya ba mutumin ya katsesa da fad'in "Shut up you fool... Kar ka sake min magana har sai ka sami ci gaba a aikin da na saka ka...." Daga haka katse wayar yayi yana tsaki..... Lamid'o ya shafi naman goshinsa kafin ya shige motar yana tsaki ya bar wajen cikin sauri..... **** *Tambuwal* Mamaki ne ya cika Dadda jin wai shugaban Hizba ne ke sallama, Dadda ta yafa mayafi ta fice domin jin da mai yazo tunda dai tasan sun rabu lafia..... Tana fitowa ta hangesu su biyu yau bada uniform suka zo ba shiga ta manyan kaya sukayi jampa harda hula.... Aiko suna ganinta suka k'araso cikin sauri oga sai faman sunne kai yake... A cikin ranta tace "Wannan wage baki da yake uwa gonar auduga tasan bana lafiya gashi sai sinne kai yake uwa k'adangare... Kad'a kai kurum tayi tana jiran k'arasowarsu taji da abinda suka zo domin tana dai-dai dasu... Ga mamakinta suna k'arasowa suka zube a k'asa suna gaisheta ai itama sai ta zube masu a k'asa ta shiga mad'e tana janyo mayafi tana gaishesu tana kwarkwasa... A'a Oga Ayuba ya kalli abokinsa Malam Habu cikeda mamaki ganin abinda Dadda ke masu suda sukazo domin neman auren d'iyarta..... Dadda ta mik'e tana mai ci gaba da mad'e take fad'in "Allah sarki aima baku sanar dani kuna tafe ba shiyasa tun wancan lokacin naso ka amshi lambata ko ni na amshi naka... Allah sarki ashe dai kuna tafe...." Bakin oga Ayuba na rawa yake fad'in "A... A.. Ai Hajiya dama zamu....." Saurin katsesa tayi da fad'in "Kar ka damu ka kirani Hindu... Eh Hindu sunan kenan... Kar ka dami kanka kirani da sunan yanka kurum....." Ta k'arashe tana wasa da yatsun hannunta sai ka rantse budurwace gaban saurayi.... Tun Malam Habu na mamaki har abin ya soma basa takaici ganin abinda wannan dattijuwan matar ke masu, wai dama wannan ce matar da abokin nasa yace ya samu.... Takaici ya ishesa jin Dadda tana fad'in bari ta kawo masu tabarma da ruwan sha.... Ai hiran da ba'a k'arasaba kenan suka ce mata zasu tafi aima basai sunsha ruwa ba a k'oshe suke.... K'afafuwan Oga Ayuba har na hard'ewa ya nufi mota Malam Habu na take masa baya.... Dadda bata bar k'ofar gidan ba bata daina masu mad'e tana d'aga masu hannu ba har saida taga wulk'awar motarsu.... Suna wucewa tayi k'wafa kana tace "'Yan cin k'aniya ni dama nasan sai ka biyo d'iyata... Toh baza'a bayar d'inba ka wani turo hula gaba uwa masinjan k'auye, yo mai Mairo zatayi da kai... Ai Mairo saifa na darje wannan koni nan nafi k'arfinka balle Mairona farin wata sha kallo hasken rana haske duniya Dustin Arfa a ganki a barki..... Gobe ku sake dawowa ni ce dai zan fito maku....." Tana ida fad'in haka ta maida k'ofar ta kulle.... Yanda ta hangi Mairo na kwance tana bacci ta k'arasa gareta ta zauna daga gefe had'ida k'urawa Mairo idanu tana tuna tun farkon had'uwarsu soyayyar yarinyar ya shiga ranta... Tana son Mairo fiye da komai na rayuwarta... Bata san soyayyar kowa ba sai na Mairo, bata jin rana tsaka akwai abinda zai iya rabata da Mairo... Zatayi komai domin kare Maironta..... Ta saki murmushi tana mai gyara mata kwanciyarta..... **** *_Safiyar ranar Alhamis_ Abuja* A yanda ta shigo gidan a birkice zaisa ka gane ba lafiya take ba... K'ok'arin saita kanta tayi kana ta gyara zaman mayafinta dake bisa kafad'arta ta soma takunta cikin k'walisa kaman yanda ta saba... Hayaniyar 'yan gidan taji daga parlorn dake gefe can alamun kowa na shirin tafiya babban taron da sukedashi a family d'in.. Yau rana ce da za'a bud'e Cibiyar taimaka wa nakasassu wanda Nana Asma'u ta jajirce wajen ganin wannan abu ya tabbata, tun tana k'arama batada burin da ya wuce taga ta taimaki 'yan uwanta masu fama da lalura ta nakasa ko wace iri ce.... Nana H ta yatsina fuska ganin yanda kowa ke farin ciki a gidan, ganin bata hango Nana A a wajen ba ya tabbatar mata cewa tana d'akinta tana shiryawa... Murmushi ta saki kafin ta nufi upstairs.... Aiko tana bud'e k'ofar ta hangeta zaune gaban dressing mirror tana shafa mai.... Asma'u ta sakarwa 'yar uwarta murmushi lokaci guda Nana H ta maida mata da martanin murmushin kana tace "May I....?" Cikeda jin dad'i Asma'u ta shiga jinjina mata kai tana fad'in "Please come in sis...." Nana H ta k'arasa shigowa had'i da maida k'ofar d'akin ta rufe... Saman bakin gado ta samu ta zauna tana mai duban 'yar uwar tata... Nana H na karantar 'yar uwar tata take tambayarta "Sis, have you picked out your clothes for the event...?" D'an dubanta Nana A tayi kana ta girgiza kai tace "Wllhi I haven't sis... I'm so nervous, I know there will be alot of people.... Kinsan ban saba shiga mutane da yawa ba...." "Ya Allah Nana A what have you been doing...? Tsoron mutane ko, kar ki damu everything will fine... Trust me OK...." Murmushi Nana A tayi kana tace "Tunda kinzo sai ki zab'a min...." Nana H ta shiga jan kumatun Nana A tana fad'in "Goodness, what kind of sister do I have, batasan ta zab'i kaya to her own taste ba..?" Nana A na murmishi cikeda jin dad'i take fad'in "Best in the world I guess...." Murmushi Nana H d'inma tayi kana ta mik'e ta isa closet d'in 'yar uwar tata ta shiga zab'a mata kaya masu jida kyau... Harta covers d'in da Nana A ke sakawa sabida ruf'e k'afafunta yau Nana H ce ta zab'a mata.... Abinda zai baka mamaki yau har kwalliya Nana H tayiwa 'yar uwarta wacce sam kwalliya bai gabanta.... Ammah da shigowarta d'akin kenan don ganin ko Nana A ta shirya sai gani tayi Hafsat yau ita kewa Asma'u kwalliya sai raha da farin ciki suke, abunda suka jima basu gani ba a gidan.... Ammah da tuni farin ciki ya mamayeta batasan sanda k'walla suka ciko idanunta ba, kullum burinsu da fatansu kenan 'yan uwan su so junansu... A hankali ta silale ta bar d'akin don bataso tayi distracting nasu.... Tas Nana H ta shirya 'yar uwarta ta kuwa yi kyau sosai tayi kama da 'yar uwarta babu abinda ya rabasu don irin kwalliyar dake fuskarta Nana H tayi mata... Nana Asma'u ta Kalli fuskarta a madubi cikeda mamaki tana shafawa take fad'in "Nana H I look different... Wannan kwalliyar tai yawa, please a rage...." Nan da nan Nana Hafsat tayi kicin-kicin da fuska tace "Au bakison kiyi kama irin tawa sabida banida hali mai kyau koh... Idan bakison duk wani abinda zan maki fine, inma bakison ganina a taron naki ne fine.. Sai nayi tafiyata....." Ta k'arashe tana k'ok'arin barin d'akin... Saurin rik'ota Asma'u tayi kana ta shiga girgiza kai tana fad'in "I love it sis... Kiyi hak'uri kinji.... And I look beautiful just like you.... I'm sorry kinji Sis." Murmushi Nana Hafsat tayi kana tayi hugging 'yar uwar tata tana fad'in "Is OK... Kar kiyi kuka ki b'ata gayunki don nasan kad'an da aikin ki...." A tare suka murmusa kafin suka jera da taimakon Nana H suke sauk'owa daga matakalan benen... Gaba d'aya suka mimmik'e suna hangosu yanda suke sauk'owa kamanninsu ya fito sosai yau.... Babu kaman Lamid'o wanda ya kasa d'auke idanunsa daga duban Asma'u, bai tab'a zaton tanada sihirtaccen kyau irin na yau ba, shi dama suka jera itada Hafsat d'in sai yake ganin tafi Hafsat kyau... Wani abu yake ji na tsargansa gameda Asma'u.... A b'angaren Ayiya kuwa tab'e baki kurum tayi zuciyarta na raya mata akwai abinda Nana Hafsat ke shiryawa tasan haka kurum bazatayi wannan kirki ba , amma koma menene tana biye da 'yar Albarka duk yanda ta sanya k'afafunta... Siraj kam sosai yaji dad'in abinda Nana H tayi, shi dama kullum burinsa yaran su had'e kansu, abin ya birgesa sosai, har yake ji zai tsaya a gama event d'in gaba d'aya dashi dukda tulin aiki dake gabansa.... Gaba d'aya suka d'unguma suka nufi sabon cibiyar taimakawa masu nakasan, lallai Asma'u 'yar dangice kuma suna k'aunarta.... *** Kai ya d'aga yana kallon foundation d'in wanda yasha kwalliya ga guragu da dama da dai sauran masu naksa sai tururwan shiga suke ba'a hana masu nakasa shiga bakaman mai lafiya ba da sai anga invitation card d'inka... Junaid ya janyo hular sanyinsa ya rufa a kansa cikin zuciyarsa yake furta _it is now or never_ Lokaci guda shima ya kutsa cikin masu nakasan ya shige.... *SameenaAleeyou📚* [12/19, 12:07 AM] ‪+234 810 044 6653‬: *FUSKA UKU*🏮 *11* *©Sameena Aleeyou... ✍🏽* Tunda taga Lamid'o na rawan jiki akan Nana A taji dama bata mata makeup d'in ba, abinda ya dad'a bata haushi yanda aketa zuzuta kyaun da Nana A tayi.... Koda shike babu yanda za'ayi a had'a nakshasshe da mai lafiya... Lokaci guda ta Saki murmushi sanda ta tuna hakan.... Suna isa fili ya kuma kacamewa musakai bayin Allah kowa k'ok'arinsa yaga wannan gwarzuwar macen da Allah ya mata zuciya mai kyau, mai k'aunar taga farin ciki a fuskar musakai, mai burin ta datse yawan barace-barace da musakai keyi, mai fatan taga ko wani musaki Allah ya azirtasa da sana'a domin dogaro da kai..... Duk wani kacaniya da ake Nana A ta kasa fitowa daga mota banda bugu babu abinda k'irjinta keyi tun wayewar garin yau.... Ayiya na k'ok'arin bud'e k'ofa Nana A ta kamo hannunta ta dunk'ule sosai cikin nata idanunta sunyi rau-rau... Murmushi Ayiya ta sakar mata kana tace "Muje 'yar Albarka yau burinki ne Allah ya cika maki shi...." K'ak'aro murmushi tayi tana duban Ayiya kana ya soma magana cikin tsananin sanyin muryarta.... "Ayiya bansan meke shirin faruwa dani ba, bansan meyasa k'irjina ke tsananin bugu ba, bansan mai zaije yazo a taron nan ba.... Burina kenan tsawon rayuwata sai gashi yau da Allah ya cika min wannan buri nawa inajin kaman wani abu zai faru dani kaman....." Ayiya ce tayi saurin katseta ta hanyar rufe mata baki da hannunta guda tana mai girgiza mata kai alamun ta daina fad'in haka, lokaci guda take fad'in "Daina fad'in haka 'yar Albarka babu komai cikin taron nan sai tarin alkhairi da izinin Rabbi, ki kasance mai kyakkyawan zato kinji... Ke d'in alkhairice ga 'yan uwanki masu fama da lalura irin taki... Maza kintsa kanki ki fito muje na tabbata isowarki kawai ake jira...." Tana ida fad'in haka ta sakar mata murmushi... Murmushin ta maida mata dashi itama kana Ayiya ta soma ficewa lokaci guda driver ya fito ya bud'ewa Nana A bayan motar k'irar Camry.... K'afafunta wad'anda ke rufe cikin sauciki su suka soma fitowa daga cikin motar, a dai-dai lokacin Dattijuwa Ayiya ta k'araso ta tallafawa Nana Asma'u ta ida fitowa daga cikin motar.... Nana A ta d'aga kai sama tana duban ginin wanda a kullum take mafarkin kasancewar hakan sai gashi Allah ya cika mata burinta, lokaci guda ta saki murmushi had'ida hamdala kafin ta dubi Ayiya tace "Alhamdulillah Ayiya Allah ya cika min burina, burin da ya jima yake kwance cikin zuciyata, wanda nake kwana dashi kuma nake tashi dashi...." Ayiya ta kuma kamo hannun Nana A kana tace "Haka ne 'Yar Albarka Allah shine abin godiya... Maza mu k'arasa na tabbata isowarki kawai ake jira...." Nana A ta kuma sakin murmushi kafin suka nufi cincirindon mutanen, securities d'in Siraj sai taimaka masu suke faman yi..... Daga yanda yake zaune cikin wheelchair d'insa yana hangosu,.... Fuskokin da bazai tab'a mancewa dasu ba sune suka sake bayyana gabansa, fuskokin da yake kwana yake tashi dasu FUSKA UKU wad'anda yake kwana yake tashi da burin ganin bayansu, idanunsa ya soma sauk'a kan Ahidjo wanda bai mance ba shine yaga bindiga rik'e a hannunsa, gashi nan da matarsa sai raha da farin ciki suke.... Lokaci guda idanunsa suka sake sauk'a kan Lamid'o mutumin da bazai tab'a mancewa ba shi ya soma tattaka k'afarsa da iya k'arfinsa mutumin da ya soma janyo sanadi na kasancewarsa cikin nakasa, gashi a yanzu ya kuma zama k'akk'arfa fiyeda yanda yake a baya, alamun kwamciyar hankali ya dad'a samunsa.... Lokaci guda idanunsa ya sake sauk'a kan mutumin da yafi tsana gaba d'aya a cikinsu, mutumin da yayi sanadiyan rabuwarsa da farin cikinsa ZEENATU mutumin da ya janyo masa fad'awa k'uncin da yake ciki a yau wanda baya tunanin zai tab'a gushewa daga cikin zuciyarsa, baya tunanin wannan ranar tana zuwa... Gabaki d'ayansu Junaid yake bi da kallo abubuwan da suka faru a baya na dawo masa, lokaci guda yaji zuciyarsa na masa wani irin zafi, k'aran harbin da akayima Zeenatu ihunta da maganganun da sukayi cikin waya ba daina yawo a kwanyar Junaid da kunnuwarsa ba, gaba d'aya baisan mai ake gudanarwa a taron ba sai kafe FUSKA UKU da idanu da yayi, ji yake da yanada hali ya shak'esu d'aya bayan d'aya sun daina numfashi kaman yanda suka raba Zeenatu da rayuwarta..... **** *Misau* A guje yauma ta shigo gidan tana ihu tana kuka hannunta yayi jajazir alamun k'una,... Innah na surfen wake tayi jifa da tab'arya a tamanin ta nufo Deejo tana sallalami tana tafe hannu ganin yanda hannun Deejo ya d'ura ruwa yayi jazir alamun k'una.... Kuka Deejo take tana fad'in "Innah dan Allah ki ceceni kada ta kasheni, wllhi tace kasheni zatayi muddin ban amso mata kud'in Lado mai gurmi ba.... Innah dan Allah ki b'oyeni kice mata na mutu ko zan huta... Innah kiji tausayina dan Allah...." Ta k'arashe tana kuma fashewa da wani sabon kuka... Innah ta gyara d'aurin zaninta tana kuma tafe hannaye cikeda mamakin yanda Duniya ta lalace a yau, shin har yaushe za'a daina samun matsalan kishiyar uwa a k'asar hausa? Shin yaushene addini zai wadace mutane su gane cewa shi yaro na mutum guda bane? Shin har yaushe son zuciya da son abin duniya zai bar zukatan mutane A DUNIYAR MU? Yaushe za'a daina wulak'anta d'iyoyi mata a wannan rayuwa....? Yaushene mutane zasu fahimci shi d'a a hannun marik'insa walau iyaye walau akasin haka amanace....? Tirk'ashi tabbas d'an Adam nada babban k'alubale a gabansa..... Innah na cikin wannan tunani ta jiyo k'ara.... Krarau! An banko k'ofa an shigo, ga tsananin mamakinta Gaje ce ta taso mijinta gaba tana surfa masa ruwan bala'i tana fad'in yayi iyakawa shegiyar d'iyarsa da wannan gidan da mutanen ciki.... Ai Deejo na jinsu tuni tayi cikin rumbu ta b'oye tsakankanin buhuhuna ita kanta Innah batasan yanda akayi Deejo ta b'ace a wajen ba kawai dai bud'e idanu tayi taga babu Deejo a wajen, iyaka dai tasan Deejo na cikin gidan bazata fice ba saidai ta nemi wajen b'uya sabida jiyo sautin Gaje da tayi..... "Toh annamimiya shugaban munafukai na duniya maza a fito mana da d'iyarmu tinda ita Allah yayi bamu sallamatawa bariki ba.... Fito mana da ita ehe....." Gaje ta k'arashe tana shan d'amara uwa 'yar wasan tashe.... Tun daga waje Baffah ke jiyo hayaniyar Gaje, yau wani ikon Allah haka kurum yaji ya baro kasuwa ya dawo gida aiko sai ga abinda ya tadda, Gaje ta yanda shiga bata nan take fita ba, sai tsine-tsine da rantsuwa take tana fad'in Innah Balki ta fito masu da d'iyarsu.... Baffah ya d'anyi gyaran murya yana duban Innah Balki kana yace "Bilkisu kin tabbata Deejo bata shigo gidan nan ba...?" "Malam wai kaima ka yarda da maganar wannan matar ne... Idan taga Deejon ta d'auketa mana... Neman tashin hankali kawai irin nata, yarinya ana azabatar da ita yo mai kuwa zai hanata gudu...." Mahaifin Deejo kuka yake sosai yana fad'in Deejonsa bata gudu ba Deejo tana nan bazata gudu ba..... Baffah ya girgiza kai cikeda tausayin Malam Ard'o mahaifin Deejo, dafa kafad'ansa yayi ya soma basa baki cikin harshen fillanci Gaje kuwa bata daina bala'i tana fad'in a fito masu da d'iyarsu ba... K'arshe bincike ta shiga yi a gidan tana lek'a lungu da sak'o, harta madafi saida Gaje ta lek'a bataga Deejo ba, wani ikon Allah, Allah bai bata basiran lek'a rumbu ba... Haka suka k'araci bincikensu babu Deejo... Yanda Baffah yaga hankalin Innah bai wani tashi ba yasan tasan wani abu gameda b'atan Deejo.... Gaje fah bataji ba bata gani ba daga gidan kad'an kan Mijinta sukayi suka nufi gidan Mai Unguwa don bata yarda ba Innah Balki bace ta b'oye Deejoh..... *** Cikin lumana da kwanciyar hankali taron ke gudana, bayan an saurari jawabai daga b'angarori da dama aka soma raba kyaututtuka wa duk wani mai nakasa da ya halarci taron, a lokacin ne hargowa ya kuma b'arkewa sosai... Ana tsaka da wannan hidima wayar Siraj ta soma ruri, lambar Nadiya shi ya gani b'aro-b'aro ana tana kiransa, baisan dalilin fad'uwar gaban da yaji ya sauk'a masa ba sanda yaga kiran nata, yau gaba d'aya ko waya da ita baiyi ba.... A hankali ya soma k'ok'arin barin wajen dan keb'ewa yana kutsa cikin jama'a... A dai-dai lokacin Nana H da Lamid'o suka kalli juna wanda su kad'ai suka san ma'anar kallon nasu... Cikin sauri Lamid'o ya takewa Siraj baya..... Lamid'o na isowa yanda Siraj ke tsaye yana amsa wayar ai shima sai ya tsaya cak yana duban Siraj wanda ke faman salati babu k'akk'autawa... Cikin sauri Lamid'o ya k'arasa yana tambayarsa "Siraj lafiya... Make faruwa waye ba lafia....?" Duka tambayoyin lokaci guda Lamid'o ke jerowa Siraj..... Cikin sauri Siraj ya katse wayar yana fad'in "Maama I'll be right there.... Zanjeni asibitin yanzu, kin kwantar da hankalinki insha Allah Nadiya zata sami sauk'i, zanjeni yanzu....." Yana ida wayar ya soma tafiya cikin sauri yanai ma Lamid'o bayani.... "Lamid'o I've to go... Nadiya tayi accident a hanyarta na zuwa taron nan, tana asibiti unconscious, mahaifiyarta ce ta kirani yanzun nan take sanar dani....." Wani irin bugu k'irjin Lamid'o yayi yana mai girgiza kai yake salati yana jajanta yanda lamarin ya faru.... Nana H da isowarta wajen kenan taji suna batun.... Wani irin kuka ta saki tana kuka sosai take fad'in "Uncle mai ya sami Nadiya... Dan Allah mai ya sameta kada kucemin wani abu ne ya sami k'awata... We were together yesterday har tace min zata zo ta taron Nana A da akeyi yau.... Uncle ina Nadiya take.....?" Kuka yaci k'arfin Nana H.... Saurin rungumota Siraj yayi yana lallashi dukda shima k'arfin halin kawai yake... A hankali yake shafa kan Nana H yana fad'in "Is OK baby.... Nadiya zata sami sauk'i insha Allah... Ki daina kuka kinji koh...." Jinjina masa kai kurum take ba tareda iya furta koda kalma ba.... Sanda Lamid'o ya sanar dasu Ammah abinda ke faruwa nan suka ce basuci ta zama ba dole su tafi duba Nadiya da halin da take ciki.... Sosai hankalin Nana A ma ya tashi taso ta bisu asibitin amma Siraj ya buk'aci ta zauna a ida taron itada Ayiya, hakan kuwa akayi, Gaba d'aya Lamid'o saiji yayi tashin hankalin da Asma'u ta shiga ya d'aga masa hankali, baison ganin hawayenta sam, gaba d'aya baisan mai yake ji gameda ita ba... Kusanta ya matso sosai had'i da kwantar da murya ya soma lallashi yana bata baki "Nana....." Ya kirawo sunanta a hankali.... D'ago idanu tayi tana dubansa kafin yaci gaba da fad'in "Everything will be alright OK.... Kin kwantar da hankalinki kinji...." Cikin nuna damuwa sosai ta shiga jinjina masa kai tana goge hawayen idanunta take fad'in "Please keep us posted Uncle Lamid'o.." Cikeda kulawa ya jinjina kai yana fad'in "I'll insha Allah ok.... Just take care of yourself ok...." Jinajina masa kai ta kuma kafin sukayi sallama da Ayiya cikin sauri yabi bayan su Siraj Gaba d'aya suka d'unguma suka nufi asibiti cikin tashin hankali..... Siraj yaso Ahidjo ya wuce da Nana H gida sabida yanda hankalinta ya tashi sosai amma ta doge tace itama asibitin zata, tana son ganin Nadiya tasan halin da take ciki... Sosai ta baiwa Ahidjo tausayi ganin yanda hankalinta ya tashi dukda a kwana biyun nan ya d'auke mata gaba d'aya amma yau sai ta basa tausayi, rungumeta yayi cikin jikinsa yana kuma lallashinta yana fad'i mata Nadiya zata sami sauk'i... Idan ka kalli Siraj dole ya baka tausayi driving kawai yake amma kasan hankalinsa baya jikinsa, shi kansa tausayin kansa yake, Allah sarki Nadiya Allah sa kar itama ta mutu ta barsa, a hankali yasa hannunsa yana goge idanunsa da yaji suna k'ok'arin kawo ruwa... Lamid'o dake zaune gefensa a hankali ya sadda kansa cikin zuciyarsa yake ji tamkar tausayin Siraj na ratsa sa tako ina..... Tunda suka tafi hankalin Nana A bai kwanta ba gaba d'aya sai ta koma wani iri, tana wajen ne kurum amma hankalinta bai wajen.... Ma'aikatan wajen sai kai komo suke suna rabon kayan tallafin ... Gaba d'aya Nana Asma'u ji tayi bazata iya jure zaman wajen ba har a gama taron.... Haj Larai k'awar marigayiya mahaifiyarsu itace a matsayin mai kula da komai na cibiyar, dole Ayiya ta sameta ta sanar da ita zasu tafi sabida halin da Nana A ke ciki gaba d'aya tunda 'yan uwan nata suka tafi hankakinta bai kwanta ba.... Cikin sauri suka nufo waje dandatson musakai sai rapka tafi suke tunda suka hangi fitowar Nana Asma'u..... Cikin tafiyarta wanda yafi kama da d'ingishi take takawa lokaci guda wayarta dake cikin jaka ya shiga ruri lokaci guda ta soma k'ok'arin ciro wayar daga jaka, ga jama'a sai faman mik'a mata gaisuwarsu suke... Garin kiciniyar ciro waya a jaka wayar ta fad'i k'asa... Dai-dai ta sunkuya d'aukan wayar kenan shima ya kai hannunsa.... Wani irin bugu k'irjinta yayi ta shiga bin hannun nasa da kallo.... Lokaci guda Nana A tayi saurin d'aga hannunta tana kallon mutumin wanda ke ta faman had'a mata wayarta data tarwatse a k'asa..... Saida ya ida had'a mata wayar tas kafin ya d'ago fuskar sa suna duban juna.... *SameenaAleeyou📚* [12/19, 6:38 PM] ‪+234 810 044 6653‬: *FUSKA UKU*🏮 *12* *©Sameena Aleeyou...✍🏽* Murmushi kwance saman fuskarsa yake dubanta yanda tayi sakare tana dubansa.... Gaba d'aya tayi nisa duniyar kallon wannan gurgu dake zaune cikin kekensa a gabanta.... Muryarsa ta jiyo yana fad'in "Miss here you go....." Ya k'arashe yana mai mik'a mata wayar.... Saurin saita kanta tayi kana tasa hannu ta amshi wayar had'ida k'ak'aro murmushi saman fuskarta... "Na gode bawan Allah....." ta fad'i still murmushi saman fuskarta Shima murmushin yake kana yace "Babu komai, ki dinga kula sabida wayoyi irin naku faduwa k'ank'ani suke su sami matsala ga tsadan gaske...." Yana ida fad'in haka ya soma tura kekensa da niyar barin wajen... Yanda yayi maganar cikeda kulawa ya sanyata kuma dubansa tana mai juya wayar hannunta.... Cikin sauri ta bi bayansa tana fad'in "Amm.. Nace ba....." A hankali Junaid ya kaikaito yana dubanta.... Murmushi saman fuskarta tace "Na gode sosai...." Da gefen bakinsa ya murmusa kana yace "Babu komai fah...." Zai soma tafiya Asma'u ta kuma tsaida shi da fad'in "Tareda kai akayi taron nan gaba d'aya...?" ta tambaya tana dubansa A hankali ya jinjina mata kai ba tareda ya furta komai ba.... Cikeda mamaki tace "Toh ya ban ganka da wani kyauta ba ko bai iso kanka bane....?" Junaid ya kuma murmusawa kana yace "Kar ki damu Miss na kyautar da nawa ne ma wanda yafini buk'ata, da inada hali nayi makamancin abinda kikayi da nayi domin taimaka wa 'yan uwanmu masu lalura irin tamu, saidai dukda haka na gode ma Allah da ya bani ikon halartar wannan taro da kika gudanar, naji dad'i sosai kuma na yarda akwai mutanen kirki A DUNIYAR MU..." Asma'u ta kuma binsa da kallon mamaki, ashe dai akwai mutane irinta da yawa, lokaci guda ta sakar masa murmushi kana tace "Niyyanka na alkhairi Allah ya biyaka, idan bazaka damu ba dan Allah inason sanin sunan ka sannan inaso kayi register da foundation d'in nan please....." Junaid ya kuma d'an murmusawa yana dubanta yanda take maganar alamun ta gaji da tsayuwa sabida lalurar k'afarta kana yace "Da alama kin gaji da tsayuwa..." Gyara zaman mayafin doguwar rigarta tayi tana d'an waige-waige yanda zata hango abin zama nan kuwa ta hangi wata kujera daga can gefe, cikin d'ingishi ta nufi kujeran saidai kafin ta k'arasa ga kujeran Junaid ya isa ya d'auko mata kujeran.... Ta bisa da kallo fuskarta d'auke da murmushi..... Gyara zaman kujerar tayi tana mai furta kalmar godiya kana ta zauna bisa kujeran suna fuskantar juna... Ta kuma gyara zaman gyalenta da iska ke faman fifitawa kana tace "Umhum ina saurarenka ka sanar dani sunanka..." Junaid ya sauk'e hular sanyi dake kansa fuskar sa ya bayyana sosai wanda hakan saida ya kuma sanya Asma'u sabon fad'uwan gaba.... Tabbas ya lura da hakan kuma da biyu yayi hakan, yasan dalilinsa nayin hakan... Saida ya d'an mik'e sosai cikin keken nasa kana ya soma fad'in "Sunana Junaid.... Saidai register da foundation d'inki ne bansan ko zan iya ba....." "Junaid..." Ta maimaita a hankali kana taci gaba da fad'in "Dan Allah kar ka yanke hukunci cikin gaggawa, kayi shawari ko zaka iya register damu please... Mutane irinku mukeso a wajen nan.... Please Junaid..." Sunansa data ambata k'arshen kalamanta saida ya sanyasa d'ago idanu yana dubanta... A hankali ya saki murmushi kana yace "Shikenan zanyi yanda kika ce Miss.. Zanyi shawari...." Asma'u ta murmusa cikeda jin dad'i kana tace "You can call me Asma'u or Nana A haka ake kirana a gidanmu...." Junaid ya kuma murmusawa gani she's so naive, she can trust easily, sam manipulating d'inta bazai masa wahala ba..... "OK.... Asmah..." Kallonsa tayi jin sunan da ya kirata dashi wanda babu wanda ya tab'a kiranta dashi... _Asmah_ ta maimaita a hankali, tabbas sunan ya mata dad'i..... Gani irin kallon da yake mata ya sanyata sadda kanta k'asa lokaci guda bugun k'irjinta ya k'aru... Sun shafe kusan minti guda babu wanda ya kuma magana har saida suka jiyo muryar Ayiya tana fad'in " 'Yar Albarka ina kika shige inata nemanki, hankalina duk ya tashi...." Saurin mik'ewa Nana A tayi ta nufi Ayiya tana fad'in "Ayya 'yar tsohuwata I'm sorry gani nan a nan, na fad'a maki kar ki damu bazan b'ata ba...." "Yo ba dole na damu ba, tun d'azu nida Larai muke nemanki, lafiya kikazoki nan kika zauna....?" Sai sannan Nana A ta juyo yanda ta bar Junaid a zaune da niyyan introducing d'insa wa Ayiya saidai wayam bataga kowa ba, babu Junaid a wajen..... Mamaki ya cikata, toh ina ya shige yanzu yanzun nan..... Ganin tana waige-waige ya sanya Ayiya tayata dube-duben tana fad'in "Menene kam kika gani....?" D'an sauk'e ajiyan zuciya Nana A tayi kana tace "Muje Ayiya, mu k'arasa asibitin mu duba jikin Nadiya..." Ayiya ta jinjina mata kai kana ta rik'o hannunta suka soma tafiya, har lokacin Nana A bata dawo dai-dai ba.... *** *Tambuwal* Wayar ce ta kuma shigo mata tana duban lambar ba tareda ta d'aga ba, tasan bazai tab'a barinsu ba, bazai tab'a bari mata Mairo har abada ba, shin ko wannnan garin zasu bari su kuma komawa wani garin, bata jin zata iya damk'a Maironta wa mutumin da tasan cutar da ita zaiyi sannan bata jin zata iya maida Mairo ga danginta tunda tasan dangin nata cikin had'ari suke rayuwa, tabbas tasan ALHAJI BULAMA bazai tab'a barin dangin Mairo ba sai yaga bayansu, itako bazata bari tanaji tana gani ta tura Mairo cikin wannan musiba ba, gwara su ci gaba da yawonsu wa gari wa gari itada Maironta, tinda dai ya mik'a mata ita a hannunta toh yayi kuskure domin Mairo ta zama d'iyarta na har abada, bazata tab'a sanar da ita cewa ba itace ta haifeta ba..... Bata ida tunanin ba wayar ta kuma k'ara.... Dadda tayiwa wayar k'uri domin babu abinda ta tsana kaman taga kira da bak'uwar lamba.... Saida aka kira sau uku a na uku tayi ta maza ta d'aga don ko babu komai tasan dai-dai da ko wani shege take.... Daga d'aya b'angaren dariya ya fashe dashi kana yace "Bintu kenan..... Ina Mairo ta... Da fatan tana lafia....?" Kaman bazatayi magana ba sai kuma tace "Alhaji barka da rana....." "Baki amsa min tambayata ba, Ina Mairo..?" Kasa furta komai tayi tana tunanin ta yanda akayi Alhaji Bulama yake samun layinta..... Tabbas dole ta tattari Mairo su kuma yin hijira kafin ya cimmasu.... "Kina jina Bintu... Mairo amana ce a hannunki kuma nasan kina son Mairo fiyeda komai A DUNIYARKI kici gaba da kulamin da Mairo har na k'arashe cikita burina A DUNIYATA na auri Mairo na bata duk wani kulawa da gata da na hanata samu daga danginta...." Dadda ta katsesa da fad'in "Alhaji yanzu a shekarunka har kana tunanin auren yarinya kaman Mairo.. Haba Alhaji dan Allah ka k'yalemu haka nan, wllhi Mairo soyayyata da duk wani kulawa tawa ya isheta, dan Allah ka....." Dakatar da ita yayi da fad'in "Bintu kenan, ashe ke har kin isa ki sanar dani abinda zanyi...? Idan ban mance ba da hannayena na mik'a maki Mairo shekaru ashirin baya ashe kuwa kinga dawo da ita hannuna bazai maki wahala ba... Kar kiyi tunanin zaki tab'a b'ace min a fad'in k'asar nan domin kinsan duk yanda kika tafi zan cimmaki....." Daga haka bai saurari cewarta ya katse kiran.... Dadda tabi wayar da kallo tana tunanin lamarin.... Kai inaa wllhi bataga mahaluk'in da zai rabata da Mairo ba ko shi waye, duk k'arfin arzikinsa duk k'arfin mulkin sa, Mairo d'iyarta ce duk bala'in da za'ayi.... Ta k'arashe tunanin nata tana wani irin huci tamkar mai shirin taran fad'a..... **** Cirko-cirko suka taddasu a asibitin ga mahaifiyar Nadiya sai kuka take Ammah na gefe na bata baki, Lamid'o na ganinsu ya k'araso da sauri ya taresu, Nana H kuwa tayi lamo jikin Uncle Siraj idanunta gaba d'aya sun kod'e alamun taci kuka, daga ita har Siraj d'in dole su baka tausayi... Cikin sauri Nana A ta k'arasa garesu had'i da zama b'angaren Uncle Siraj ta dama ta shiga lallashinsu daga shi har Nana H d'in... Nan Lamid'o yake sanar da Ayiya an shiga aiki wa Nadiya sabida had'arin da tayi ba k'aramin had'ari bane.... Kowa yayi cirko-cirko da kalan addu'an dake bakinsa..... *** *Misau* Baffah na zaune tsakar gida yana cin abinci kafin lokacin komawa kasuwa tayi ya koma yaji motsi daga cikin rumbu.... Tun yana jiyo motsin kad'an har dai yaji da gaske motsi ne.... K'uri yayima k'ofar rumbun ba tareda yaci gaba da cin abincin ba.... Kaman 'Yar kyanwa haka ya hangeta tana fitowa daga tsakankanin buhuhuna..... Mamaki ya cika Baffah, abin har yaso basa dariya... Banda yarinta irinta Deejo ya zaki shige tsakankanin buhuhuna na abinci idan tsautsayi ya auka buhu ya fad'o maki fah...? Ya d'an girgiza kai had'i da yin murmushi tana lek'e-lek'e alamun tana son fitowa kana yace "Fito abinki Deejo Gaje bata nan...." Cikin sauri Deejo ta k'arashi fitowa, dai-dai lokacin Innah ma ta fito don taji maganar Baffah tasan da Deejoh yake..... Itama Innah mamaki ne ya cikata ganin Deejoh ta fito daga cikin rumbu, ashe nan ta shige ta b'oye, ita kanta Innah saida Deejoh taso bata dariya... Baffah ya lura da yanda Deejoh ke rik'eda hannunta idanunta sunyi rau-rau "Subhanallahi Deejoh mai ya sami hannun...?" Ya tambaya cikeda kulawa.... Nan Innah ma ta k'araso tana fad'in "Haka fah hannun nata da ciwo dama ta shigo, taho mu gani Deejoh... " Ta k'arashe tana fitowa daga d'akin.... Sosai hannun Deejoh ya k'one, abin tausayi idan ka gani, Innah kaman zatayi kuka sanda Deejoh ke basu labarin k'unar.... Oh Duniya abin tsoro, kasa ruwan zafi ka k'ona d'an mutum don bakai ka haifa ba, sai kace wani kaza.... Nan Baffah ya shiga had'a mata garin magani ya barbad'a mata a wajen k'unan dama Allah yasa ya iya ire-iren wad'annan magunguna na gargajiyan.... Innah ta zuba mata abinci paten dankalin hausa taci tayi nak sai bacci yayi gaba da ita.... Har d'aki Innah ta kaita ta kwantar saman gadonta mai rumfa... Zaune tayi gefenta had'ida k'ura mata idanu tausayinta na kuma ratsa ta, a haka ta dawo tsakar gidan ta tarar da Baffah na shirin komawa kasuwa, d'an zama gefensa tayi tana dubansa... Dubanta shima yayi kana yace "Tayi bacci koh....?" A hankali Innah ta jinjina kai... Kana ta muskuta tana mai fad'in "Yanzu Malam haka zamu zuba idanu ana cutar da yarinyar nan... Malam anya bazaka duba maganata ta kwanaki ba....?" Shiru Baffah yayi yana nazarin maganar nata kana ya sauk'e ajiyan zuciya yace "Shikenan babu damuwa anjima idan na taso daga kasuwa zan sami su Malam D'alha muyi maganar, idan yaso ko gidan Mai Unguwa ne sai muje, babu damuwa na fahimceki tabbas zaman yarinyar a hannun Gaje akwai cutarwa, kuma nasan da niyyan taimako kikayi hakan, babu komai Bilki na maki alk'awari wannan karan kam da yardar Allah Deejoh bazata koma gidan Gaje ba....." Ya k'arashe yana duban matar tasa wanda farin ciki da take ciki ya gaza b'uya.... Allah na gab da cika mata burinta... *** Kallo d'aya yayiwa Nasaar ya watsar... Sandarsa da yake dogarawa ya kama sannan ya mik'e tsaye yana kuma duban Nasaar dake zaune gabansa kana yace "Nasaar na yarda dakai d'ari bisa d'ari kuma nasan bazaka failing d'ina ba....." Dattijo d'an kimanin shekaru 70 a duniya ya fad'i yana duban Nasaar d'in... *SameenaAleeyou📚* [12/26, 12:44 AM] ‪+234 810 044 6653‬: *FUSKA UKU*🏮 *14* *©Sameena Aleeyou...✍🏽* K'uri ya mata babu ko k'yafta idanu yanda take kan faman murmushi, shid'inma murmushi ne kwance saman kyakkyawar fuskarsa... Asma'u ta tsargu da kalan kallon da Junaid ke faman binta dashi.... D'an ware idanunta tayi kana tace "Ya dai...?" Junaid ya kuma murmusawa had'i da girgiza kai kana yace "Has anyone ever told you that you are so beautiful... and especially when you smile....?" Ya k'arashe kannennun idanunsa akanta.... Murmusawa ta kuma yi had'i da rufe fuskarta da tafukan hannu tace "You so funny you know.... Now is your turn ka bani labarinka kafin su soma nemanmu a ciki...." Junaid ya d'an gyara zamansa kana yace "Would it be OK if I start calling you Beautiful...?" Kallonsa tayi yanda yayi maganar da iyaka gaskiyansa kana ta sadda kanta k'asa... Ganin tayi shiru tamkar mai tunani ya sanyasa matso da kekensa kusanta sosai kana ya d'an sassauta murya "Asmah...!" Bata d'ago ta dubesa ba bata amsa sa ba, kwantar da murya ya kuma kaman mai son yin rad'a... "Asmah I'm sorry idan bakiji dad'in maganata ba, and I promise bazan sake ba kinji, amma ko baki k'yaleni na kiraki da Beautiful a baki ba... In my heart zan ci gaba da kiranki Beautiful...." Wani irin yanayi takeji wanda bata tab'a tsintar kanta ciki ba, jin muryarsa take yana ratsa duk wani sassa na jikinta, ji take tamkar a wata duniyar ta daban suke..... Junaid na hankalce da ita, shikansa yasan plans dinsa suna tafiya yanda ya kamata.. D'an gyaran murya yayi kafin yaci gaba da fad'in "Asmah labarinki yayi shige da nawa, nima na rasa iyayena duka saidai ni banida wasu relatives a k'asar nan sabida iyayena ba 'yan k'asar nan bane, I was very young when my parents passed away... Ban san kowa nasu ba, koda na tafi k'asarsu ban san ta yanda zan soma neman danginsu ba.... I've no family... I'm all alone...." Ya k'arashe cikin siga na tsananin tausayawa... Tunda ya soma magana take dubansa tausayinsa na ratsa b'argo da tsokarta.... Hannu tasa ta d'an goge hawayen da suka zubo mata kana tace "Allah sarki, labarinka yafi nawa abin tausayi sabida ni ko babu iyayena inada 'yan uwana wad'anda suke matuk'ar k'aunata.... Allah ya gafarta wa mahaifanmu baki d'aya, and insha Allah wata rana zaka sami danginka....." Ta k'arashe murmushi saman fuskarta.... Junaid ya amsa mata da ameen yana mai hango fuskar Siraj a tattareda Asma'u, tabbas ji yake kaman ya shak'eta a wajen ya k'untatawa Siraj kaman yanda ya k'untata masa amma dole yabi komai a sannu muddin yana son cimma burinsa..... *** Zaune yake a Office d'in nashi yayi k'uri ma hotonta cikin wayarsa, shi kansa ya soma tsoron kansa, ya soma yarda da batun Ayiya, toh ko dai da gaske aljanarce ta auresa, but how could that be possible... No..no baiso yasa ma ransa da gaske haka d'inne, zaici gaba da addu'a mahaifiyarsa tana tayasa, idanma wani abu ne ke faruwa da rayuwarshi koda a b'oyene Allah ya bayyanar masa... Saidai ya d'au alwashi ma kansa bazai kuma neman wata mace ba tsoron kada ya jefa rayuwarta cikin had'ari.... A hankali ya sauk'e ajiyan zuciya kana ya furta "Allah ya maki rahama Nadiya....." K'aran da wayar talho d'in dake gefensa yayi ne ya sanyasa dawowa daga duniyar tunanin da ya tafi, a hankali ya d'aga wayar had'i da k'arawa a kunnensa... "Yes Janet....." D'an dafe goshinsa yayi yana mai sauraron sakatariyan nasa kana yace "OK, send him in please....." Daga haka ajiye wayar yayi jim kad'an Nasaar ya shigo office d'in.... Cikin sauri Nasaar ya k'araso had'i da mik'awa Siraj hannu sukai masabaha lokaci guda suke gaisawa kana Siraj ya nunawa Nasaar kujera yana fad'in "Please seat Attorney...." Nasaar ya zauna yanaima Siraj godiya..... Gaisuwan ta'aziya Nasaar ya kuma yima Siraj da rashin da aka masa kafin ya sako masa wani zancen wanda ya shafi kasuwancin su.... Siraj ya d'auko wata jarida dake gefen table d'insa yana nunawa Nasaar yake fad'in "Naga an saka wad'anan estates d'in a kasuwa...." Nasaar ya matso sosai yana kallon estates d'in kana yace "Yeah na gani nima a wasu jaridun...." Siraj ya jinjina kai kana yace "I think I'm interested, get contact with the owner as soon as possible, and keep me posted.... Nayita neman wayan Lamid'o bai shiga amma tunda kazo shikenan....." Nasaar ya jinjina kai kana yace "OK sir, right away..." Ya k'arashe yana k'ok'arin mik'ewa had'ida sallama wa Siraj... Har ya kai k'ofa Siraj ya kira sunansa, dawowa da baya Nasaar yayi yana sauraren Siraj d'in cikeda rusunawa.... Siraj yaci gaba da fad'in "About that girl.... Yarinyar da kake nema mata aiki, k'anwar matarka...." Nasaar ya murmusa cikeda jin dad'i kana yace "Ai Sir tunda naga kwana biyun nan kaima baka zauna ba sannan ga rashi da aka maka shiyasa kawai na bar maganar zuwa wani lokacin..." Siraj ya jinjina kai kana yace "Haka ne,.... Babu damuwa kana iya zuwa da ita gobe insha Allah...." Nasaar da murmushin sa ya k'aru cikeda farin ciki yace "Really Sir..... Thank you Sir.... I'm forever grateful.... Na gode Sir...." Murmushi kawai Siraj keyi kana yace "You've always been at good service to this company.... And this is the least I can do.... Besides kanada amana Nasaar so I'm quite sure duk wanda zaka kawo companyn nan mai amana irinka ne...." Nasaar ya kuma masa godiya cikeda jin dad'in irin yarda da Siraj yayi dashi...... *** Lamid'o na shigowa gidan ya hangi Malam Sile zai tafi d'auko Nana A daga foundation... Cikin sauri ya fito daga motarsa ya nufi Malam Sile nan yake sanar dashi zai tafi d'auko Nana Asma'u ne lokacin tashinta yayi, "Malam Sile ka barshi kawai ni zan d'aukota...." Cewar Lamid'o Kallon mamaki Malam Sile ya bisa dashi kana yace "A'a rankashidad'e kar ka damu aiki na nake...." Lamid'o ya murmusa kana yace "Kar ka damu ni na saka kaina...." Dai-dai lokacin Ayiya ta k'araso tana gyara mayafinta take fad'iwa Malam Sile ta fito.... Ganin Lamid'o wajen ya sanyata fad'ad'a murmushinta suka shiga gaisawa, nan Malam Sile ke sanar da ita buk'atar Lamid'o... Ayiya ta dubi Lamido da murmushi tace "Anya kuwa Sarki zaka kula min da d'iyata har ka kawota gida...." Lamido na murmushi yake jinjina kai kana yace "Insha Allah Ayiyarmu nayi alk'awarin kawo maki d'iyarki har gida sound and safe...." Murmushi saman fuskarta take jinjina kai tana hango wani Al'amari idanun Sarki kaman yanda take kiran Lamido kana tace "Toh shikenan tunda kace haka, barin koma ciki na had'a maku sauk'a mai kyau kafin ku iso...." Murmushi fal fuskar Lamido yake sunne kai yana fad'in "Yauwa Ayiyarmu... Idan na dawo akwai maganar da nakeso muyi...." Ayiya ta amsa masa tana mai jinjina kai zuciyarta fari k'al hasashenta ya kusa tabbata.... Daga yanda take tsaye jikin window tana hangosu murmushi take har Lamid'o ya fice, cikin zuciyarta taci gaba da raya abubuwa da dama, lokaci guda ta sauk'e labulen ta shiga dialing layin mijinta taji ko ya sauk'a lafia..... *** Suna haraban foundation d'in yana jira azo d'aukanta kafin ya tafi yayinda sauran ma'aikatam wajen keta masu sallama suna tafiya, idan ka gansu dole su baka sha'awa yanda suke cikin farin ciki,.... Nan suka hangi wata bak'ar Mercedes ta danno cikin foundation d'in.... Junaid ya dubeta da murmushi saman fuskar sa kana yace "Seems your driver is here.... Zanyi kewarki kafin gobe Asmah...." Mamakin motar da ta gani ya hanata amsa maganar Junaid, da gaske motar Uncle Lamido take hangowa na shigowa cikin foundation d'in.... Junaid ya bita da kallo yanda take kallon motar.... A hankali shima ya maida dubansa ga motar, lokaci guda jijiyoyinsa jikinsa suka mimmik'e sake arba da yayi da d'aya daga cikin FUSKA UKU wad'anda yafi tsana fiyeda komai a rayuwarsa, Ji yake tamkar yayi tsalle ya shak'esa sanda ya hangesa ya nufosu murmushi saman fuskarsa.... Nana A da murmushi ta nufi Lamido don tarbansa.... "Uncle L yau kaine a foundation d'in namu, da ka sanar dani kana tafe da an shirya maka wani abin, gashi lokacin tashi yayi mutanen namu duk sun tafi, sannu da zuwa Uncle...." Murmushi Lamido keyi yana dubanta yanda take burgesa komai nata a nitse, "Toh Nana mu gaisa first mana, besides ni zuwa d'aukan princess nayi ba ziyara na kawo ba, idan princess tai min izini mu k'arasa na bud'e mata marfin mota sabida Ayiya na gida na had'a mata delectable meal...." Murmushi tai tana dubansa lokaci guda kunyarsa ya rufeta... Murmushin shima yake kana yace "So shall we...?" Jinjina masa kai tayi tana gyara zaman side back d'inta, cikin sauri Lamid'o ya k'arasa ya nufi motar don matso mata dashi kusa... Sai lokacin Nana A ta juya ga Junaid wanda ta barsa zaune nan wajen, saidai ga mamakinta babu Junaid a wajen, d'an lellek'awa tayi taga dai da gaske baya wajen... Murmushi kawai ta d'anyi had'ida girgiza kai don tasan Junaid mutum ne da baison mutane sosai.... Lamido da kansa ya bude mata marfin mota, sai faman treating d'inta yake tamkar sarauniya, abin har ya d'an baiwa Nana A mamaki, is awkward yanda yake bata wani sabon kulawa... Saida ya biya store ya mata shopping dukda tak'i amsa, abin sai yana mata wani iri haka nan... Koda ta masa maganar bata son shopping d'in sai cewa yayi ai bazata fad'awa Siraj haka ba, kuma idan ta d'aukesa dai-dai da Siraj ya kamata ta amshi kyautar sa.... Da wad'annan dalilai Lamido ya kashe bakin Nana A har suka iso gida.... Suna isowa Motar Siraj na shigowa, Nana H dake mak'ale a window saurin fitowa tayi ta nufi Siraj dake k'ok'arin fitowa daga motarsa, tsalle tayi ta rungumesa tanai masa sannu da dawowa... Lamido ya bita da mugun kallo yayinda Nana A ta fadada murmushinta ta nufi kawun nata da 'yar uwarta, sam Lamido baison zaman Nana H a gidan gashi yanzu dole ta zauna tunda mijinta baya nan, tsaki yayi cikin ransa suna aika ma juna muggan kallo su biyun... "Sweetheart ya Heedj ya isa lafia, nayita trying layinsa but I couldn't reach him..." Siraj ya fad'i yana rik'eda Nana H gefen k'irjinsa... Mak'alewa cikin jikinsa ta kumayi tana zuba masa shagwab'a, Siraj ya mik'a d'aya hannunsa ya kamo Nana A suna gaisawa da Lamido dake rik'eda shopping bags... Kallon munada magana Siraj yayiwa Lamido kafin ya dubi Nana A yace "Sweetheart ya foundation din naku hope komai na tafiya normal...?" Cikeda jin dad'i tace dashi "Komai lafiya Uncle, ina jin dad'i sosai..." Siraj ya murmusa kana yace "Glad to hear that...." Wani irin haushi ne ya tokari Nana H ganin yanda kowa keson farantawa Nana A, wai meke shirin faruwa ne, ta lura Uncle nason baiwa Nana A matsayi dai-dai da nata cikin zuciyarsa, dole tasan abinyi right away.... Lamido bai bar gidan ba har saida sukayi dinner, kowa ya fahimci Lamido courting Nana A yake, da alama sauran jama'an gidan sunyi na'am idan ka cire Siraj... Sanda Lamido ya mike don masu sallama Siraj yabi bayansa.... Har Lamido yakai k'ofa ya jiyo muryar Siraj a bayansa... "You and I need to talk...." Siraj ya fad'i babu alamun wasa a tattaredashi... Murmushi Lamido yayi kana yace "OK Uncle...." Murmushi Siraj yayi kana yace "Uncle? Not yet, let's talk at my study...." Babu musu Lamido ya take masa baya... "Lamido kasan na sanka, farar sani, nasan kalan neman matanka, wannan dalili yasa bazan bari ka nemi niece d'ita ba, cos you'll end up hurting her.... Don't even start Lamido....." Murmusawa Lamido yayi yana zaran pens dake ajiye cikin d'an cup saman table a study d'in kana yace "Siraj I love your niece so much, my intentions for her are pure, please Siraj let me court her..." Kallonsa Siraj yayi babu ko k'yafta idanu kana ya girgiza kai yace "Lamido kar mu fara abinda zai janyo mana sab'ani, you're like a brother to me, Nana A is my niece.... I love you both and I don't wanna lose either of you..... Please try to understand me, I'm only trying to protect my niece.... "Na fahimceka Siraj sannan zan tabbatar maka bazan tab'a cutar da niece d'inka ba, and I'm the right man for her., have a good evening..." yana ida fad'in haka ya nufi k'ofa... Nana H dake mak'ale tana saurarensu cikin sauri ta bar wajen zuciyarta na mata wani irin dad'i *** Dariya Dattijon ya fashe dashi yana duban Nasaar kana ya shiga bubbuga sandar hannunsa jikin center table yake fad'in "Very well.... Da kyau Nasaar, yanzu na yarda zaka kawo min Laushi group har hannuna har d'akin baccina..... I want to see him dead.... Dole ya mutu bayan na mallaki kamfanin kaman yanda mahaifinsa da wansa suka mutu...." Ya kuma yin wata murmushi cikin muryarsa da tsufa ya kama cikin zuciyarsa yaci gaba da fad'in _Mas'ud ka mutu ka bar baya da k'ura.... Zan ci gaba da azabtar da zuri'arka ta fuskoki daban-daban._ Murmusawa ya kumayi kana yaci gaba da zancen zucin _Hajiya Mairo baki aureni ba zan auri jikarki wacce kike mafarkin sake gani a rayuwarki,.... Ba'a fad'a da Bulama a zauna lafia... Har wad'anda basuzo ba a zuri'arka sai ya shafa Mas'ud..._ Yana ida zancen zucinsa suka ci gaba da tattaunawa da Nasaar Nasaar na ficewa da kad'an Lamid'o ya shigo gidan, da k'yar gurds suka barsa ya shigo parlorn.... Alhaji Bulama na zaune saman kujeransa na alfarma Lamido ya k'araso yana huci sosai.... Murmushin bosawa Alhaji Bulama yayi kana yace "Mai ya kawo ka nan, na d'auka na maka iyaka da nan gidan har sai ranar da ka cika min burina, you're worthless.." Lamid'o na huci sosai yake duban Alhaji Bulama yana fad'in "BABA I might be worthless amma ka sani bazan tab'a yin abinda kake umarta na ba, zanyi komai to ruin Siraj but I can't kill him, bazan iya kasheshi ba....." Tsawa Alhaji Bulama ya daka masa kana yaci gaba da fad'in "Kar sake kirana Baba na fad'a maka, zaka ci gaba da kirana Sir har sai ranar daka cika min burina, shashasha kawai k'aton banza, ni banma ga amfaninka a kamfanin ba, kana nan kana bin ko wata mace kaman matashin bunsuru... Tashi ka fice min daga gida kar ka sake dawowa idan ba ni na nemeka ba...." Ya k'arashe cikin tsananin daka tsawa lokaci guda yake dungurin Lamid'o da sandarsa ta dogarawa... Mik'ewa Lamid'o yayi cikin wani irin huci ya fice daga gidan, duniyar tai masa zafi, baima sami zarafin yin maganar da ya kaisa wajen Baban nasa ba .... *** *Misau* Duhu ya somayi sosai sanda ya shigo garin, babu wani abunda ya canza a garin sosai hakan yasa bai mance hanyar gidan mahaifin nasa ba.... Tunda ta dawo gidan Innah aka hanata fita ko wace iri saiko islamiya, yau tunda aka tashi ta mak'ale gidansu Hurera ta sami hallon talabijin, duba agogon bangonsu Hurera tayi taga lokaci yaja sosai tasan Innah zata nemeta kuma zata mata fad'a.... Cikin Deejoh ya bada sautin tsoro domin sam bata k'aunar ta b'atawa Innah... "Hurera dan Allah rakani hanya..." Ta fad'i idanunta sunyi rau-rau "Cab kema dai Deejoh da neman fitina kike sarai kinsan lungun nan baida kyau kika zo kika b'ige da zama abinki, na fita da daren nan Ya Munkaila targad'ani zaiyi don ya hanani fita bayan makarantar dare..." Deejoh tazo wuya ganin gidansu Hure tazo amma take mata wulak'anci, cikeda masifa take fad'in "Toh karma ki rakani din mana sai me, don kinga nazo kallo gidanku koh, wllhi bazan sake zuwa gidanku ba, wake jin tsoron hanya kada ma ki rakani.... Kiyi zamanki banson rakiyar...." Ta k'arashe tana zura hijab d'inta cikin fushi ta suri jakarta, Hure na biye tana bata hak'uri inaa Deejoh tayi zuciya ta fice.. Sai zuba sauri take cikeda tsoron hanya yanda gari yayi duhu *SameenaAleeyou📚* [12/26, 8:15 AM] ‪+234 810 044 6653‬: *FUSKA UKU*🏮 *13* *©Sameena Aleeyou...✍🏽* Mik'ewa tsaye Nasaar yayi yana gyara zaman suit d'insa kafin ya d'anyi gyaran murya "Alhaji I thought very well kafin na yarda zan taimakawa Junaid... Besides shi kansa Junaid k'ok'ari yake yaga Laushi's on the ground... So I assure you zamu had'a team mai kyau da taimakon Junaid...." K'uri ya masa yana dubansa kafin ya k'arasa saman kujerar ta alfarma ya zauna lokaci guda ya shiga jinjina kai kana yace "Very well, I'm glad to hear that.... I know I can always count on you Attorney...." Mik'ewa Nasaar yayi had'ida saita suit d'insa kana ya d'an rusuna yace "I'll go ahead Sir..." Dattijon bubbuga sandar dake hannunsa yayi saman k'aton wooden center table dake gabansa ba tareda ya furta komai ba... Lokaci guda Nasaar ya fice daga parlorn bayan wasu tirk'a-tirk'an guards sun bud'e masa k'ofar.... *** Likita ne ya fito daga d'akin tiyatan yana zare rufin bakinsa da hancinsa, gaba d'aya suka nufesa hankali tashe.... Rasa abin fad'a masu yayi, ya dubesu gaba d'aya kana yace "Ina mahaifinta...?" Cikin sauri mahaifiyar Nadiya tace "Ni ce mahaifiyarta, mahaifinta baya k'asa yayi tafiya..." Jinjina kai likita yayi kana yace "Can.... I.... have a word with you..." Ai jin haka ya sanya mahaifiyar sakin k'ara tana girgiza kai take fad'in "Mai ya sami d'iyata Doctor pls tell me... Ka sanar dani....." Sosai Ammah ta rik'eta tana lallashi hawaye na bin k'uncinta itama... Siraj ne ya k'araso gareshi kana ya d'an janyo likitan yana fad'in "I'm her fiancee zaka iya fad'a min komai..." Jinjina masa kai likitan yayi suka soma tafiya lokaci guda Lamid'o ya take masu baya.... Dubansu Dr yayi yanda sukayi cirko-cirko kana yace "Kuyi hak'uri...munyi iyaka k'ok'arinmu..." Baikai aya ba Siraj ya mik'e yana hawaye.... Tuni jikinsa ya basa Nadiya ma tafiya zatayi ta barsa... Wannan wace irin k'addara ce ta rayuwa.... Innalillahi wa Inna'ilaihirraji'un.... Baisan lokacin da yayi bursting cikin kuka sosai ba.... Lamid'o yayi saurin k'arasawa ya rungume abokinsa ya shiga basa baki.... K'irjin Lamid'o sai bugu yake yasan hakan ka iya faruwa.... Shi kansa Lamid'o baisan Siraj ya kamu da soyayyar Nadiya a d'an k'ank'anin lokacin ba har haka.... Yanda suka hangosu suna fitowa daga office d'in Dr ya tabbatar masu wani abu ya faru.... Ganin Siraj na kuks shar-shar Lamid'o ya rik'osa yasa su fahimtar Nadiya babu.... Wani irin k'ara mahaifiyarta ta saki had'i da zubewa k'asa... A guje Nana H ta k'araso ga Siraj suka rungume juna suna kuka sosai... Nana A kuwa juyawa tayi ga Ayiya ta rungume tana kuka sosai itama... Kallo Lamid'o yabi Nana A dashi wani irin al'amari yake ji gameda ita, bai tab'a jin hakan ga wata d'iya mace ba... Ji yake kaman ya k'arasa ya rungumeta cikin jikinsa sabida har cikin ransa yake jin zafin kukan nata... Shin mai ke shirin faruwa dashi? Shin son Nana A yake ko me.....? K'aran da wayarsa yayi ya sanyasa dawowa hayyacin sa.... Ganin mai kira ya sanyasa ficewa daga wajen domin amsa kiran.... *** *Misau* Zaune suke gaba d'aya a fadar Mai Unguwan ana maida bayani... Mai Unguwa yaji komai kuma ya gamsu da komai domin ciwon dake jikin Deejo kawai ya isa shaida Gaje bata isa ta musa cewa bata musgunawa Deejoh ba..... Mai Unguwa iyaka yayi wa Gaje tsakaninta da Deejoh ya kuma tabbatar idan ya kuma jin tayiwa Deejoh wani abin toh gaban sarki zasu tafi.... Gaje kaman mutuniyar arziki sai jinjina kai take tana fad'in babu abinda zai kuma faruwa..... Innah dai duban Gaje kawai take yanda take rantse-rantse bazata kuma musgunawa Deejoh ba tsoron kada akaita gaban sarki amma kam tasan wannan k'aryace Gaje bazata tab'a k'yale Deejoh ba... Bayan Mai Unguwa ya sallami matan Malam Sanda mahaifin Ahidjo ya gyara zamansa kana ya soma fad'in "Allah gafarta dama wani hanzari ba gudu ba.... Wannan mata kaman yanda kowa ya sani a garin nan tafi k'arfin Malam Ard'o bashida cewa a gidansa sai abinda tace.... Kuma Allah gafarta yanda ta gama rantse rantsen nan a nan zaiyi wuya ta aiwatar da abinda tace zata aiwatar.... Allah gafarta idan Malam Ard'o zai amince zan nemawa d'ana Ahidjo auren Deejoh....." Murmushin dake bisa fuskar Malam Ard'o ya kasa gushewa shikam hakan sai yafi masa sabida yasan d'iyarsa ta tsira muddin ta fita daga hannun Gaje... Muryar mai unguwa ne ya katsewa Malam Ard'o tunanin da yake..... "Anya kuwa Malam Sanda, shin yaron nan naka bashine akace ka sallamasa wa bariki ba, shin baka tunanin wannan yaro naka bazai amince da auren da zaka masa ba.... Sannan idan akayiwa Deejoh haka ba tareda amincewarta ba kaman an shiga hakkinta....." Malam Ard'o ne ya katse Mai Unguwa da fad'in "Allah shi taimakeka ni wllhi yafi min, Deejoh ta auri koma waye ta rabuda uk'uba na Gaje yafiye min wllhi,... Ni zanfi farin ciki ma Allah shi taimakeka...." Gyara zama mai Unguwa yayi kana yace "Toh Alhamdulillahi tinda an sami fahimta daga b'angare biyun.... Kuyi duk wasu shirye-shirye da zakuyi ni nan zan saka rana...." "Allah shi gafarta ban tari numfashinka ba amma da sadakin d'ana nake tafe idan babu damuwa ga Malam Mudi da Malam D'alha gaka nan cikon na uku kun isa shaidu, inaga a d'aura auren yanzu kawai yarinyar ta fita hannun azzalumar matar nan ta huta...." Cikin sauri Malam Ard'o ya shiga jinjina kai yana fad'in "Wannan gaskiya ne, domin yau nasan Gaje kwana zatayi tana dukan Deejoh ta musamman da aka kawota k'ara, ni kaina nasan yau da k'yar zansha a hannunta...." Cikeda tausayawa suke jinjina al'amarin gidan Malam Ard'o ... Mai Unguwa ya jinjina kai kana yace "Shikenan babu damuwa shaidu sun cika Malam Sanda ka gabatar da sadakin d'anka sharud'an aure ya cika...." Cikin sauri Malam Sanda ya gyara zamansa had'i da zaro kud'ad'en da ya taho dasu daga kasuwa dama yau 'yan rance sun biyasa.... A k'ofar gidan Mai Unguwa aka d'aura auren Aliyu da Khadijah kan sadaki naira dubu ashirin lakadan ba ajalan ba..... *** Gaba d'aya gidansu Nadiya suka nufa kan kace mai dangi da abokan arziki sun cika gidan, Allah sarki Nadiya shikenan an rufe nata chapter d'in ta zama tarihi cikin k'ank'anin lokaci, 'yan uwa muji tsoron Allah mu shuka khairan A DUNIYAR MU.... Yau dai Nana H harda su saka hijabi kaman ba ita ba, kana ganin zaman hijab d'in a jikinta kasan bata saba sakawa ba, yanda ta koma sukuku da ita zai tabbatar maka mutuwar ta shigeta.... Ahidjo da Lamid'o suna tareda Siraj wajen makokin maza yanda aka kafa manyan runfuna a farfajiyan gidan, gaban Ahidjo haka kurum ya dinga fad'uwa, gaba d'aya mutuwan Nadiya ya shiga jikkunansu, tunanin iyayensa ya shiga zarya a kwanyarsa, haka kurum yaji yana so yaje gida ya duba iyayensa da zaran an gama zaman ukun Nadiya.... *** Deejoh na zaune tsakar gida tana wanke-wanke wa Gaje dukda k'unan dake hannunta , Gaje na daga gefe tana 'yan wak'e wak'enta tana auna kalan cin uwar Deejoh da zatayi, kai yau a bulus zata kaitawa Lado suyi abinda sukaga dama da ita shida 'yan dabansa su Muntala, wllhi ko babu asi yau saita sallama masu 'yar banza shegiyar yarinya mai idanu uwa ta mujiya, baka hango komai a fuskar sai idanu da d'an k'aramin bakin munaduncin... Tayi k'wafa tana mai ci gaba da rigar geronta.... Kaman daga sama suka jiyo muryan mutane suna sallama, ganin Hajiya Uwa ce matar Mai Unguwa ya sanya Gaje mik'ewa tana washe baki had'ida goge ruwan hannunta jikin zani take fad'in "A'ah lale lale,.... Hajiya yau kece gidan namu, kai barka da zuwa.... Lale marhaban....." Ta k'arashe tana baza masu tabarma.... Deejoh kam baki sake ta bar wanke-wanken da take ta shiga bin su Hajiya Uwa da kallo... Tsawa Gaje ta daka mata tana fad'in "Toh mayya kin zuba masu ta mujiya salon suje su k'ware... Zaki tashi a wajen ko kuwa.....?" Deejoh jiki har na rawa ta mik'e a wajen... Su Hajiya Uwa suka bita da kallon tausayi.... Lokaci guda Hajiya Marka kishiyar Hajiya Uwa ta gyara zama tana duban Gaje tace "Aima ba zama mukazo yiba, amarya muka zo d'auka....." Kaman daga sama Gaje taji batun, ajiye kwanun sha na ruwa data kawo masu tayi kana tace "Na'am Hajiya mai kika ce? Amarya amrya kuma a nan gidan.....? Kai k'ila dai mak'ota ne ba nan ba...." Hajiya Uwa ta gyara murya tace "A'a ba nan bane gidan Malam Ard'o mahaifin Deejoh.....?" Murya na rawa Gaje take jinjina kai tana fad'in "Iiii eh k'warai kuwa nan ne... Amma gidan nan babu amarya...." Uwa ta murmusa kana tace "K'warai kuwa akwai amarya a gidan nan yanzu haka ita mukazo d'auka zamu tafi da ita...." Gaje fah taga rainin hankalin nasu yayi yawa mik'ewa tsaye tayi tana gyara d'aurin zani take fad'in "Toh annamimai munafukai sa idinawa masu bacci da ido guda, ku tashi maza a tashi a bar min gida bana son munafuncin banza munafuncin wofi a gida uwar wa kukaga amaryar mutane da shegen munafunci da saka idanu a rayuwar wasu... Maza a tashi a fice min a gida ehe..." Ta k'arashe tana cin d'amara uwa 'yar dambe.. Mik'ewa Marka tayi had'i da kwab'e mayafinta kana tace "Badai fad'a kikeso ba, toh bisimillah kinzo gidanta, dai-dai da kutirinki nake barin fad'a maki,.... Wllhi yanzu sai na lallasa maki duka a wajen nan...." Hajiya Uwa ta mik'e tsaye ta rik'e 'yar uwarta tana fad'in "A'a Marka kar ki biyeta mu aiwatar da abinda mijin mu ya turo mu muyi gaba kinsan sanyi ya kad'a marassa lafiyan kwanya dole yayita motsawa ba laifinta bane...." Haba nan fah Gaje ta kuma hawa.... "Yo har ni za'azo har cikin gidana ayimin bariki, wai ku ga masu zaman lafiya ko... Munafukai ai babu zaman lafiya tsakanin kishiyoyi sai na munafunci.... Ku fita kafin ranku ya b'aci, wayema zai auri Deejoh banda munafunci irin naku...." "Billahillazi Yaya ki barni na watsarwa matar nan hak'wara, ta k'arashi rashin kunyarta akaina amma Allah koda wasa kada ta kuskura ta maki, banza kin zaci ko wace Mace jakace irinki, mai kishin jahilci da d'iyar cikinki..." Gaje ta kuma hayayyak'a.... Deejoh dake mak'ale bayan k'ofa ta gama jin komai kukanta ya k'aru..... Innalillahi shikenan waye Baffanta ya aura mata, mai ya kawo matan Baba mai Unguwa gidansu...? Toh wai da gaske aure aka mata, aure da wane...? Kukanta ya tsananta saidai da ta tuna zata rabu da kurkukun Innah Gaje sai taji sanyi cikin zuciyarta, ko kuturu ne ko makaho ne ya fiye mata zama gaban Iya Gaje.... Marka bata kuma bin takan Gaje ba ta shige d'aki ta janyo Deejoh dake kuka sosai.... Shigowar Mai Unguwa da Malam Ard'o ya sanya Gaje shiga hankalinta.... Tabbas da gaske dai aure akayiwa Deejoh babu saninta, kururuwa ta dinga kurmawa tana fad'in Malam Ard'o ya cuceta don yaga ba ita ta haifi Deejoh ba shiyasa ya mata haka.... Kai tsaye gidan Mai Unguwa aka wuce da Deejoh dake kuka sosai, Kintsata Marka tayi ta dinga lallashinta tana sanar da ita ta kwantar da hankalinta mijinta ma ba mazaunin gari bane, kuma bazama ta gansa nan kusa ba balle hankalinta ya tashi, kawai dai anyi auren ne don a rabata da ukuban da take fuskanta na matar Uba... Da wannan batu na Innah Marka ya sanya hankalin Deejoh d'an kwanciya... Da shike akwai k'awarta Haule 'yar islamiyarsu d'iyar Marka amaryar Mai Unguwa a gidan sai ta d'an sake sukayita hira da Haule.... Da yamma lis Marka da Uwa suka d'auki Deejoh suka kaita gidan Baffah Sanda, Deejoh kam sai mamaki take ganin ba'a kaita gidan wani miji ba sai gidan Innar ta k'ila dai dama babu wani auren da aka mata, an dai rabata ne da Innah Gaje... Allah sarki Deejoh ji tayi kaman an tsundumata a Aljannah gata gidan Innarta babu damuwan Gaje..... *** Kallonta yayi cikin idanu kana ya girgiza kai "You know Nana H you're impossible.... How could you do that... Meyasa...." Katse sa tayi da fad'in "Stop acting like you care... Kar ka manta na fad'a maka Uncle Siraj is mine... He's mine, ni kad'aina ... And who ever try to get in my way..... I'll get rid of him in every possible way I can ko shi waye...." Matsowa dab da ita yayi had'i da kamo k'ugunta ya matseta sosai cikin jikinsa kana ya soma fad'in "Hafsat don't you dare hurt your sister.... Kar ki cutar da Nana A I beg of you..." Murmusawa ta kuma yi tana dubansa kana tace "Really.... Meye had'inka da 'yar uwata don't tell me kaima ta siye zuciyarka da salihancin nata.... Oh'o 'o h Darling I don't get you.... What are you trying to say...?" Fuskarta ya d'ago suna duban cikin idanun juna yake fad'in "I love your Sister Nana H.... I love her so much, and I'm ready to build my own family with her....." Dariyan rainin hankali ta fashe dashi kana tace " You're deluding yourself here darling, na lura tun ranar da aka bud'e foundation d'inta kake binta da mayen kallo..." tayi wani murmushi kana taci gaba da fad'in "Nayi mata kwalliya irin nawa shiyasa kake ganinta tamkar ni, nasan idan ka sami chance na kashe mijina zaka kashe shi for us to be together..... Lamid'o you love me... I know you does..." Ta k'arashe tana kuma shafan fuskar sa... B'anb'areta yayi daga jikinsa kana yaci gaba da fad'in "Look Nana H I know we made alot of mistakes in the past... Na cutar da abokina nabi matarsa sannan na cutar da d'aya abokina nabi niece d'insa da aurenta.... But.... things are different now, dan Allah na rok'ek'i mu mance duk abinda ya faru a baya wllhi I'm serious I love Nana A... I love her so much.....kin fahimta....?" Ya k'arashe yana duban cikin idanunta... Cikeda mamaki take dubansa kafin ta soma girgiza kai tana fad'in "You gone insane Lamid'o, you're unbelievable.... After all that had happened between us, kana tunanin zan bari ka auri 'yar uwata...? Lallai kayi hauka... Wllhi kayi hauka Lamid'o, wllhi baka isa ka auri wata mace ba alhalin ina raye...." Kallonta yake yanda take faman huci kafin ya kwashe da dariya yana mai dubanta, lokaci guda ya saita kansa kana ya soma fad'in "Kar kiyi tunanin zan biki da lallama, bari kiji na fad'a maki ni ba Siraj bane sannan ni ba Ahidjo bane.... Tsakanin FUSKA UKU bakisan wa kike so ba, you're so selfish, kin raba Ahidjo da danginsa kin hana Siraj aure sannan kina tunanin ni Lamid'o zaki min abinda kika masu ne....?" Yayi wata murmushi kana yaci gaba da fad'in "Nafi k'arfinki wllhi kuma idan ina numfashi sai na auri Nana A saidai ki mutu randa kika ganta a gidana a d'akina muna shan soyayya and there's absolutely nothing you can do about it darling...." Murmusawa tayi tana dubansa kana ta janyo necktie d'insa fuskokinsu dab da juna take fad'in "I like to mess with other people, that's my personality.... Allah baka sa'a gaka ga Nana A...." Tana ida fad'in haka ta suri handbag d'inta ta shiga taku tana kwarkwasa ta bar masa gidan.... Kallo ya bita dashi had'ida fuzar da iska, bazai bari Nana H ta hanasa samun farin cikinsa Asma'u ba, he would do everything in his power to stop her.... Da wannan tunanin ya mik'e ya nufi kitchen d'insa don samawa kansa abinci.... *** Kallo tabi Ahidjo dashi sai faman shirya kayansa yake cikin jaka, a hankali ta k'araso ta rungumesa ta baya idanunta sunyi rau-rau "Sweet da gaske tafiya zakayi, toh yaushe zaka dawo? Kasan bazan iya jure rashinka ba...." Juyo da ita yayi suna fuskantar juna kafin ya masu masauk'i saman gadon, fuskarta ya d'ago ya shiga share mata hawayenta kana yace "Sweet I promise bazan jima ba, besides tafiyar nan daga office ne badon haka ba da bazan yita ba.... Hafsat ko ina naje always remember that you are here in my heart..." Ya k'arashe yana nuni da k'irjinsa... A hankali ta furta "I love you my Detective..." Rungumeta yayi cikin jikinsa had'ida lumshe idanu kafin shima ya furta "I love you too Sweet...." Shirya kayan da ba'a k'arasa ba suka lula duniyar ma'arauta... *** Tafe suke cikin foundation d'in suna zazzagawa ko wani fanni suna gani, kama daga fannin masu koyan d'inki da masu koyon had'a takalma da dai sauransu... Nana A ita ke tura Junaid dake saman Kekensa, idan ka gansu sai sun burgeka yanda suke cikin farin ciki... Aunty Larai ta bisu da kallo fuskarta d'auke da murmushi, abotan Nana A da Junaid abin burgewa ne, lokacin sallah nayi zasu bar duk wani aikin dake gabansu su tafi sallah, duk yanda zasu zaga cikin foundation d'in tare suke zuwa, a d'an kwanaki biyun sabo ne sosai ya shiga tsakanin Nana da Junaid... Dai-dai k'asar wata bishiya ya d'ago yana dubanta fuskarsa d'aukeda murmushi kana yace "Aren't you tired... Ki tsaya mu huta a nan don nasan kin gaji da turani...." Murmusawa itama tayi kana tace "Kaman kuwa kasan na gaji... Kasan yanayin tafiyar tawa sai a hankali..." Murmushi Junaid ya kuma yi kana ya isa ya janyo mata kujera suka zauna k'ark'ashin bishiyan, dubanta yayi yana mai gyara zamansa cikin kekensa yake fad'in "Umhum ina saurarenki, kina bani labarinki...." Nana A ta murmusa "Haka ne ina baka labarina.. Inama na tsaya...?" Ta d'an murmusa had'ida sadda kai k'asa kana taci gaba da fad'in "Yauwa na tuna... Kana ji ba..." Jinjina kai kurum yayi yana dubanta babu ko k'yafta idanu sanda taci gaba da fad'in "Mu Uku Mummyn mu ta haife mu, Ni Nana Asma'u da kuma 'yan uwana guda biyu Nana Khadija da Nana Hafsat... A lokacin da aka haifemu anyi babban buki a family d'inmu, yara uku 'yan mata lokaci guda gashi mahaifiyarmu dama bata tab'a haihuwa ba wannan dalili yasa soyayyarmu yayi tasiri a zukatan kowa cikin danginmu, haka muka taso cikin soyayya tsakanin iyayenmu 'yan uwa da kuma abokan arziki.... A lokacin munada shekara uku mahaifinmu ya tattaremu gaba d'aya family d'insa harda Momyn mu, Daddy kaman yanda Ammah kakarmu ta bamu labari mutum ne da baya so wani driver yake tuk'asa, duk nisan waje haka yake zuwa babu driver dukda cewa a lokacin shi yake running Kampanin Kakan mu marigayi Mas'ud Laushi, Daddy bai ragewa Uncle Siraj komai ba, haka shima Uncle Siraj bai yarda da d'aukan driver ba, su kuma ra'ayinsu kenan.... A wannan tafiyar k'addara ta had'arin mota ya auka mana yanda motar Daddy ta kufce ta fad'a k'asan bridge.... A wannan had'arin motar muka rasa mahaifanmu gaba d'aya...." Hawaye suka zubo mata, lokaci guda Junaid ya mik'a mata handkerchief, ta dubesa had'ida k'ak'aro murmushi kana ta karb'i handkerchief d'in tana furta "Na gode..." Saida yayiwa iyayenta addu'an samun rahama ta d'an sami nutsuwa kana taci gaba da basa labari... "Daddy da Momy suka mace a wannan had'arin, muka rasa 'yar uwarmu guda d'aya Nana K wanda ko gawarta ba'a gani ba, hasalima ana tsammanin ruwa ne ya tafi da ita... Ni kuma Nana Asma'u kaji sanadin rasa k'afata guda da nayi... Nana Hafsat ce kawai bata sami ko k'warzani ba a wannan had'arin kaji ikon Allah...." shiru ya d'an biyo baya kafin taci gaba da fad'in "A haka muka taso mu biyu gaban Kakarmu Ammah da kuma Uncle d'inmu Siraj sai kuma Nanny d'inmu Ayiya wacce nake jinta tamkar uwa a gareni... I love her dearly, kaji tak'aitaccen tarihin Nana Asma'u....." Ta k'arashe kwantaccen murmushi saman fuskarta... *SameenaAleeyou📚*[12/28, 9:38 AM] ‪+234 802 741 0766‬: *FUSKA UKU*🏮 *15* *©Sameena Aleeyou...✍🏽* Daga nesa ta hango wasu samari zaune k'asar wata rumfa nan fah Deejoh ta k'ara sauri tana karanto duk addu'an da yazo bakinta, k'ila da tabi maganar Innah da ba haka ba, wayyo Innarta... Ire-iren abubuwan da ta rink'a tunowa kenan. Tsabagen tsoro ji tayi kaman sun mik'e sun nufota Ai a d'ari Deejoh ta kwab'e takalmanta ta rungumesu a hannu ta shiga falfala gudu da 'yan k'afafunta... Dai-dai bishiyar dake k'ofar gidan nasu yayi parking motarsa, ya d'aga kai yana kallon yanayin garin lokaci guda yaji murmushi na zuwa fuskarsa, haka kurum wani irin sanyi yaji zuciyarsa na masa, lokaci guda yaji burin sake ganin iyayensa ya k'aru cikin zuciyarsa... A hankali ya soma tafiya ya nufi zauren mahaifin nasa, cak ya tsaya cikin zauren yana k'arema wajen kallo yana tuna abubuwan da suka faru shekarun baya lokacin yana yaro kafin ya tafi karatu cikin yaran masu hannu da shuni har wani tunani ya gifta kwanyarsa, lokaci guda Ahidjo yaji jikinsa ya masa sanyi sosai, a hankali ya soma d'aga k'afafunsa da niyyar shiga cikin gidan saidai kafin ya sauk'e k'afa guda yaji an banko k'ofar zauren an shigo a guje... Kira kawai take k'wand'arawa Innah tana fad'in tazo ta ceceta saiji tayi ta fad'a jikin mutum... Gaba d'aya bata fahimci waye ta runguma ba itadai kawai nata tunanin Innah ce, sosai ta k'ank'anemasa tana tsalle tana "Innah ki rufe k'ofar wllhi su Lado ne dasu Muntala, Innah bazan sake maki taurin kunne ba wllhi bazan sake fita ba tareda izininki ba...." Duk wannan zuban da take bata saki Ahidjo ba wanda ya rasa abin fad'i ga duhu balle yaga wacece wannan yarinya iyakaci dai yayi tunanin k'ila gamo yayi... Tun daga bayin take jiyo ihun Deejoh tasan za'a rina hakan Deejoh gidan k'awaye ta wuce shiyasa bata dawo ba ga d'an karan tsoro, girgiza kai kurum Innah tayi ta nufi zauren tana fad'in "Wai dama ina kika tsaya ne, Deejoh bakijin magana, ina kike ki k'araso ki sameni yau nida ke ne...." Gaban Deejoh ya yanke ya fad'i jiyo muryar Innah daga cikin gida, toh waye wannan ta rik'e kodai Baffah ne, amma ai da ya mata magana, wayyo Allahn ta kodai su Lado ne suka biyota suka lab'e a zaurensu... Sai lokacin ta lura wannan ai yama fi Innarta girma, jikinta ya d'auki rawa ta kasa sakinsa sai rawa da jikinta keyi.... Isowar Innah zauren tana kiran Deejoh alamun tana nemanta taga tamkar mutane a tsaye amma basa motsi, toh kodai idanunta ne... K'arasa shigowa zauren tayi tana gyara d'aurin kwalinta takai hannu jikin k'wan wutan ta d'an motsa sa don ya b'aci dama sai an d'an tab'a yake kamawa.... Ai Innah na kunna wutan Deejoh ta d'ago kai tana kallon mutumin data rik'e shima idanunsa k'ur akanta... Wani k'ara ta saki lokaci guda ta shikashi... Shid'inma matsawa gefe yayi a razane yana tunanin gamo yayi da gaske, domin yanda k'wan wutan ya haske fuskarta baka ganin komai sai k'walk'walan idanunta da tsoro ya cikasu ga uwar ja gira saikace muciya aka zana, shi bai tab'a ganin irin kwalliyan ba yayi zaton kwalliyan aljanu ne.... Innah da ta kasa furta komai sai hawaye dake gangaro mata tafiya kawai take ta nufi yanda Ahidjo ke tsaye, hannayenta na rawa ta shiga shafa fuskarsa tana hawaye.... Shid'inma kallonta yake yana murmushi lokaci guda yake girgiza mata kai alamun ta daina kuka, a hankali yakai hannunsa fuskarta ya shiga share mata hawayen ta.... Ai Deejoh kam sai ta samu TV gyara tsayuwarta tayi da kyau rungume da takalmanta tana kallon ikon Allah, wannan D'an gayun kuma daga? Ta tambayi kanta.... Murya na rawa Innah take fad'in "Kaine da gaske, da gaske ka dawo garemu ne, ko kuwa wannan karanma sak'o kazo bamu kayi tafiyarka, dan Allah ka zauna damu kaji, kar ka kuma tafiya ka barmu kaji d'ana..." Ta k'arashe tana kuka sosai Ahidjo ya kuma rik'o fuskar mahaifiyarsa yana share mata hawaye yake fad'in "Innah ba sak'o nazo baku ba, nazo ne sabida ku sabida na sake ganinku, sannan wannan zuwan nawa na maki alk'awarin ba kaman ko wanne bane zan kwana maki biyu Innah..." Daga yanda Deejoh ke tsaye tana duban wadannan bayin Allah wanda takeji kaman ta masu kuka, kenan wannan D'angayun shine yaron Innah tilo da ya tafi bariki, Allah sarki Innar ta wani sabon tausayin Innah ya taso mata, cikin sauri ta nufi cikin gida don shiryawa D'angayu abinci tasan Innah zataji dad'in hakan... Gaba d'aya Innah ta gaza sukuni Ahidjonta yazo gida, yau gaba d'aya mancewa da d'iyarta Deejoh tayi ko k'yafta idanu kan Ahidjo batayi, yo ita ko d'an kunyar nan ta fulani bata jisa ba koda shike k'ila don ta jima bata saka shi idanunta bane.... Suna zaune tsakar gida tana basa labarin Baffahn sa bai dawo ba da kuma irin fushin da yake dashi kaman daga sama suka jiyo k'auri daga kitchen wai Deejoh na girki.... Daga k'auri sai ihunta suka jiyo tana k'wallawa Innah kira, daga Ahidjo har Innah a d'ari suka nufi kitchen d'in salati da sallallami saman bakin Innah, sai sannan Innah ta tuna da Deejoh, tsaye suka ganta a kitchen d'in sai tsalle take ga wuta ya kama cikin tukunyar wanda zallan mangyad'a ce sai albasa ta d'ora bisa kurho d'in, Innah kame baki kawai tayi tana duban Deejoh tana tunanin yaushe ta soma girki a gidan... Ahidjo kuwa cikin sauri ya isa ya sauk'e tukunyar ya kashe wutan yana duban Deejoh wacce ya rad'a mata suna da Aljanar da yayi gamo da ita.... Toh wai shi a ina Innah ta samo wannan yarinya mai shegen tsoron tsiya da ihu, ya tsani hayaniya gashi ya tadda wannan creature d'in gidansu, anaya ma zai iya kwanakin da yace zaiyi da wannan yarinyar a gidan....? Muryar Innah ya katse masa tunanin sa sanda ta isa tana duba hannunsa tana tambayarsa bai k'one ba... Girgiza mata kai kurum Ahidjo yayi yana murmushi yake fad'in "Babu komai Innah babu abinda ya sameni...." Kafin ya rufe baki Deejoh ta k'araso wajen a guje da ruwa cikin mod'a ga dukkan alamu daga randa ta d'ibo ruwan sabida sanyin da ruwan kedashi tamkar daga fridge aka ciro... Aiko tana isowa batayi wata-wata ba ta shek'awa Ahidjo a jikinsa gaba d'aya ita a dole zafin k'unan da yayi ya d'auke.... "Sannu D'angayu barin k'aro wani ruwan...." Ta kuma nufan k'ofa cikin sauri zata k'aro wani ruwan.... A d'ari Innah ta rik'ota tana fad'in "Ke Deejoh wai lafiyarki....." Ahidjo dake faman binta da kallo da jik'ekk'en jikinsa sunan da yaji Innah ta kirata dashi ya maimaita cikin ransa _Deejoh_ Innah taci gaba da fad'in "Kanki guda Deejoh ya zaki jik'asa, jibi yanda kika masa daga sauk'ansa ,shin tarban da zakiyima Yayan naki kenan, ko so kike ya ce maki 'yar k'auye... Haba Deejoh...." Banda rarraba idanu Deejoh bata komai, abinka da yarinta sai lokacin take jin kunyar abinda ta masa... Kai a k'asa tace "D'angayu kayi hak'auri.." Innah baki sake tace "Ke banson sakarci Yaya zaki ce...." Deejoh ta d'ago jagiranta da tun zuwan Ahidjo ya basa tsoro tana dubansa tace "Yaya D'angayu kayi hak'uri ciro rigar na shanya maka ita...." Ta nufishe tana jiran ya kwab'e rigar ya bata.... Innah ta dafe kai kurum tana jinjina shirirtar Deejoh... Shiko Ahidjo yama kasa d'aga idanunsa daga dubanta wannan wata irin yarinya ce.... Muryar Baffah suka jiyo daga tsakar gida alamun ya dawo, a guje Deejoh ta kuma ficewa tana sannu da zuwa wa Baffah... K'irjin Innah kuwa bugawa yayi tsoron yanda Baffah da Ahidjo zasu kaya, tasan mijin nata na tsananin fushi da d'an nasu.... Tuni Deejoh ta amshi bakkon da Baffah ya shigo dashi ta kai masa d'aki sai saka mata albarka yake murmushi kwance saman fuskar sa... A dai-dai sanda Innah da Ahidjo suka fito daga kitchen d'in Baffah ya hangesa, tilon d'ansa wanda ya sadaukar da komai nasa just to make him win, dukiyarsa da k'arfinsa a k'arshe ya watsa masa k'asa a idanunsa... Lokaci guda murmushi dake saman fuskar Baffah ya d'auke cak..... Ahidjo yana hango hakan fuskar mahaifinsa yayi saurin sadda nasa fuskar k'asa... Innah ko gaba d'aya jikinta sai ya kuma yin sanyi, a hankali ta soma takowa ta nufo Baffah.... Zatayi magana Baffah ya dakatar da ita ta hanyar d'aga mata hannu still idanunsa kan Ahidjo wanda ya sadda nasa fuskar k'asa... Cikin dakekkiyar murya Baffah yace "Mai ya kawo ka gidana....?" Shiru Ahidjo bai iya furta komai ba sai zafi da k'irjinsa ke masa yasan zai fuskanci hakan daga mahaifinsa, amma dole ya nemi gafaran mahaifinsa koda bazai gafarta masa ba..... "Tambayarka nake...." Baffah ya kuma fad'i cikin dakekkiyar murya.... A hankali Ahidjo ya furta "Baffah kayi hak'uri...." Bai kai aya ba Baffah ya shige d'akinsa cikin sauri zuciyarsa na masa wani irin zafi...... Innah ta kai dubanta ga Ahidjo dake tsaye wajen tamkar wanda aka dasa kafin tayi saurin sa kai tabi bayan mijinta,... Deejoh kuwa gaba d'aya sai taji jikinta yayi sanyi bata tab'a ganin Baffah cikin yanayin ba kenan shi baya farin ciki da dawowar d'an nasu... Allah sarki, sosai suka bata tausayi, su Innah da Baffah mutane ne masu karamci wanda samun irinsu a wannan duniya tamu tai k'aranci, nasu jarabawan kenan kan tilon d'ansu D'angayu... Kasa fita tayi daga d'akin ta isa can k'urya ta zauna tana tunanin nata mahaifin wanda ke hannun azzalumar kishiyar mahaifiyarta, Allah sarki rayuwa.... *** Zaune yake a parlornsa tunanin abubuwa da dama sun kasa barin kwanyarsa, dafe kansa yayi yana duban kwalban barasa dake gabansa, maganganun Babansa ya shiga yawo a kwanyarsa, shida gidan mahaifinsa amma bashida ikon shiga, ya tirsasa masa abota da Siraj ya tirsasa masa kutsawa cikin familyn Siraj saida ya saba da Siraj yake jinsa kaman d'anuwa sannan ne mahaifinsa ke neman bijiro masa da abinda bazai tab'a yuwa ba, shifah cutar da Siraj da yakeyi ba'a son ransa bane toh yanzu kuma ta yaya zai soma dab'awa Siraj wuk'a a ciki, tabbas zai iya kashe kansa kenan, uwa uba yanzu da yake matuk'ar k'aunar d'iyar Yayan Siraj yanzu da yake neman yardar Siraj fiyeda lokutan baya ta yaya zai soma janyo abinda zai saka ma Siraj da family d'insa shakku akansa, shin waima meye dalilin mahaifinsa na neman ganin bayan ziri'ar Siraj, he needs to find out, dole yasan asalin dalilin mahaifinsa na ganin bayan zuri'ar Mas'ud Laushi.... Ya k'arashe tunanin yana kwankwad'ar barasar sa.... Knocking d'in da ya jiyo daga k'ofarsa ya sanyasa saurin mik'ewa yana neman wajen b'oye barasar domin ba kowa yasan yana sha ba idan ka cire Nana H.... Yana cikin dibi-dibin b'oye kwalbar giyar ta bud'e k'ofar parlorn ta shigo... Wani mugun tsaki ya buga yana watsa mata muguwar kallo.... Fashewa tayi da dariyar had'i da ajiye handbag d'inta saman hannun kujera ta nufi Lamid'o tana karairaya.... Saida ta iso har gabansa tana wani tottoshe hanci take fad'in "Oh what's this smell for... Gosh it's terrible.... Oh wait you seems very depressed meke faruwa darling...." Lamid'o da tuni yazo wuya fincikota yayi da k'arfin gaske yana fad'in "What the hell brought you here,.... Didn't I tell you to stay away from me.... Stay out of my life, kar na sake ganin k'afafunki a gidana...." Murmushin rainin hankali ta masa tana mai shafa fuskarsa take fad'in "Oh Darling seems you're tipsy don't worry I can take care of you OK...." Ta k'arashe tana wasa da yastun hannunta saman fuskar sa... Hankad'eta gefe yayi ya shiga nunata da yatsa yana fad'in "Nana H ki fita daga rayuwata, kafin na zame maki bak'in kumarci a rayuwarki... I love Nana A and I want to marry her as soon as I proved to Siraj that I'm her Mr Right...." Dariya ta kuma fashewa dashi tana nuna sa da yatsa take fad'in "Su Mr Right manya... Lallai you are fooling yourself, ai bari kaji na fad'a maka idan kana mafarki gwara ka farka, wllhi wllhi ina raye bazan tab'a bari ka rab'i 'yar uwata ba balle kayi tunanin aurenta.... You're just making a fool out of yourself, idan ka tak'ura zan fasa k'wai zan sanar da Heedj who you really are, zan sanar dashi kalan amanarsa dake ci, sannan kowa zai tsaneka ya juya maka baya including gurguwar masoyiyarka....... So darling ina shawartarka mu ci gaba daga yanda muka tsaya...." Ta k'arashe tana masa wasu salo... Murmushi yake yana dubanta kana yace "Do you really think I'm scared of your threats...." Ya kuma murmusawa had'i da girgiza kai kana yaci gaba da fad'in " Kin b'ata wllhi, baki k'aramin komai ba sai k'arfin gwiwa, kedai kawai hassada kike Nana A ta auri wanda take so tunda ke wanda kike masifar k'auna babu aure tsakanin ku shiyasa kika zama trash mai kula ko wani irin shirgi... Wllhi Ahidjo bai dace dake ba sam and I'm hoping one day zai sami mace da ake kira mace ba irinki muna mata ba.... Wani abu ma sai randa kika rako Nana A d'akina don na tabbata kece zaki mata babbar k'awa na kashe maki idanu na maki godiya na kuma sallameki na janyo Matata....." Bai kai aya ba ta daka masa wani irin tsawa har b'ari jikinta keyi k'walla na neman ciko idanunta... Lamid'o ya kuma murmusawa kana yace "Does it hurt....? Na tabbata yanzu zaki kwashi k'afarki ki fice daga gidan nan....." "How dare you Lamido, ni kake fadawa maganganu haka.... Just who the hell do you think you are...?" Ta murmusa kana taci gaba da fad'in "If I were you I wouldn't be so sure... You've no idea what I'm capable of..... You can't get rid of me so easily... Wllhi zan shayar dakai mamaki... Mu zuba dani da kai.." Tana kaiwa aya ta suri Jakarta ta fice fuuu tamkar zata tashi sama..... Tana ficewa ya buga tsaki had'ida rufe k'ofar gidan gaba d'aya.... *** *Tambuwal* Yanda take huci zai tabbatar maka cikin tsananin fushi take, Zaliha da Ummanta sai faman bawa Mairo baki suke amma tamkar da dutse suke, sunsan halin Mairo zata iya kwana a haka ba tareda ta furtawa kowa komai ba idan ranta ya b'aci irin haka..... Aiko tana jiyo salesman Dadda ta mik'e ta shige uwar d'akin Umman Zaliha ta maida k'ofar ta rufe.... *SameenaAleeyou📚* [12/28, 9:38 AM] ‪+234 802 741 0766‬: *FUSKA UKU*🏮 *16* *©Sameena Aleeyou...✍🏽* Mik'ewa Zaliha tayi ta baiwa Ummanta da Dadda waje don su tattauna.... Umma ta gyara zamanta tana duban Daddah da gaba d'aya damuwa ya nuna saman fuskarta kana ta soma fad'in "Daddah dan Allah kada ku bar garin nan, kada ki k'untatawa d'iyarki, ta riga ta saba da garin da kuma mutanen dake ciki mai yasa kike son dasa damuwa cikin zuciyarta....? " Ta k'arashe damuwa k'arara a fuskarta Girgiza kai kawai Daddah take tana duban Umman Zaliha lokaci guda take fad'in "Rabi bazaki gane bane duk abinda nakeyi duk gujema zaman garuruwa da nakeyi sabida kub'utar da d'iyata nakeyi, bamu tab'a jimawa a wani gari ba kaman yanda muka jima a nan, Rabi bazan zuba idanu inaji ina gani na rasa tilon d'iyata ba...." Umman Zaliha ta sauk'e ajiyan zuciya kana ta matso kusan Dadda sosai ta kamo hannayenta kana ta soma fad'in "Daddah Mairo tana jin dad'in zamanta a nan tana jin dad'in sana'arta a nan, ina jiye maki tsoro kada ki rasata garin kareta da kikeyi, bazance ina son jin sirrinki ba amma ya kamata ki daina rufawa d'iyarki duk wani sirri, ki dinga fad'a mata abubuwa, abin yana damun Mairo sosai sanin cewa tsawon rayuwarta akwai abinda kike b'oye mata..... Dan...." Ganin yanda Daddah ke watsa mata kallon daina wahalar da fatar bakinki ya sanyata had'iye zancenta don tasan Daddah yanzu sai ta tara mata jama'an unguwa abin fad'a bai mata kad'an koda shawarinka tazo nema idan ba'abi ra'ayinta ba toh kuwa zaman bazai k'are da kyau ba.... Mik'ewa tayi tana gyara d'aurin kwalinta had'i da d'aukan mayafi tana fad'in "Yo aikin banza aikin wofi, Mairo dai d'iyata ce kuma banga watsettsen da zai rabani da d'iyata ehe... Yo kuma duk matsugunin da naga dama nan zamu tsuguna ke baki isa ki hana ba... Banda shegen felek'e da firirita zaki wani kwantar da murya wai ke ga mai shawari koh... Toh shawarin yaci uwatai.." Ta k'arashe tana dukan k'ofan d'aki da iya k'arfinta tana kwad'anra kirawa Mairo uwa zata b'alle k'ofar.. ... Zaliha da Ummanta tsaye sukayi suna kallon ikon Allah, baka isa ka kwab'i Daddah ba ta hayayyak'oka da bala'i , kan kace mai mak'ota sun soma taruwa.... Aiko nan Daddah ta bar bugun k'ofa ta dawo kansu da bala'i.... "Toh munafukan banza 'yan hana ruwa gudu, uwar me kuke kalla.... Zaku fice ko sai na k'araso wajen....!" Aiko kan kace mai sun soma watsewa domin sanin kansu ne kad'an da aikin Daddah ne ta jibgi mutum idanma ka kai k'ara station ba saurarenka za'ayi ba domin rankatatab garin babu station d'in da Daddah da d'iyarta basu zaga ba sabida tsananin masifarsu da bala'in su... Mutum d'aya ne tasan zai iya yima Mairo magana tayi hak'uri gashi baya nan yau kusan sati biyu, tabbas shi kad'aine mai iya sasanta Mairo da Daddah idan sunyi fad'arsu tasan yau kam zaiyi matuk'ar wuya Mairo ta saurareta, haka nan take idan ta hau dokin fushi bata k'aunar maganawa kowa, fushinta yakanyi wuyan sauk'a idan ba dukan mutum tayi ba wannan shine d'abi'ar Mairo ka taro fad'a da ita toh kuwa jikinka zai gaya maka koda kafi k'arfinta zaku dambatu yanda kasan 'yar wasan kokawa haka nan take, sanin bazata iya dambatuwa da Daddanta ba ya sanya take avoiding Daddah muddin sukayi fad'a irin haka... Wannan shine d'abi'ar da Daddah ta tada d'iyarta Mairo bisa, tun tana k'arama tana makarantar primary take koyar da ita fighting back kan duk wanda ya takali fad'a da ita, Mairo bata kawo k'ara saidai a kawo k'ararta, ko cikin k'awaye Mairo ta shiga toh babu k'awar data isa juya Mairo saidai Mairo ta juyata, uwa uba Mairo tanada farin jini da saurin shiga zuciyar duk wanda ta rab'a ko ya rab'eta... Sam Daddah bata koya wa Mairo karb'an abin hannun kowa ba musamman samari wannan dalili ya sanya ta koyar da ita dogaro da kai tun kafin ta kawo yanda take a yanzu... Juyin duniyar nan Mairo tak'i fitowa daga d'akin Umman Zaliha dole Daddah ta koma gida ba don taso ba, jigum tayi tana tunanin lamarin..... Kaman daga sama taji sallaman sa, a zabure ta mik'e tana tunanin anya badai kunnuwanta bane suke mata k'arya sabida tsananin buk'atar dawowar nasa da take.... Sallaman data kuma ji ya tabbatar mata shid'in ne ya dawo... Cikin sauri ta isa tanai masa lale ta bud'e k'ofar... Yauma sanye yake da kayansa ta bautan k'asa da alama sauk'arsa kenan don ta gansa da jakka..... "Daddarmu barka da gida, da fatan na sameku lafiya...." Ya fad'i sanda ya zauna bisa turmi yana kwab'e takalminsa irinta 'yan bautan k'asa.... Daddah ta amsa masa da sakin fuska tana masa barka da dawowa, lokaci guda ta mik'e ta nufi kitchen don kawo masa abinci.... Jim kad'an ta fito da flask d'in tuwo da miya... Saurayin da murnansa ya karb'i Flask d'in daga hannunta yana fad'in "Aiko dai wallah bazank'i ba don tunda muka taso bamu tsaya cin abinci ba nasan zan samu a gidan nan shiyasa ma na soma biyowa nan...." Ya k'arashe yana mai isa bakin famfo ya wanke hannayensa sai ci gaba da zuba yake ba tareda Daddah ta amsa sa ba... Kai k'arshe ya dawo ya soma yankan lomar tuwonsa Daddah bata amsa sa ba kaman yanda suka saba.... Hakan ya tabbatar masa akwai matsala sai sannan ya lura baiga 'yar bala'i Mairo ba... Waige-waige ya soma yaji gidan shiru babu Mairo babu k'awayenta 'yan sana'ar bead.... Karkato da dubansa yayi ga Daddah yana duba wacce ta had'e hannaye biyu ta zuba tagumi..... Ajiye kwanon abincin yayi yana duban Daddah da kyau kana yace "Daddarmu lafiya banga yaranki ba.....?" Sauk'e ajiyan zuciya tayi had'i da tab'e baki kana tace "Yo uwar gayya bata nan ina kuwa zaka gansu Nazeeru am..." Saurayin da ta kirada Naziru murmushi yayi don yasan fad'a Daddah da Mairo sukayi kana yace "Amma dai lafiya koh...." "Yo ina kuwa lafiya ai kaima tunda kaga haka kasan jiranka kurum nake ka ida cin abincin nan muje ka lallashota yanda ka saba ta dawo gida, kasan maganar ne kurum bata tsallakewa.... Maza ida tura tuwon...." Ta k'arashe tana tura masa ledar pure water.... Nazir yayi murmushi kana yace "Shine wai kika saka kanki a damuwa, toh wai idan mukayi auren haka zakike damuwa...." Yana maganar yana k'unshe dariyarsa... K'iris ya rage bata kwad'a masa takalmin gefenta ba tana fad'in "Uwar aure zakuyi ba aure ba, idan kuma kunnani kake son sakeyi sai muji kasan sarai zan kwab'e mu daku dakai...." Nazir ya had'iyi lomar tuwonsa dariya na neman k'warar dashi yake fad'in "Ai babban gangancin da mutum zaiyi shine ya nemi auren Mairo d'iyar Daddah, wllhi wllhi Daddah duk sona da mace mai kyau bazan iya sauk'e idanuna kan Mairo ba hasalima bana mata kallon mace, duk mace mai dokuwa da maza kam ai ta wuce mace......" Bai kai aya ba ta katse sa da fad'in "Kar kuma ka zagar min d'iya ehe, yo da ace ban koya mata k'watan 'yanci ba ai da yanzu kun hure mata kunne da k'aryarku ta samari, maza ida ci ni da Allah muje dare nayi...." Tsame hannunsa yayi cikin tuwon yana d'an darawa yake fad'in "Aima na k'oshi saidai a baiwa almajirai sauran....." Kaman jira take nan ta tasa gaba suka fice..... NAZIR matashin saurayi ne wanda yake bautan k'asa a garin, a lokacin dasu Daddah sukayi hijira daga garin Kazaure ta jihar Jigawa zuwa garin Tambuwal ta jihar Sokoto a lokacin Nazir ya taho garin Sokoto don yin bautar k'asa, a motar kasuwa suka had'u da Nazir yayinda taimako ya shiga tsakaninsu, sukayi rabo ta mutunci dukda ad'an zamansu a motar saida sukayi fad'a da mutane da dama cikin motar amma basuyida Nazir ba, wani ikon Allah sanda suka sauk'a unguwar da zasu zauna saiko suka had'u da Nazir shima gidan da ya kama d'an k'asa dasu kad'an ne... Nazir d'an asalin garin Jigawa ne, yakan je gida bayan sati bibbiyu yakai ziyara wani sa'in har tsaraba yakan yiwo wasu Daddah, haka kurum Allah ya had'a jininsu tun taimakonsu da yayi a mota, sam bai tab'a nuna interest d'insa kan Mairo ba saidaima ya taya Daddah yak'i da samaruka masu son Mairo tunda ya lura da abinda Daddar take so kenan, dad'ida k'arin yarda dashi da Daddah tayi har hoton matar da zai aura ya nuna masu sannan wani sa'in sukan gaisa da ita a waya, har sabo saida ta shiga tsakaninsu da budurwar Nazir, wani sa'in musamman take kira taji dramar Daddah da Mairo a cewarta dariya suke bata.... Lura da yanda Nazir ke tsananin son budurwarsa basu mintuna kad'an sai sunyi waya kaman su cinye juna ya kuma sa Daddah sakin jiki dashi, Allah sarki gashi ya kusan cika shekara guda d'insa ya kammala bautar k'asar sa tasan dole su rabu dashi nan bada jimawa ba, tabbas Nazir zai barsu da kewa..... Agogon hannunsa ya duba sanda suka fito daga gidan, agogon ta nuna k'arfe 10:00pm duban Daddah yayi ita fa bilhakk'i da gaskiya gidan mutane ta nufa a daren nan.... Dubansa tayi ganin ya tsaya mata k'obarare kana tace "Miye ka tsaya min uwa dogari mu k'arasa mana...." "Daddah amma bakiga lokaci ba koh.. Dare yayi ki bari da safe idan Allah ya yarda zanje da kaina na maki alk'awari kafin ki farka bacci da Mairo zan shigo maki gida, amma yanzu dare yayi ina saurayi na shiga gidan matan aure... Ko yaya kika gani Daddarmu...." K'uri ta masa kana ta jinjina kai tace shikenan Naziru tunda kace haka, Allah shi kaimu safiyar.... Gaskiya ne kaje gida ka huce gajjiya kaima...." Nan sukayi sallama Daddah ta komo gida cikeda kewar Maironta.... Nazir kuwa gida ya wuce yana tunanin mai ya had'a Mairo da Daddah fad'a bayan tafiyarsa, Allah sa dai ba abinda yake tunani bane, tabbas idan abinda yake tunani ne aiki ya jik'e masa, gwara yasan abin yi tun wuri, da wannan tunani ya isa gida. ..... *** *Misau* Daga bakin k'ofar mahaifin nasa ya durk'usa saman gwiwoyinsa yanayin zaman rak'umi, kansa a k'asa yaci gaba da fad'in "Baffah ka yafe min, kayi hak'uri kada kace na fice maka a gidanka wllhi banida yanda yafi nan na sani....." Sai sannan Baffah ya d'ago idanu yana dubansa cikeda takaici da tsananin mamaki kana yace "Ni zaka rud'a ka yaudara da kalamai Ahidjo? Shin yaushe ka d'auki hakan cikin zuciyarka? Shin yaushe ka bamu wannan matsayin,? Shin sau nawa akayi haka amma kana komawa can barikin zaka kuma mancewa damu.... Shin a haka kake so kayi albarka....? Ahidjo maike damunka a rayuwa? Mai muka maka da tsanani da kake kunyar nunawa duniya cewa mune mahaifanka? Mai ka d'auki wannan rayuwar? Mai ka d'aukemu da sai lokacin daka bushi iskanka zaka waiwayomu shin a haka kake neman albarka Aliyu? Shin a haka kake fatan gamawa da duniya lafiya? Kayi ma kanka hisabi tun a duniya.... Kuma bari kaji na fad'a maka, wllhi wllhi kaji na maka rantsuwar d'an musulmi sam rashinka a gareni bazai tab'a ragina da komai ba, damuwata d'aya tak shine mahaifiyarka.... Kayi yanda kake so da rayuwarka ni Sanda ban haifi d'an da zai sakani ciwon zuciya ba.... Maza tashi ka fice min a d'aki...." Ya k'arashe yana janyo radio d'insa... Ko motsi mai kyau Ahidjo ya kasa kansa a k'asa yana tunanin maganganun mahaifinsa zuciyarsa bai daina masa ciwo ba, wllhi shi kansa baisan meke damunsa ba, baisan tak'amaimen dalilin da ya sanya watsar da iyayensa ba iyakaci yasan addu'a ce kawai zasuci gaba da masa..... Yana cikin tunanin ya jiyo muryar Baffah cikin tsananin daka tsawa yana fad'in "Ka fice min nace kafin ranka ya b'aci...!" Sim-sim ya mik'e ya bar d'akin, rasa maike masa dad'i yayi gaba d'aya, can ya hangi Innah k'ofan fanninsa da tuni suka gina masa cikin gidan dukda ba zuwa yake ba balle zama, d'aki ciki da parlor dai-dai k'arfin talaka da kuma makewayi mai tsari... Jikinsa ya kumayin sanyi shakka babu yasan kintsa masa wajen Innah take, nauyi da k'aunar mahaifiyarsa ya cika zuciyarsa,.... Ganin wayar matarsa na shigo masa ya sanyasa ficewa daga gidan don amsa wayar, ya nufi yanda yayi parking motarsa k'ofar gidan.... *** *Abuja* 8:00am Sanye yake cikin suit d'insa ruwan toka da alama shirin office yayi, saman stool dake ajiye gaban dressing mirror ya zauna yana gaida Ammah dake zaune saman k'aton royal bed d'inta tana afa magungunanta na safiya..... "Baba na an fito.....?" Ammah ta tambaya tana kora maganin nata da ruwa cikin glass cup.... "Eh Ammah ya k'arfin jiki kuma?.... " "Alhamddulillahi da sauk'i sosai kwana biyun nan bana gane ma jikin kasan k'uran hazon nan sai a hankali musamman masu ciwo irin namu...." Siraj ya jinjina kai kana yace "Haka ne Ammah, Allah ya baki lafiya,.." Ammah ta amsa da ameen kafin ta k'arada "Sirajo nikam nace ba yaya gaskiyar zancen da nake ji d'in nan, da gaske abokin naka yana son Nana Asma'u ne ko kuwa dai kawai hasashen su Ayiya ne....?" Ta k'arashe tana duban Siraj dake shafa wayarsa.... Lokaci ya maida wayar aljihu ya nitsa hankalinsa sosai yana duban Ammah kana ya soma fad'in "Ammah dama maganar da na shigo muyi kenan, amma naji numfashin naki kaman nason tashi, dan Allah ki dinga kiyaye k'uran nan.... Kuma inaga ya kamata ki koma checkup kwannan nan...." "Kayya Sirajo am ni banson wani yawo a jirgin nan mutum kaman tsuntsu kaga fah yanzu ko inhaler ban amfani dashi, kaga kuwa ai Alhamdulillahi..." Siraj ya jinjina kai kana yace "Toh Ammah Allah k'ara maki lafiya.... Kan batun Lamid'o da Nana A jiya da dare munyi maganar and he's serious, da gaske sonta yake, toh amma dai ban basa go ahead ya nemeta ba sai nayi magana da ita Asma'un....." Ammah ta fad'ad'a murmushinta tana furta "Alhamdulillahi kai Masha Allah, ai hakan yafi, kaga duba da lalurar da Asma'u ke fama dashi gwara ta auri wanda aka sani d'in ba bare ba, kuma Lamid'o ai yaro ne mai hankali ga natsuwa, Allah sa Asma'u ta amince dashi ni sai nafi kowa farin ciki....." Bata kai aya ba sukaji muryar Nana H da shigowarta kenan tana fad'in "Yarda kam dole Nana A tunda babu wanda ya tab'a furta mata kalman so, kuma wllhi na tabbata shima ba tsakani da Allah yake sonta ba saidon dukiyar da mahaifinmu ya bar mana...." A tare Ammah da Siraj suka juyo suna dubanta yanda tayi maganar har zuciyarta "Sweetheart ya zaki ce haka....?" Siraj ya tambaya yana duban Nana H wacce ke tsaye tsgege akansu hannaye hard'e a k'irji "Uncle it's obvious.... A fili yake, no man, no man in this world will fall in love with a woman that has only one leg, haba Uncle open your eyes and see, wllhi wllhi Lamid'o ba tsakani da Allah yake son Nana A ba, ya mak'ale a company yana cin dukiya jikinsa still bai ishesa ba sai ya nemi niece d'inka... Wllhi Uncle...." Siraj ya katseta da fad'in "Shut up Nana H... Haba have some respect, ko kin mance Lamid'o abokina ne huh...?" Ammah cikeda jin dad'i take jinjina kai, yau ita kanta taji dad'in tsawatarwa da Siraj yayiwa Hafsat, domin ita kanta tana son ganin Nana A a gidan miji kafin ta bar duniya... Siraj yaci gaba da fad'in "Nasan Lamid'o abokin mijinki ne so dukda haka ban yarda ki tsoma kanki cikin alak'arsa da Asma'u ba, ki bar min komai kin fahimta koh...." Kallon mamaki kawai take binsa dashi yanda yake ya mata fad'a, wai ita d'in Uncle love kema haka kuma Ammah na kallo bata bi bayanta ba tana shiru, duk akan wannan tsinanniyar gurguwar 'yar uwar tata, toh wllhi dole tasan abinyi, wllhi bazata tab'a bari makirci da munafuncin Nana A ya saye zukatan mutanen gidan ba, babu babban shege irin Lamid'o da ya soma kawo wannan matsala, wllhi shima sai ta shayar dashi mamaki..... Ko kallo basu isheta ba ta fice fuuu kaman zata kifa k'asa.... Siraj ya yunk'ura zaibi bayanta Ammah ta dakatar dashi tana fad'in "K'yaleta, gwara daka mata hakan, banda yarinta irinta Nana Hafsat ai Lamid'o shine dai-dai Asma'u, zata sauk'o da kanta idan ta fahimci hakan.... " Jinjina kai kurum yayi kafin yace "Ammah kinsan hakinta idan tayi fushi bata sauk'owa da wuri...." Ammah ta d'an murmusa kana tace "Ai haka mahaifinsu yayan ka yake idan yayi fushi sam baya sauk'owa da wuri, toh haka Nana Hafsatu take, kaga ita kuma Asma'u mai sanyin zuciya ce kaman mahaifiyar su,..." shiru ya d'an gifta sanda ta tuna 'yar uwarsu Nana Khadija... Lokaci guda taci gaba da fad'in "Allah sarki Nana Khadija ita kuma da tana raye k'ila da tayi fad'a fiyeda na Hafsat kasan masu sunan Khadija ba tayan baya ba wajen fad'a..." Gaba d'aya suka murmusa daga ita har Siraj d'in kafin Siraj yace "Da yanzu ta girma ta zama kamansu, tabbas da mun samu FUSKA UKU iri guda a family saidai kowa da irin halinsa cikinsu... Allah ya jik'an Yaya da Aunty Zainab yasa suna Aljannah...." Ammah ta amsa da ameen jiki a sanyaye kafin Siraj ya mik'e yana fad'in "Ammah ni zan wuce office idan na dawo zamuyi maganar insha Allah..." "Toh Babana Allah shi taimaka koh, a dawo lafiya...." cewar Ammah dake bin d'an nata da kallon tausayi, kullum cikin masa addu'a take Allah ya yassare masa matslolinsa na rayuwa.... Kwance ya hangi Nana H saman gado sanda zai wuce k'ofar d'akin nata, girgiza kai kurum yayi ya fice ba tareda yabi takanta ba... Tana jin k'aran takalminsa yana sauka daga bene kuma taji tsayuwansa a k'ofar d'akin, da a baya ne da Uncle Siraj bazai fita ba sai ya shigo ya lallasheta,... Duk a dalilin Nana A yanzu Uncle love ke mata haka, wllhi ta tsani Asma'u kuma bazata tab'a bari Uncle ya mata rabin soyayyar da yake mata ba...." Ta k'arashe tana huci tamkar wata kububuwa *** Shigarsa office d'in da kad'an Nasaar ya shigo da sallama... Siraj dake faman duba wani tabloid dake hannunsa ajiywa yayi yana fad'in "Barrister barka da isowa...." Lokaci guda yake zama bisa kujeransa had'i da kurb'an coffee d'insa dake faman tururi.... Cikin sauri Nasaar ya k'araso cikeda rusunawa ya mik'awa Siraj suna gaisawa... "Sir barka da safiya...? " "Barka Nasaar, ya al'amra..?" "Lafia lou Sir......" Shiru ya d'an ratsa tsakani har Nasaar ya soma tunanin kodai Siraj ya mance appointment d'insu da k'anwar matarsa ne.... Siraj ya katse shirun da fad'in "Lafia dai koh Attorney, ka samu kaga client d'in kuwa....?" Nasaar ya d'an shafi kansa kana yace "Sir dama zuwa 11am muke da appointment dashi.... Yanzu tafe muke da k'anwar matar nawa wacce kace zaka ganta yau....." Saurin cire cup d'in daga bakinsa yana fad'in "Aff haka fah, I almost forgot, babu damuwa ka shigo da ita kafin na shiga wani sabgan...." Cikeda jin dad'i Nasaar yace "OK Sir right away.... Na gode fah Sir, Allah k'ara girma..." "Babu komai Nasaar...." Siraj ya fad'i yana kuma duba news d'in da ya tafi da hankalinsa cikin jaridar.... Tunda yaji an tab'a k'ofar yaji ya daina fahimtar komai cikin jaridar, ji yayi ya k'agu ya d'ago idanunsa yaga sabuwar sakatariyan nasa wacce yasan itace ke k'ok'arin shigowa, sallamarta da ya jiyo cikin siririyar muryarta ya kuma tafiya da wani b'angare na tunaninsa..... A hankali ya zame idanunsa daga saman jaridar ya maida idanunsa zuwa ga k'ofa, tun daga k'afafunta ya soma duba.... Sanye take cikin doguwar riga ta atampa kalan shud'i mai manyan zane, ta yafa mayafi kalan hoda wanda ya tafi da kalan jikinta... Idanunta a k'asa sanda Siraj ya k'ura mata dogayen idanunsa akanta, so yake ya d'auke idanunsa daga dubanta amma ya kasa,... Saida ta iso dai-dai bakin table d'insa taja ta tsaya sihirtaccen murmushi saman fuskarta... "Barka da safiya Sir... May I....?" Ta k'arashe tanai masa nuni da kujerar dake gaban table din had'i da juya idanu *SameenaAleeyou📚**FUSKA UKU*🏮 *FUSKA UKU*🏮 *17* *©Sameena Aleeyou...✍🏽* Ko motsa idanunsa daga kan Azeeza ya kasa, k'yam ya kafeta da idanu babu ko k'yaftawa fuskar nan nasa kuwa lokaci guda ya had'eta gaba d'aya.... Azeeza tasha jinin jikinta domin fuskar Boss d'in nata yafi kama da a kirasa Tyrant.... A hankali ta zame hannunta daga jikin kujeran tana d'an gyara mayafinta had'i da yin gyaran murya.... Sai lokacin Siraj ya dawo daga duniyar tunanin da yayi nisa cikinta, gyara zamansa yayi saman kujerarsa ta alfarma kana ya mata nuni da kujeran dake gaban table d'in "Please sit down...!" Yayi maganar babu alamun wasa a fuskar sa... Murmushin yak'e kawai Azeeza tayi kana ta zauna tanai masa godiya. .. Ya jima yana wasu 'yan rubuce rubucensa ba tareda yace mata kanzil ba, har dai Azeeza ta saduda cewa wannan Tyrant d'in baida niyyan mata magana.... Kaman kuwa yaji zancen zucin nata mik'ewa yayi yana daidaita zaman suit d'insa kana ya soma tafiya ya nufi k'ofa waya mak'ale a kunnensa.. Baki sake Azeeza ta bisa da kallo, lallai wannan ya cika d'an rainin hankali toh mai yake nufi da zamanta a nan ita da ta shigo interview yayi tafiyarsa ya barta, what does this mean....? Babu mai bata amsa tambayarta, kaman daga sama ta jiyo muryarsa yana fad'in "Get my things over there and follow me...." daga haka sa kai yayi ya fice daga office d'in... Azeeza tabi bayansa da kallo kafin ta maido da dubanta ga table d'in nasa tana lissafin toh waima wasu stuff yake nufi, file d'in kenan hala.... Cikin sauri ta shiga had'e takardun tabi bayansa cikin sauri kafin ya b'ace mata, da shike kana iya hango wajaje da dama cikin Company d'in abinka da ginin da yasha kwalliya da glass... Daga office d'insa ya hangota rungume da file sai sauri take tana bin bayan Siraj, k'irjinsa ya buga, ta yaya Siraj zai fita da Azeeza daga soma aikinta a company d'in... K'irjin Nasaar ya shiga masa zafi sosai, meyasa ma tun fari ya aminta Azeeza tayi aiki da Siraj, anya baiyi kuskure ba? Kai dole yasan abin yi he loves Azeeza so much bazai iya barinta ma kowa ba, Azeeza tashi ce.... A hankali ya shafi naman goshinsa yana tunanin tun wuri gwara ya sanar da ita abinda ke cikin zuciyarsa kafin yayiwa kansa sakiyar da ba ruwa.... Gaba d'aya files d'in neman watsewa kawai suke a hannunta, kuma sabida tsaban mugunta subi ta lift basu biba, ta matakala Siraj yabi dasu, ta gaji iyaka gajjiya,.... Da k'yar take numfashi sabida yanda ta jigata, a wahalce ta soma fad'in "Sir! Please Sir wllhi na gaji, dan Allah kace mun iso floor d'in, wayyo Allah na wllhi na gaji bazan iya ci gaba da tafiya ba....." Ta k'arashe tana durk'usawa wajen gashi takalamin k'afarta wedge ne mai tudun gaske.... Juyowa yayi yana dubanta yanda ta durk'usa a wajen alamun gajjiya, a hankali ya tako ya dawo da baya had'ida d'an kwanto da kansa dab yanda take a durk'ushe kana ya d'an rage murya yace "You have to... You must, if you really need this job.... This is also part of your interview... Oya tashi muje, we almost there...." Yana ida fad'in haka ya mik'e yana mai ci gaba da tafiya.... Harara kurum ta rakasa dashi tana nan durk'ushe a wajen, lokaci guda ta tuna she's doing this for her only brother, she promised not to let him down... She really need to put up with this Tyrant, lokaci guda ta mik'e taci gaba da binsa, ganin ya kusa b'ace mata ya sanyata k'walla masa kira tana binsa cikin sauri.... Saida suka kusa zagaya cikin kampanin tana biyeda Siraj wanda ko a jikinsa da jigatan da tayi wayarsa ma yakeyi, da alama bai fin mintuna goma bai d'aga waya ba.... Saida suka iso dai-dai wajen wasu kujeru na shak'awata Siraj ya k'arasa saman guda d'aya ya zauna, waya manne a kunnensa yake mata nuni da kujeran gefe... Saida ta juya idanu had'i da jan k'aramin tsaki kana ta ajiye file d'in saman table d'in da iya k'arfinta kafin ta zauna had'i da hard'e k'afafu d'aya kan d'aya, fuzar da iska tayi ta shiga bin Kampanin da kallo, tabbas babba ne sabida koda zasu zo bata nan suka shigo ba.... Wani ma'aikaci ne mai sanye da farin uniform ya k'araso da tray a hannunsa glass cup guda biyu bisa, ya ajiye masu saman table d'in had'i da gaida Azeeza, ko amsa sa batayi ba don gaba d'aya wani irin haushin Siraj take ji.... Saida ya shafe mintuna kusan talatin yana wayar kafin ya d'an sarara da wayar nasa, idanunsa naga wayar yake fad'in "K'arfe takwas nake shigowa building d'in nan, before 8am my coffee must be ready ko wace rana, sannan ba'a k'aramin komai kan schedules d'ina idan suka riga suka zama ready... Abu na gaba I don't tolerate coming late, and.... You also need to prioritize your job, bana d'aukan excuses....." Lokaci guda ya d'auki glass cup d'aya ya kurb'a yayinda Azeeza ke faman binsa da kallon mamaki.... Murya a d'an dake tace "Naji dokokinka Sir and insha Allah zan kiyaye...." Batakai aya ba ya katseta da fad'in "Abu na k'arshe bana tolerating kawo samari wajen aiki, as far as kina wajen aiki babu kula samari koda a waya ne sai lokacin tashi yayi... Kin fahimta...?" Ya k'arashe yana ware mata dogayen idanunsa a fuskarta wanda tuni ya sanyata sadda nata idanun k'asa... A hankali ta shiga jinjina masa kai, dole ta masa biyayya idan ta tuna wa Junaid take duka wannan.... Lokaci guda ta jiyo muryarsa yana ci gaba da fad'in "Good, so now Janet zata nuna maki komai.. Congratulations once again Miss Azeeza...." Ya k'arashe yana mik'ewa tsaye... Yanda ya ambato sunanta babu ko gargada ya sanayata kuma dubansa saidai tuni ya bar wajen cikin tafiyarsa da tafi kama da sassarfa... Azeeza tabi bayansa da kallo, ya bar wayansa guda a wajen ga shirgin takardun da ya sanayata tattarowa, uwa uba ita batama san ta yanda ta nufa ba a wannan huge building d'in.... D'an fuzar da iska tayi sanda tunanin Nasaar ya fad'o mata kafin ta ciro wayarta cikin jaka ta shiga dialing layin Nasaar.... *** *Misau* Shikam yanzu har ga Allah yarinyar dariya take basa tama daina basa takaici, murmushi mai bayyana hak'wara yayi sanda ya tuna safiyar yau yanda ta shigo masa d'aki gaba gad'i babu ko sallama balle neman izinin shiga wai ita a dole ta kawo masa abin kari, yanda ta gansa daga shi sai gajeren wando ya sanyata k'walla ihu wanda saida su Baffah da Innah suka nufo wajen, abinda zai kuma baka dariya sai tsalle take tana rintse da idanu tana fad'in D'angayu kayi hak'uri wllhi Innah ce ta aikoni, wllhi ba laifina bane..... Har saida Innah ta kad'ata d'aki kafin tayi shiru ta daina tsalle-tsalle da rintse idanun, shi baima san yanda Innah ta samo yarinyar ba don ko d'azu da ya tambayeta yanda ta samo yarinyar sai ce masa tayi zata sanar dashi komai, shi sam ji yayi bai sake da zaman yarinyar a gidan ba... Wata iriyar yarinya mai ban takaici da dariya... Girgiza kai kurum yayi kafin ya janyo wayarsa ya shiga dialing layin matarsa.... Bugu biyu a na uku ta d'aga har lokacin bata daina kukan abinda Uncle Luv yayi mata ba.. "Hello Heedj...!" Kasa ci gaba da magana tayi sai sabon kuka da ta fashe masa dashi... Hankali tashe Ahidjo ya mik'e had'i da ficewa cikin sauri sabida k'aranci service na waya dake cikin gidan... Daga yanda Deejoh ke shanya ta hango fitarsa cikin sauri, sauri-sauri itama ta take masa baya.. Daga d'aya b'angaren cikin kuka Nana H taci gaba da fad'in "Heedj I just can't stand them all anymore... Dan Allah ka dawo wllhi duk sun tsaneni a gidan wariya suke nuna min.... Heedj ka dawo dan Allah bazan iya rashinka na tsawon kwanaki ba...." ta k'arashe cikeda kuka irinta makirci.. Ahidjo ya shafi naman goshinsa cikin sigan lallashi ya soma magana.... "Alright sweetheart, I'm sorry OK, ki kwantar da hankalinki ki daina kuka I'll soon comeback to you insha Allah OK... As soon as I'm done with this investigation zan dawo kinji sweet...." Cikeda shagwab'a tace dashi "I love you my Heedj..." Murmushi ya d'anyi soyayyar matarsa na kuma dabaibaye zuciyarsa kana yace "And I love you too Sweet... So much... Ki daina kuka ki kulamin da kanki kwanan nan zan dawo kinji koh...." Ya k'arashe cikin sigan lallashi Kalamansa na k'arshe kurum Deejoh taji, toh da waye D'angayu ke waya, da gaske har zai kuma tafiya ya bar Innah... Allah sarki ta taya Innah murnan dawowarsa sai gashi kuma kwana d'aya tak yayi yana maganar komawa.... Lokaci guda taji jikinta yayi sanyi sosai... Cikin sauri ta juya zata shige cikin gida saidai tuni Ahidjo ya ganta, mamaki ya cikasa, maike damun wannan yarinyar? Lab'e take masa kokuwa mai.. Lallai gwara ya saita ta tun wuri kafin ta jik'a masa aiki.... A d'ari ya take mata baya taku kad'an ya cimmata a dai-dai zauren shiga cikin gidan, lokaci guda yakai mata damk'a.... Deejoh uwar tsoro zata saki ihu Ahidjo yayi amfani da hannunsa guda ya toshe bakinta... Giran sama da k'asa ya had'e yana watsa mata mugun kallo lokaci guda ya sungumeta ya nufi sashensa da ita... Deejoh sai faman wutsil-wutsil take tsoro ya cikata domin kuwa tun ba yanzu ba Innah tasha fad'i mata kada ta yarda wani namiji yakai hannu jikinta, don namiji na tab'aka zakayi abin kunya abin nunawa a gari, shikenan ta shiga uku ta mutu ta lalace shikenan D'angayu ya tab'ata wayyo Allahnta, shisshiginta ya janyo mata.... Bai direta ko ina ba sai d'akinsa... Zata kurma ihu ya zare mata manyan idanunsa yana fad'in "Kika ce fit sai na maki d'an karen duka a d'akin nan... Mayya kawai, mai na maki kike bibiyata, ke mayya ce....?" Ya k'arashe yana kuma zare idanuwa.... I zuwa lokacin idanun Deejoh sunyi rau-rau banda karkarwa babu abinda jikinta keyi... Ahidjo ya kuma matsowa kusa da ita ta matse jikin garu... Murya a dake yaci gaba da fad'in "Kina jina idan naji kin sanar da Innah wani abu gameda maganar da kikaji inayi a waya sai na harbeki da bindiga. Ai kinsan bindiga koh...?" Cikin sauri ta shiga jinjina kai hawaye na neman ciko idanunta... Ahidjo ya kad'a kai kana yaci gaba da fad'in "Idan naji kincewa Innah zan tafi sai na harbeki da bindiga ta tana nan cikin mota, kuma saura naji bakinki... Has anyone ever told you how disgusting you are..?" Ya tambaya yana kuma matso da fuskarsa dab nata... Yo ita yaushema ta fahimci abinda yake nufi, kallonsa kurum take da idanunta da tuni sunyi rau-rau.... "Stop staring at me mayya kawai..." Ya fad'i yana kuma watsa mata mugun kallo... Ganin yanda ta razana sosai yasan ko kusa bazata sanar da Innah tafiya zaiyi ba... Murmusawa yayi kana yace "Daga yau sunanki Disgust kinji koh... Fad'a inji..." Kasa fad'i tayi sai zazzare idanu da takeyi... "Au bazaki fad'i ba...." Ganin na k'ok'arin matsowa ya sanyata saurin fad'in kalman da ya umarceta ta fad'i dukda batada tabbacin cewa dai-dai ta fad'i.. Yanda ta furta kalmar sosai ta baiwa Ahidjo amma ya gimtse, kamo hannunta ya kuma yi yana fad'in "Zo ki fice min a d'aki , na sake ganin kinmin lab'e sai na fasa kanki da bindiga..." Har sunzo k'ofa yaga tana share hawaye... Cak ya tsaya yana dubanta kana yace "Had'iye kukan nan ki kuma goge fuskarki, idan kikacewasu Baffah na maki wani abu kin san sauran...." Ganin ta masa biris tak'i share hawayen ya sanyasa saka hannunsa ya shiga goge mata hawayen, aiko nan hannunsa ya b'aci da jan hodan Deejoh da kuma gazal d'inta.... Ahidjo ya kuma yin tsaki yana duban yanda ya b'ata farin hannunsa... Cikin sauri ya kuma finciko hannunta ya nufo da ita waje, saidai suna fitowa sukayi kicib'is da Innah ta nufo sashen nasa... Kan su ankare sallaman Gaje har cikin kunnuwansu, tanayi tana watsa k'afafu, yanda taga Innah tsaye sororo tana duban su Ahidjo da Deejoh wacce Ahidjon ke rik'e da hannunta ai sai Gaje ta saki salati da sallalami tana tafe hannaye take fad'in "Inyi abin yazo, ashe dai Deejoh har an tare d'akin miji... Yo wannan dank'areriyar motar da na gani k'ofar gida ashe ta mijin naki ne... Oh Deejoh an sami duniya an mance Ard'o, toh zuwa nayi na shaidawa mijin naki mune nan iyayenki ehe dole ko mai akaci a bamu..." Tsaban shock da ya tsinci kansa ciki kasa sakin hannun Deejoh yayi, sai wani irin kallon mamaki da tuhuma da yake bin Innah dashi wacce itama tuni yanayinta ya kuma canzawa... Deejoh kanta bata fahimci abinda ke wakana ba saidai tayi k'arfin halin fuzge hannunta daga rik'on da Ahidjo ya mata ta nufi Innah a guje.... *SameenaAleeyou📚* *18* *©Sameena Aleeyou...✍🏽* Kallon Innah ya kuma yi a karo na biyu idanunsa sunyi jajir sosai... A hankali ya soma fad'in "Innah is that really true... Innah da gaske ne aure kuka min without my knowledge...? Innah aure kuka min da gaske ki amsa min....?" Ya k'arashe yana zaro idanu waje wanda shi kansa baisan yana hakan ba... Gaje dake tsaye gefe yab'e da baki tana kallon ikon Allah sallalami ta soma tana tafe hannaye.... "Oh yau naga duniya, haka kurum a lik'a wa mutum abunda baiji ba bai gani ba bai yaba ba.... Yo ina wannan had'edd'en saurayin ina Deejoh.. Nima dama nasan za'a rina haka.... Haba, haba ai wllhi wannan cutarka kawai akayi yaro mai kyau, wllhi wllhi kar ka yarda, kuma nan da kake ganin Deejoh k'aramar da ita babu kalan mazan da bata sani ba, duk lungu da sak'o da take zagawa talla sai ta mik'a kantawa maza, ni dama zuwa nayi naga kalan zaman da take a gidan sai gashi na tarar angon nata ya iso.... Ayyiriri dole nayi gud'a dukda babu hancin..." Ta k'arashe tana darawa... Tunda ta soma magana Ahidjo ke dubanta, what's all this.... Meke shirin faruwa dashi, meye wannan....? Ko motsawa daga yanda yake ya kasa, dole ma ya tafi ya barsu ya sami k'wakk'waran dalilin da zai tafi abunsa, shine aka masa aure, auren ma a rasa da wanda za'a masa saida wannan yarinyar, haba haba... Ina zai kai wannan hallitar, ko don basu tab'a ganin kalan matarsa bane shiyasa zasuyi kuskuren lik'a masa wannan abar.... No no this is impossible, this can't be... Wllhi bazai d'auki wannan abun ba, ba dashi ba..... Lokaci guda ya juya ya barsu nan tsaye ya wuce d'akinsa... Innah da idanunta suka ciko da k'walla kallon takaici kurum take aikawa Gaje ba tareda ta iya furta koda kalma ba, Gaje kuwa dariya ta fashe dashi had'i da tafe hannaye kana ta matso dab da Innah had'i da sassauta murya tana fad'in "Ai baki sani ba, insha Allahu sai ya dank'arawa Deejoh saki don a rayuwar Deejoh babu jin dad'i, wahala ce ta kamaceta kuma zata dawo nan gaba na taci gaba da bauta daga yanda ta tsaya, wllhi wllhi ina numfashi bazan tab'a barin Deejoh taji dad'in rayuwarta ba.... Bokana yafi naki na fad'a maki...." Tana ida fad'in haka ta kuma murmusawa taja k'afaunta ta fice tana wak'enta dangin su Ayye cika dubaye. Wanda kasan da gayya kawai take..... Sauk'e ajiyan zuciya Innah tayi had'i da goge hawayen da ya zubo mata, ta kalli k'ofar d'akinta wanda tunda aka soma maganar Deejoh ta shige ciki a guje tana kuka.... Ta kuma duban k'ofan d'akin Ahidjo wanda tuni ya rufe k'ofar shima, gaba d'aya Innah ta rasa da waye zata soma cikinsu, anya Gaje tanada zuciya cikin k'irjinta? Tabbas idan tanadashi yayi bak'ink'irin da mugunta da hassada ,k'yashi da sauran muggan abubuwa.... Ta Allah ba tata ba, da yardar Allah Ubangijinta zai shige mata gaba, lokaci guda Innah taji k'arfin tunk'aran yarantan, wajen Deejoh ta soma nufa ta hangeta tak'ure k'uryar d'aki tana kuka... Ta yaya za'a ce D'angayu ne mijinta, ta yaya hakan zai kasance bayan tun had'uwansu kafin su san sud'in ma'arauta ne D'angayu ya tsaneta, ya kirata da sunaye marassa kyau ciki harda Mayya, toh inaga ance zasuyi zaman aure, ashe dai da gaske auren aka mata, ga maganganun da Iya Gaje ta ida fad'i akanta, Allah Sarki lallai maraici mugun ciwo ne ta tabbata da mahaifiyarta na raye k'ila da wasu abun baza'a mata ba.... Hannun Innah da taji saman kafad'unta ya katse mata tunanin lokaci guda ta d'ago kai tana goge hawayen da ya wanke mata fuska..... *** *Tambuwal* Shiru Nazir yayi yana duban Daddah k'irjinsa na bugawa, she's damn serious garin zasu bari..... D'an gyaran murya yayi kafin ya soma fad'in "Daddah gaskiya wannan karan bazanbi bayanki ba, ya kamata ku nitsu waje guda keda d'iyarki koda ba aurarta zakiyi ba, don nima bana goyon kiyi aurenta sai mahaifinta ya bayyana sabida gudun wulak'ancin mutane da kuma zarginsu, amma Daddah is high time ki sanar da Mairo wacece ita, sannan ki daina gujewa mutane ku nutsu waje guda, a yanda na sanki da taron fad'a ban zaci har akwai D'an Adam d'in da zai baki tsoro da shakku ba har ya sanyaki gujema gari wa gari...." Tunda ya soma magana hanci d'age take dubansa, babu abinda yafi k'ona mata rai kaman cewa da yayi tsoron wani takeji, yo wani d'ancin k'aniya zataji tsoro, Mairo itace rayuwarta idan ta tsaya ta fuskanci matsalanta gaba da gaba tabbas dangin Mairo zasu rabata da ita, don dai Bulama ba tsoronsa take ji ba, duk randa sukayi gaba da gaba wllhi alwashi ta d'auka sai ta watsar masa da ragowar hak'waran gabansa koda zai mata d'aurin rai da rai.... Ganin Daddah ta masa shiru babu amsa yasan idan ya sake magana abun bazai masu da kyau ba.... A hankali ya mik'e had'i da d'an rusunawa kana yace "Daddah ni zan wuce, sai anjima...." A dak'ile tace dashi "Mu jima da yawa...." Nazir ya hangi k'ofar d'akin Mairo wanda tunda ya rakota cikin gidan ta k'ule uwar d'akin ta saka sakata... Ya d'iba mintoci tsaye a wajen kafin ya fice.... Daddah ta kuma jan tsaki had'i da tab'e baki kana ta soma fad'in "Shegen felek'e da firirta, ya wani soma min turancin iskancin banza saikace ni nace masa yawo wa gari wa gari na damuna, ba don kar naci masa mutunci ya daina shigo min na rasa mai shawo min kan Mairo ba da ya gane kurensa... Matsolon banza kawai..." Tana kaiwa aya ta mik'e ta nufi kitchen don girka wa Maironta abinda tafi so D'anwake..... Nazir yana isa gida ya kunna wayarsa aiko take yaga sak'insa ya shigo, dama yasan za'a rina.... D'an dafe kansa yayi had'i da fuzar da iska.... Allah sa dai kar matan nan ta janyo masa rashi, dole ya shawo kanta cikin kwanakin nan.... Da wannan tunanin ya kunna laptop d'insa ya tarar wasu sak'on a email d'insa..... *** *Abuja* Suna gefe suna supervising ma'aikata lokaci guda sabo mai tsanani na kuma shiga tsakaninsu.... Aunty ce ta k'araso rik'eda crutches d'inta tana nuna masu wasu takardu had'ida neman shawarinsu kan sana'o'i da zasu k'ara a foundation d'in tunda gashi anyiwa sabbin shigowa register.... "Junaid mai ka gani...?" Aunty Lami ta tambaya tana duban Junaid wanda ya d'anyi shiru kaman mai nazari..... Jinjina kai yayi kana yace "Gaskiya ne Aunty Lami ya kamata a k'ara yawan sana'o'in tunda ci gaban foundation d'in ne...." Asma'u tayi shiru tana nazari kana tace "Nima zanso hakan Aunty amma tunani na d'aya kar najewa Uncle da maganar yaga kaman karb'an kud'i kawai nake sonyi tunda dole a saya machines...." Aunty Lami data kawo shawarin shiru ta d'anyi tana nazarin batun kana tace "Gaskiya ne Nana A, kuma dududu ba'a jima da bud'e Foundation d'in nan ba, mu bari idan mun saida abubuwan da ake kan had'awa da jarin sai mu k'aro wasu machines d'in ko yaya kuka gani....?" Ta k'arashe tana dubansu Junaid ne ya d'an turo wheelchair d'insa kusansu sosai kana ya soma fad'in "A tunanina mu k'aro yawan machines d'in tunda mun riga munyi register ma wasu bazamu barsu babu aiki ba, sannan kud'in nan dole daga Company zai fito ba daga aljihun Uncle d'inki ba, besides shi kansa Uncle idan yaji abinda za'ayi da kud'ad'en zai farin ciki.... Ko yaya kuka gani.....?" Ya k'arashe yana dubansu da innocent face d'insa.... Aunty Lami da Asma'u suka kalli juna kafin suka murmusa, Aunty Lami tace "Gaskiya ne Junaid, kayi gaskiya kuma na gamsu da shawarinka...." Murmushi kawai Asma'u tayi tana duban coworkers d'in nata, har cikin zuciyarta take jin dad'i tun bayan da ta gama jami'a ta zama bored a gida bata zuwa aiki amma yanzu tana jin dad'i sosai, zuwa Foundation yakan sakata farin ciki da mutanen dake ciki..... Tuni itama ta amince da shawarin Junaid ta kuma tabbatar masu cewa yau d'in nan da zaran ta koma gida da yardar Allah zatayiwa Uncle maganar washe gari ta taho masu da feedback.... Akan haka suka samu matsaya ko wannensu cikeda farin ciki.... Shi kad'ai yake duban Nana A yanda take murmushi yana sak'a abubuwa da dama cikin zuciyarsa, he's gonna use her and ruined Siraj completely...... Koda Lamid'o ya Krista don zuwa d'aukarta sai sanar dashi tayi zata dawo da Aunty Lami don zasu biya duba kayayyakin da ya kamata su k'aro a foundation d'in nasu... Aiko nan driver d'in Aunty Lami ya kwashesu gaba d'aya Junaid na gaba yayinda Aunty Lami da Nana A ke zaune a baya, sai raha suke gaba d'ayansu, sosai suka sake da juna, store daban daban suka biya... *** Fasa shiga motar yayi tunda tace masa basai yaje d'aukarta ba, lokaci guda ya rufe motar yana k'ok'arin komawa cikin gida yaji mutum rungume dashi ta baya.... Ko ba'ace masa ba yasan itace.... A fusace ya juyo yana k'ok'arin b'anb'areta daga jikinsa yake fad'in "Let go of me you piece of garbage....." Saidai kafin ya ankare ta soma sunbatarsa ta ko ina kaman tsohuwar mayya... K'ok'arin k'wace jikinsa yake yana fad'in "Nana H what do you think you are doing.... Just... Let go of me.... Ki sake ni nace...." Kaman cewa yake ta k'ara, fad'i take "No darling I know you want this.... Just don't deny it... Don't you miss me.... Abunda muka saba ne Lamid'o.. I told you can't get rid of H so easily.... Mu ci gaba kawai daga yanda muka tsaya...." Ta k'arashe tana kuma masa wasu salo... Da k'arfin gaske ya murd'e hannayenta had'i da fincike jikinsa yana fad'in "You really are insane.... Bakida hankali Nana H... Sau nawa zan sanar dake I love your Sister, I love her so much... With all my heart... Get this pls....." Huci take tana dubansa lokaci guda hawaye ya ciko idanunta, cikin zafin rai ta soma fad'in "Lamid'o you can't do this to me... I know you love me... Wllhi kana sona, you're only confused, dan Allah kar ka juya min baya, wllhi bazan iya jure rashinka ba.... Please don't... I love you wllhi..." Cikeda tausayi yake dubanta yana tunanin duk yanda akayi kwanyarta nada matsala, girgiza kai yake still na rik'eda kafad'unta kana ya soma fad'in "Nana H, you're sick, you really need to see a doctor... Or if you want I'll talk to Siraj kina buk'atan likitan kwanya.... Please Nana H ki yarda kiga likita, ta yaya zaki makance akan Maza uku duka ke kad'ai.... Wllhi na jima da sanin soyayyar da kikewa Siraj ya wuce na Kawu kawai, soyayyar da bazai tab'a faruwa tsakaninku ba kike masa.... Nana H you can't go on like this... Na rok'r arzikinki dan Allah ki barni na jarabba soyayya da Nana A for the first time in my life.... Dan Allah... Wllhi na sani kamuwan Allah ne ya jefa min soyayyar Asma'u cikin zuciyata tunda a baya banza bola na d'auki mata, sai gashi soyayyar macen dake da nakasa jikinta ya hanani sukuni bayan dubun 'yan matan dana wulak'anta abaya duk a dalilinki... Nana H I beg of you ki rabu dani dan Allah..." Kuka sosai ta fashe dashi had'i da fad'awa cikin k'irjin Lamid'o..... *Hetches ina gaisuwa😎* *SameenaAleeyou📚**FUSKA UKU*🏮 *19* *©Sameena Aleeyou...✍🏽* A hankali ya cire jikinsa daga nata yana binta da kallon tausayi yanda take kuka sosai... "Look Nana H ki rik'e mijinki and try to change for the best, Ahidjo na k'aunarki sosai pls kar kiyi wasa da damanka, oya let me walk you out...." Ya k'arashe yana mai nuna mata hanya... Lokaci guda taci gaba da huci tana dubansa... "Lamid'o bazanyi abinda kake umartana ba, bazan fita daga rayuwarka ba, sannan idan baka d'aga idanunka kan 'yar uwata ba I'm afraid things might get worse, I'm.... capable of doing anything,...." Daga haka ciro shades d'inta tayi ta rufe idanunta dashi ta fice daga gidan.... Kallo yabita dashi har ta fice kafin ya fuzar da iska ya nufi cikin gidansa.... Shi kad'ai ya kifa kansa yana tunani... Ya kamata ya takawa mahaukaciyan nan birki before she does something drastic, and especially to Asma'u... Yasan Nana H bata hankali zata iya yin komai d'in kaman yanda tace.... Lokaci guda ya mik'e ya kuma suran car keys d'insa ya fice a gidan.... *** Zaune suke a parlor shida Ammah suna tattauna wasu 'yan lamra, dowawarsa kenan shima d'in ko sashensa bai nufa ba.... Ko sallama babu tasa kai ta shigo gidan har lokacin shades d'in manne idanunta... Ko kollon arziki basu isheta ba balle su sami darajan gaisuwa ta nufi up stirs abinta.... Daga Ammah har Siraj kallo suka bita dashi, Siraj yayi saurin mik'ewa ya isa gareta yana kirawo sunanta, inaa ko kulasa batayi ba tasa kai abinta har saida ta shige d'akinta... Zata maida k'ofan ta rufe Siraj yayi saurin rik'e k'ofan ya shige d'akin... "Uncle please not now...." Ta fad'i tana ajiye jakanta had'i da kwab'e dogayen takalmanta.... "Nana H, Sweetheart are you still mad at me? Look I'm sorry, kiyi hak'uri kinji... Ina sonku both you and your Sister and bazan bari inaji ina gani na bari wani abu ya cutar daku ba, idan har na bari hakan ta kasance toh kuwa ina mai tabbatar maki bazan tab'a yafewa kaina ba.... I'll never ever stop being over protective... Sabida a idanuna har gobe ku yara ne, yaranda nake d'auka a kafad'una, sannan dukda banida cikakken hankali da girma sanda mahaifanku suka rasu bazaisa nace kud'in ba amana bace a hannuna.... I love both so much... Like my own..." Tunda ya soma magana take dubansa da idanunta da suka kuma yin rau-rau, lokaci guda ta k'arasa cikin sauri had'i da rungumesa ta shiga rera kuka.... Lallashinta Siraj yake yana bata hak'uri, Nana H taci gaba da fad'in "Uncle please kar kayiwa kowa irin soyayyar da kake min cikin zuciyarka, Uncle please don't ever stop loving me... Kaji Uncle, wllhi idan ka daina sona mutuwa zanyi...." Dafe da bayanta Siraj yake fad'in "That will never happen, never ever Sweedy... You are my Favorite Niece, and you'll always hold that special place in my heart...." Ya k'arashe yanai mata nuni da k'irjinsa murmushi kwance saman fuskar sa..... Murmushin itama take dad'i ya mamaye zuciyarta... Siraj na murmushi yana kuma calming d'inta yake fad'in "Let's have lunch outside... I'll just get changed OK..." Ya k'arashe yana fad'ad'a murmushinsa... "Oh really Uncle... Oh you the best.... I love you...." Ta fad'i tana tsalle had'i da rungumesa... "Anything for my precious.. Mu jira Nana A ta dawo sai mu fita gaba d'aya koh... Ko ya kika gani....?" Nan da nan tayi kicin-kicin da fuska baki a ture take fad'in "Uncle nidai just the two of us ya isa besides bamusan yaushe zata dawo ba, and I'm starving already...." "Alright fine, barin canza I'll be down in a bit...." Cikeda murna ta masa rakiya har k'ofan d'akinta kafin ta dawo da baya had'i da lumshe idanu.... "Uncle Siraj is the most kindhearted person I've ever known...." Ta fad'i idanu a lumshe, sauri-sauri itama ta canza shigar nata zuwa wani silk material d'inkin doguwar riga wanda ya kwanta a jikinta sosai kana iya ganin suran jikinta yanda ya bayyana tamkar ba d'iyar musulmi ba... Kaico Allah ka wadatamu da karatun addini..... *** Tafe suke a mota bayan sun tashi a aikin, donma ta d'an tsaya ta jira Nasaar ya kammala wasu ayyukan a nasa a office d'in, kallonta da wistiyar idnu yayi yaga gaba d'aya hankalinta bai wajen, da alama bata ji dad'in aiki da Siraj ba a ranarta na farko.... D'an gyaran murya yayi kana yace "So how did it go.... Ya kika sami boss d'in naki, mai kirki ko kuwa akasin haka....?" Ya tambaya idanunsa naga kwalta... D'an fuzar da iska tayi kana tace "Not too bad.... Dama nayi tunanin hakan zata rina faruwa, what matters is that I got employed sannan zanyi amfani da damata na taimakawa d'an uwana ya cika burinsa, it breaks my heart seeing him spending the rest of his life on that wheelchair...." Ta k'arashe had'i da sauk'e nannauyan ajiyan zuciya kafin ta d'ago ta dubi Siraj sosai fuska cikeda damuwa take fad'in "But do you think I'm doing the right thing.. Kanaga ban taimakawa b'arna ba... What if Allah ya tuhumeni, mai zance wa ubangiji na.... Anya banyi kuskuren taimakawa Junaid ya d'auki fansarsa ta hanyar da bata dace ba.... I'm afraid... Wllhi ina tsoron kar abubuwa su zama worse ta dalilina...." Rage speed yayi had'ida d'an dubanta kafin ya maida idanunsa ga kwalta yana mai ci gaba da fad'in "Zeeza you're not doing anything wrong.... FUSKA UKU sun cutar da Junaid cuta mafi muni a duniyarsa, kuma kaman yanda Junaid ya fad'i a wannan duniya tamu ko kace zakayi shari'a da mai kud'i bazakayi nasara ba, wannan shine hanya mafi sauk'i da zai rama abinda aka masa tunda bazai iya yafewa ba...." Murya na rawa Azeeza take fad'in "But Barrister meyasa shi bazai zamto daga cikin bayin Allah masu yafiya da hak'uri ba, Allah fah yana son masu afuwa..... Da ace iyayenmu suna raye na tabbata da bazasu goyi bayan wannan fansa da Ya Junaid ke neman d'auka ba.... Barrister pls stop him kaji dan Allah...." D'an murmusawa Nasaar yayi yana shiga kwana kana yace "Zeeza kenan, Yayanki yayi nisa da burin d'aukan fansa, I don't think akwai wani mahaluk'in da zai hanasa k'arasa abinda ya riga ya soma, abinda ya zab'a kenan mu taimaka masa ya k'arasa tunda shi aka zalunta.. Na sani Fansa ba abune mai kyau ba amma muddin baki so ki rasa yayanki dole ki taimaka masa ya cika burinsa, kar ki mance kin rasa iyayenki already.... Junaid kawai kike dashi, and fasa d'aukan fansar nan ga Junaid na nufin rasa rayuwansa ne, you perfectly well know this...." A hankali ta sauk'e ajiyan zuciya had'i da gyara zamanta cikin motar, tabbas abinda Barr ya fad'i gaskiya ne, kuma idan tace ta cire kanta tabbas zata iya janyowa Nasaar ya rasa aikinsa, tunda idan Siraj yasan komai harda shi za'a kora..... A hankali tasa tafukan hannayenta ta rufe fuskarta.... Nasaar na hankalce da ita bai zarce dasu ko ina ba sai wani eatery mai d'an sauk'in kud'i.... Mamaki ya cika Azeeza ganin yanda Nasaar ya kawota... K'ak'aro murmushi ta d'anyi kana tace "Kai Barr wllhi I'm OK, you don't have to worry about me... Wllhi da mun wuce gida kawai...Kar ka damu I can still cook. Kuma kaga su Hammad na tabbata sun koma gida and they must be hungry....." Kallonta yake tunda ta soma magana kana ya d'an murmusa yace "I insist, please let's eat here.... Sannan kar ki damu dasu Hammad zamu sai masu a nan idan munci, kinga kema kin huta da girki sai ki huta kawai...." Kaman bazata fita daga motar ba sai kuma ta d'an murmusa ta bud'e marfin motar ta fito tana fad'in "OK shikenan babu damuwa, tunda kace haka, don ni dama yarana ne banso a barsu da yunwa...." Annurin fuskar Nasaar ya k'aru jin yanda Azeeza ke matuk'ar k'aunar yaransa.... A tare suka jera suka shige har cikin restaurant d'in, suka sami table suka zauna kafin waiter ya k'araso yana tambayansu order..... *** Cak ya tsaya yana sauraren mahaifin nasa daga cikin waya yanda yake ci gaba da maganar cikin fad'a... "Look, I'm not paying you huge amount of money to be Imbecile.... Ta yaya zaka fad'i min haka, no bazasu bar wannan garin ba, kada ka kuskura ka bari su bar wannan garin, wllhi wllhi idan suka b'ace maka ni da hannayena zan kasheka..... Kaji na fad'a maka.... Useless kawai....! " Daga haka katse wayar yayi yana huci lokaci guda yake dogara sandarsa yana masifa shi kad'ai... Dai-dai nan Lamid'o yayi sallama ya shigo wargajejen parlorn.... Kallon wulak'anci Alhaji Bulama ya watsa masa ba tareda yace komai ba har ya isa saman kujeransa ya zauna.... Saman carpet d'in dake baje tsakiyar parlorn Lamid'o ya durk'usa saman gwiwoyinsa yana gaida mahaifin nasa..... Bai amsa ba sai kunna sigari da yayi yana zuk'a idanunsa naga tapkeken k'ofar glass dake can bayan parlorn..... Lamid'o ya k'ara fad'in "Daddy mun yini lafiya....." "A gidan uwarka na yini lafiya, shege tsinanne maras neman albarka, har sau nawa zan ce maka ni ba mahaifinka bane har sai ka cika min burina.... Shashasaha kawai k'aton banza....." Tunda Alh Bulama ya soma magana Lamid'o ke huci, zuciyarsa na masa wani irin zogi da rad'ad'i... Murya a dake ya soma fad'in "Alh Bulama I'm sorry, but I can't do what you are asking me to do... I just can't.... Sannan nazo nan ne na sanar da kai koda bazaka saurareni ba.... Zan nemi auren Asma'u Laushi d'iya ga marigayi....." Baikai aya ba yaji sauk'an sanda a kafad'arsa Alh Bulama ya kwad'a masa.. Cikin huci yaci gaba da fad'in "I see.... So wannan shine reason d'inka? Shine dalilin da yasa ka zama soko maras amfani, na turaka ka min aiki ashe kana can kana hauka kan gurguwar mace.... What's gotten into you Lamid'o... Giyan naka ya soma fad'a maka k'arya har haka.... Toh wllhi baka isa ba.... Baka isa kazo min da wannan cancen ba kana jina.....!!" Ya k'arashe cikin tsananin daka tsawa... Sassauta murya Lamid'o yayi yana fad'in "Please Baba ka k'yaleni na sami farin ciki na... I dedicated my entire life wajen yin duk wani aiki daka umarceni,...." Ya d'an ja fasali hawaye na neman ciko idanunsa yake ci gaba da fad'in "Daddy.... I never loved any woman before .... I just took women for granted that I thought it was my right to discarded them like an old socks when I'm tired with them.... Now I've punished for that arrogance fate gave me the only woman who could put me on my place.... That woman is Nana Asma'u... I love her with all my heart..." Shaye da mamaki kurum Alhaji Bulama ke duban Lamid'o lokaci guda ya kece da dariya kana yace "Bansan bakada hankali ba sai yau.... Idan karen hauka ya cije ka ka kuma zuwa min da zance makamanciyar wannan... Wllhi wllhi kaji na maka rantsuwa rufeka zanyi a d'aki a nemeka a rasaka, kuma banda abinka ai idan ka tonawa Sirajo ko kai wanene shine mutum na farko da zai soma dab'a maka wuk'a.... Ban fara irin wannan wasan dakai ba... Maza tashi ka bani waje... And don't forget I have eyes everywhere.... Don't try anything foolish...." Daga haka mik'ewa yayi ya shige d'akinsa.... Lamid'o ya dafe kansa yana tunanin ta yanda zai soma b'ullowa lamarin.... Tabbas yaji mahaifinsa na waya kenan ba dashi kad'ai mahaifinsa ke aiki wajen ruining Laushi Family ba harda wasu, dole ya zak'ulo koma wanene ta haka ne kurum zaisan bak'in k'udirin da ya jima cikin zuciyar mahaifinsa.... Da wannan tunanin ya mik'e zai fice daga parlorn.. Har ya kai k'ofa ya hangi wayar mahaifin nasa saman table cikin sand'a ya dawo da baya ya d'aga kai sama yaga babu wata camera a parlorn, lallab'awa yayi ya suri wayar ya fice cikin sauri...... *** Dai-dai k'ofar restaurant d'in yayi parking kafin ya juyo ya dubi Nana H dake faman bin restaurant d'in da kallon k'yama kana yace "Sweetheart muje koh...." Girgiza kai tayi tana mai murmusawa disbelievingly kana tace "Oh wait... Uncle I don't know that you're eating in this kind of place.... It doesn't suite your personality.... Haba Uncle ai da kunya aga muna shiga restaurant d'in nan...." Ta k'arashe tana kuma yamutsa fuska.. Murmushi kawai Siraj yayi kana yace "Yeah wani sa'in nakan je wurare masu sauk'i domin nayi experiencing rayuwa mai sauk'i, yin hakan nada kyau... Kar ki damu abincinsu da dad'i na tabbata you'll definitely love it... Oya zo muje....." Ya k'arashe yana ficewa daga motar..... Yatsina fuska ta kuma yi ba don taso ba ta sauk'o daga motar suka nufi cikin restaurant d'in, cikin sauri ta sakale hannunta cikin na Siraj ganin wasu 'yan mata a gefe suna binsa da mayen kallo... Tunda Nasaar ya soma magana ta kasa ci gaba da cin abinci sai faman bugu da k'irjinta keyi, da gaske Nasaar sonta yake, toh anyama ita tama san meye soyayyan?...... Muryasa ya katse mata tunaninta sanda yaci gaba da fad'in "Azeeza tun ranar da na soma had'uwa daku a train station, tun ranar da na soma d'aura idanuna akanki Allah ya jarabceni da k'aunarki.... I love you Zeeza like I never loved anyone before..... Dan Allah ki zamto mahaifiya ga yarana wanda suka rasa tasu mahafiyar...." Ya k'arashe idanunsa kan fuskarta... A hankali ta d'ago idanu tana dubansa ba tareda ta iya furta koda kalma ba... Cak Siraj yaja ya tsaya sanda ya hangi table d'insu Nasaar.... Bata iya baiwa Nasaar amsar tambayarsa ba sai fad'uwar gaba mai tsanani da ya ziyarceta, lokaci guda tamkar wacce aka zabura ta waigo tana duban bayanta, aiko nan ta hangesa tsaye hannunsa sakale cikin na wata kyakkyawar budurwa maijida gayu, ganinsa da budurwar sai yafi haifar mata da fad'uwan gaba fiyeda tambayar da Nasaar yayi mata....... *SameenaAleeyou📚*[1/7, 8:47 AM] ‪+234 802 741 0766‬: *FUSKA UKU*🏮 *20* *©Sameena Aleeyou...✍🏽* Lokaci guda Azeeza ta saita kanta sanin cewa janyo hankain Siraj ya auka wa soyayyarta shine mak'asudin soma aiki a kampaninsa, amma kam tasan ba abu bane mai sauk'i ta iya abinda Yayan nata ya umarceta domin kuwa Siraj nada wani irin baiwa da gizo wanda ba ko wani d'an Adam Allah ke badawa ba.... Nasaar ne yayi saurin mik'ewa ya isa ga Siraj yana gaidashi, shiko Siraj d'in idanunsa k'yam kan Azeeza ganin yanda tayi banza kaman bata gansa a wajen ba dukda ya kasance Oganta wajen aiki, takaicin yarinyar ya kuma turnuk'esa... Nasaar yaci gaba da fad'in "Sir ku zauna mana barin je na sami waiter d'in, ku zauna please ga menu...." Banda kallon wulak'anci babu abinda Nana H keyima Nasaar, koda ya gaidata ma a yastine ta amsa.... Fuska babu yabo babu fallasa Siraj yace "Kar ka damu Nasaar waiter d'in zai k'araso... If you don't mind zamu zauna a table d'inku...." Nasaar ya fad'ad'a murmushinsa yana fad'in "Sure Sir... this will be a huge honor ...." Ya k'arashe yana gyaramasu kujerun.... Gaba d'aya tak'i yarda ta d'ago kai su had'a idanu da Siraj shiko ko k'yafta udanu akanta baiyi.... Har saida ya zauna saman kujeran kafin Azeeza tayi ta maza ta d'ago kai suka kuwa had'a idanu.... Lokaci guda ta saki murmushi had'ida yin fari da idanu tana fad'in "Barka da rana Sir, what a coincidence....!" "Barkanki...." Ya fad'i a tak'aice... Murmushi bai bar saman fuskar Azeeza ba ta maida dubanta ga Nana H wacce ke binta da kallon tsana "Barka da rana Hajiya, it's a pleasure meeting you..... Oh by the I'm Azeeza.. And.... His new secretary..." Ta k'arashe idanunta kan Siraj wanda mamakin yanda Azeeza ke faman zuba ya hanasa tab'uk'a komai... Wani irin murmushin rainin hankali Nana H tayi tana bin hannun Azeeza da kallon k'ask'ance alamun tafi k'arfin ta mik'a mata hannu suyi masabaha kana tace "Oh! What an introduction... It's good that I bumped into you, Janet tasan dokokina akan Uncle love sabida haka kema ya kamata ki sani... Kodayake seems you're on a date bai kamata na katse maku soyayyarku ba... Keda saurayin naki kun dace, if I'm not mistaken kaman kaman nasan fuskar nasa a Laushi group...." Isowan waiter ne ya katse shiru da ya gifta tsakanin tun sanda Nana H ta soma magana.... Siraj shi ya bada order d'in nasu lokaci guda Azeeza ta saita kanta don ta lura wannan matar cikakkiyar 'yar bariki ce kuma taji ta kirawo Siraj da Uncle kenan ba matarsa bace... Gyara zama Azeeza tayi fuskarta cikeda murmushin girma kana tace "Allah sarki gashi kuma ni bana bin doka ko wacce iri ce idan ba ta Allah bace.... Ya kenan za'ayi...?" Siraj ya kasa furta komai sai kallon mamaki da yake binta dashi... Nana H kanta mamakin Azeeza ya hanata daina kallonta... Shiko Nasaar ganin Azeeza na neman yin b'aranb'arama ya sanya sa mik'ewa babu shiri yanai ma Azeeza idanu kafin ya furta a d'an daburce.... "Em.... Em zamu wuce Sir, yara sun dawo daga school su kad'aine a gida.... Azeeza tashi mu k'arasa gida...." Ya k'arashe murmushin yak'e saman fuskar sa.... D'an far Azeeza tayi da idanunta kana tace "Kai brother da wuri haka...?" Tayi maganar cikin sigan shagwab'a wanda ya kuma tunzura Nana H, wannan wacce irin shegiyar yarinya Uncle ya samu matsayin sakatariya,....? Muryar Azeeza ya kuma dawo da Nana H daga duniyar tunanin da ta tafi.. "Toh Sir sai mun had'u a company... Enjoy your meal...." Ta k'arashe tana wani kashe masa idanu.... Ai bata ida fita daga cikin kujeran ba Nana H ta mik'e a fusace ta shak'o mayafin Azeeza tana fad'in "Shegiya karuwa wllhi Uncle Luv yafi k'arfinki kuma wllhi sai kin kampanin tunda bana ubanki bane....!" "Hafsaaat! " Siraj ya kirawo sunanta cikin daka tsawa kana yaci gaba da fad'in "Lafiyanki k'alau, kanki guda zaki tara mana mutane.... Meye haka kike tunanin kinayi..?" Nasaar hankali tashe ya shiga baiwa Siraj hak'uri yana fad'iwa Azeeza su bar wajen... Nana H taci gaba da fad'in "Uncle wllhi karuwace bakaga fari da idanun da take maka ba, Uncle bakaga felek'en da take maka ba...." "Ya isa pls....!" Siraj ya katse ta... Shaye da mamaki take dubansa yanda yake daka mata tsawa kan wata banzar secretary... Azeeza kuwa murmushin cin nasara tayi had'i da cire hannun Nana H daga jikin mayafinta kana ta d'an marairaice fuska tana duban Siraj tace "Sir kayi hak'uri dukda bansan matsayinta a wajenka ba, but what she just did was an insult... A distinguished person like you bai kamata a bada kai in public irin haka ba.... I'm sorry Sir, Allah ya huci zuciyarka..." Ta maido da dubanta ga Nana H tanai mata kallon naci uwaki a bariki, bata furta mata komai ba sai murmushin da ta sakar mata kana tasa kai ta fice daga restaurant d'in.. Yanayin abubuwan da Azeeza kewa Siraj har cikin ransa yakeji dukda yasan acting ne kawai ba gaskiya ba tinda shi da gaske soyayyar Azeeza Yake... D'an gyaran murya yayi had'ida baiwa Siraj hak'uri kafin yabi bayan Azeeza cikin sauri.... Nana H baki sake tabi bayan Azeeza da kallo... Lallai wannan shegiyar yarinyar zataci uwarta ta gyara mata zama... Bata san wacece H ba, batasanta ba, tabbas da batayi gigin shiga gonarta ba... Kambala'i wai ita wannan kucakar zata nunawa bariki, wannan yarinyar a shekare ai bazata wuce sha tara ba, har ita H kaman wannan yarinyar zata taka ta zata shige.... Tayi wata silent murmushi kana taci gaba da zancen zucin nata. .. Zan koya maki hankali yarinya, aiki a Laushi Group ya zama min dole, dole na karb'i gurbin aikin da nak'i karb'a a baya ko don na saita wannan k'aramar 'yar iskar yarinyar... Barin Uncle da irin wad'annan karuwan had'ari ne.... Maido da dubanta ga Siraj tayi wanda ya had'e hannayen sa biyu alamun tun fitar su Azeeza tunani yake.. Ita gaba d'aya ta lura dashi tunda suka shigo wannan gidan cin abinci yanayin Siraj ya canza, gaba d'aya ji tayi tama k'oshi da abincin... "Uncle....!" Shiru bai amsata ba, alamun yayi nisa duniyar tunani.. "Uncle Love...!" Ta k'ara fad'i da d'an k'arfi wannan karon... "What Azeeza...!!" Ya fad'i a d'an harzuk'e... Da gaske kiranta yayi da Azeeza.... Lokaci guda bak'in ciki ya kuma turnuk'eta.... A fusace ta suri handbag ta nufi k'ofa.. Waiter na tafe da tray yana fad'in "Miss here is your order....." Cikeda masifa ta dubi waiter d'in kana tace "You know everything here is disgusting... I lost my appetite, excuse me..." Siraj ya shafi kansa wasu irin tunani suna yawo a kwanyarsa, baiso ya sakawa ransa haka d'in ne... Cikin sauri ya mik'e yabi bayanta yana mai kiran sunanta.... *** Tak'aitaccen dariya yayi idanunsa naga kwalta yake fad'in "Kai a gaskiya kinyi k'ok'ari ban zaci zaki iya abinda kikayi ba...." Murmushin itama tayi kana tace "Hmm wllhi Barr kar kaji bugun da k'irjina keyi, gaba d'aya tunani nake Siraj zai iya firing d'ina sai gashi ya kasa katab'us, domin daga fari na zaci matarsa ce...." Nasaar ya d'an kuma murmusawa kana yace "D'aya daga cikin 'ya'yan marigayi Yaya ga Siraj ne, Siraj yanaji da ita sosai fiye da d'ayar niece d'in tasa...." Shiru Azeeza tayi tana nazarin maganganun.... lokaci guda take mamakin yanda Nana H ke kishin kawun nata, abin ya zarce misali. Abin tamkar a shirin film.... Suna isowa gida, Nasaar ya d'an juyo yana dubanta had'i da kashe murya.... "Zeeza ya maganar tamu.....?" Ya k'arashe yana narkar mata da idanu..... Lokaci guda k'irjin Azeeza ya kuma bugawa... D'an sadda kanta k'asa tayi murmushi saman fuskarta... Ganin haka ya sanya zuciyar Nasaar yin sanyi ga dukkan alamu Azeeza ta fad'awa soyayyarsa.... Murmushi ya sakar mata kana yace "Kar ki damu I'll give you enough time to think....." Still idanunta a k'asa ba tareda ta iya furta koda kalma ba. Isowar Taheera wajen tanai masu oyoyo ya katse shirun nasu.... Tuni Azeeza ta fice had'i da rungumar Taheera... Nasaar ya bisu da kallo zuciyarsa nai masa wani irin sanyi.... *** *Misau* Misalin k'arfe 8:00pm ya fito rik'eda jakar kayansa don ya tabbata Baffah bai shigo gida ba yana masallaci sannan saida ya tabbata Innah ma ta soma sallah sannan ya fito.... Kallo yabi gidan dashi yana zancen zuci... Tabbas yaso zama wannan karan ya nemi albarkan iyayensa saidai bazai iya ba.... Bazai iya zama bayan aure su tilasta masa tarewa da wannan yarinyar ba.... A hankali ya furta "I'm Sorry Innah.... I'm sorry....." Lokaci guda yasa kai zai fice sai ji yayi an rik'o jakansa.... Shaye da mamaki ya juyo yana dubanta... Hawaye kwance saman idanunta sukayi ido hud'u.... Girgiza masa kai ta shiga yi tana mai ci gaba da hawaye take fad'in "Dan Allah kar ka tafi.... Kada ka kuma tafiya ka bar Innah... Wllhi idan ka tafi zata kuma komawa cikin damuwa da k'unci.... Ince sabida ni zaka bar gidan? Toh na maka alk'awari zan tafi, zan koma ga Iya Gaje koda zata ke yankan naman jikina ne.... Idan dai hakan zaisa ka zauna, idan hakan zaisa farin cikin Innah ya dawwama..... Innah da Baffah mutanen kirki ne dan Allah kada ka tafi ka k'yalesu kaji... Kaine farin cikin su....." Ta k'arashe murya na tsananin rawa... Tunda ta soma magana yake duban fuskar ta, badon muryarta da yaji ba sai yace ba ita bace sabida tunda yazo gidan bai tab'a ganinta babu kwalliyan aljanai ba sai yanzu, kenan wanke kwalliyan tayi, asalin kalan fuskarta sai ya fito da kyaun tsari babu zanen gira dasu hodar nan da take shafawa.... Muryar Baffah ya katse shirun nasu... "Khadijatu sakar masa jakarsa yayi tafiyar sa, idan sabida auren Deejoh zaka tafi... Ka tafi Aliyu dama ba yau bane fari... Kada ma ka fake da auren Deejoh... Fice min a gida....." Dai-dai lokacin Innah ta fito casbaha a hannu tana hawaye take fad'in "Malam dan Allah kada kace haka kada kace yayi tafiyarsa, dan Allah Malam..." Katseta Baffah yayi ta hanyar d'aga hannu kana yace "Ki k'yalesa ya tafi dama bamu muka gayyatosa ba shi ya kawo kansa... Kuma wllhi wllhi kaji na maka rantsuwan musulmi aurenka da Deejoh babu fashi tinda ba kai ka biya sadakin ba....." Daga haka Baffah yasa kai ya shige d'akinsa.... Cikin sauri Ahidjo ya take masa baya, nan ya tarar Baffah na k'ok'arin zama ya cire hulansa... Durk'usawa yayi saman gwiwoyinsa daga can gefe, shiru ya gifta tsakani kaman babu mai cewa komai... A hankali Ahidjo ya soma fad'in "Amma Baffah da an nemi shawarina kafin a aura min yarinyar nan.... Baffah gaskiya...." Tsawan da Baffah ya buga masa ya hanasa ci gaba da magana... Cikin tsananin fushi yaci gaba da fad'in "Har ni kake cewa ba'a nemi shawarinka ba... Kai wanene... Waye kai da sai an jira shawarinka... Sanda zakayi auren barikin naka shawarin wa ka nema... Sabida bakada mutunci zaka dubi tsaban idanuna kace a nemi shawarinka.... Toh ank'i a nemi shawarin naka sai ka d'auko bindiga ka harbeni tinda ban nemi shawarinka ba..... Kuma barin fad'a maka idan ka fice ka tafi ka nemi wani uban bani ba kaji na fad'a maka....." Daga haka uwar d'aki ya shige ya bar Aheedjo durk'ushe a wajen abin duniya ya damesa..... *** *Tmbuwal* Duban Mairo ta kumayi a karo na biyu tana mai ci gaba da tura kaya cikin jaka..... Ganin Mairo batada niyyan tashi balle ta had'a kaya ya sanya Daddah daina abinda take ta isa ga Mairo... Hannayen Mairo ta kamo tana mai duban fuskar ta.... Murya a hankali tamkar ba Daddah ba ta soma fad'in "Mairo kiyi hak'uri wata rana komai zai zama labari, nasani a matsayina na mahaifiyarki ban kyauta maki ba, ban barki kin nemi ilimin zamani yanda kikaci buri ba, sannan ban barki kin zab'i abokin rayuwarki ba iya shekarunki.... Mairo ki sani Daddah na yin duka wad'annan abubuwa ne sabida tseratar dake da kuma mutuncin ki.... Mairo wllhi nafi k'aunarki fiye da kaina, na tabbata wata rana koda bani raye zaki fad'i hakan.... Maza tashi ki kintsa domin ficewar dare nake so muyi banso ma mutan unguwa suga fitarmu...". Kallon mamaki kurum Mairo ke bin Daddah dashi, kafin kaga hawaye a idanun Mairo sai waje ta b'aci yau saiga k'walla suna zarya idanun Mairo.... "Daddah idan da sabo na saba da hijira saidai naji mamaki yanda ke kanki kinsan baki adalci wa rayuwata kuma har kina iya fad'in haka... Daddah na sani wani sirrin rufamin da zakiyi zaifimin sama da bayyana min da zakiyi, domin wani abin a barsa a sirrance yafi... Sannan ni Daddah har yau Allah bai had'ani da wanda zan gani nace ya kwanta min ba har wai naji na sami mijin aure.... Abu guda da yafi damuna shine rashin yarda da kanki da kika kasa yi... Daddah idan sabida mahaifina kike hijira gari zuwa gari na rok'i arzikin ki ki barni nayi ido hud'u dashi. Muyi gaba da gaba dashi mu daina wannan wasan b'oyon na rok'eki kimin wannan sadaukarwan dan Allah Daddah....." Ta k'arashe muryarta na tsananin rawa... Daddah ma tuni idanunta sukayi rau-rau ganin hawaye cikin idanun d'iyarta... A hankali ta janyo Mairo ta rungume tana fad'in "Na kusa sanar dake komai d'iya da izinin Allah... Yanzu tashi mu samu mu isa tasha...." Mairo ta d'ago kanta daga k'irjin Daddah tana dubanta kana tace "Ina muka nufa yanzu....?" Daddah na murmushi tace da ita "Gabashin k'asar nan can Jihar Yobe....." Cikin zafin nama kaman wacce aka takala ta mik'e ta shiga had'a kayanta da na sana'arta... Ta jima tana rik'eda wata sark'ar da Zaliha ta had'a mata tana duba kafin ta saki murmushi ta jefa sark'ar cikin jaka tana mai fad'in "Zanyi kewarki Zaliha...." *** Tinda ya had'a wayar caji bai kuma bi takanta ba, asubahin fari yaji k'aran waya ya cika masa kunne, nan ya tuna ashe jiya ya d'auko wayar Daddy zaiyi bincike cikinta saidai ya kasa bud'e lock d'in wayar hakan yasa bai kuma bi takan wayar ba, ya bari akan sai zuwa safiya yasan abinyi.... Cikin sauri kaman zai kifa ya isa ga wayar yana kallon lambar da ake kira dashi babu suna... Lokaci guda Lamid'o ya d'aga wayar ya k'ara a kunnensa... Hankali tashe Nazir da bai jira wata-wata ba ya soma fad'in "Boss wllhi sun tafi an wayi gari ban samesu gidansu ba... Boss Mairo sun bar gari......" Cikin sauri Lamid'o ya cire wayar daga kunnesa k'irjinsa naci gaba da bugu A hankali ya furta "Mairo!..." Dabara ta fad'o masa cikin sauri ya katse kiran ya tura sak'o cewa yana wajen da bazai iya magana ba.... Aiko kan kace mai sak'on Nazir ya shigo... _Boss there's problem.... wllhi bansan yaya akayi hakan ta kasance ba, kuma bansan ina suka nufa ba, amma yanzu haka tashan motoci na nufa..._ Lamid'o yafi good five minutes yana bin sak'on da kallo kansa na kuma d'aurewa... Toh wacece Mairo... Daddy yankan kai yake ko menene.? Shin kodai Mairo ce silan rasa mahaifiyarsa tinda yasan lokutan baya da wayonsa mahaifinsa na cin zarafin mahaifiyarsa.... He really needs to find out koma wacece.... Lokaci guda ya ajiye wayan ya nufi bathroom donyin alwalan sallan asuba.... *SameenaAleeyou📚* [1/7, 10:09 PM] ‪+234 803 596 9052‬: *FUSKA UKU*🏮 *21* *©Sameena Aleeyou...✍🏽* Sauri-sauri Nazir ya nufi tasha saidai unfortunately ya tarar motar asuba ta bar tasha... Babban abinda yafi damunsa baisan yanda suka nufa ba.... Ya jima yana bulayensa a tashan kafin ya dawo gidan yana kuma dubawa har gari ya soma haske... Lokaci guda ya tuna Zaliha yasan dole Mairo ta masu sallama kuma ta sanar dasu yanda suka nufa... Cikin sauri Nazir ya nufi gidansu Zaliha yana bugun k'ofa.... *** *Yobe _Damaturu_* Sauri-sauri ta gama shirin tafiya wajen aikinta, shagon d'inki da wata attajirar mata ta bud'e a unguwar domin taimakawa mata marassa sana'a.... Tana d'aga jakan nata hotonsu ya fad'o daga ciki, tsohon hoto da suka d'auka lokacin Junaid na asibiti.... Murmushi kwance saman fuskarta take shafa hoton fuskar Junaid da Azeeza... A hankali ta furta "I miss you my children...." Lokaci guda ta ciro wayarta ta shiga dialing layin Junaid.... Bugu biyu Junaid ya d'aga kiran da murnansa "Umma Marie... I miss you sweetheart...!" Ya k'arashe dariyan farin ciki saman fuskar sa... "Nayi kewarku nima Junaid... Ya kuke ya al'amra suke wakana... I hope kuna cikin k'oshin lafiya....? I worried so much about you..." Ta k'arashe cikin rawar murya Murmushi ya kuma yi kana yace "You don't have worry... Muna nan lafiya... And everything is going well just like the way I planned.... Umma nayi kewarki..... Please don't cry kinji...." Murmushi Umma Marie take tana goge hawayen da suka zubo mata kana tace "Ina Azeeza...?" "Ta tafi aiki, bata jima da ficewa ba...." D'an jim tayi kana tace "Junaid kardai amfani kake da k'anwarka domin d'aukar fansar ka... Junaid... Anya anya kuwa Junaid... Na fara tsoron Fansar nan taka kada reshe ta juye da mujiya, Junaid dan Allah ka bar komai wa Allah ka dawo...." Junaid na huci sabida duk sanda aka masa maganar d'aya daga cikin Fuskoki ukun nan sai yaji ya tsani komai a duniyarsa face burin d'aukan Fansa..... Murya a dashe yake fad'in "Umma Marie Shari'a ma ta aminta da idan an zalunceka ka rama matuk'a bazaka iya yafewa gwargwadon zaluncin da aka maka amma kuma yin afuwan yafi alkhairi.... Umma wllhi wllhi bazan barsu ba har sai na cika burina... Kawai ki ci gaba da min addu'a... Kici gaba da mana addu'a daga ni har Azeeza...." Shiru ya d'an ratsa tsakani kafin ta jinjina kai tace " Amma kuma shari'a bata amince maka ka d'auki doka a hannunka ba Junaid, shin baka tunanin tarin had'arin dake cikin yin hakan... Sannan zaka iya zaluntar wanda baiji ba bai gani ba duk a dalilin fansar ka... Junaid....." Katseta yayi da fad'in "Umma must we have to talk about this again.... I'm not backing down... Not until I destroyed them all....!" Cikin tsananin huci yake maganar.. Dan sauk'e ajiyan zuciya tayi kana tace "Shikenan Junaid tunda dai hakan ka zab'a amma ka sani duk abinda zakayi ka ringa tuna mahalliccinka har kullum wasilcina a gareka kenan..... Ka gaida min Azeeza idan ta dawo ka kulamin da kanku.. I love you both...." Junaid ya saki murmushi har cikin ransa yake jin k'aunar Umma Marie kana yace "Insha Allah Ummah... We love you too... Sai mun sake magana..." Suna ida wayan ta zura hijab d'inta ta d'ibi kayan aikinta tayi ficewarta wajen sana'arta... *** *Abuja* Tun daga gate yake jiyo sautin dirin mahaifinsa cikin tsananin fad'a ya tara ma'aikatan gidan gaba d'aya... "Wani sabon iskanci kuka d'auko... Ta yaya za'ace kamata a gidan nan na ajiye abu na nema na rasa.. Waye ma suka gyara parlorn jiya...? Wllhi wllhi kunji na ratse rasa wayar nan na dai-dai da rasa rayuwanku... Idanma akwai d'an lek'en asiri cikin ku ne zan gama daku gaba d'ayanku in seconds.... Ku b'ace a gani dolaye kawai... Awa d'aya tak na baku ku nemo wayar nan yanda ta shiga ta fita idanma a shara kuka saka. .." Cikin sauri ya soma tattara zurmemen jallabiyarsa ya nufi d'aki yana dogara sandarsa... Yana shigewa Lamido ya shigo parlorn.... Nan da nan ma'aikatan suka soma gaidasa... Saida ya tabbata hakulansu baya wajen kana yayi saurin jefa wayar tsakankanin kujeru... Lokaci guda yake tambayarsu mahaifin nasa nan suke sanar dashi ya shige d'aki... Parlorn k'asa ya dawo ya zauna gami da had'e hannayensa waje guda yana tunanin ta yanda zai b'ulla wa lamarin..... Wani ma'aikaci guda ne ya k'araso yana tambayar Lamid'o mai za'a kawo masa... Girgiza kai kurum Lamid'o yayi yana murmushi kana yace "Babu komai Ayuba ci gaba da aikin ka. ." Ayuba ya risina had'i da amsawa kafin yayi wucewarsa... Dokan gidan Alh Bulama ne mata basa masa aiki tun bayan rasuwar matarsa mahaifiya ga Lamid'o.... *** Ammah na hankalce dashi yanda yake cakalan abinci tamkar baya so, kai da ganinsa kasan wani abu na damunsa.... Ajiye spoon d'in hannunta tayi tana mai ci gaba da karantarsa lokaci guda ta d'anyi gyaran murya kana tace "Babana wai lafiya, meke damunka?... " Siraj ya d'an fuzar da iska had'ida shafe goshi kana yace "I'm fine Ammah.. Mai kika gani....?" "Gaba d'aya gani nayi yau d'in kaman bakai ba, tun d'azu tunani kake ka kasa cin komai sannan yau kayi lattin tafiya office ba kaman kullum ba.... Akwai abinda ke damunka ne.... Share it with me please... Baka da wacce ta fini....." Siraj ya d'an kuma gyara zamansa cikin kujeran kana yace "Ammah is somehow complicated.... I just don't know... Bansan ta yaya zan soma maki bayani ba but all I can say is that....." Fsali ya d'an ja had'i da fuzar da iska.. Ammah ta bisa da kallo damuwa fal fuskarta... "Umhum ina jinka Sirajo meke faruwa....?" "Ammah wata yarinya ce take yunk'urin shiga rayuwata.... Nayi k'ok'arin na mata mugunta ko kuma duk wani wulak'anci don kawai taji bazata iya hak'uri dani ba amma yin hakan da nayi sai naga kaman k'aimi ya k'ara mata wajen matsowa kusa dani... Ammah you know me... You know my problem.... Banso wata rai ta kuma salwanta a dalilina..... And you know the worse part of it is that I can't avoid her... Dole kullum na kasance tareda ita.... Ammah I'm afraid...." Ya k'arashe idanunsa saman plate d'in pancakes d'insa..... A hankali Ammah ta mik'a hannunta ta rik'o na Siraj tausayinta na ratsa b'argo da tsokarta kana tace "Sirajo a koda yaushe ka tuna kanada family d'inka and we all love you so much...." Kasa furta komai Siraj yayi sai kallon Ammah da yake yi wasu irin ruwa na neman ciko idanunsa.... Cikin rawar murya ya soma fad'in "Ammah your love is simply enough for me.... But Ammah I'm also human and I've feelings... and......" Kasa ci gaba da magana yayi sabida wani irin nauyin mahaifiyar tasa da yaji... Ammah ta shiga jinjina kai tana dubansa kana tace "Haka ne Siraj, abinda ka fad'i haka ne... And it breaks my heart seeing you like this babu aure.... Ka kai shekarun aure ko nace ka wuce, sannan ga girma da dukiya sun zauna maka, tabbas abinda ya ragi rayuwarka kenan iyali amma ka sani komai mukk'adari ne daga Allah. Kuma kowa da ka gani a duniyar nan da akwai ta yanda Allah zai jarabcesa... Wani ta fannin iyayensa, wani ta fannin auratayyarsa wani ta fannin kasuwancinsa... Kai ga su nan da dama... Koda za'ace kai kullum cikin farin ciki da jin dad'i kake babu tawaya ko nak'asu a duniyarka toh ka sani haka d'in ma jarabawa ce babba... Siraj wannnan jarabawarka ce a rayuwarka, kaci gaba da hak'uri har kaci jarabawarka, na tabbata addu'o'inmu bazasu fad'i k'asa banza ba.... Jikina yana bani ka kusa fita daga wannan k'angi na rayuwa.... Da izinin Allah...." Ta k'arashe murmushi kwance saman fuskarta... Mik'ewa Siraj yayi ya isa ga mahaifiyarsa had'i da rungume kafad'unta daga yanda take zaune kana yace "I love you Ammah.... I love you so much....." Ammah na murmushi ta mik'a hannu ta shafi sumarsa kana tace "Allah shi maka albarka.... Maza zauna ka k'arasa breakfast d'inka ka samu ka tafi aiki lokaci na k'urewa...." Ya kuma murmusawa kana ya koma mazauninsa yana fad'in "Toh Ammah ta.... Nana A ta wuce Foundation koh....?" Ya tambaya sanda yake kai abinci bakinsa... Ammah ma ta d'an gyara zamanta had'i da janyo plate d'inta gabanta tana fad'in "Wai ai wannan agogoce sarkin aiki, sam batako jin k'iwan fita dukda lalurarta, ai anything 7:30 ta bar gidan nan... Jiki na na bani zata zama babban jigo a rayuwan nakasassu da dama nan gaba.... Asma'u 'yar albarka ce...." Murmushi kurum Siraj keyi kana yace "Shiyasa sai na nastu sosai na tantance irin mijin da ya kamata ya mallaketa sabida sanyin halinta da kyawawan d'abi'unta na gari bata cancanci namijin da zaizo daga baya yana goranta mata nakasun dake jikinta ba. .." D'ago kai Ammah tayi tana dubansa kana tace "Babu wanda ya dace da ita sai Lamid'o... Sirajo, Lamido ya sami goyon bayana tinda yaron arziki ne , da zaran iyayensa sun dawo daga k'asar Amurkan kurum sai ayi bikin kuma jiya da dare munyi magana sosai da Nana A kuma na fahimci itama tana jin wani abu a tattare dashi... Dan Allah mu k'yaleta ta sami farin cikinta muddin ya tabbata shid'in ne.... Kaga babu wanda ya tab'a cewa yana sonta sai shi d'in...." Siraj ya d'anyi shiru kana ya jinjina kai yace "Ammah bawai nak'i maki bane, na sani Lamid'o abokina ne koma nace d'an uwana ne amma ya kamata ya gane ba neman kai muke da Nana A ba... Aiko abubuwa da dama da nasan yanayi marassa kyau muddin ya tabbata min ya daina aikatasu ni daina zan d'auki Nana Asma'u na basa aurenta, amma.... Kawai dai I need more time Ammah.... Ki bar min komai a hannu na... Ni zan wuce office...." Ya k'arashe yana mai mik'ewa tsaye... "Toh Babana Allah dai ya shige mana gaba... Baka tambayi 'yar rigimarka ba...?" Ta k'arashe cikin sigan zolaya... Murmusawa yayi kana yace "Fushi take dani Ammah... Idan ta tashi a bacci zan kirata a waya...." Daga haka ya suri wayoyinsa da keys ya nufi k'ofa... Ammah na murmushi ta rakasa da kallon k'auna kana tace "Toh a sauk'a lafiya Babana... Allah ya tsare...." Ameen kurum Siraj ya amsa mata dashi yana mai k'ok'arin k'ara wayar salulansa dake faman ringing a kunnensa... Yana ficewa Ayiya ta take masa baya don taji tattaunawarsa da Ammah... Yana k'ok'arin shiga mota ta kame marfin ta rik'e.... Cikin sauri ya dasa aya wa wayar nasa yana duban ikon Allah.. Wannan mata ta matsa masa da yawa... "Lafiya...?" Ya tambaya yana dubanta Ayiya ta gyara tsayuwarta kana tace "Lafiyan kenan.. Kana jina sarai naji kana son hana 'yar albarka aure sabida ku taru ku zama d'aya tinda kai ka kasa auruwa.... Kana jina... Wlhi wllhi baka isa ba, Sarki ya auri 'yar albarka an gama... Banda neman dalili ince abokin ka ne kuma da yanada wani hali mai muni da tuni ya bayyana mana, ai itama wancan 'yar gaban goshin naka abokinka ta aura mai yasa ita datace taji ta gani tana so baka hana ba sai Asma'u ce zaka hana ko? K'aramar danga mai dad'in tsallaka koh... Toh wllhi baka isa ba, idan kai aljana ta aureka ta hanaka aure toh alajni bai auri Asma'u ba... Aurenta da Sarki babu fashi ehe....!" Tunda ta soma magana yake binta da kallon mamaki sam wannan matar fad'a bai mata wahala... Fuska a tamke ya furta "I don't have your time..." Lokaci guda ya shige motarsa ya barta nan tsaye tana ci gaba da sababi Har ta komo cikin gidan bata daina sababiba koda Ammah ta tambayeta lafiya sai ce mata tayi Sirajo ne ya zageta tsaf da kalman nasara.... Sosai Ammah ta dinga dariya har saida taji tari na neman shak'eta kafin ta tsagaita dariyar tata abinka da asthmatic, tasan bazai wuce akan Nana A Siraj da Ayiya sukayi fad'a ba... "Toh wai mai ya had'aku...?" Ammah ta tambaya "Iyaka na masa kan maganar auren d'iyata da Sarki, bai isa ya hana ba... D'iyata zatayi aure insha Allahu don banida burin da ya wuce naga d'iyoyinta don nasan ita ba juya bace kaman su o'o masu Zeus asibiti a juye mahaifa wai sabida gayu...." Ta k'arashe tana gatsine da fuskarta ta b'angaren da Nana H ke sauk'owa daga bene... Sarai Nana H tasan wannan habaicin da ita Ayiya take... Tab'e baki kawai tayi kana ta k'araso ga Ayiya tana tambayarta Uncle Siraj, ga dukkan alamun tashinta daga bacci kenan domin kuwa kayan baccin ne jikinta... Nan Ammah ke sanar da ita ya fice.... Wani k'atutun bak'in ciki ya tokareta, yanzu duk yanda take fushi da Uncle Luv bai tsaya ya lallasheta ba yasa k'afa yayi ficewarsa... Aiko dole tabi bayansa taji dalili... Ko cin abincin batayi ba ta haura sama ta tsalo wanka ta nufi Laushi Group... *** Ya jima mak'ale jikin k'ofar yana sauraren wayar da mahaifinsa keyi kafin ya sad'ad'o a hankali, a farfajiyan ya tarar da Ayuba ya d'an janyo hannunsa suka keb'e... "Lafia rankashidad'e? " Ayuba ya tambaya tsoro bayyane saman fuskar sa.... "Ayuba ina fata baku sanar dashi na zo gidan nan ba...." Jinjina kai Ayuba yayi kana yace "Rankashidad'e babu wanda ya sanar dashi kuma ko tambayarka baiyi ba, iyakaci dai ce masa mukayi an sami wayarsa cikin kujera... Domin wayar lambobi k'alilan ne cikinsu wanda nake tunanin tsirarun mutane ne yake kira.." Lamid'o ya jinjina kai kana ya furta "Good, toh yanzu kasan abinda nake so dakai....?" Ayuba ya jinjina kai alamun a'a "Sai ka fad'i rankashidad'e..." Hannu Lamid'o yasa a pantpocket d'insa ya zaro kud'ad'en da bai k'irga ba 'yan d'ari biyar ya dunk'ulawa Ayuba a hannu kana yace "Wani aiki zaka min....." Ayuba ya zaro idanu yana kallon Lamid'o da tulin kud'in da ya damk'a mar a hannu..... *** *Laushi Group* Da k'asaitarta ta shigo Kampanin duk yanda ta wuce kuwa sai ta kwashi gaisuwa, yau d'in a Nana H d'inta ta fito ko ita ko Azeeza, yau dole tayi sanadin aikin Azeeza kowa ya huta..... Sai faman d'add'aga hanci take tana tafiyar izza tunda itama tanada kaso cikin kampanin.... Kai tsaye b'angaren president ta nufa wato Siraj Laushi.... Sai ka shiga wani rantsettsen parlor kafin ka tadda office d'in Siraj wanda sakatariyarsa ke zaune cikin kujeranta mai juyawa.... Tun daga cikin glass Azeeza ke hangota aiko ta saki murmushi domin kuwa tsaf ta gane ta.... A hankali ta furta "Duk wacce kika zo da ita zaki samu.... Ko sallama bataci darajanyi ba ta nufi main door d'in office d'in... Azeeza bata ce mata k'ala ba sai murmushi da take... Nana H taji k'ofa a gark'ame... A wulak'anci ta juyo tana duban Azeeza kana tace "Kee! Ina mai office d'in...?" Yanda kasan tayi da dutse haka Azeeza ta mata banza taci gaba da sabganta... Nana H tazo wuya, wai wannan yarinyar kanta guda kuwa... A fusace ta nufota had'i da buga table d'in tana fad'in "Ke are you deaf bakiji tambayar da nake maki ba...?" Sai sannan Azeeza ta d'ago kai had'i da cire glasses fari k'al mai d'an girma wanda da gani na k'arin gayu ne kana ta d'an murmusa tace "And who are you....?" Kambuuu ai Nana H sai ta saki baki tana kallon salon iskanci wai bata ganeta ba bayan jiya jiya suka had'u.... Murmushin rainin hankali Nana H tayi kana ta shiga nuna Azeeza da hannu tana fad'in "Bari kiji na fad'a maki you little brat, ni ba sa'arki bace kuma a yanzu naga dama wllhi aikin ki a kampanin ya zama tarihi shegiya 'yar matsiyata dama ance baku iya samun waje ba sai kun nuna yunwa, toh uncle yafi k'arfinki, k'aramar karuwa..." Dariya mai d'an sauti Azeeza tayi kana tace "This suits you... Ai sai yanzu na ganeki da kika soma haushi... Gashi kuma kashh anyi rashin sa'a My Sir hutawa yake he already ordered me not to let anyone in... Kiyi hak'uri ki koma kya iya dawowa wani lokacin... Aww wait do you even have an appointment with him, ko kawai zuwa kikayi haka nan...?" Ta k'arashe tana maida glasses d'inta... Nana H kasa gaskgata abinda take gani tayi, wai dai da gaske itace wata banza ke watsa wa magana a kampaninsu ofishin Uncle Love d'inta... Tsaban b'acin rai har wani rawa jikinta keyi ta d'aga hannu zata kai wa Azeeza mari tana fad'in "How dare you....!!" K'am Azeeza ta rik'e hannun Nana H tana wani irin murmushi take fad'in "Don't try... Don't you dare try this nonsense with me....." Hannun Nana H bai bar b'ari ba take duban Azeeza cikin rashin yarda bata zaci shed'anan yarinyar yazo har nan ba... Cikin sauri ta ciro wayarta daga jaka ta shiga dialing Uncle Luv, k'iris ya rage bata yarda wayar ba sabida yanda hannunta ke karkarwa... Saidai ga mamakinta ringing wayar taji a gabanta, aiko ta kai dubanta table d'in Azeeza taga wayar Siraj na faman ruri... K'walla ne kurum taji suna neman ciko idanunta saidai bazata iya kuka gaban wannan k'aramar 'yar iskar ba.... Azeeza ta murmusa kana tace "Kawai dai kink'i bin shawarina ne... Kiyi hak'uri ki tafi My Sir hutawa yake, kingama wayarsa a nan bashida lokacin amsa wayar kowa... Idan kuma zaki jira ya gama hutawarsa toh bismillah you're welcome...." Ta k'arashe tana nuna mata kujera... Dubanta kurum Nana H take da rianannun idanunta kana tace "You've no clue who you really messing with.... You'll regret this very moment.... Mark my word.....!" Daga haka sa kai tayi had'ida ficewa daga building d'in cikin sauri..... Azeeza ta sauk'e ajiyan zuciya domin yanayin da taga fuskar Nana H ya canza lokaci guda ya d'an bata tsoro k'arfin hali ne kurum irin nata... Takai dubanta ga wayar Siraj ta tuna fad'uwa yayi sanda zai fice meeting ta d'auka ta ajiye masa... Zama tayi dab'as cikin kujeranta tana mamakin wacce irin SHAK'UWA CE ke tsakanin Siraj da d'iyarsa Nana H.... *** *Misau* Murmushi yayi mai bayyana fararen hak'waransa yasan ta hakane kurum zaisa ya sami amincin iyayensa ta yanda bazasuyi zargin komai ba, lokaci guda ya fito daga b'angaren nasa ya nufi sashen su Innah... Zaune ya tadda Innah tana tankad'en bushasshiyar kub'iya na miyan dare yayinda Deejoh ke faman tsince waken da za'a saka a miyar... Murmushi kwance saman fuskar sa ya k'arasa ga Innah.. Nan Innah ma ta fad'ad'a murmushinta, yayinda walwalan Deejoh ya d'auke gaba d'aya domin kuwa tunda tasan shid'in mijinta ne wani nauyinsa mai girma ya kamata wanda batasan sanda ya shigeta ba... Ahidjo ya d'an saci kallon gefen da Deejoh take sanda suke gaisawa da Innah kana yace "Innah dama so nake Deejah ta rakani gari domin akwai wasu 'yan sayayyan da nake so nayi tunda zama a nan ya kamani...." Innah cike da mamaki take dubansa baki har kunne kana tace "Ahidjo da gaske ka fasa tafiya, da gaske bazaka tafi ba, aikinka fah..." Mamaki ya cika Ahidjo jin ko zancen d'aya matar tasa basayi sai aikinsa kana ya d'an saita kansa had'i da jnjina mata kai kana yace "Kar ki damu Innah dama banzo ba saida na d'auki hutu wajen aiki.... Zan jirata a sashena idan ta gama shiryawa..." Daga haka mik'ewa yayi ya nufi sashensa ya bar Deejoh da fad'iwan gaba... Ita kiranta da Deejah da yayi abin sai ya mata banbarak'wai don babu wanda ya tab'a kiranta da Deejah sai Deejoh... *SameenaAleeyou📚**FUSKA UKU*🏮 *22* *©Sameena Aleeyou...✍🏽* Wani k'ullin gari Lamid'o ya ciro cikin aljihunsa ya mik'awa Ayuba.... "Karb'i mana.." Ya fad'i yana damk'a masa garin.... Girgiza kai kurum Ayuba yake tsananin tsoro ya wanzu a fuskar sa kana yace "Rankashidad'e a gaskiya bazan iya aikin da kake umartana ba... Rankashidad'e bazan iya kashe Alhaji ba... Bazan iya ba....!" Ya k'arashe cikin tsananin rawar murya.... Lamid'o ya d'an murmusa da gefen bakinsa kana yace "Malam Ayuba kenan, wannan magani da ka gani bata kisa bace, kawai kasan yanda za'ayi ka saka masa a abinci yaci, idan ka tabbata yaci sai ka kirani.... Ni kuma zan k'arasa sauran aikin...." Malam Ayuba yayi shiru ba tareda ya iya furta koda kalma ba rungume da sandar mop.... Lamid'o ya d'an murmusa yana bubbuga kafad'an Malam Ayuba yake fad'in "Nasan matsalarka...." Lokaci guda ya zaro sauran kud'ad'en dake aljihunsa ya damk'asu wa Malam Ayuba kana yace "Idan har ka taimakeni burina ya cika akwai kyauta mai tsoka wannan sharan fage ne....." Sauk'e ajiyan zuciya Ayuba yayi kana yace "Toh.... Toh ai kitchen ba aikina bane... Kuma..." Baikai aya ba Lamid'o ya katse sa da fad'in "Ai a gidan kake aiki, kawai kar ka damu kayi yanda nace d'in....." Lamid'o bai jira cewarsa ba ya fice cikin sauri.... *** Gaba d'aya Nazir ya gaza sukuni sabida yanda Alhaji Bulama ya d'aga masa hankali sai ya nemo su Mairo yanda suka shiga suka fita, gashi lambobin Mairo da Daddah gaba d'aya babu mai shiga, haka sukayita trying shida Zaliha.... Shar-shar da hawaye Nazir ke faman masu kuka yana fad'in she left without saying goodbye... Jikin Zaliha da Ummanta gaba d'aya sai yayi sanyi ganin zogen saurayi na masu kuka... Cikin kuka yaci gaba da fad'in "Zaliha wllhi son Mairo nake, wllhi k'ainarta nake.. Yanzu dan Allah babu yanda za'ayi na samesu... Wayyo Allah ni Nazir nayi nauyin baki, danasani da tuntuni na sanarda Mairo abinda ke cikin raina koda Daddah zata juya min baya... Gashi yanzu na rasata. Na rasata for good..." Ya k'arashe cikin tsananin kuka... Dukda Zaliha ma kukan tafiyar aminyar tata take babu sallama k'ok'arin saita kanta tayi don sai tafi tausayin Nazir sama da kanta kana tace "Nazir kayi hak'uri ni na tabbata Mairo batada caji ne a wayarta amma da zaran tayi chaji zata kiramu, ni nasan Daddah ce ta tilasta mata barin garin nan... Kayi hak'uri kaji, idan na samu wani labari gameda su zanyi maza na sanar da kai insha Allah..." Nazir ya jinjina kai yana mai godiyawa Zaliha, Ummah ta fito da abinci ta tirsasawa Nazir cin abincin dole domin a yanda suka gansa yinin rana d'aya kurum basa tunanin ya iya ya saka wani abu a cikinsa... *** "Hello gorgeous...!" Sassanyar muryarsa ya katse mata tunanin da take..... Murmushi ta sakar masa had'i da rufe file d'in dake gabanta kana tace "Barka da shigowa I thought ka tafi gida ai..." Murmushi Junaid ma ya sakar mata kana yace "Haba dai yaya za'ayi na tafi ban maki sallama ba, kema kinsan bazan tab'a yin haka ba... Why are you all alone here, ba dai aiki kika ci gaba da yi ba... Come on stop stressing yourself please...." Ya k'arashe yana turo wheelchair d'insa har saida ya iso gaban table d'inta kafin ya shiga tattara mata kayanta yana had'awa waje guda... Nana A kuwa sai binsa da kallo take tana d'an murmushi mai sauti take fad'in "Kai Junaid dan Allah ka bari zan tattara... Besides ba aiki nake ba kawai dai dubawa nake...." D'ago rikatattun idanunsa yayi yanai mata wani irin duba wanda ya sanyata d'auke idanu daga dubansa... Junaid ya d'an murmusa ganin ta kasa duban cikin idanunsa kana yace "Are you sure you're telling the truth...?" D'an jinjina masa kai tayi kana tace "Uhum..." "Alright fine.... I'll go ahead, see you tomorrow..." Bata iya amsa sa ba sai kallo data d'an bisa dashi.... Jikinsa ne ya basa tana dubansa, a hankali ya d'an karkato aiko nan suka had'a idanu... Sauk'e ajiyan zuciya tayi had'i da sakar masa fake smile.... Junaid ya d'an girgiza kai kana ya d'an dawo da baya yana karantar ta.... K'asa ya d'anyi da muryarsa yana fad'in "Hey what's wrong... Is there any problem....?" D'an girgiza kai tayi had'i da d'an bud'e idanu kana tace "Why... Me? Problem... Do I look I've one...?" Murmushi Junaid keyi kana yace "Asmah kinsan na sanki yanzu at least koba farin sani ba amma dai na sanki a iya zaman da mukayi.... Meke damunki please.... Share it with me may be I can help...." Ya k'arashe fuskarsa fal damuwa kana iya gano tsan-tsan damuwar cikin idanunsa... Shiru tayi ba tareda ta iya furta koda kalma ba, Junaid kuwa sai faman aika mata muguwar kallo yake.... Ganin zata d'ago fuskarta yasa sa saurin saita kansa kana yace "I'm sorry... If you don't want to talk about it... But whenever you need a friend, always remember that I'll be here okay...." Murmushi ta sakar masa had'i da sauk'e nannauyan ajiyan zuciya kana tace "Na gode Junaid..... Na gode daka shigo rayuwata ina jinka kaman d'an uwana kaman brother na...." Murmushi ya sakar mata kana yace "Tabbas Allah ne ya had'amu sabida mun shiga matsala kusan iri d'aya abrayuwa...." Jinjina kai ta d'anyi kafin tasa tafukan hannayenta ta d'an shafi fuskarta , a hankali ta soma fad'in "Junaid I'm so confused.... Ayiya da Ammah suna farin ciki kuma sun basa full supports d'insu.... But yanda matsalan yake Uncle Siraj ne... Dukda abokinsa ne har yanzu bai basa go ahead ba.... Im a little confused, bansan nawa zanbi cikinsu ba, or maybe I should just follow my heart...." Tunda ta soma magana ya kafeta da idanu k'irjinsa naci gaba da bugu, wato shege shi yasan makwancin shege shiyasa Siraj yak'i aminta niece d'insa ta auri Lamid'o... Lokaci guda ya d'an saki murmushi yana ci gaba da kissama shirinsa cikin zuciyarsa... Lokaci guda ya jefo mata tambaya... "What's your heart keeps telling you.... Do you really love him....?" Kallonsa tayi yanda ya jefo mata tambayar idanunsa sun firfito waje sosai alamun yana cikin tashin hankali... Sauk'e idanunta k'asa tayi ba tareda ta iya basa amsa ba..... "Asmah....!!" Ya kira sunanta a hankali "Asmah please look up....!" Kasa d'ago kai tayi sai bugu da k'irjinta ke famanyi bata zaci wannan babban tambayar daga gareshi ba... Saurin mik'ewa tayi tana tattaran kayanta saman table take fad'in "Muje nasan Malam Sile ya iso, muje muyi dropping d'inka...!" Kafeta yayi da idanunsa wanda suka sauya launi, sosai yaci serious... Lokaci guda ta kuma jiyo muryarsa "You haven't answered my question Asmah... Do you really love him? Why are you confused....?" "Junaid we talk about this next time please, I'm exhausted already..." Murmushi ya sakar mata kana yace "Ki kwantar da hankalinki and please ko kinje gida karki stressing kanki wajen tunani kinji, sannan ki ci gaba da addu'a..." Murmushi ta sakar masa kana tace "Na gode Junaid naji dad'in shawarinka... And I'll like to introduce you to my family, already Ayiya taji labarinka kuma tanaso ta had'u da kai...." Murmushi kwance saman fuskarsa yace "Nima inaso na had'u da Ayiyan nan don nasan tanaji dake, kar ki damu soon zanje insha Allah, kinga a yanda nake yanzu haka bai kamata naje ba, ya kamata na d'an shirya...." Asma'u ta murmusa cikeda jin dad'i suka ci gaba da hiransu cikin jin dad'i har suka fito farfajiyan foundation d'in , tuni Asma'u ta mance wani damuwa dake cikin zuciyarta... **** Daga bakin k'ofar d'akin ya tsaya hard'e da hannaye yana duban Deejoh dake faman shiryawa.... Tana k'ok'arin saka hijab suka had'a idanu, yana sanye cikin k'anan kaya shigarsa tun na d'azu... Cikin sauri ta sadda idanunta k'asa... A hankali Ahidjo ya soma takowa cikin d'akin, kafin ya ida shigowa Deejoh ta durk'usa tana gaidashi domin taga haka Innah keyiwa Baffah kuma harga Allah sosai yanzu take ganin girmansa... Tunda yake babu bil adaman da ya tab'a tsugunawa ya gaidasa bayan 'yansanda 'yan uwansa masu sara masa.... Baice komai ba sai kallon da yake binta dashi, sosai yarinyar ta basa tausayi k'aramace sosai wacce ya kamata ace a dai-dai wannan lokaci tana class ne ba zaman aure ba... "Kin gama sgiryawa...?" Ya tambaya yana dubanta Jinjina masa kai kurum tayi ba tareda ta iya amsawa ba... Ahidjo ya jinjina kansa yana dubanta yanda ta cukuikuye hijab d'in a k'irjinta don tunda ya shigo ta kasa k'arasa saka hijab d'in... Taso basa dariya yanda take faman rarraba idanu amma ya d'an gimtse kana yace "Toh yaya yau bakiyi kwalliyar ba, ko baki son fitar ne...." Idanunta a k'asa tana faman rarrabasu, da k'yar ta iya girgiza masa kai wanda bai fahimci amsar me take nufi ba.... Matsowa kusanta yayi tayi saurin d'ago idanu ta dubesa sai kuma ta maida dubanta wani gefen... Nan ma murmushi yayi kana yace "Ina kayan kwalliyan naki...?" Ta kuma dubansa cikeda mamakin yanda ya sauya gaba d'aya, kaman ba shine shekaran jiya ya kirata da mayya ba... "Ni bazanyi kwalliya ba kuma ai Innah ce tace sai na raka ka, ai cewa kayi ni mayya ce..." Tayi maganar bakinta a ture Yanda ta fad'i masa cikin zuciyarta kai tsaye ya birgesa... D'an bakin nata yake kalla yanda ta turosa gaba kana ya gyara tsayuwarsa had'ida d'an sakin murmushi yace "Aw ashe dai fushi ake dani, shiyasa baza a min kwalliya ba, toh kiyi hak'uri kinji... Bani kayan kwalliyan naki...." D'ago idanu tayi tana dubansa cikeda mamaki, saikace bashid'inba.... Lokaci guda ta mak'e kafad'a murya can k'asan mak'oshi tace "Dama bawa kai nayiba ba fah..." "Toh a waye kikayi, samarukanki....?" Nanma d'agowa tayi ta d'an dubesa sai kuma taji dariya, wai samarukanta ita inama taga samaruka... "Banidasu...." Ta fad'i a tak'aice.... Ahidjo ya kuma murmusawa yana zira hannaye cikin aljihu kana yace "Hakan yafi... Muje dare yanayi...." Ya fad'i yana duba agogon dake d'aure hannunsa... Kallo tabisa dashi har ya fice kafin ta d'an rintse idanunta, lokaci guda ta zira hijab d'in sanda taji muryar Innah na k'walla mata kira..... Koda suka fito zasu tafi sayayyan Ahidjo shi ya bud'e mata k'ofa da kansa ya umarceta data shiga.... Gaje data nufo gidan tagajan magajan nan ta hangi kayan Al'ajabi wai Deejoh na shiga k'arfen nasara k'irar zamani.... K'iris ya rage bata d'ibi jiki ta fad'i ba.... *** Sauk'arsu kenan a birnin Damaturu, basu san yanda suka nufa ba, babu wanda suka sani a garin....... Mairo batabi takan Daddah ba ta shiga k'ok'arin zak'ulo wayarta cikin jaka saidai wayam bataji wayar ba, Daddah na hankalce da ita saidai bata tambayeta abinda take nema ba.... "Kinga maza mik'e mu shiga gari har Allah yasa mu dace...." Daddah ta fad'i tana kuma gyara mayafinta had'i da janyo k'aton akwatinta... Kallonta kawai Mairo take cikeda takaicin hali irin na Daddah, yanzu ina zasuje da wannan shirgin kayan nasu su ba kowa suka sani gari ba, ga yanayin garin ga kuma yanayi na rashin yarda da ake ciki.... Suna zaman zamansu a Tambuwal ta hura masu wuta... Daddah kam tuni ta soma tafiya tana rarraba idanu tana kallon yanayin garin... A kufule Mairo tace "Toh yanzu dan Allah Daddah fisabibillahi ina muka nufa.... Waye muka sani...?" "Ke dallah banson felek'e da d'in can garuruwan da muka zauna waye muka sani duk ba daga baya muke sabawa ba...." Mairo tayi k'wafa had'i da jinjina kai kana tace "Ai dai kinsan duk yawon da mukeyi arewa maso yamma muke yi bamu tab'a nufowa arewa maso gabas ba kindai san ana fama da matsalar tsaro tam! Wllhi aka ganmu da kayan nan za'a iya kamamu...." Yab'e baki Daddah tayi kana tace "Yo a kamemun mana, uwar wa muke tsoro dallah wuce muje ni bansan Mairo ta da tsoron takife ba...." Tana ida fad'in haka ta janyo hannu Mairo suka sa kai... **** Wani kanti mai kyau Ahidjo ya kaisu ya umarceta itama ta fito ta zab'i abinda take so, fir Deejoh tak'i yarda ta fito don gaba d'aya gani take kaman kowa a garin su yake kallo duk yanda suka wuce.... Da k'yar Ahidjo ya shawo kanta ta fito suka shiga Kantin, kaya sosai ya dinga jida yayinda Deejoh ke biye dashi uwa rak'uma da akala , itakam sam bata saki jiki da shi d'in ba.... Ahidjo ya d'an juyo suka had'a idanu lokaci guda ya sakar mata murmushi, dole ya jata sosai a jiki domin yasan itace kawai zata iya sanyawa iyayensa su amince ya tafi ba tareda sun masa baki ba.. Ahidjo ya umarce mai kanti da ya kawo masa kayan kwalliya, nan ya sai mata masu kyau ba irin wad'anda take amfani dasu ba.... Dangin kayan abinci kayan ciye ciye da na amfanin yau da kullum ya sai masu gaba d'aya gidan, Deejoh kam mamakin tulun kud'in da ya kashe tayitayi,... Sanda zasu koma ma da kansa ya bud'e mata k'ofa, tayi k'ok'arin sakar masa murmushi.... Suna tafe a mota yake tambayarta ina ta tsaya a karatu?... "Karatun Allo kawai nayi Iya Gaje ta hanani boko..." D'an karkatowa yayi ya dubeta kana yace "Wacece Iya Gaje? " "Mama ta ce...." ta basa amsa a tak'ice.... Bai kuma cewa komai ba sai maida hankalinsa ga tuk'i da yayi.... *** Unguwar dake kusa da tasha suka nufa saidai suna isowa mashigar unguwar suka had'u da wasu soji guda biyu masu tsaro, idan akwai abinda Daddah ke shayi a rayuwarta toh shakka babu Soja ne..... *SameenaAleeyou📚**FUSKA UKU*🏮 *23* *©Sameena Aleeyou...✍🏽* *SAMEENA ALEEYOU NOVELS Mi Familia😍 Allah shi bar so da k'auna fatan Alheri gareku gaba d'aya♥* Suna k'arasowa wajen Daddah ta durk'usa tana gaidasu had'i da janyo hannun Mairo tanai mata alamu data gaisar da sojojin.... Tab'e baki kurum Mairo tayi had'i da karkata kallabinta don ko kallon arziki sojin basu samu daga gareta ba.... Daddah ta maido da dubanta ga sojojin tana fad'in "Yallab'ai kuyi hak'uri kunsan matafiyi da yunw....." Bata kai aya ba guda d'ayan ya daka mata tsawa "Kee!! rufe mana baki, daga ina kuke da wannan lodin kayan...?" Tsawan da ya darara mata saida ya sanyata zabura... Saurin washe baki tayi tana fad'in "Bak'ine mu Rankashidad'e... Yanzu sauk'armu garin...." "Oya ku paka gefe we need to search your stuff...." Daddah ta mik'e tana gyara d'aurin kwalinta take fad'in "Yallab'ai wai mai kace....?" Sai sannan d'aya mai jan idanu uwa gauta yace "You no dey hear talk... Ka matsa gefe aka ce...!" Ya k'arashe cikin daka tsawa.. Cikin sauri Daddah ta janyo Mairo tana fad'in "Au toh toh.... Ai sai mu matsa gefen mai yayi zafi shiba wuta ba, aima ba sai kun tsaya d'aga jijiyan wuya ba...." Tsawan da d'ayan ya kuma daka mata ya sanayata had'iye zancen nata.... Gefe sojojin suka d'an matsa suna tattaunawa kafin suka kuma nufosu.... Daddah dai sai karanto ya Salamu ya Dafi take, karatun ta na allo ya shiga dawo mata, hardasu Alu ambaki duk saida ta karanto duk na neman tsari da wad'annan Sojojin.... D'aya wanda hausan yafi zama bakinsa yace "Ina kuka nufa da wad'annan kayan...?" Izuwa lokacin Daddah ta soma k'uluwa da tambayoyin sojojin tinda tabisu a sannu.... Yab'e baki tayi kana tace "Nace maku bak'ine mu shigowarmu garin kenan..." "Bak'i bakuda wajen zuwa....?" Ya tambaya yana ajiye zungureriyar bindigar dake rataye kafad'arsa a k'asa Sojan nan bai ida d'agowa ba ya jiyo muryar Mairo tana fad'in "Cirani muka shigo....!" Yanda tayi maganan babu ko shakka balle tsoro a tattarre da ita... K'uri ya mata yana mamaki taunar chewing gum ma take... A duniya babu abinda Soja ya tsana kaman raini... Dole ya koyama wannan k'aramar marar kunyar hankali... Kira ya doka wa d'an uwan nasa still idanunsa kafe kan Mairo yana kissama yanda zai keta mata haddi da k'arfin tsiya.... Nan ya umarce d'an uwan nasa da ya bincika kayan Daddah ya tabbata babu komai... Aiko Daddah tana ganin an janyo akwatinta ana k'ok'arin bud'ewa tayi wuf ta kame akwatinta don idan akwai abinda tafi tsana shine a bincika mata kayanta don ko Mairo tasan dokan Daddah bata son bincike sabida sirri da take yawan b'oyewa... Soja na jan akwati Daddah na kuma rungumo akwatinta tana rantsuwan baza'a bud'e mata ba... Shiko d'aya kan Mairo yayi ya janyota zai shige da ita d'an bukkan nasu... Nan shima suka shiga kokawa da Mairo... Daddah ta hangi Mairo hannun Soja batasan sanda ta sunkuya had'i da danna bakinta saman hannun Sojan nan ba lokaci guda ta had'e hak'waranta ta gantsara masa wani irin gigitaccen cizo... Ai a d'ari ya saki akwatin yana yunk'urin janyo bindigar sa yaji sauk'an akwati gadon bayansa... Take a wajen ya zube yana tale gadon bayansa... Daddah ta kuma rungumo akwatin tayi bukkan dataga d'ayan ya janyo Mairo... Aiko tana isa take sauk'e masa aka shima ya saki k'aran azaba... Cikin sauri ta taimakawa Mairo ta mik'e had'i da tsatta masa miyau kafin suka fito a guje kafin wad'annan Sojin su mik'e.... A guje suka kutsa cikin unguwar domin sunsan muddin sojin nan suka mik'e zasu harbesu da bindiga... Wani k'aton shagon d'inki suka soma hangowa aiko nan suka shige ciki a guje suna neman d'auki.... Ganinsu haka kan kace mai 'yan shago an soma watsewa, daga mai haye taga sai mai kwanciya flat k'asar shago... Mace d'aya ce bata gudu ba ta tsaya tana binsu Daddah da kallon mamaki yanda kasan wasu ribatattun yak'i.... *** Abin hawa Junaid ya tare ya hau ya nufi gida, Asma'u tsaye tana masa waving har ya wuce... Ta kuma duba agogon hannunta lokaci guda wayar Ayiya ya shigo mata, da murmushi ta d'aga wayar had'i da zolayan Ayiya... "Kardai 'yar tsohuwa ta damu da rashin dawowata gida har yanzu....? " Ta fad'i tana fad'ad'a murmushinta... "Yo ba dole na damu ba yau kin jima da yawa, yamma tayi fah... Inji dai lafiya...." Nana A ta kuma murmusawa kana tace "Lafiya lou Ayiya mun tsaya mun duba wasu abubuwa ne nida Junaid, bai tafi ya barni ni kad'ai ba yanzu ma k'in tafiya yayi saida na shaida masa I'll be fine.... Junaid yanada mutunci sosai Ayiya,...." Ayiya ta murmusa kana tace "Ni kaina naji ina son Junaid d'in nan tun kafin na gansa...." Nana A tayi murmushin jin dad'i kana tace "Ayiya dole ki sosa idan kin gansa, yanada zuciya mai kyau.." "Allah sarki Allah saka masa da alkhairi kula min da d'iyata da yakeyi, barince ma Sile kin gama yaje ya d'aukoki...." Nana A ta kuma murmusawa saidai kafin takaiga bada amsawa Ayiya ta hangi motar 'yar uwarta Nana H tazo d'aukarta.... Shaye da mamaki take kallon motar kafin ta d'an saita kanta tace da Ayiya... "Ammm Ayiya shikenan basai Malam Sile yazo ba Nana H tazo d'auka ta...." Bata jira cewan Ayiya ba ta katse kiran domin already Nana H ta cakka birki gabanta... Lokaci guda ta shiga zuge glass d'in motar murmushi saman fuskarta.... Mamaki bai bar saman fuskar Nana A ba wai da gaske itace Nana H tazo d'auka ko kuwa dai wani uzirinta ya kawota.... Bata ida tunanin ba ta jiyo muryar Nana H cikin k'atuwar Range Rover d'inta tana fad'in "Hello Sis.... Shall we..?" Still mamaki saman fuskar Nana A, a hankali ta furta "Nana H are you serious you are here to fetch me....?" Nana H ta murmusa had'i da d'aga giranta guda d'aya kana tace "Sure I'm here to fetch my one and only Sis.. Come on get in the car...." Murmushin saman fuskar Nana A ya fad'ad'a cikeda jin dad'i ta bud'e marfin motar da shike k'afarta nada matsala da k'yar ta d'an iya kama motar ta shige.... Fuskar Nana H d'auke da alamun damuwa take duban 'yar uwar tata take fad'in "Oh careful Sis... Ko nazo na taimaka maki ne...?" Ta k'arashe tana yatsina fuska... Cikeda jin dad'i Nana A tace "Kar ki damu Sis zan iya... Na gode da kika tuna dani...." Mirmushi Nana H tayi lokaci guda tayi key wa motar kana tace "Kai haba Sistu, banida wacce ta fiki duk fad'in duniyar nan kar ki mance mun zauna mahaifa guda for good nine months kafin muzo duniya.... Ki daina damuwa idan na nuna kulawata akanki... Nana A wllhi bakida wanda yafini..." Nana A ta murmusa dad'i fal zuciyarta kana tace "Gaskiya ne Sister banida wanda yafiki... I love you..." Nana H ta kuma murmusawa sanda ta maida dubanta ga kwalta kana tace "Shiyasa nake so idan na baki shawari ki d'auka kuma ki yarda dani kan bazan so naga wani abu ya cutar dake ba....." Ta k'arashe fuska fal alamun damuwa K'aran da wayar Nana A yayi ne ya katse masu firan tasu... Da fari'arta ta d'aga wayar ganin Uncle Siraj ne mai kiranta... "Assalamu alaikum... Uncle barka da yamma....!" Jin da Siraj take waya ya sanya Nana H ta juyo ta bata wani kallo... Daga d'aya b'angaren Siraj yace "Nana A what happened... Ya akayi baki dawo gida ba har yanzu, yanzu shigowata gida Ammah tace min baki dawo ba... Hope all is well...?" Ya k'arashe murya fal damuwa... Murmushi ta sakar masa mai d'an sauti kana tace "Uncle har hankalinka ya tashi haka na rashin ganina a gida... Naji dad'i kun damu dani gaba d'aya, d'azu Ayiya ta kira so worried, and Nana H tazo d'aukata na musamman sannan gashi kaima ka kira domin jin lafiyata... I feel loved.." Ta k'arashe cikin tsananin jin dad'i Banda uwar harara babu abinda Nana H ke aika mata, cikin ranta tayi k'wafa ganin hankalin kowa ya tashi kan wannan gurguwar.... Bata kuma sauraren wayar Nana A da Siraj ba sai ciro wayarta da tayi ta tura sak'owa Lamid'o... _Super boyfriend, your precious flower is with me... And guess what sweetheart.... I'm the one driving sai yanda naga daman kaita... I told you so.. I can be very dangerous..._ Daga haka ajiye wayar tayi had'i da juyowa ta dubi Nana A ta sakar mata murmushi kana tace "So tell me about you and Lamid'o..." Murmushi Nana A tayi had'i da d'an bud'e idanu kana tace "Sis kinsan Uncle baiyi na'am dashi ba har yanzu...." Nana H ta murmusa kana tace "Precisely sabida ya sansa farin sani ne tinda abokinsa ne and he don't want you getting hurt.... Toh amma kefa do you feel anything for Lamid'o...?" Kallonta Nana A tayi kafin ta d'anyi shiru kaman mai nazari... "Kar kiji kunyata Nana A idan baki sharing dani ba duk fad'in duniyar nan da waye zakiyi... Do you love him as well...?". D'an sauk'e ajiyan zuciya Nana A tayi kana ta d'an jinjina kai "Of course Nana H I do feel something for him.... But I'm not really sure if that's love... And quite alright ina respecting d'insa sosai...." Murmusawa Nana H ta kumayi kana tace "My sister is finally in love... Ko babu komai dai kinji irin dad'in da mace keji idan namiji yace yana sonta tinda babu wanda ya tab'a fad'a maki haka before.." Lokaci guda Nana A ta d'an b'ata fuska ba tareda ta furta komai ba.... D'an dubanta Nana H tayi taga yanda mood d'inta ya canza lokaci guda alamun maganar ya mata zafi kana tace "Oh... Hey I'm sorry, don't take it personal kinji... Just joking...." D'an murmushi Nana A tayi wanda yafi kama da yak'e kana tace "Kar ki damu banyi fushi ba besides gaskiya kika fad'i babu wanda ya tab'a cewa yana sona before shiyasa bazanyi wasa da damata ba now that Uncle Lamid'o is in love with me...." Kalman Nana A na k'arshe sosai ya soya mata zuciya wai wannan musakiyar ma har tasan taso namiji... Ji tayi dama bata kawo maganar ba... K'aran shigowar sak'o a wayarta ya sanyata dubawa tana mai rage speed d'in motar... _Nana H please don't... Don't hurt her, I beg you.... Na yarda Mu had'u a Gwarimpa by 8 can gidanki but please don't hurt Nana A..._ Tana ida karance sak'on ta saki murmushi had'ida cilla wayar backseat... Fira sukaci gaba dayi da Nana A har suka isa gida.... *** Baffah fuska d'aure yake duban kayayyakin da Ahidjo ya sayo ya kawo gidan, ya kuma duban Innah yace "Zuba masa kayansa ba cewa mukayi muna cikin talauci ba ya ci damu, dama can baisan cinmu ba balle shan mu...." Jikin Innah yayi sanyi yayinda Ahidjo ya kuma sadda kai.... *SameenaAleeyou📚**FUSKA UKU*🏮 *24* *©Sameena Aleeyou...✍🏽* "Baffah dan Allah kayi hak'uri ka yafe min...." Ya fad'i yana kuma sadda kai k'asa.... Idan darduman da Baffah ke bisa ya amsa toh kuwa shakka babu shima zai amsa... Radio ya kunna yana mai kishingid'a kaman baisan da hallita a wajen ba.... Ahidjo ya dubi Innah da tuni idanunta sukayi rau-rau, bai sake cewa komai ba ganin Baffah ya juya masa baya sai mik'ewa da yayi jiki babu k'wari yana shirin barin d'akin... "Zo nan!... " Muryar Baffah ya katse sa. "Tattari kayanka ban buk'atar ganinsu a nan...." "Baffah....!" "Ka tattara nace koh...." Bai tattara ba sai durk'usawa da yayi kana ya soma fad'in "Baffah meyasa kaki amsar tuba na, nasan nayi kurakurai da dama a baya amma wllhi na gane kurena Baffah bazan kuma tafka kuskuren da nayi a baya ba.... Baffah dan Allah ka yafe min kaji Baffah na...." Ya k'arashe cikin rawar murya... "Aliyu tashi ka fice min a d'aki....!" Kalmar da Baffah ya fad'i masa kenan.... Jiki babu k'wari bai kwashi kayan ba ya mik'e ya fice daga d'akin... Ahidjo na fitowa ya hangi Deejoh ta rafka uban tagumi alamun taji fad'an da Baffah ke masa.... Kallon kallo suka shiga yiwa juna shida Deejoh kafin yasa kai ya nufi b'angarensa... Cikin sauri ta mik'e tabi bayansa Sanda Ahidjo ya fice Innah ta dubi Baffah sabida sosai ranta ya sosu da abinda Baffan keyi... "Haba Malam, haba Malam yanzu shikenan bazaka sami gurbin yafiya wa yaron nan cikin zuciyarka ba, shikenan fah mana tilo, kuma ya ijiye aikinsa da iyalinsa ya zab'i ya faranta mana yanzu mai kake tunani idan ya koma 'yar gidan jiya...." Dubanta kawai Baffah yayi fuska babu walwala kana yace "Ni nasan abinda nakeyi, na kuma san halinsa... Idan har da gaske yake ya tuba zamu gani... Jikina yana bani Aliyu wani abin yake k'ullawa, ki d'ibi kayansa ki maida masa nikam bani buk'ata, kuma k'warar shinkafarsa ban yarda a girkata a tukunyan gidana ba kinji na fad'a maki..." Daga haka Baffah ya gyara kwanciyarsa yana mai ci gaba da saita radio d'insa... Innah ta matsi k'wallan da suka zubo mata cikeda takaicin mijinta na ta d'ibi kayyakin ta fice daga d'akin... ** Zaune ta samesa waya manne a kunnensa, da alama da abokan aikinsa yake wayan.... Can gefe ta samu ta zauna Ahidjo ya bita da kallo yana mai ci gaba da magana a wayar, lokaci guda kuma ya mik'e ya fice still wayar manne kunnensa.... Yana ficewa ta mik'e ta shiga tattara masa d'akin, kayayyakinsa da suke bisa katifa gaba d'aya ta tattaresu ta kinke, ta fice sashen Innah d'auko tsintsiya.. Innah na ganinta ta d'au tsintsiya da parker ta tambayeta ina zata da tsintsiya.. D'an rakub'ewa tayi kana tace "D'akin Yaya zan share..." Har cikin ranta taji dad'in hakan, da alama Deejoh da Ahidjo sun soma sakewa da juna, lallai shawarin Hinde ya mata amfani, ga dukkan alamu auren da aka masa zaisa ya zauna dasu sosai... Tsaf Deejoh ta share masa d'akin, ta linke masa abin sallahn sa harda k'aramar k'ur'ani ta gani saman abin sallar... Ta saki murmushi tana mamakin ashe duk gayun nan nasa dai bai mance mahallicinsa ba, lokaci guda girmansa da take gani ya kuma k'aruwa.... Ya d'an jima tsaye bakin k'ofa yana kallonta yanda ta zage sai gyara d'akin take, lokaci guda ya tsinci kansa da sakin murmushi, ashe dai yarinyar tanada hankali dukda tarin shiririta da take dashi, koda shike yasan shiriritar ma ta yarinta ce, ya tuna tunda sukayi aure da Nana H bata tab'a ganin wani abu nasa ta kintsa ba saidai ta umarce mai aiki tayi shid'inma sai taga bai d'age abinsa bane take umartan mai aikin, talk less of share masa d'aki saidai ma'aikata suyi... Shimfid'arsu kuwa da suka kwanta idan ba shi ya tattare ba toh kuwa shakka babu mai aiki ce zatayi... Ahidjo ya kuma sakin murmushi had'i da girgiza kai.... Juyowar da zatayi kuwa suka had'a idanu dashi yana nan tsaye hard'e da hannaye... Murmushi ya sakar mata yayinda tayi saurin janyo hijab d'inta ta saka... K'arasa shigowa d'akin yayi yana mai k'arewa d'akin kallo kana yace "Sannu da aiki..." Murmushi kawai ta sakar masa ba tareda ta furta komai ba... Idanunta a k'asa tace dashi "Dama gani nayi d'akin yayi k'ura shine... Shine na share..." Tayi maganar tana wasa da yatsun hannunta, lokaci guda tasa kai zata shige saidai kafin ta fice taji tattausan hannunsa ya kamo nata... K'irjinta ya yanke lokaci guda, tayi saurin d'ago kai tana dubansa, wannan murmushin ne dai saman fuskar sa... "Yaya zaki tafi bayan baki sanar dani abinda ya kawoki ba, ko kin mance ina waya kika shigo, ko yauma lab'e kike min kiji wayata da matata...." Cikin sauri ta shiga girgiza masa kai kana tace "Wllhi Allah ba lab'el nake maka ba..." Tayi maganar kaman zata kurma ihu... Ya d'an gimtse fuska kana yace "Toh mai ya kawo ki idan ba lab'el kikazoyi ba...." Deejoh ta rasa mai zatace, wannan shine tsile, ita harga Allah tazo ganin yanayin da yake ciki ne domin sosai ya bata tausayi sanda ya fito daga sashen Baffah.. Toh ma mai zata soma fad'a masa, wani dalili ne ya kawota d'akinsa.... Ganin tayi shiru ta rasa abin fad'i ya sanya Ahidjo sakin murmushi kana yace "Kar ki damu nan ai d'akin mijinki ne ko kin shigo bakiyi laifi ba..." D'akin mijinki da ya fad'i sai ya sanya jikinta yin sanyi, itakam wllhi harga Allah tama mance wai shid'in ne mijin da aka d'aura mata, tafi danganta gaskiyan labarin da tatsuniya sabida ko a mafarkanta D'angayu ya zarce irin mijin da take tunani, ina ita ina shi, wannan ko a 'yan gayun ma ba kowwacce bace ta dace dashi, wai ita Deejoh, Deejohn Iya Gaje itace wannan mutumin ya zamto mijinta, gashi har yana fad'i da bakinsa.... Bata ida tunanin nata ba taji ya kamo d'aya hannun nata ya mata masauk'i saman katifarsa yana fad'in "Zauna muyi magana"... Gefe da ita ya da ita ya zauna ta d'an matsa can k'arshen katifar a d'arare... "Deejah ina so ki saki jikinki muyi magana... Ko kema baki son ganina ne kaman yanda Baffah baison ganina...?" Da sauri ta girgiza masa kai alamun a'a... Ya jinjina kai had'i da furta "Good, kina jina ko....?" Ta jinjina masa kai alamun eh... Ahidjo ya kuma gyara zama kana ya soma fad'in "Kinga yanda Baffah ke fushi dani, kinga irin k'ok'arin da nakeyi wajen ganin na kyautata alak'ata dashi a matsayinsa na mahaifina.... Deejah duk duniyar nan ke kad'aice zaki taimaka min na sami soyayyar mahaifina da na rasa, ko baki so na sami albarkar sa...?" A hankali ta furta "Ina so ka gyara alak'ar ka da mahaifanka.." Ahidjo ya murmusa kana yace "Shiyasa nake so ki saki jiki sosai dani, ina so mu k'ulla shak'uwa tsakaninmu a matsayina na mijinki, idan Baffah ya lura da alak'a mai kyau dake tsanani na dake zai amince nayi na'am da zab'insu kuma hakan zaisa ya yafemin... Deejah inaso na tafi dake gidana Abuja na sakaki a makaranta kiyi karatu mai zurfi..." Lokaci guda Deejoh ta shiga washe baki jin zata shiga makaranta, amma data tuna wai tafiya da ita zaiyi sai kuma taji murnan ta ragu.... Ahidjo na hankalce da ita yanda da fari ta soma murna daga baya kuma mood d'inta ya canza... Kwanto da fuskarsa yayi kusan nata kana yace "Baki son karatun ne...?" Da sauri ta girgiza masa kai alamun a'a kana tace "Ina so sosai, babban burina kenan a rayuwata.... Amma ni banson binka nasan idan na tafi shikenan bazan sake ganin Babana ba kuma Innah da Baffah ai nima zasuyi fushi dani mutanen gari zasuce nima na gudu bariki...." Kalamanta na k'arshe ya kusa sanyasa dariya wai zasuce ta gudu bariki... Gimtse dariyarsa yayi kana yace "Babu wanda zaice bariki kika gudu tunda mijinki kika bi, ko su Innah ma bazasu ce haka ba..... Ko baki son bin mijin naki ne....?" Yanda yayi maganar ya bata dariya, saurin rufe fuskarta tayi tana murmusawa ba tareda tace komai ba... Ledan sayyayan da ya mata fitansu d'azu ya janyo kana yace "Bud'e fuskarki..." Kaman bazata bud'e ba sai kuma ta sauk'e hannayen nata a hankali idanunta a k'asa sabida sabuwar kunyarsa da ya shigeta..... Mik'a mata ledar yayi kana yace "Wannan naki ne..." Tabi ledar da kallo kana ta dubesa.... "Karb'i mana..." Ya sake fad'i yana dubanta.. A hankali ta girgiza masa kai kana tace "A'a na gode...." Ahidjo ya d'an d'aure fuska kana yace "Mai yasa bazaki karb'a ba...?" Idanun Deejoh a k'asa tace dashi "Ai Baffah zaiyi fad'a idan na karb'a..." Murmusawa ya d'anyi yana mai dubanta yace "Waye yace maki Baffah zaiyi fad'a, kin tab'a ganin miji yayiwa mata kyauta tak'i karb'a.... I'm your husband Deejah... You're my responsibility, kar ki sake k'in karb'an wani abu daga wajena kinji... Idan su Baffah sunk'i karb'an kyautata ke ya zama maki dole ki karb'a kinji koh... Oya gashi amsa...." Ya k'arashe yana mik'a mata... Hannu tasa ta karb'a had'ida d'an durk'usawa kana tace "Na gode Allah k'ara bud'i...." Godiya da addu'ar data masa ya sanyasa binta da kallo wani abu na tsargar masa cikin zuciyarsa, har cikin ransa dad'i yaji donshi tunda yake kyauta dukda shid'in ba gwanin kyauta bane bai tab'a yin kyauta aka gode masa irinta yau ba... Ashe kayi kyauta ayi maka godiya akwai dad'i shikam bai tab'a sani ba sai yau... Har Deejoh ta fice daga d'akin bai daina binta da kallo ba.... **** *Abuja* "A gaskiya Yaya Junaid kurum naji ban yarda da niece d'in nan tasa ba, gaskiya ni ina zarginta cikin FUSKA UKU in fact kawai ni jikina na bani itace FUSKA UKU, inaso na shiga jikinta sosai domin akwai abubuwa da dama da nake son sani gameda ita.." Junaid da ya k'urama waje guda idanu d'ago rinannun idanunsa yayi yana dubanta kafin yace "Ba wannan na aikeki ba, you know nothing Azeeza.... Abinda na umarceki kawai zaki min... Rayuwar Siraj nace ki shiga... Kin fahimta..." Ya k'arashe yana bud'e mata idanu.... Jinjina masa kai kurum tayi kana tace "Shikenan Yaya zanyi yanda kace..." Jinjina mata kai shima yayi kana yace "Good, Umma Marie ta kira baki nan zan kirata yanzu na had'aku..." Azeeza harda d'an tsallen murnarta take cewa "Da gaske Yaya, dan Allah kira min ita... I miss her so terribly...." *** *Damaturu* Zaune take da bak'in nata wad'anda ta masu masauk'i a yammacin ranar, ganin kiran Junaid na shigo mata ya sanyata saurin mik'ewa tana fad'in bari ta amsa kira... Jinjina mata kai kurum Daddah tayi tana mai ci gaba da kai lomar tuwo... Ta dubi Mairo data kafa goran Fanta a baki tana kwankwad'a ta d'an yafaci cinyar Mairo tana mai k'asa-k'asa da murya tace "Kinga Mata 'yar aljanna bata sanmu ba ta bamu masauk'i ta karrama mu.. Allah dai ya biyata...." "Ameen.." Mairo ta amsa dashi lokaci guda ta tintsire da dariya.... Daddah ta bita da kallon tuhuma kana tace "Yo mai kuma nayi...?" Mairo ta d'an tsagaita dariyarta kana tace "Wllhi Daddah Sojojin nan kawai nake tunani... Wato ranar da matar nan tasan kalan mutanen da ta baiwa masauk'i inaga ranar zata sallame mu...." Yab'e da baki kurum Daddah ke dubaunta kana tace "Allah bazai amshi bakin ki ba, ni daga yau na zama salihatu kuma ai. ...Ke fita wannan bazan kuma ba balle nayi arangama da Sojin nan..." Mairo ta murmusa tana maida kallabinta gefen goshinta domin idan da sabo yabi jikinta kana tace "Toh Allah sa Daddah ta, Allah sa daga garin nan bama kuma hijira ba...." Daddah bata amsata ba sai kai lomar tuwonta take..... Dai-dai nan Umma Marie ta k'araso tana fad'in "Ayya kuyi hak'uri na barku ku kad'ai..." "A'a wllhi ai babu komai, Allah dai ya biyaki da Aljannah Mariya, samun irinki wannan zamani namu sai anji jiki...." Daddah ta fad'i tana kuma karyar lomar tuwo... Murmushi kawai Umma Marie take tana jin k'aunarsu har cikin ranta lokaci guda suka ci gaba da fira garin da suka baro... *** Tana jin k'aran bell tasan shine ya iso, cikin sauri ta mik'e tana kuma sauk'e wuyar rigarta ta isa k'ofan tana bud'ewa saiji tayi ya mak'ure wuyarta da iya k'arfinsa ya had'eta da garu yana fad'in "What the heck did you do Nana A... Where's she... Tell me, What did you do to her....?" K'ok'arin k'wace wuyarta take amma ta kasa, sosai Lamid'o ya shak'eta... Duk iyaka k'ok'arinta ta kasa k'watan kanta sai faman k'ak'ari take tana shure-shure... Har cikin ransa yake ji kaman ya gama da shegiya kowa ya huta, domin Nana H ta wuce annoba a cewarsa Flower vase dake gefenta tayi k'ok'arin rarumowa don k'watar kanta.... Aiko Allah ya bata sa'a ta d'auko vase d'in nan lokaci guda ta sauk'ewa Lamid'o akai... K'ara ya saki had'i da zubewa gefe.... Nana H ta samu ta mik'e tana watsa masa mugun kallo lokaci guda ta shiga sosa wuyarta yanda ya shak'eta.... Ta jima tana zube gefe itama tana sosa wuyarta had'i da yin tari kafin ta zamto dai-dai... Sai sannan ta hangi Lamid'o ko motsi baiyi ga jini a k'asar wuyarsa... Dafe kanta tayi cikeda tashin hankali ta shiga fad'in "Oh no no what have you done Nana H...." Kaman zautacciya take shiga jijjiga Lamid'o shiru kakeji baya mosti... K'aran da wayar Lamid'on yayi ya kuma razanata... Cikin sauri ta ciro wayar daga aljihunsa tana kallo... Lamba ce kawai babu suna... Hannunta na rawa ta d'aga wayar had'i da k'arawa a kunnenta ba tareda tace komai ba.... Daga d'aya b'angaren Malam Ayuba yace "Rankashi dad'e na zuba masa maganin cikin shayinsa kuma na tabbata yasha, na cika nawa aikin rankashidad'e saura naka...." Wani irin bugu k'irjin Nana H yayi... Lokaci guda ta katse kiran tana tunanin waye Lamid'o ke yunk'urin kashewa.... *SameenaAleeyou📚**FUSKA UKU*🏮 *25* *©Sameena Aleeyou...✍🏽* Ta jima rik'eda wayar a hannunta tana tunanin waye Lamid'o ke k'ok'arin rabasa da rayuwarsa... Toh kodai Uncle Siraj yake yunk'urin kashewa tunda gashi itama yayi yunk'urin kasheta, tabbas Uncle Siraj baya goyon bayan relationship d'insa da Nana A itama kuma bata goyon baya, in fact gaba d'aya gidansu su biyu ne basu goyi bayan abin ba wato shine yace bari kawai ya kashesu ya huta.... Lokaci guda jikinta yaci gaba da k'yarma Uncle Siraj d'inta... No no ina bazai mutu ba.... Jiki na rawa ta rarumo wayarta hannayenta har suna wani irin karkarwa ta shiga dialing layin Siraj.... Sau uku tana kira gashi dai wayar tana ringing amma ba'a d'agawa... Ji tayi tamkar an sauk'e mata guduma a k'irjinta... Cikin muryar kuka take fad'in "No no my Uncle love is alive... I know he's alive... He won't leave me... Yana raye bazai tab'a barina ba I'm sure of it....." Duk sunbatun da take Lamid'o dake faman nishi da k'yar yana kallonta, murmushi ya saki a hankali dukda jin jiki da yakeyi... Lokaci guda wayar Lamid'o ta sake ruri... Nana H ta kuma zabura tamkar zautacciya... Ta yunk'ura zata d'auka saiji tayi Lamid'o ya janyota da iya k'arfinsa yana k'ok'arin k'watar wayar yake fad'in "Give me that.... Idan kika d'aga wayar nan sai na fasa maki kai wllhi...." Bata saki wayar ba take fad'in "How dare you... You traitor , bayan duk abinda ya maka is that how you repay him akan kawai yace bazai baka auren 'yarsa ba... You should be ashamed of yourself Lamido.... Na rantse da Allah wani abu ya sami Uncle Siraj kaima zaka mutu....!" Ta k'arashe tana wani irin huci... Murmushi Lamid'o yake bayan ya k'waci wayarsa da k'arfin gaske, yana shafa k'eyarsa yanda jini ya d'an zuba ya kuma damk'ota da iya k'arfinsa lokaci guda annurin fuskarsa ya d'auke cak.... Cikin wani irin huci yake fad'in "Wannan shine abinda na tanadar ga duk wanda yace zai hanani samun farin cikina Nana A.... And let me remind you this young lady... You're messing with the wrong person..." Yana ida fad'in haka yayi jifa da ita jikin kujera ya fice cikin sauri yana kuma dialing layin Malam Ayuba... Da k'yar Nana H ta isa ga wayarta ta janyo ta kuma dialing layin Siraj... Tana kira kuwa ya d'aga wannan karan... Wani irin nannauyan ajiyan zuciya ta sauk'e kana tace "Uncle kana ina ne..? Are you sure you're fine... Where are you please....?" Yanda tayi maganar cikeda damuwa bai baiwa Siraj mamaki ba tinda yasan ta saba masa hakan amma wannan karan jin muryar nata cikin wani irin yanayi ya d'an sanyasa damuwa... Murya cikeda kulawa yace "Sweetheart lafiya... Meke faruwa... Gani a hanyar gida.. Hope all is well...?" Sauk'e ajiyan zuciya tayi kana tace "No babu komai Uncle, kasan kana huld'a da mutane da dama so you need to be very very careful, kasan mutane nowadays ba abin yarda bane..." Murmushi Siraj yayi kana yace "Kar ki damu sweetheart zan kula da kaina sosai insha Allah I promise you, so ki kwantar da hankalinki koh...." Cikeda jin dad'i ta amsa masa kana ta hanging up wayar.... Zama tayi cikin kujera had'i da cunk'ushe sumarta waje guda... Duniyar tai mata zafi batasan da waye zata soma ba, bata san ta yanda zata b'ullowa lamarin ba... Ga Lamid'o ga wancan shegiyar sakatariyar Siraj d'in wacce ke neman zame mata alak'ak'ai.. Koda shike wannan yarinyar mai sauk'i ce.... Lokaci guda ta saki murmushi tana hango fuskar Azeeza cikin idanunta mai zubin taliya a cewarta..... *** Yana isa gidan suka keb'e da Malam Ayuba... Malam Ayuba yace "Yallab'ai tuntuni na saka masa maganin a shayi kuma na tabbata yasha.." Lamid'o ya jinjina kai cikin ransa yace idan kuwa yasha he probably fell asleep by now.... Lokaci guda ya dubi Malam Ayuba kana yace "Na gode Malam Ayuba kana iya tafiya..." Malam Ayuba ya kuma masa godiya kafin ya fice... Kai tsaye sashen mahaifin nasa ya nufa, aiko kishingid'e ya taddasa jikin kujera Television na faman aiki.... Cikin sand'a ya isa yanda keys d'in d'akinsa yana neman Key d'in domin kuwa yasan halin mahaifinsa sam bai barin d'akinsa a bud'e kuma baka isa ka shiga masa d'aki saidai shi ya umarceka, babu mai shiga sai masu gyara masa kuma suma a gabansa suke gyaran, shi kansa Lamid'o rabonsa da shiga d'akin idan bai manta ba tun yana matashi d'an shatakwas, mahaifinsa bai yarda da kowa ba..... Cikin sand'a ya d'auki keys d'in ya isa k'ofar d'akin ya soma gwadawa, cikin sa'a a gwaji na uku k'ofar ta bud'e saida ya sauk'e ajiyan zuciya had'ida yin hamdala kafin ya shiga d'akin.... Cikin sauri ya nufi drawers ya soma bincike.... Abinda ya basa mamaki hoton su Nana H tun suna yara ya soma zak'ulowa, FUSKA UKU jikin hoton kamannin su iri guda... Guda d'aya daga cikin 'yanukun an zana mata jan marker.... Sosai Lamid'o ya tsaya yana duban hoton.... Bai gama mamaki ba saida ya d'ago wasu hotunan wanda akasari na iyalan gidansu Siraj ne hardama wad'anda bai sansu ba wanda shakka babu yasan bazai wuce Yayan Siraj marigayi bane da matarsa... Kan Lamid'o ya kuma d'aurewa, domin kuwa sunan mahaifiyarsu Siraj kenan Mairo... Toh kodai itace... Kai bazai yuwu ita bace tinda a wayar yaji ana cewa Mairo sun gudu.... "Toh wacece Mairo...?" Ya tambayi kansa a hankali.... Cikin sauri yaci gaba da bincika duk wasu takardu dake wajen... Baiga komai ba bai fahimci komai ba, saiko hotunan family d'in Siraj da ya gani kala daban daban, wanda yasan mahaifinsa ya jima yana bibiyan wannan family... Toh amma su waye suka gudu har hankalin mahaifinsa ya tashi haka.... Lokaci guda ya mik'e had'i da fuzar da iska don bai sami abinda yake nema ba, mugun kallo kurum ya watsa wa mahaifin nasa sanda ya fito lokaci guda ya tuna guy d'in da ya kira mahafin nasa tunda ya d'auki number sa zaiyi yanda zaiyi ya sanar dashi mai mahaifinsa ke k'ullawa ko nawa zai kashe.... Cikin sauri ya fice daga gidan ya nufi gidansa ya shirya tsaf don zuwa ganin farin cikinsa Nana A.... Wani kulawa da soyayya Lamid'o ya dinga nunawa Nana Asma'u wanda ba kad'an ya tab'a zuciyar Nana H ba, haka aka watse aka bar masu parlorn don su samu su fahimci juna.... Siraj na mik'ewa Nana H tabi bayansa tana mai watsawa Lamid'o harara... Murmushi kurum Lamid'o keyi yana aika mata da wasu kallo da ita kad'ai tasan ma'anoninsu... *** *Misau* Tsaye yake jikin motar sa waya manne kunnensa daga d'aya b'angaren Sabi'u abokin aikin nasa da suke wayar tare yace "DT amma kanaga zamanka a Misau bazai kawo mana matsala a binkicen da mukeyi ba, we really need you here...." Ya k'arashe murya cikeda damuwa... D'an shafe goshinsa Ahidjo yayi kana yace "Sabi'u ni kaina na sani ya kamata na dawo, kasan abu da iyaye kuma babu wanda yasan Misau nazo sai kai kad'ai ko matata bata sani ba.... Yanzu abinda nake so da kai ku sake komawa ku bincike guy d'in sosai nasan anything next week zan dawo insha Allah... Just keep on the good work..." Sabi'u ya d'an shafi k'eyarsa kana yace "Shikenan Detective Allah ya nuna mana, agaida mutan gida...." Ahidjo ya amsa masa kana sukayi sallama ya katse kiran, zama dirshan yayi cikin motar nasa yana tunanin ya kamata ya koma kafin abubuwa su rincab'e masa a office... Gaje kuwa tun da ta hangesa ta soma sauri uwa zataci da k'asa, sai faman wage baki take.... Tana isowa ta soma magana cikin dashesshiyar muryarta wanda da k'yar yake fita... "Salama alaikum, salama alaikum.... Bakin bariki..." Karkatowa kurum yayi yana binta da kallon mamaki wai bak'in bariki.... Kafin ya sami zarafin magana Gaje taci gaba da fad'in "Baka gane ni ba koh.... Toh nice dai uwar goyon matarka Deejoh wacce ta cinye uwarta ta kuma kama kurwan ubanta dake kwance yana jinya, nima don kurwata tafi k'arfinta ne shiyasa bata kama ba.... Yanzu maganar da nake maka ni ce nan mai biyan hayan gidan ubanta ga bashin kud'in magani ya mana katutu... Tinda na rasa Deejoh na rasa 'yar talla shine nazo......!!" Aya ta saka wa maganganun nata ganin bindiga a gaban motarsa a ijiye cikin motar tasa..... Gaje ta kuma ware idanu tabbas bindiga take gani ra'il ainu ba cikin shirin wasan kwaikwayo ba.... Waige-waige ta soma tana neman ta wani hanya zata arce... Ba komai ya fad'o mata rai ba sai tunanin k'ila d'an fashi ne ko d'an shan jini bacin haka mai ya had'asa da bindiga.... A tamanin ta tattare zaninta ta rik'e a hannu ai kafin ya sami zarafin magana ta arce a guje.... Ahidjo ya bita da kallon mamaki yana tunanin k'ila tab'in hankali takedashi domin maganganunta ma gaba d'aya baiyi kama dana masu hankali ba... Girgiza kai kurum yayi yana mamakin yanda Deejoh ta zauna da wannan mata... Lokaci guda yaji yana son sanin komai gameda Deejoh, cikin gida ya shige ya kuma samu Innah ce kawai zaune a tsakar gidan.... Innah ta fad'ad'a murmushinta tana fad'in "Baba wuro an shigo...." Murmushi kwance saman fuskarsa ya zauna daga can gefen tabarman yana gaida Innah.... ta kuwa amsa masa da sakin fuska... Nan ya shiga d'an waige waige yana neman ta yanda zaiga Deejoh... Tsaf Innah na hankalce dashi... "Ahidjo lafiya dai koh.... Naga sai dube dube kake..?" "Lafiya lou Innah, kawai dai naga ke kad'ai kike zaune banga Deejoh ba...." Innah ta d'an murmusa cikeda jin dad'i kana tace "Deejoh na ciki na bita karatunta na allo kada su gudu mata tunda kaga yanzu ba zuwa take ba.." Ahidjo ya jinjina kai had'i da gyara zama kana yace "Innah ni dama akwai abinda nake son tambayarki gameda Deejoh...." Gyara zama Innah tayi tana dubansa cikeda kulawa tace "ina jinka..." "Innah wai dan Allah mai yasa akayiwa Deejoh aure a 'yan shekarunta... Sannan wacece ita, mai yasa matar nan tace min ita uwar goyonta ce sannan da na tambayi Deejoh cemin tayi mahaifiyarta ce... Innah menene gaskiyar Al'amarin... Ina son sani a matsayina na mijinta..." Innah ta murmusa had'ida kalmashe k'afafunta kana tace "Allah sarki Deejoh, ashe ce maka tayi Gaje mahaifiyarta ce..." Ahidjo ya jinjina kansa alamun eh... Innah ta kuma murmusawa had'i da girgiza kai kana taci gaba da fad'in "Gaje ba mahaifiyar Deejoh bace kishiyar mahaifiyarta ce, mahaifiyar Deejoh ta rasu da jimawa, mahaifinta kuwa bashida ta cewa a gidansa sai abinda Gaje tace.... Deejoh marainiya ce wacce ta tashi cikin tsananin maraici... Tausayi da k'ok'arin ceto rayuwar Deejoh daga hannun muguwar nan yasa muka nema maka aurenta domin bamuda zab'i, hakan ne kawai zai fitar da ita daga k'angin data tsinci kanta ciki.... Kaji tak'aitaccen tarihin Khadijatu...." Jinjina kai yayi cikeda tausayin Deejoh kana ya mik'e yace da Innah "Idan ta gama karatun ta kawo min shayi d'akina..." Innah ta jinjina kai tace "Toh Babana zata kawo maka...." D'an rusunawa yayi had'i da amsawa kafin ya nufi verandar Baffah ya gaidashi dukda a ciki-ciki yake amsa masa... Tinda ya shige d'aki tausayin Deejoh da tunaninta ya cika zuciyarsa, shi harga Allah a tsarinsa idan ya tafi da ita ba'a matsayin matarsa zai tafi da ita ba saidai ya tafi da ita matsayin 'yar aiki da aka tilasta masa zuwa da ita daga gida don harga Allah baisan ta yanda zai soma sanar da matarsa aure aka masa ba, auren ma da k'aramar yarinya wanda da yayi aure da wuri da ya haifeta.... Shi bama wannan ba, tausayi yarinyar take basa ya zaci Fulani sun daina wannan auren wanda shi a wajensa child abuse ne ashe dai basu daina ba.... Shafe sumarsa yayi had'i da d'an fuzar da iska.... Sallaman ta ya katse masa tunanin da yake... Idanunta a k'asa har ta k'arashe shigowa d'akin yayinda Ahidjo ya shiga bin duk wasu b'angarori na jikinta da kallo... Bai tab'a k'arewa jikinta kallo ba sai yau, shi kansa baisan dalilinsa na yin hakan ba, iyaka dai yasan so yake yaga yanayin girman jikinta da har za'ayi tunanin mata aure don shi kullum fuskarta kawai yake kalla.... Gefensa ya nuna mata yace ta dawo wajen ta zauna.... Ba tareda ta kawo komai cikin zuciyarta ba ta komo wajen ta zauna.... Ahidjo yaci gaba da kurb'an shayinsa yana kuma k'are mata kallo.... Ji yake wani abu na tsargar masa cikin jikinsa.... Tunda ya soma bin jikinta da kallo yake jin wani abu nai masa yawo... Saurin rintse idanunsa yayi yana k'aryata zuciyarsa dake gaya masa wani abu gameda Deejoh.... Deejoh kam gaba d'aya ji tayi yau d'in bata sake dashi ba... Ji tayi tsikar jikinta na tashi musamman data d'ago idanu taga irin duban da yake mata.... Gabanta ya yanke ya fad'i lokaci guda.... Ta d'an yunk'ura zata tashi, harda d'an rawar murya take fad'in "Barin je kar Innah ta nemeni..." Saidai kafin takai aya taji hannunsa cikin jikinta ya rik'ota... Dubansa ta d'anyi cikeda tsoro saidai kafin tayi magana ta jiyo muryarsa na fad'in "Innah bazata nemeki ba tasan kina wajena.... Kuma kin mance nace yau zakimin labarinki...." Itakam wani irin kunyarsa da nauyinsa takeji.... Bata iya cewa komai ba sai zama da tayi wannan karan daga can gefe ta zauna.... A hankali yaci gaba da sipping shayinsa lokaci zuwa lokaci yana dubanta, ko wannensu da abinda ke sak'awa cikin zuciyarsa.... Koda ya gama shan shayin ma kasa sakin jiki tayi dashi, shi kad'ai ya dinga mata labarai dana ban dariya da kuma na wajen aikinsa, k'arshe har hiran matarsa saida ya mata, abubuwan da take so da wad'anda bata so, kalan soyayyar dake tsakaninsu da sauransu.... Dukda Deejoh batasan meye kishi ba amma saida taji wani abu cikin zuciyarta... Batasan sanda tace "nuna min matar taka naga hotonta..." Wayarsa ya janyo dashike itace saman screen ya d'an danna power buttom ta kawo haske, kyakkyawan fuskar Nana H ya bayyana... Jikin Deejoh yayi sanyi, domin kuwa duk yanda 'yar gayu takai ga gayunta matar Yaya Ahidjo takai... Kallo Ahidjo ya bita dashi ganin yanda yanayinta ya canza lokaci guda kana yace "Yayadai? Ko bata maki kyau bane....?" Murmushin yak'e Deejoh tayi kana tace "Tamin kyau sosai, ta iya gayu itama kaman kai....." Ahidjo ya murmusa kana yace "Kar ki damu idan mun tafi Abuja har gayu zata koya maki dan naga kema kina son kwalliya da gayu...." Cikeda jin dad'i ta shiga wage baki tana fad'in "Nima zan zama 'yar gayu....?" "Ahidjo ya kuma jinjina mata kai kana yace "Sosai kuwa zaki zama 'yar gayu kema kawai ki tayani rok'on Baffah ya amince mu tafi...." Deejoh ta kuma jin dad'i gashi zata shiga makaranta gashi zata koyi gayu ai tuni tace "Da sassafe insha Allah zan tambayi mana Baffah..." Ahidjo yace "Yauwa Deejah ta, ki dage cewa ke mijinki kike son bi kinji... Ki dage kina so mu tafi don ki fara zuwa makaranta...." Deejoh ta jinjina kai tace "Haka zance masu shida Innah dama sun san ina son makaranta sosai..." Murmusawa yake yana dubanta had'ida jinjina yarinta irinta tata kana yace "Muje na rakaki d'aki toh...." Babu musu ta mik'e suka nufi k'ofa... Har d'akin Innah ya mata rakiya, basu sami Innah a d'aki ba don har ta wuce b'angaren Baffah... Ahidjo ya mata rakiya har cikin d'akin kafin ya juya zai fice... Juyowa yayi ya d'an dubeta had'i da sakar mata murmushi kafin ya fice... Deejoh ta kwanta saman gado had'ida rintse idanu zuciyarta naci gaba da bugawa da sauri da sauri... Shiko tunda ya koma d'akinsa kasa barci yayi sai faman juyi yake saman katifa ba tareda sanin abinda ke damunsa ba..... *** Wasa-wasa shak'uwa da sabo sun shiga tsakanin Ahidjo da Deejoh sosai a 'yan kwanakin, duk sanda suka keb'e tsintar kansa yake cikin yanayi na tsananin buk'ata, baisan dalili ba amma kam idan bai k'aryata zuciyarsa ba sha'awar Deejoh ke d'awainiya dashi, shi kansa abiga abin sha'awar a jikinta ba amma ko yaushe suka keb'e sai yaji hakan, ba abin ya avoiding d'inta ba plan d'insa ya b'aci... A b'angaren Lamid'o da Nana A abubuwa basu tafiya yanda ya kamata domin kuwa Nana H ta kasa ta tsare duk wani yunk'urin da Lamid'o yayi sai ta toshesa, shi kansa Siraj yak'i approving d'insa har yanzu... A b'angaren Junaid kuwa ko yaushe k'ok'arin janyo hankalin Nana A yake garesa, shak'uwa da amintaka na musamman ta kuma shiga tsakaninsu, duk yanda ka gansu a foundation toh tare suke, har wasu a foundation d'in suka soma zargin ko soyayya suke, Aunty Lami da kanta saida ta fad'i hakan... Murmushi kawai Nana A da Junaid keyi sai yace shi k'anwa ya d'auketa... Zaune suke wajen da suka saba zama har Malam Sile yazo d'aukarta, fuskarta kawai zaka duba kasan tana cikin tsan-tsan damuwa... Junaid ya kuma dubanta yana karantarta kana yace "Asmah that guy is your Uncle's friend.... look I'm not saying you should reject him or something.... Abinda nake nufi Uncle Siraj yafi kowa sanin Lamid'o maybe yanada reasons d'insa da yasa baya sonki dashi... Sannan Nana H abokin mijinta ne kaman yanda kika fad'a min, so kinga itama ta yuwu tasan wasu abu da dama gamedashi wanda ke baki sani ba...." Ya kuma marairaice fuska had'ida kwantar da murya kana yaci gaba da fad'in "Look Asmah.... I care about you and I don't want you getting hurt.... Think about this please..... Kinji.." D'an murmusawa tayi cikeda jin dad'in yanda Junaid ke mata magana kana tace "Shikenan Junaid. I'll think about it I promise you..." Murmushi shima ya sakar mata kana yace "Murmushi yafi kyau da kyakkyawar fuskar ki...." Ya k'arashe yana binta da wani irin kallon k'urillah wanda ya sanyata murmusawa had'i da rufe fuska tana fad'in "Ni daina ka daina kallo na haka..." "Why, am I not allowed...?" Ya tambaya teasingly Hararan wasa ta aika masa kana tace "Kai ba.... Kana son wasa ko a wajen aiki.." Murmusawa ya kumayi sanda ya shiga tura tayun wheelchair d'insa yake fad'in "Believe me wa ke kad'ai kawai nake wasan....." Nana ta bisa da kallo cikeda tausayin sa duk sanda ta tuna bashida kowa.... Suna a wajen ta hangi motar Nana H yauma ita tazo d'aukarta... Murmushi kwance saman fuskar Nana A take duban Junaid kana tace "Finally yau zanyi introducing d'inka wa 'yar uwata Nana Hafsatu..." lokaci guda k'irjin Junaid ya buga sanda yabi Nana A da kallo... Bai sami zarafin magana ba sai k'aran parking d'in motar Nana H da sautin ya dira cikin kunnuwarsa... D'ago idanun da zaiyi sukayi ido hud'u da Nana H tana takowa cikin k'asaita da yanga kaman yanda ta saba.... Tana k'wrasowa wajen Nana A ta k'arasa tayi hugging d'inta cikeda jin dad'i tana fad'in "Sistu yauma kin tuna dani, naji dad'i sosai..." Nana H bata sami daman amsata ba sai duban Junaid da take babu ko k'yafta idanu... "Asma'u wanene wannan....?" Nana H ta tambaya idanunta akansa yayinda shima nasa idanun k'ur akanta... *SameenaAleeyou📚**FUSKA UKU*🏮 *26* *©Sameena Aleeyou...✍🏽* *Fatan Alheri Aysha Sada Machika Novels...💖* Lokaci guda Junaid ya sakarwa Nana H murmushi kana yace "You must be Nana H...?" Yatsina fuska kurum tayi tana binsa da kallon k'ask'anci kafin ta sami zarafin magana muryar Nana A ya katse ta... "He's Junaid my coworker....." Ta kuma maido da dubanta ga Junaid kana taci gaba da fad'in "Junaid wannan itace Nana H 'yar uwata da nake baka labari..." Kallon Nana H kurum Junaid yake yana jinjina kai kana yace "I see, Barkanki Nana H is a pleasure meeting you, naji labarunki da dama daga 'yar uwarki......" Ya k'arashe murmushi kwance saman fuskarsa Kallon tuhuma Nana H ke bin Nana A dashi kana tace "Wait... Wait Nana A wai kina nufin har ma irin wad'annan shirgin kike bada labarina na.... Niko mai zai had'ani da nakasassu da zakizo foundation d'inki kina labarina... Kar ki sake banaso, banson komai yayi associating d'ina da nakasassu kin fahimta koh..." Ta k'arashe tana kuma yatsina fuska... Sosai jikin Nana A yayi sanyi da irin cin zarafin da Nana H taiwa Junaid, cikeda fushi take fad'in "Haba Nana H, meyene haka, meye laifin mai nakasa, shin mu muka so muga kanmu haka? Ba Allah bane ya jarabcemu, kema fah bakifi k'arfin Allah ya jarabceki ba... Kuma idan kana raye tabbas ba'a k'are maka halitta ba... This is...." "Ya isa da Allah, ba wa'azi nace kimin ba, idan kina iya tafiya kizo mu tafi, idan kuma bazaki tafi ba fine... Ni kinga tafiyata tinda ke bakisan meke maki ciwo a rayuwa ba..." Ta k'arashe tana karkad'an d'an makulin motar har ta isa ga motar tata... Nana A da jikinta yayi sanyi gaba d'aya juyowa tayi tana duban Junaid da ya raka Nana H da wani irin kallo shi kad'ai yake sak'e-sak'e cikin zuciyarsa... Kafin Nana A ta sami zarafin magana ya sakar mata murmushi kana yace "It's nothing, kar ki damu kinji.... Nasan akwai mutane irin haka so bai dameni ba, kuma banyi fushi ba, ba kowa bane zai iya zama da mai deficiency irin namu bai k'yamacesa ba ko ya nuna masa ya fisa ba.... That's why bazan tab'a auren mace mai cikar halitta ba sabida gudun gori a gaba..." Kallo Nana A take binsa dashi lokaci guda take auna kalaman nasa... Mai yake nufi da bazaiyi aure ba sai mai nakasa... Kenan itama idan ta auri mai lafiya irin haka ka iya faruwa da ita..? bata kai ga samo amsar tambayarta ba ta jiyo muryarsa yana fad'in "Please kar ki bari wann maganar ya dameki... And promise me bazaki samu sab'ani da 'yar uwarki akan wannan maganar ba..." K'ak'aro murmushi tayi tana jinjina sanyin zuciya da kyakkyawar d'abi'a irinta Junaid kana tace "I promise you, bazan kuma tada maganar ba..." Murmushi shima ya sakar mata kana yace "Thank you.... See you tomorrow, you take care Okay...." Ya k'arashe yana tura tayun wheelchair d'insa zuciyarsa nai masa wani irin zafi... Tabbas Nana H batasan su waye sanadin kasancewarsa saman wannan kujera ba da bata soma magana makamancin haka ba, amma itama kwanannan zata tsinci nata mijin saman irin kujeran da yake bisa.... Ya k'arashe tunanin nasa wata irin murmushi mai cikeda ma'anoni kwance saman fuskarsa... *** Tin daga nesa Nasaar ya hangosu Azeeza na biyeda Siraj yayinda waya ke manne kunnen Siraj, shifah sam baison k'eb'ewar Azeezarsa da Siraj especially now that they're in relationship... Wani irin kishin Siraj yakeji maras misaltuwa, gani yake kaman ya tapka ganganci tinda ya bari Azeeza ta soma aiki a Laushi Group, baida zab'i hakan ne kawai zaisa Junaid ya kuma aminta dashi har ya basa auren tilon k'anwarsa tinda yasan har abada Azeeza bazata tab'a zama mallakin Siraj ba... Shi kansa bazai tab'a bari ba ma, Azeeza tasa ce shi kad'ai... Cikin sauri ya mik'e yabi bayansu... Dai-dai haraban kampanin suka tsaya lokaci guda wani security ya k'araso da motar Siraj wajen kana ya mik'awa Siraj d'in keys cikeda rusunawa.. Siraj ya bud'e motar ba tareda ya dubeta ba yace "Get in the car..." Sosai wannan jin kan nasa ke bata takaici idan ta tunawa Junaid take aikin sai kawai ta watsar ta shanye duk wani jidakan da yake mata, abin nasa har mamaki yake bata... K'arasawa tayi ta bud'e marfin motar ta shige.... Aiko kaman jira yake tana shigewa yayi key wa motar suka bar wajen ba tareda tasan ina suka nufa ba.... Hankalin Nasaar yakai k'oluluwa wajen tashi, cikin sauri ya zaro wayarsa ya turawa Azeeza text yana tambayarta ina zasuje itada Siraj... Take ta masa reply da batasan yanda suka nufa ba don ta tambayesa yafi baki biyar bai bata amsa ba... Nasaar ya kuma tura mata da sak'on ta kula da kanta kar ta bari Siraj ya mata wani mugun abu.... Azeeza ta tura masa da reply kar yaji komai she can take care of herself... Sauk'e ajiyan zuciya Nasaar yayi yana kuma karanta sak'on Azeeza don shi da niyyan bin bayansu yayi Azeeza ta kwab'esa acewarta kar Siraj yayi suspecting wani abu.... Lokaci guda ya kuma tura mata da wani sak'on _I love you so much my Zeeza.._ Murmushi Azeeza take tana bin screen d'in wayar da kallo, sak'on da Nasaar ya turo mata, hankalin Siraj rabi naga kwalta rabi naga Azeeza da tuntuni ya fahimci sak'o take karantawa tana kuma maida reply.... Zuciyarsa ta shiga raya masa da saurayi take yi, k'irjinsa ya shiga masa zafi, cikin dakekkiyar murya yace da ita "Bance maki babu kula samari during working hours ba.... Ke da waye kike chatting...?" Karkatowa tayi tana dubansa yanda yayi maganar babu alamun wasa a fuskarsa abin har yaso bata dariya... Batakai ga basa amsa ba taga ya mik'o mata hannu yana fad'in "Bani wayar...." Mamaki ya kuma cikata... "Amma dai Sir cikin rules d'inka baka hana amsa sak'o a rubuce ba amsa Kira ne dai ka hana, so I see no reason da zai sa ka amshe min wayata..." Ta k'arashe tana jujjuya masa maidaidaitan idanunta masu yalwan suma sama da k'asa... Siraj ya bita da kallon mamaki yanda sam bata tsoronsa dukda k'arancin shekarunta, shi da yawan 'yan matansa tsoronsa sukeji idan ya kafa masu doka basa takawa amma wannan yarinyar ko shakkarsa bataji a matsayinsa na shugabanta... Wata zuciya tace meyasa kake dangantata da sauran 'yan matanka ko ka mance ita employee d'inka ce not your girlfriend.... Mai yasa zai dameka...? Take b'angare na zuciyar tasa ta basa amsa da _Because you love her.._ Saurin rintsa idanunsa yayi had'i da saita kansa kafin ya maida hankalinsa ga driving lokaci guda ya d'an saki murmushi da gefen bakinsa wanda sai ka kula sosai ka gane hakan kana yace "It suits you, ina son mace mai tsiwa..." Yayi maganar can k'asar mak'oshi Karkatowa tayi tana dubansa mamaki saman fuskarta sai ka rantse bashi yayi maganar ba kana ta d'an murmusa had'i da juya idanu tace "Shiyasa kake son niece d'incan taka.." Ya kuma murmusawa sanda yake karyan kwana ba tareda ya dubeta ba yace "She's my Fav...." Azeeza ta murmusa tace "Sir nifa ba tsiwa na maka ba at least sai ka sanar dani yanda zamuje..." Nan ma idanunsa naga kwalta yace da ita "What if saidaki zanyi....?" Murmushi ta kumayi kana tace "Ai babu wanda zai iya sayana, tsadace dani...." Sai sannan Siraj ya maido da dubansa gareta kafin ya maida idanunsa kwalta yana mai fad'in "You sure about that...?" Ba tareda ta dubesa itama tace "Umhum sosai ma...." Dai-dai lokacin yayi parking k'ofar wani rantsettsen boutique na mata Wanda ya amsa sunarsa.... Azeeza ta bisa da kallo fuska cikeda alamun tambaya.... Lokaci guda yayi unlocking motar ba tareda ya dubeta ba yace "We're here to buy you new set of clothes... Ya kamata ki canza wardrobe d'inki idan kina son yin aiki dani....." Daga haka sa kai yayi ya shine cikin boutique d'in... Baki sake ta bisa da kallo tana mamakin k'arfin hali irin na Siraj, toh ita kuma ce masa tayi tana buk'atan canjin wardrobe ko me... Meye ma laifin kayan da take sakawa da zaice she need a change of wardrobe.... Lokaci guda ta shiga bin kayan jikinta da kallo shaye da tsananin mamaki.... *** Nana A ta kuma duban Nana H sabida d'aurewa da kanta yayi kana tace "Ina ne nan, ina kika kawoni....?" Kamo hannayen Nana A Nana H tayi lokaci guda idanunta sukayi rau-rau kana ta soma fad'in "Sistu..... I..... I don't know how to explain it, kawai gani nayi gwara na kawoki ki gane ma idanunki, don idan na fad'i maki ba yarda zakiyi ba...." Kan Asma'u ya kuma d'aurewa, girgiza kai ta d'anyi kana tace "I still don't get you... Wai menene ke faruwa Nana H...?" Wannan karan tsoro ya d'an nuna saman fuskarta... Kamo hannayen Asma'u Nana H tayi suka nufi cikin gidan.... Cak Nana A ta tsaya a k'ofa kana tace "Sistu bazan shiga ba sai kin sanar dani yanda kika kawoni...." Murmushi Nana H tayi kana tace "Asma'u kin yarda dani, kin yarda bazan tab'a cutar dake ba...?" Nana A ta jinjina kai a hankali... "Good.. Nan da kike gani ba gidan kowa bane sai gidan Lamid'o... D'azu Heedj ya turo min sak'o ta wajen Lamid'o, nayita kiransa ya kawo min sak'ona bai kawo min ba shine na yanke shawarin zuwa na amsa da kaina.... Toh da nazo amsa shine naga wani abu... Something terrible... Abinda baki bazai iya fad'i ba...." Aya ta dasawa kalaman nata sabida rawa da muryarta ya soma yi... Nana A cikeda tashin hankali ta soma hawaye tana tambayar Nana H mai ya sami Lamid'o dan Allah ta sanar da ita.... Bata bata amsa ba sai kamo hannunta da tayi suka nufi cikin parlorn... Abinda suka soma karo dashi shi yafi komai d'aga hankalin Asma'u... Kwalaben barasa ne kusan kalan biyar a wajen, da wasu shirgin kayan maye... K'irjinta yayi wani irin yankewa ya fad'i.... Ta shiga bin hotunansa dake parlorn da kallo tana addu'an inama ba shi bane, saidai zuciyarta ta aminta mata tabbas gidansa ne.... Wani d'aki suka hanga a bud'e Nana A ta soma tafiya ta nufi d'akin jikinta na wani irin rawa... Saidai kafin ta isa d'akin taja ta tsaya cak sabida wani kayan tashin hankalin da kunnuwanta suka jiyo mata... Muryar mace take ji cikin sautin da bai kamata ba tana ambaton sunan Lamid'o cikin wasu irin sumbatu marassa dad'in saurare wanda dagaji kasan masha'a kurum suke aikatawa.... Jikin Nana A ya d'auki b'ari innalillahi kawai take ambata ba tareda ta iya motsa koda d'an yatsanta ba.... Cikin sauri Nana H ta k'arasa ta Lakota suka nufo waje kana ta rungumeta tana bata baki... "Kiyi hak'uri Sistu shiyasa banso kika gani ba amma bazan iya b'oye maki ba sabida bana son na cutar dake... Wannan shine Lamid'o wannan ne real identity d'insa... Asma'u Lamid'o bai kamaceki ba, Lamid'o ba irin mijin da ya dace dake bane.... I'm sorry Sister banson ganinki broken....." Tsananin kukan Nana A ya k'aru tanayi tana k'unshe bakinta, lokaci guda ta shiga janyo hannun Nana H tana fad'in "Mu bar wajen nan, dan Allah Nana H mu bar wajen nan kinji...." Ta k'arashe cikin shesshek'ar kuka... Rungumeta Nana H tayi suka fice daga gidan suka nufi mota... Wani munafukin murmushi Nana H tayi kana ta dubi Nana A da kanta ke kife saman cinyarta tana kuka mai tsuma zuciya kana tace "Wllhi bazan barshi haka nan ba, wllhi sai na ci masa mutunci shi bai isa ya wulak'anta 'yar uwata ba yayi tunanin he can get away with it...." Ta k'arashe maganar nata cikin tsananin huci sai ka rantse iyaka gaskiyarta kenan.... Lokaci guda ta nufi cikin gidan Lamid'o mayaudarin murmushi saman fuskarta... Nana A kam ko zarafin amsata bata samu ba don batama fahimci mai take nufi ba, sautin budurwar Lamid'o data jiyo ya kasa b'acewa daga kunnuwarta... Nana H na shiga gidan ta dubi su Linda da Bash dake faman bunka sigari, lokaci guda ta ciro check cikin jakanta ta wurgi Bash dashi kana tace "Make sure you tidy up this mess kafin ku bar gidan nan... Kuyi sauri yana iya dawowa any moment....." Tana ida fad'in haka ta fice cikin sauri... Bash da Linda harda ihun murna sanda sukabi check d'in da kallo... *** Kallonsa take yanda yaketa jidan kaya wanda akasarin kayan abaya ne irinta larabawa.... Idan tayi magana ma ba amsata yakeyi ba balle taji dalilinsa na mata shopping... Lokaci guda ta b'ata rai sosai murya cikeda tsiwa tace "Sir wllhi wllhi kaji na rantse ko ka saya min kaya bazan saka ba tinda bace maka nayi banida kaya ba...." Karkatowa Siraj yayi yana dubanta kana yace "A haka kike tunanin zan barki ki dinga ratsa cikin maza kina saka d'inkin atampa riga da skirt ko wani gardi na ganin jikin ki, banson ki dinga janyo hankalin employees d'ina kanki don dokar Kpaninmu ne ba'a soyayya..." Shaye da mamaki take dubansa, wai kishinta yake ko mai.... Bata kai ga samo amsa ba yaci gaba da umartan masu kantin da su fito masa da designers dogayen riguna 'yan dubai.... Wayarsace tayi k'ara ya d'aga lokaci guda yana mai ambatan sunan Nasaar.... Lokaci guda yake furta "What!!!!.... Okay okay I'll be there in a bit... Kar ka bar wajen just keep an eye please...." Daga haka katse kiran yayi had'i da robbing nape d'insa warily.... Kallo ta bisa dashi kana tace "Problem....?" D'an dubanta yayi kana yace "An emergency happened in the office, my presence needs there immediately, so zan kira niece d'ita Nana H ta kaiki gida, kar ki bar wajen nan kinji koh, just wait here...." Ya k'arashe yana zira wayarsa a aljihu cikin sauri ba tareda ya jira amsarta ba ya isa yayi settling bills ya fice a fujajan yana neman layin Nana H... Kambuu wannan matar zai kira wai ta kaita gida... Azeeza ta fad'i cikin zuciyarta... Lokaci guda kuma ta shiga tunanin toh waima wani emergency ne ya faru? Tinda taji Nasaar ne ya kirasa tasan bazai wuce kishi irin na Nasaar bane kurum, yayi hakan ne don b'ata masu fitar tasu.... Toh kodai ta tafine kar ta jira wannan mahaukaciyar niece d'in tasa... Wata zuciya tace jirata kurum tinda yace haka.. Waje ta samu ta zauna tana mai kiran layin Yayanta Junaid... *** Nana H na ida parking wayar Siraj ya shigo mata, kafin ta sami zarafin sanar dashi abinda ke faruwa tsakanin Nana A da Lamid'o Siraj ya soma sanar da ita buk'atarsa... Wani irin bugu da k'irjinta yayi k'iris ya rage wayarta bai sullub'e daga hannunta ba.... *SameenaAleeyou📚**FUSKA UKU*🏮 *27* *©Sameena Aleeyou...✍🏽* Cikin gida Nana A ta shige har lokacin hawaye bai daina zarya saman fuskarta ba... Ammah da Ayiya suna parlor ta wucesu ba tareda tace dasu komai ba... Gaba d'aya hankulansu tashi yayi ganin yanayin nata, Ayiya tabi bayan Nana A tana tambayarta abinda ya faru, inaa Nana A sam bata sami zarafin amsata ba, hankalin Ayiya idan yayi dubu ya tashi... Cikin sauri ta fice daga parlorn tana rangad'awa Malam Sile kira, bata hangi kowa ba sai Nana H da tayi zaune cikin mota ta rasa meke mata dad'i... A d'ari Ayiya ta nufi Nana H tana fad'in "Ni dama nasan za'a rina... Muguwa mai mugun hali uwar mai kika mata....?" Ta k'arashe tana fincikan marfin motar Nana H Wani banzan kallo Nana H ta watsa mata irina banida lokacinkin nan kana ta karkato da kyau tana duban Ayiya dake faman huci kana tace "Wannan shine lokacin da nake jira yazo... Barikiji na fad'a maki Nana H ta wuce duk wani tunaninki, tuggunki da kuma makircinki... Sannan da kikazo kina min shouting akai mai yasa baki tsare d'iyar taki kin tambayeta ba....?" Ta kuma murmusawa kana taci gaba da fad'in " Kije ki tambayeta mai Lamid'o Sarki naki ya mata na tabbata daga nan zaki sami cikakkiyar bayani don ni banida lokacinki...." Tana ida fad'in haka ta finciki motar ta tayi gaba Ta bar Ayiya tsaye a wajen tana faman tururi *** Shafa kansa Lamid'o yayi had'i da fuzar da iska kana ya kuma damk'e wayar yana mai ci gaba da fad'in "Look zan biya ko nawa ne.... Just tell me wani aiki kake wa Bulama...." Nazir ya shafi kansa yana muzurai kana yace " Kaman nawa zaka biyani....?" Cikeda jin dad'i Lamid'o yace "Ka fad'i amount d'in da kake so...." Nazir baki sake yace "Haba rankashidad'e don't take me for a fool mana... A waya fah muke maganar nan.. Naji alert kafin na baka duk wani information da kake nema gameda Mairo, I'll send my bank details ka fahimta...." Lamid'o ya murmusa kana yace "Babu matsala sai na jika daga yanzu zuwa anjima..." Daga haka katse kiran Lamid'o yayi had'i da sakin murmushi, zuciyarsa tana kuma tunzurasa wajen sanin wacece MAIRO.... Suna ida waya Nazir ya kuma ficewa ya nufi gidansu Zaliha ko an sami wani labari gamedasu Mairo, don tunda su Mairo suka bar garin cikin neman yanda zai samesu yake wayoyinsu gaba d'aya baya shiga... *** *Damaturu* Cikin tsananin fushi Mairo ta kuma duban Daddah kana tace "Daddah fisabilillahi mai yasa zaki karya min SIM d'ina mai yasa zaki min haka, haba Daddah shin kina kyautawa rayuwata kenan...?" Daddah dai tinda ta soma magana tab'e baki kurum take ba tareda ta furta koda kalma ba k'arshe da abin ya isheta mik'ewa tayi tana duban Mairo kana tace "Wai kin mance duk garin da muka baro toh doka ce mu canza layi...? Mairo wai meke damunki ne, shin karya layin waya yau ya zamto bak'on abu a wajenki ne... Sanin kanki ne bazamu tab'a canza gari bamu canza layi ba.... Idan da sabo ya kamata wannan ya zame maki jiki...." Ta k'arashe tana janyo kayan sana'arta kasancewar yau zasu fara halartar shagon d'inkin su Umma Marie don tuni ta sama masu gurbin aiki a wajen.... Mairo kaman ta fashe ta dubi Daddah tayi k'wafa kana tace "Amma dai kinsan cewa akwai mutane masu mahimmacin a rayuwata da muka baro a Tambuwal, yanzu fisabillillahi ina zan sami Nazir da Zaliha....?" Tsuka Daddah taja bayan ta sake baki tana dubanta kana tace "Yo sai mai, ke duniyar nan da kike gani mutum ba abin yarda bane ka gama rayuwa da wani yana nan yana binka da sharri, ki ciresu a ranki idan da rabon ku sake had'uwa wani lokacin sai kiga Allah ya had'aku..... Karma kiyi hushi Mairamu na, Allah sa haka shine alkhairi don layin waya kam tun muna kwalta na tauneta...." Girgiza kai kurum Mairo tayi cikeda takaici kana ta isa saman carpet ta suri Jakarta ko takan Daddah bata kuma bi ba tayi ficewarta, dai-dai lokacin Umma Marie ta iso tana tambayar Daddah ko sun shirya... Daddah na washe baki take fad'in "Mun shirya Mari 'yar aljannah ke kawai dama muke jira.." Umma Marie ta murmusa cikeda jin dad'i kana tace "Madalla mu k'arasa waje toh kar lokaci ya k'ure mana...." A waje suka tadda Mairo d'aurin kallabinta a goshi don yau a sama take jinta tinda Daddah ta takaleta, k'iris kawai take jira.. Suna fitowa Mairo tayi gaba abinta, tana tafiya tana 'yan wak'e-wak'enta, Umma Marie sai murmushi take don tasan bazai wuce Daddah bace ta takali Mairo, a d'an zamansu tare har ta fahimci su duka biyun mafad'ata ne amma suna birgeta sosai, har cikin ranta take jin k'aunarsu.... Dakura ce zaune bakin shagon sai faman fetsa rashin kunyarta ga duk wanda taga dama take, dama haka nan Dakura take akwaita da fad'an rashin gaskiya harta Hajiya Yagana mai shagon d'inkin tasan halin Dakura, gashi ta zame mata k'arfen k'afa ta kasa korarta, Dakura masifeffiya ce ta k'arshe, da yawan customers da suka daina kawo d'inki Dakura ce ta koresu.... Tinda su Daddah suka shigo Dakura ke binsu da kallon banza haka nan tak'i jinin Umma Marie sam basu shiri, saidai Umma Marie mace ce mai tsananin hak'uri da kai zuciya nesa wannan dalili yasa bata kula Dakura koda ta takaleta da fad'a.... Wasu kujeru Umma Marie ta nunawasu Mairo tace su zauna kafin Hajiya Kaltume mai Masana'artan ta iso.... Mairo da Daddah suka nemi waje suka zauna suna bin shagon da mutanen ciki da kallo, lokaci guda Daddah ke karantar kowa.... Kowa a wajen ya masu sannu da zuwa idan ka d'auke Dakura dake faman d'age-d'agen hanci tanai wa mutane kallon banza.... K'wafa kurum Daddah tayi tana addu'an Allah sa wannan mai zubin muciyar ta takaleta..... *** Tana ida parking a k'ofar boutique d'in ta hangeta ta cikin glass tana zaune ta hard'e k'afafu tamkar wata sarauniya..... Nana H ta murmusa had'i da bud'e marfin faran Range Rover d'inta ta fito tana takunta cikin yanga da isa kaman yanda ta saba.... Tana isowa wajen ta tab'e baki tana bin boutique d'in da kallo don kantin wasu Labani's ne wanda sai ka cika kafin ka saya kaya a wajen, lokaci guda ta soma fad'in "Shidai matsiyaci bai iya samun waje ba sai yayi k'ak'a gida... Bacin haka nasan Uncle d'ina is a decent man babu abinda zai had'asa da karuwa har ya fita shopping da ita idan ba ita ta cusa kanta ba....." Ta k'arashe tana hard'e hannaye a kunkuminta... Sai sannan Azeeza ta d'ago had'i da sakin murmushi kana tace "Aww dama kece, kece Watchdog d'in tasa... Ya Allah wllhi bansan ke zai kira ba don ni ce min yayi zai kira watchdog d'insa don bazai barni na zaga city ni kad'ai ba.... Anyways since you here bari a firfito da kayan sai mu tafi koh...." Ta k'arashe murmushi saman fuskarta kafin tayi alama wa masu kantin da su fito da kayyayakinta... Nana H tamkar gunki haka ta tsaya cak tana duban Azeeza.... She couldn't believe it, wai ita ake kira watchdog....? kambala'in can, lallai Azeeza bata san da wacece take ba... Amma kam tabbas tayi na kud'inta watan cin uwarta ya kama, zata gane shayi ruwa ne, zata san ta tab'o Nana Hafsatou, zata san cewa no one messes with Nana Hetch.... Lokaci guda Nana H ta sakarwa Azeeza murmushi kana tace "Mu k'arasa banson holdup ya tare mu.." Kallo Azeeza ta bita dashi had'ida yin k'wafa, murya a hankali ta furta "Da Azeeza kike zancen muje zuwa, da yanda duk kika zo min ina dai-dai dake.... Mamaki ba gama cika Nana H ba saida taga tulin kud'in da Siraj ya kashewa Azeeza.... Lallai wannan shegiyar ta tsafe Uncle amma dole tayi maganinta don ita batada boka batada Malam amma duk abinda ta saka a gaba toh fa sai tayi nasara... Lokaci guda Nana H ta sake da Azeeza sai jefo mata fira take jifa-jifa, da sakin fuska tamkar ba Nana H ba, abun har mamaki ya baiwa Azeeza, saidai sam Azeeza bata yarda ta saki jiki da ita ba... "Azeeza ya kamata mu zama k'awaye mu daina fad'a tinda naga da gaske Uncle love d'ina ya makance akanki...." Ta fad'i fuska d'aukeda mayaudarin murmushi, idanunta naga bisa kwalta... Murmusawa Azeeza tayi had'ida maida komai ba komai ba kana tace "Ni dama ban k'ullaceki ba, kece dai baki fahimci wacece Azeeza ba, ni mutum ce mai sauk'in kai amma kuma maras d'aukan rainin hankali.." Nana H ta kuma murmusawa sanda traffic light ya nuna masu koren wuta alamun an basu hannu kana taci gaba da fad'in "Ina muka nufa ne kam ban tambaya ba..." "Citec muka nufa...." Azeeza ta bata amsa kai tsaye... Lokaci guda Nana H ta d'auki hanyar unguwar tana mai ci gaba da jan Azeeza da fira.... Har gida Nana H ta ajiye Azeeza bayan sunyi exchanging phone number.... Nana H bata bar unguwar ba har saida taga gidan da Azeeza ta shige... Tayi murmushi tana dubanta kafin ta d'au wayarta ta shiga dialing layin Bash.... "Hello Bash wani aiki nake so ka min, mu had'u anjima banson b'ata lokaci...." Daga haka hanging wayar tayi tana mai murmusawa ita kad'ai, lokaci guda taja motarta ta bar unguwar... Nana H na tafiya Azeeza ta lallab'a ta fito daga gidan data shiga sauri-sauri ta fice daga unguwar ta nemi cab ta shige...... *** "Hello Nazir ina jinka...." Lamid'o ya fad'i yana kuma k'asa-k'asa da murya... Nazir yaci gaba da fad'in "Ban jima da turo masa hotunan Mairo ba, kayi iyaka bincikenka da zakayi a d'akinsa na tabbata zaka samu..... Tabbas sunanta Mairo amma bansan dalilin da yasa wasu lokutan yake kiranta Nana Khadijah ba.... Na baka duk wasu information da ya kamata na baka, kayi a hankali kar Bulama yasan wannan zancen don wllhi kasheni zaiyi.... Yana son Mairo fiyeda komai na rayuwarsa...." Lamid'o ya kuma shafa goshinsa kana yace "Kar ka damu bazai tab'a sanin komai ba... Na gode Nazir sai mun sake magana, sannan dan Allah ka sake komawa tashan mass ka ci gaba da binciken garin da su Mairo suka tafi, akwai reward mai girma da na tanadar maka..." Daga haka sallama sukayi Lamid'o ya kuma komawa cikin d'akin da sauri... Ganin babu mahaifinsa a d'akin ya sanyasa shigewa yana ci gaba da binciken sunan da Nazir ya fad'a masa... NANA KHADIJA! sunan da yayita maimaitawa kenan yana tunanin yanda ya tab'a sanin mai sunan.... Wasu takardu ya zak'ule masu k'unshe da rubutu wanda ba sai ance maka masu mhaimmaci bane.... Lamid'o zuru yayi ma takardun yana juyasu sabida gaba d'aya a sile suke.... B'arka takardan da zaiyi yayi dai-dai da shigowar mahaifinsa, wani irin bugu k'irjinsa yayi lokaci guda ya saki takardun..... Nan suka watse k'asa.... K'irjin Lamid'o ya buga sanda yabi hotunan da suka watse k'asa da kallo... Shakka babu ta jikin hoton Fuskar Nana H da kuma Nana A ce da ita, idanma baka lura da kyau ba kai tsaye Nana H zaka ce sabida sunfi tsantsan kamanni harta murmushinsu iri d'aya ne, saidai kurum Nana H ta nunama wannan gogewar fata sabida hutu da kuma tsananin wayewa.... K'afafuwan Lamid'o suka soma karkarwa sanda ya durk'usa yana shafa hotunan, tabbas sai yanzu cikaton su Nana H ta fad'o masa, sunanta Nana Khadijah wacce suke kira da Nana K, kenan bata mutu, kenan tayi surviving accident d'in.... Innalillahi wa inna'ilaihirraji'un.... Kalman dake yawo kenan cikin kwanyarsa... Mik'ewa tsaye da zaiyi yaji sauk'ar lafiyayyar mari a fuskar sa..... Dafe da k'uncinsa ya d'ago yana duban mahaifinsa.... "Daddy.... Daddy who are you.... Tell me who you really are...!!!" maganganun da yaji bakinsa na furtawa kenan, sam baiji zafin marin ba ma..... "Kayi kuskure Lamid'o da kayi tunanin wai zaka bincikeni ba tareda sanin ko ni waye ba.... Tabbas kaci nasaran gano wacece Mairo d'aya daga cikin 'yan uku masu fuska iri guda, amma ka sani gano Mairo bazai maka amfanin komai ba saidai ma jaza ma rayuwarka sabuwar rayuwar k'unci da ka kuma yi wanda bakayishi a baya ba..... Da sannu zaka san wanene Bulama...." Ya k'arashe kafurar murmushi saman fuskar sa... Lamid'o na hawaye ya durk'usa saman gwiwoyinsa yana mai ci gaba da fad'in "Dan Allah Bulama ka sanar dani ko wanene kai wllhi jikina ya soma bani bakai ka haifeni ba, wllhi baka da d'igon imani da zaka raba yarinya da real family d'inta tsawon shekaru ashirin.... Dan Allah waye kai....?" Ya k'arashe hannayensa suna tsananin b'ari alamun rok'o... Dariya Bulama ya kece dashi kafin ya buga k'ofar d'akin da sanadarsa, kan kace mai wasu k'arti majiya k'arfi sun shigo lokaci guda suka kame Lamid'o suka fice dashi... Kokawa ya shigayi dasu amma ina sarkin yawa yafi sarkin k'arfi inji hausawa, lokaci guda d'aya k'akk'arfan ya buga masa gwiwar hannunsa a k'asan wuyarsa.... Wani irin k'ara Lamid'o ya saki daga nan bai kuma sanin yanda kansa yake ba.... *** Azeeza na zaune itada Yayanta Junaid tana kora masa bayanin yanda sukayi da Siraj da kuma d'iyarsa Nana H wayar Junaid tayi k'ara ganin mai kiran ya sanyasa sakin murmushi kafin ya d'aga wayar "Detective, kana k'ofar gidan... Shigo kawai babu matsala.." Azeeza ta kallesa da mamaki kana tace "Yaya waye kuma Detective..?" "Tashi ki shiga d'aki kuma kar ki fito sai ya tafi...." amsar da Junaid ya bata kenan... A hankali ta mik'e ba tareda ta kuma cewa komai ba ta shige d'aki don tasan halin Yayan nata.... Tun daga bakin k'ofa Detective Sabi'u ke kallon Junaid idanunsa sun kad'a sunyi rau-rau.... Lokaci guda yake takowa a hankali har ya ida shigowa cikin parlorn.... Bakin sabi'u na rawa yake furta "Junaid.... Haka suka maidaka? Junaid da gaske kaine saman wheelchair...?" Lokaci guda idanun Junaid sukayi rau-rau, zazzafan murmushi saman fuskar Junaid ya k'arasa ya hugging k'afafun Sabi'u yana fad'in "Haka suka maidani Sab.... But I'm here... I'm here now with my vengeance...." Sabi'u ya durk'usa suna fuskantar juna shida Junaid idanunsa sunyi jazur sanda yaci gaba da fad'in "Kar ka ragar wa ko d'aya daga cikinsu brother.... Kana tareda goyon bayana a koda yaushe...." Junaid ya murmusa kana yace " Na gode Sab, thank you for always keeping me updated... Na gode da ka shiga rayuwar Ahidjo a dalilina...." *SameenaAleeyou...📚**FUSKA UKU*🏮 *28* *©Sameena Aleeyou...✍🏽* Durk'usawa Sabi'u yayi hannayensa saman cinyoyin Junaid yake fad'in "You don't have to thank me for anything bro, kar ka mance irin abotan dake tsakaninmu kafin FUSKA UKU su bayyana cikin rayuwanka, har kullum zaka kasance d'an uwa a gareni Junaid.... So duk abinda nayi maka kaina nayiwa ka daina godiya please...." Ya k'arashe murmushi saman fuskar sa.... Junaid ya kuma murmusawa kafin suka hugging juna shida Sabi'u nan kuma suka soma firan yaushe rabo.... *** *Misau* Kallo ya kunna masu a laptop d'insa movie d'in Avengas infinity world, lokaci guda yake mata bayani tinda yasan ba fahimtar yaren take ba.... Ga sanyi da ya kad'a sosai a garin... Ahidjo na hankalce da yanda ta tak'ure waje guda, murmushi kwance saman kyakkyawar fuskarsa yake dubanta ga tsoron movie d'in da ya cikata sabida wasu irin hallittu dake ciki.... A hankali ya matso jikinta ba tareda yace da ita komai ba, lokaci guda yasa hannayensa ya kewayeta dasu had'i da shigar da ita cikin k'irjinsa.... Wani irin ajiyan zuciya ya saki shi kad'ai had'i da lumshe idanu, shi kad'ai yasan abinda yakeji gameda Deejoh.... Deejoh kam inaa bata ma san wainar da ake tuyawa ba an saki baki da hanci ana kallon movie.... Bata ankare da abinda mijin nata keyi ba saida taji wasu bak'in al'amra a tattareda ita, k'irjin Deejoh yayi wani irin bugawa hakan yayi dai-dai da wani abin tsoro da aka nuna a film d'in... K'ara ta saki had'i da k'ank'ame Ahidjo ga jikinta dake wani irin kyarma.... Shiko dad'a matseta yayi jikinsa yana fad'in "It's OK I got you.... Tsoro kike ji, na canza maki movie d'in....?" Yayi maganar cikin wata irin sakaltacciyar murya.... Girgiza masa kai Deejoh ta shiga yi k'irjinta naci gaba da bugu tama rasa yanda zatayi ta hanasa abinda yakeyi, tsoro da firgici sosai suka cikata hakan bai tab'a faruwa da ita ba.... Lokaci guda taji kuka na zuwa bakinta don tasan shine kawai abinda zata iya.... Cikin salo da dabara ya daina sabbin wasannin dake wanzuwa a tsakaninsun, A hankali ya eungumeta sosai cikin jikinsa yana lallashinta wanda tunda yake bai tab'a yin irin hakan ba, kukan da take masa sai ya kuma janyo hankalinsa sosai a gareta, bai tab'a sanin kukan mace nasa kaji wani abu gameda mace ba sai akan Deejoh, gaba d'aya sai ya wani saki jiki yana lallashinta yana sanar da ita matsayinsa a wajenta cikin dabara da salo wanda a baya idan akace zaiyi toh zai musa.... Gaba d'aya D'ansandan ya koma tamkar farar hula... Luf ta kwanta cikin jikinsa tana maida ajiyan zuciya, lokaci guda ya yaye d'ankwalin kanta kyakkyawan sumarta wanda bai faye tsawo sosai ba ya bayyana.... Murya can k'asan mak'oshi yaci gaba da fad'in "Deee I'm your husband, you're my wife... Ko a islamiyar taku ba'a sanar daku matsayin miji ba...?" Saurin girgiza masa kai tayi kana tace "Nidai kawai don ina son binka Habuja ne shiyasa idan kace na zauna kusa da kai nake zama, amma idan su Innah suka lek'o suka ganmu haka ai ce mana zasuyi mu 'yan iska ne, nidai kawai ka daina min irin wannan wasan idan kana so nasa na matsawa Baffah da batun tafiyarmu don ni wllhi ba 'yar iska bace, ko su Lado ma Allah bai basu nasara akaina ba..." Gashi dai maganganun nata abin dariya ne amma kalamanta na k'arshe sunyi mugun d'aga masa hankali... Wani irin zabura yayi ya mik'e yana mata wani irin duba wanda ita kanta saida taji tsoronsa kana yace "Waye Lado, meye had'inki dashi....?" Idanuwarsa a waje ya mata tambayar ga wasu jijiyoyi da suka taso lokaci guda daga goshinsa.... Idanun Deejoh sukayi rau-rau ganin yanayin Ahidjo, tsoro sosai ya wanzu a fuskarta, cikin sauri ta shiga girgiza kai tana dubansa hawaye na zubowa daga idanunta.... Cikin tsawan gaske yace "Ba kuka nace ki min ba, ki sanar dani waye Lado or whatever...!!!" Deejoh ta kuma zabura kukanta ya k'aru lokaci guda ta soma fad'in "Wllhi wllhi D'angayu ni ba 'yar iska bace, ...." Take Deejoh ta sanar dashi komai gamedasu Lado, har tareta da suka shayi a hanyar makarantar allo.... Duk sanyin dake kad'awa a garin saida Ahidjo yaji wani gumi na tsartsafo masa.... Ji yake da zaiga su Lado yanzu haka a gabansa babu abinda zai hanasa harbesu har lahira.... Lokaci guda tausayin Deejoh ya kuma rufesa.... He couldn't believe she went through all this.... Ganin kukan nata na k'aruwa tana kuma fad'in ita ba 'yar iska bace ya sanya Ahidjo saurin rungumota ya manneta cikin jikinsa suna jin bugun k'irjin juna, a hankali yake furta "Ki daina kuka Dee, it hurts.... I do believe you kinji koh, na yarda ke ba 'yar iska bace, na sani... Ki daina kuka kinji...." Ya k'arashe yana mai k'urama waje guda idanu, shi kad'ai yake imagining kalan azaban da zai baiwa su Lado, fuskokinsu kawai yake kamantawa a idanun zucinsa dukda ba sanin su yayi ba... Deejoh kuwa jinjina masa kai kurum tayi had'ida yin lamo cikin k'irjinsa.... Ta jima a hakan har bacci ya soma d'aukarta.... *** Kishingid'e yake a parlorn nasa TV da AC na faman aiki, kasancewar daga aiki ya dawo inners ne kawai jikinsa sabida zafi da akeyi a garin Abuja.. Fuskar Azeeza yake hangowa shi kad'ai sai murmushi yake, hannunsa rik'eda k'aramar bracelet d'inta da shakka babu yasan a hannunta ya zame, domin cikin motarsa ya tsinta.... Lokaci guda yake tuna k'arfin hali irin na Azeeza.... Murmusawa ya kumayi, a hankali ya furta "She's crazy...." Daga bakin k'ofar ta tsaya tana dubansa, soyayyarsa na ratsa b'argo da tsokarta, kallonsa takeyi yanda yake murmushi yana juya bracelet d'in hannunsa, tausayin kanta ya kamata, wai duk tsarewa da take da hana rab'an Uncle Siraj da take bazata tab'a mallakansa ba... Meyasa meyasa Uncle bai fito cousin d'inta ba ya fito k'anin mahaifinta, shin wannan wane irin musiba ce.... Lokaci guda tasa hannu ta goge hawayen da ya gangaro mata, zuciyarta taci gaba da raya mata har abada bazata tab'a barin wata mace ta rab'i Uncle ba koda ita bazata tab'a mallakansa ba amma kam tabbas zata mutu da k'aunarsa cikin ranta.... K'ok'arin saita kanta tayi kafin ta d'anyi knocking k'ofar glass d'in... Saurin mik'ewa yayi daga kishingid'en da yake kafin ya mik'a hannu ya janyo jallabiyarsa ya zura.... Mik'ewa yayi ya isa k'ofar had'i da bud'e mata murmushi saman fuskarsa.... Ganin yanayin fuskar nata babu walwala tamkar ma kuka tayi ya sanya jikinsa yin sanyi.... Aiko kaman jira take yana bud'e k'ofar ta fad'a k'irjinsa tana kuka.... Jikin Siraj ya kuma yin sanyin, k'ok'arin janyeta yake daga jikinsa amma tak'i sakinsa, saima dad'a k'ank'amesa da tayi..... Hankali tashe Siraj ke tambayarta meke faruwa.... Juyin duniyar nan Siraj yayi Nana H ta sanar dashi meke faruwa ta kasa sai faman kuka take.... Da k'yar ya samu ya masu mazauni saman kujera yana mai ci gaba da fad'in "Nana H sweetheart wai meke faruwa, waye babu lafia cikin gidan, ko ciwon Ammah ne ya tashi....?" A tare ya jero mata tambayoyin da shike dawowarsa kenan baiko lek'a sashen Ammahn ba.... Da k'yar Nana H ta tsagaita da kukan nata kafin ta soma fad'in "Uncle do you really love me...?" Kallon mamaki Siraj ke binta dashi kana ya jinjina kai a hankali had'i da furta "Of course I do love you.... So much...." Nana H ta kuma goge hawayenta kana taci gaba da fad'in "Uncle zaka iya auren macen da zata wulak'antani taci mutuncina ta zageni...?" Cikin sauri ya shiga girgiza kai alamun a'a kana yace "Bazan bar wata mace da sunan matata ba taci zarafin 'yan uwana and especially you my sweetheart...." Ya k'arashe yana rik'o hannayenta K'aunar Siraj ya kuma ratsa cikin zuciyarta, duk duniya babu wanda ke treating d'inta da kulawa kaman yanda Siraj keyi.... "Uncle budurwarka sakatariyarka tacimin mutunci yau cin mutunci da ba'a tab'a min irinsa ba, ta kirani da sunaye marassa kyau.... She even called me your watchdog....." Ta k'arashe murya na rawa... Ga tsananin mamakinta dariya taga Siraj nayi, ta shiga tambayar kanta cikin zuciyarta kodai baiji abinda tace bane.... Muryarsa ya katseta cikin d'an sautin dariya yake fad'in "I thought wani abin ne ya faru.... Ki kwantar da hankalinki sweetheart, idan dai Azeeza ce haka take, ni kaina na soma sabo da halinta, and waye yace maki Azeeza budurwata ce....?" Ita haushi ma ya bata tama rasa mai zatace masa, da a baya ne da yabi bayanta kuma da ya rabu da budurwar rabuwa ta har abada, toh mai yake nufi... Anya wannan tsinanniyar yarinyar haka nan tabar Uncle....? K'irjinta ya shiga mata zogi da rad'ad'i.... "Naga tana shige maka da yawa ne...." Ta basa amsa kai tsaye baki a ture.... Murmusawa Siraj yayi don har cikin ransa dad'i yaji da akace Azeeza budurwarsa ce kana ya girgiza kai yace "No she's not my girlfriend, she's just.... My sectary kin fahimta....." A hankali ta jinjina masa kai had'i da sakin murmushi.... Mik'ewa yayi had'i da d'aukan remote d'in AC ya kashe ya d'au na TV ma ya kashe kana yace "Muje ban gaida Ammah ba...." Cikin sauri ta mik'e had'i da sakalo hannunsa ta shiga zuba masa shagwab'a... Ammah da Ayiya sun sakata tsakiya suna bata baki gameda abinda Lamid'o ya mata su Siraj sukayi sallama suka shigo..... Sosai Nana A ke kuka tana fad'in "Ammah Uncle yayi warning d'ina banji maganarsa ba, wllhi ban zaci haka halin Uncle Lamid'o yake ba da banyi gangancin soma soyayyarsa ba....." Ta k'arashe cikin muryan kuka... Ayiya ce ta rungumota ita d'inma idanunta yayi rau-rau take fad'in "Kiyi hak'uri 'yar Albarka ni kaina ban tab'a tsammanin haka daga Sarki ba, amma na tabbata Allah yana sane dake da sannu zai zab'a maki abinda yafi zama alkhairi....." Ammah ta cab'i zancen da fad'in "Ni banma san mai ya kaisu gidan nasa ba...." "Wai aike mijin Nana Hafsatu yayo mata ta hannun Lamid'on toh dai tsautsayin ganin faruwar al'amarin ya kaisu.... Ni nasan watsettsen yaro ne yaushe zan ma d'iyata sha'awarsa, napses kawai (Nonsense)..." Ayiya ta k'arashe tana hure-huren hanci.... Kasancewar basuji sallamar tasu ba yasa basu amsa ba da shikema Siraj ne kawai yayi sallaman.... Juyowa yayi yana duban Nana H fuskarsa fal alamun tambaya.... Saurin janyo hannunsa tayi suka shige study dake gefen parlorn.... "Ina saurarenki, meke faruwa, meye ya faru....?" Ya k'arashe babu alamun wasa a fuskarsa... Bata b'oye masa komai ba duk abinda ya faru ta sanar dashi, harma da k'arin cewa ido da ido suka kama Lamid'o.... Zuciyar Siraj ta shiga bugawa, shine Lamid'o zai yaudara don jiya jiya sukayi magana da Lamid'on har ya basa goyon bayansa saidai baima sanar da Nana A d'inba don baima zauna ba tun jiyan..... Saida yayi masa kashedi kan kar ya yaudari Nana A don bazai tab'a yafe masa ba sai gashi tun ba'aje ko ina ba ya b'ata komai..... Lokaci guda ya soma huci shi kad'ansa, yana son nieces d'insa sosai baison wani abinda zai b'ata masu don su d'in amanace a hannunsa.... Cikin sauri ya fice daga gidan yana dialing layin Lamid'o.... Kallo Nana H ta bisa dashi had'i da sakin murmushi kafin ta nufi parlor yanda su Ammah ke zaune.... *SameenaAleeyou📚**FUSKA UKU*🏮 *29* *©Sameena Aleeyou...✍🏽* Tunda ya fice yake dialing layin Lamid'o amma shiru baya shiga, har gidansa saida Siraj yaje bai samesa ba, hakan ya kuma tabbatarwa Siraj Lamid'o ya aikata laifin tinda gashi har kashe wayarsa yayi... Ransa ya kuma b'aci don saida yayi kashediwa Lamid'o akan Nana A yace yaji ya gani sai gashi kan aje ko ina ya nuna kansa, wani b'angare na zuciyarsa ya masa sanyi don gwara da halin Lamid'o ya bayyana kafin ya basa auren d'iyarsa, dama a cikin su ukun halin Lamid'o ya banbanta da nasu.... Gida ya koma kai tsaye yanda ya tadda Ammah da Nana H har lokacin suna parlorn yayinda Ayiya tayi rakiyawa Nana A d'aki don gaba d'aya ba jin dad'in jikinta take ba... Da sallama ya shigo parlorn, Ammah ce kawai ta sami zarafin amsa masa Nana H kam kallo ta bisa dashi kaman ta had'iyesa.... Cikin sauri ta mik'e tamkar wacce aka zabura ta isa garesa tana faman rik'o hannunsa take fad'in "Uncle ince dai bai maka komai ba don ni banso kaje ka samesa ba.... Kasan yanzu sai ya k'aryata ko yace bashi bane...." Ta k'arashe idanunta tar kan Siraj ko kyaftasu batayi.... Zama yayi daga can gefe had'i da shafe goshinsa yana gaida Ammah... Lokaci guda ya dubi Nana H kana yace "Sweetheart bamu waje muyi magana da Ammah...." Kallonsa tayi don tafi so ayi zancen a gabanta kana ta d'an turo baki kaman bazata tashin ba ta kuma d'aukan remote control na TV tana fad'in "Haba Uncle it's time for my reality show.... Kuma fa zan kalla ne dama...." Kafeta da idanu kurum Siraj yayi ba tareda yace komai ba don gaba d'aya Lamid'o ya gama b'ata masa rai.... Rashin walwala da annuri da ta gani a fuskar tasa ya sanyata mik'ewa baki a ture tana fad'in "Fine, zan baku waje tinda an soma b'oye min abu a gidan nan...." Daga Siraj har Ammah baki sake suke binta da kallo.... Tsananin soyayyar da sukewa Nana H ya hanasu ganin rashin kunyar nata saima watsar da zancen nata da sukayi suka soma tattauna abinda ya zaunar da Siraj kan batun Nana A da Lamid'o, Siraj ya sanarwa Ammah komai, bai sami Lamid'o ba kuma wayarsa bata shiga, hakan na nuna shid'in mai laifi ne.... Ammah ta kad'a kai zuciyarta na mata zafi take fad'in "Yayi dai-dai, kuma wllhi wllhi Sirajo kaji na rantse ko bayan raina ne ban yarda ka baiwa wannan good for nothing friend d'in naka auren jikata ba.... Kai ko k'ofar gidana ban yarda na kuma ganinsa ba, watsettse kawai gantalalle... Ni bamu ma tab'a sanin iyayensa ba, a ina ne ma kuka soma had'uwa dashi, gwara wancan d'ansandan mijin Hafsat yakan tafi yaga iyayen nasa kuma a Nigeria suke amma shi wannan babu kowa nasa da muka tab'a sani ko gani...." Siraj ya kuma tattare naman goshinsa had'i da fuzar da iska kana yace "Wllhi Ammah a sch muka had'u a United States, kuma ya shaida min iyayensa suna can States da zama Shi kuma yana son zaman Nigeria shiyasa ma nayi employing d'insa a Laushi Group..... amma ta faru ta k'are, ni zan d'auki matakin yaudarar daughter ta da yayi...." Shiru ya d'an ratsa tsakani, Siraj ya d'an kuma yin gajeren saki kana yace "Ammah wllhi I feel responsible for everything, I feel responsible for what Asma'u is going through, nayi iyaka k'ok'arina wajen ganin na tsareta daga yaudarar samarukan zamani sabida yanayin lalurar da take fama dashi, sai gashi abokina amini na ya zamto mutum na farko da zai yaidareta...." Ammah dai girgiza kai kurum tayi kana tace "Dukanmu Lamid'o ya bamu mamaki kuma mun godewa Allah da bai kaisa ga auren Asma'u ba.... Da sannu Allah zai cire mata soyayyarsa cikin zuciyarta...." Bata kai aya ba Nana H ta fito daga yanda ta b'oye tana sauraren tattaunawar tasu, tamkar wacce aka tambayeta ta soma fad'in "Uncle ka daina ganin laifinka, babu laifinka ko kadan a nan, dukkanmu saida mukaja kunnen Nana A but she wasn't listening.... And besides Nana A fah ta samu wani saurayi a foundation d'in nasu... Kaman idan ban mance ba sunansa Ju... Waye. ... Ehen Junaid, yeah Junaid.... Kawai dai shirmenta take kan Lamid'o amma na hango tsantsan soyayyar wannan cripple d'in a idanunta.... Uncle you better ask her about that cripple kafin kuma wani fitinan ya b'ullo kai don wllhi I hate seeing you cikin tashin hankali Uncle, and idan wani abu ya sameka I'll never forgive Nana A..." Ta k'arashe tana bud'e hannayenta baki a tab'e baki.... A tare Ammah da Siraj suke duban Nana H ba tareda furta koda kalma ba, sunan da ta ambata shiketa yawo a kwanyar Siraj... _Junaid_ kaman ya tab'a sanin mai irin sunan can wasu shekarun baya.... Ganin zai auka wani duniyar tunani yasa sa watsar da tunanin tinda yasan shid'in business man ne mai huld'a da jama'a da dama ta yuwu wani abokin kasuwancinsa ne mai irin sunan a can baya..... *** *Misau* Washe gari tare suka dawo daga sallan asuba shida Baffah, da alama yanzu Baffah ya soma sakewa dashi dukda ba wani sosai ba, yakan sake masa fuska ya kuma amsa gaisuwarsa, wani lokacin har fira suke d'anyi da Baffahn, hakan ba k'aramin faranta ran Innah yayi ba, taji dad'i Allah ya cika mata burinta wanda a kullum take mafarkin hakan ta kasance batada sauran buri da ya wuce taga d'iyoyin Ahidjonta suna yawo tsakani.... Tana daga d'aki tana lazimi samar shimfidar sallah tana hango su Baffah da Ahidjo wanda tinda suka dawo daga sallah suka yada zango a tsakar gidan da alama magana suke.... "Baffah dama ina so naje na gaida mahaifan Khadijah ne....." Ya fad'i kansa a k'asa Fuska babu yabo babu fallasa yace "Hakan yayi, Allah ya taimaka..." Daga haka mik'a hannu yayi ya janyo 'yar Jakarsa ta fata wanda Alqur'anin sa ke ciki ya gyara zamansa had'i da bud'e jakan, dama duk bayan sallan asuba yakanyi karatu har gari yayi haske... Ahidjo na ganin haka ya mik'e ya isa bakin parlorn Baffah yanda Innah ke nata lazimin, har k'asa ya durk'usa suka gaisa kafin ya mik'e ya nufi nasa sashen... A dai-dai bakin farandar Innah ya hangeta tana alwala, ya jima sosai tsaye a wajen yana dubanta murmushi saman fuskar sa, sam Deejoh kam batama san da mutum a wajen ba har ta ida alwalanta.... Aiko tana mik'ewa sukayi ido hud'u.... Murmushi suka sakar ma juna kafin ta sadda kanta k'asa zata wuce sim-sim gudun kar Baffah ya hangota tinda zaune yake verandar sa... Muryar Ahidjo ta jiyo a hankali yana fad'in "Dee babu gaisuwa....?" D'an tsayawa tayi had'i da dubansa kafin itama tayi k'asa da murya tace "Ba'a gaisuwa ba'ayi sallah ba...." Ahidjo ya kuma murmusawa kana yace "Idan kinyi sallan kizo mu gaisa...." D'an zaro idanu waje tayi had'i da mak'e kafad'a kana tace "Nak'i wayon...." Wannan karan murmushi nasa mai bayyana hak'wara ne ya kuma yin k'asa da murya kana yace "Zan saka maki kallo fah...." Deejoh ta kuma mak'e kafad'a kana tace "Amma dai bazakamin irin wasan jiya ba...." Cikin sauri ya shiga jinjina kai kana yace "Na yarda... I promise..." Ya k'arashe yana kashe mata idanu guda... Saurin rufe fuskarta tayi alamun kunya kafin ta shige cikin sauri... Ahidjo ya bita da kallo murmushi saman fuskarsa kafin ya d'an girgiza kai ya shige sashensa *** Wane irin killataccen d'aki aka kulle Lamid'o ciki, abincima turo masa ake ta k'asa k'ofa, Bulama ya hana ko kad'an a bud'e Lamid'o, k'arti ya saka masu tsaronsa.... Breakfast aka turo masa ta k'asan k'ofa kafin mutumin ya cire hannunsa Lamid'o yayi saurin capke hannun, mutumin nan yayi yayi ya k'wace hannunsa Lamid'o yak'i saki.... "Kaga dan Allah taimako d'aya zaka min...." Ya fad'i yana d'aure hannun mutumin jikin k'ofar.... "Wani taimako zan maka....?" Mutumin ya tambaya yana mai ci gaba da k'ok'arin k'wace hannunsa... "Wayata zaka taimaka ka d'auko min na rok'eka..." Tab'e baki mutumin yayi kana yace "Lamid'o kana neman fitina, ta ina zan samo wayarka bayan Boss ya amshe tun jiya...." Lamid'o ya shafi kansa had'i da fuzar da iska kana yace "Ka taimaka min dan Allah koda SIM d'in ne ka kawo min numbers kawai zan d'auka akwai important calls da nakeso nayi dan Allah ba don ni ba, ka min wannan taimakon ko don alkhairi da kake samu daga mahaifina...." Kaman bazaice komai ba don har Lamid'o ya cire rai kana ya jiyo muryarsa yana fad'in "Amma kasan yin hakan na daidai da rasa aiki na ko.... Gaskiya bazan iya ba, kama daina b'ata bakinka kana tambayata... Sake min hannu na tafi..." Hankalin Lamid'o ya kuma tashi bai tunanin su kansu masu tsaronsa sunada makullin d'akin a wajensu, don Bulama da kansa ya gark'ame k'ofar k'arfen ya kuma tafi da makullin..... Kaga idan ka d'auko min SIM d'ina ka bani waya ni zan maka babban kyauta, zan raba dukiyata da na jima ina tarawa kashi biyu na baka kaso guda.... Dan Allah ka taimakeni nayi waya...." Barde yaji kud'i tuni ya soma hango kansa yayi kud'i kana yace "Shikenan kar ka damu ka bani nan zuwa azahar...." Sauk'e ajiyan zuciya Lamid'o yayi kana yace "Na gode sai na jika...." Daga haka kwance d'aurin hannun mutumin yayi yana mai addu'an Allah sa Bulama bai cafke Nazir ba..... *** Tamkar zautacciya ta mik'e daga saman gadon tana fad'in "Whatt!! Bash ban gane ba, what do you mean ba kowa a gidan, Citec house no 43 kace min babu kowa, da idanuna fah naga ta shige gidan...." Bash ya kuma busa sigarinsa kana yace "Gaskiya wrong address ta baki don wannan gida ma yafi wata shida babu masu zama cikinsa...." Huci kurum Nana H keyi zuciyar nai mata zafi, wato Azeeza tama raina mata hankali... Lallai yarinyar nan batasan da wanda take ba, lokaci guda wani tunani ya fad'o mata.... Murmusawa tayi kana tace "Ka gane Bash ka bar wajen kafin securities suyi suspecting wani abu.... Zamuyi magana kawai..." Bata jira cewan Bash ba ta katse wayar tana fashewa da wata irin dariya don tasan ta gama da Azeeza a babin Uncle..... Time ta duba agogon ya nuna k'arfe 6:48am tsuka ta buga kafin tayi saurin fad'awa bathroom don yin wanka, rabonta da tashi farar safiya irinta yau ta mance idan ba tafiya tayi kwanan cikin jirgi ya kamata ba, dolema ta tashi yau taji ya Bash ya k'are da Azeeza a daren jiya sai gashi Bash bai tadda kowa gidan ba balle wata wai Azeeza.... *** K'arfe 8:30am Siraj ya fito cikin shirin tafiya office kai tsaye d'akin Nana A ya nufa domin duba yanda ta kwana dashike jiya gaba d'aya basu samu sunyi magana ba.... Ayiya na tayata shiryawa sukaji knocking d'in Siraj, Ayiya ce ta basa izinin shigowa yayinda Nana A taci gaba da shirinta,... Gaisawa Siraj da Ayiya sukayi kafin Ayiyar ta fice tana fad'in bari ta sanarwa Malam Sile ya fito da mota.. Murmushi saman fuskar Nana A ta isa ga Siraj tana mai gaishesa... Saurin rik'o hannunta yayi suka zauna saman chaise lounge murmushi saman fuskarsa "Morning sweetheart, how was your night...?" Da murmushinta ta amsa da "Lafia lou Uncle, baka tafi office ba....?" Siraj ya kuma murmusawa cikeda tausayin niece d'in nasa kana yace "Bazan tafi office banga halinda kika kwana ba Baby...." Cikeda jin dad'i tace "Kai Uncle babu komai fah, ya wuce a wajena, and insha Allah na ciresa daga raina har abada.... He's already in the past, na maka alk'awari Uncle...." Ta k'arashe murmushi saman fuskarta.... Murmusawa ya kumayi kana yace "Masha Allah, haka nake sonji, Allah ya maki albarka ya zab'a maki abinda yafi zama alkhairi....." Da murmushi saman fuskarta ta amsa da "Ameen Uncle..... Na gode...." Siraj ya kuma murmusawa cikeda tausayinsu su duka biyun, haka tasu jarabawar tazo masu rashin abokan zama gashi shekarunsu yakai su mallaki abokan zama tuntuni, ga gata ga dukiya Allah ya hore masu, tabbas d'an Adam bai cika goma ba dole kowa a samu lapses a rayuwarsa.... "Kin tabbata zaki iya zuwa office yau? " Ya tambaya yana dubanta Jinjina masa kai tayi kana tace "Zan iya Uncle, is better na fita d'in than na zauna a gida doing nothing, ...." Ya kuma jinjina kai yana fad'in "Gaskiya ne fitar zai keeping d'in busy... Muje muyi breakfast koh...." Ya k'arashe yana mai taimaka mata wajen mik'ewa tsaye.... A tare suka sauka nufo downstairs, har cikin ranta dad'i taji yanda Uncle Siraj ya kwantar mata da hankali, tabbas ko mahaifinsu iyakacin kulawar da zai basu kenan.... *** Kallon Nasaar ta kumayi tana juya zoben d'an yatsanta lokaci guda take wani irin mayaudarin murmushi kana ta kuma kwanto da fuskarta dab nasa tace "Attorney nasan ka ganeni tsaf.... Kayi tunani kan maganar da na fad'a maka sai na jika...." Ta k'arashe tana wasa da d'an yatsanta saman fuskarsa.... Ko motsi mai kyau Nassar ya kasa sai bin Nana H da kallo da yake babu ko k'yafta idanu, ko pen d'in hannunsa ya kasa ijiyewa, har lokacin bai daina jin motsin yatsunta saman fuskar sa ba..... *SameenaAleeyou📚**FUSKA UKU*🏮 *30* *©Sameena Aleeyou...✍🏽* Cikin dabara Barde ya saka SIM card d'in tsakiyar abinci da wayar salula kana ya turawa Lamid'o ta k'asar k'ofa lokacin da ya kawo masa lunch.... Lamid'o yana bud'e abincin ya kuwa tcinci sim card ciki da wayar salula k'irar Nokia 3310 tsakiyar shinkafa.... Hannayensa har suna rawa sanda ya zak'ulo sim card d'in ya soma had'a wayar..... Layin Nana A ya soma kira sanda ya had'a wayar domin da ita ya kwana ya tashi cikin zuciyarsa, soyayyarta a kullum ninkuwa yake a cikin zuciyarsa.... Saidai tunda ya soma kiranta bata d'aga ba, gashi dai wayar na ringing amma ba'a d'agawa.... Hankalin Lamid'o ya tashi sosai, yana tsananin buk'atar jin muryarta... Nana A kuwa zaune suke itada Junaid yana bata baki gameda abinda Lamid'o ya mata sanda wayar Lamid'on ya shigo mata, nunawa Junaid fuskar wayar tayi yana kallon mai kira.... Cikin sigan kwantar da hankali Junaid yace "Ki d'aga wayar kiji mai zaice maki...." Girgiza masa kai tayi kana tace "I don't want to hear any of his lies again.... Bazan d'aga ba, na goge shi a babin rayuwata,... He's already in the past..." Kautar da fuska Junaid yayi had'i da sakin murmushi mai cikeda ma'anoni kana ya maido da dubansa ga Nana A lokaci guda fuskarsa ta canza tayi jazir abinda su Lamid'o suka masa shida farin cikinsa Zeenat ya dawo masa, jijiyoyin goshinsa sukayi rud'u-rud'u sanda ya soma fad'in "Da ace zanga wannan Lamid'on da sai yanda k'arfina ya k'are.... Sabida ya hurting d'inki Asmah.... It hurts me seeing you suffering like this...." Kallonsa kurum Nana A take wasu sabbin k'walla na k'ok'arin ciko udanunta, ashe akwai mutanen da suka damu da damuwarta har irin haka bayan family d'inta, lokaci guda take jin al'amari mai girma gameda Junaid na ratsa ko wane k'ofa na zuciyarta, Junaid ya wuce aboki a gareta tabbas d'an uwa ne.... Murmushin k'arfin hali ta sakar masa kana tace "Kar ka damu Junaid, wllhi komai ya wuce a wajena, haka Ubangijina yaso ya jarabceni, shi bawa a koda yaushe rayuwarsa jarabawa ce walau jin dad'i yake ko ko akasin hakan, idan kayi tawakkali da kalan jarabawan da mahaliccinka ya d'auro maka toh sai ka samu dacewa da reward mai girma a gaba..." Ta k'arashe murmushi mai sanyi samar fuskarta.... Maganganun Nana A sun saka jikin Junaid yin sanyi for the first time da yaji zuciyarsa tana barazanar karaya da burin d'aukan fansa.... Ganin sanyayan kalaman Nana A na neman cin galaban akan dadd'en burinsa da ya rayu shekaru hud'u akansu yasa sa saurin tura wheelchair d'insa ba tareda ya kuma ce da ita komai ba ya fice daga office d'in nata... Tissue paper ta zaro daga cikin kwali had'i da goge fuskarta tana mai bin bayan Junaid da kallo, tausayinsu su duka biyu na ratsa zuciyarta don tasan su d'in sun had'u da babban jarabawa a rayuwarsu.... Shigowar Aunty Larai ne ya sanyata saita kanta don bata so a gane halin da take ciki.... *** Cikin sauri ya shiga neman layin Nazir hannayensa har rawa suke.... Bugu biyu kuwa Nazir ya d'aga kaman jira yake... "Ina ka shige tun jiya nake nemanka, ina tsammanin Bulama yana suspecting d'ina da bud'e maka sirrinsa don yanzu haka ce min yayi duk abinda nake na baro na taho Abuja, Lamid'o I hope ba fayyace masa komai kayi ba...." Cewar Nazir daga d'aya b'angaren Shafe kansa Lamid'o yayi kana yace "Ince bakazo Abuja ba...?" Nazir yace "Yaya za'ayi nazo bayan nasan babban laifin dana tafka masa dukda cewa kai d'ansa ne..." "Yauwa Alhamdulillah, Nazir you better get lost sabida nayi imani Bulama ya kama ka bazai rage maka rai ba... And please koda ka sami wani information gameda Mairo kada ka sanar dashi, sabida a yanzu nasan wacece Mairo, nasan nufin Bulama akanta, don Allah kada kayi yasan yanda suka tafi...." Nazir ya murmusa kana yace "Lamid'o kenan nasan abinda nake, yanzu haka ina airport ne, na yanki ticket already k'asar zan bari kafin ya cimma ni don I'm pretty sure his boys are after me.... And about Mairo or Khadijah na koma tashan motar ban bar wajen ba saida na sami wanda yasan garin da suka nufa a ranar, garin Damaturu ta jihar Yobe suka nufa a yanda na iske labarin, so probably suna can suna rayuwa.... Ina son Mairo da Daddah kaman 'yan uwana na jini, sannan na jima ina karesu daga sharrin Bulama ba tareda saninsu ba, tabbas nasan bak'in nufinsa akan Mairo kuma nasan idan yayi idanu hud'u da Daddah kasheta zaiyi shiyasa nake bibiyansu don na karesu daga sharrinsa... Dan Allah ka d'aura daga yanda na tsaya, kasan yanda zakayi ka kub'utar dasu daga sharrin Bulama.... Na barka lafia jirginmu zai tashi...." Daga haka katse kiran Nazir yayi yayinda Lamid'o yayi sakare da waya a hannu.... Shikam yama rasa sahun da zai jefa Bulama ciki.... Yanzu yaya za'ayi ya kare Mairo daga sharrin Bulama, bai kamata ya soma sanar da Siraj long lost niece d'insa is alive, sannan maiyasa ita wacce take rik'eda Nana K d'in bata nemi iyayenta ta maidata wajensu ba....? Kai wannan Al'amari akwai abin dubawa ciki, bai kamata ya soma sanar dasu Siraj kai tsaye ba dole su zargesa da wani mummunar abu tinda ba ce masu zaiyi mahaifinsa ne ya sace Nana K ba, dole Siraj yayi tunanin ya shigo jikinsa ne da mugun nufi wanda a yanzu sam babu hakan a zuciyarsa... Yanzu ya zaiyi waye zai samu ya kawo Nana K ga dankinta lami lafia kafin komai ya bayyana.... Lokaci guda tunanin Ahidjo ya fad'o masa... A hankali ya furta _"Heedj"_ kana yaci gaba da fad'in "Tabbas Heedj ne kawai zai min wannan babban alfarmar tinda Shi police officer ne sannan Nana K sister matarsa ce shima, yasan zaiyi iyaka k'ok'arinsa saidai zai sanar dashi this should be between them.... Da wannan tunani Lamid'o ya shiga dialing layin Ahidjo... Saidai duk kiran duniyar nan yayi wayar Ahidjo bai shiga.... A hankali ya fuzar da iska had'i da dafe kansa yana tunanin mafita... *** *Misau* Iya Gaje ce zaune tana faman tankad'en garin tuwo lokaci guda tana watsa bak'ar magana wa Malam Ard'o kan ya saida d'iyarsa Deejoh ya sallameta wa mayu 'yan shan jini.... Gashi tinda Deejoh ta auri bak'on bariki ko k'eyarta ba'a sake gani ba.... Duk wannan sababi da takewa Malam Ard'o k'ala bai ce mata ba, idan da sabo toh fah ya saba da halin Iya Gaje..... Kaman daga sama suka jiyo dadd'an sauti mai cikeda kamala da k'warjini ana sallama.... Malam Ard'o ya mik'e yana fad'in "Gaje barin amsa sallama...." Ai baikai aya ba ta katse sa da fad'in "Toh uban 'yan tsugudidi ni na aike ka ko me, daga jin wannan murya bak'in arziki ne, ni zan duba ko waye....." Ta k'arashe tana watsa masa bahagon duba kafin ta mik'a hannu saman katanga ta janyo wani mayafinta da yaji daud'a ta yafa a kafad'a ta nufi k'ofar tana 'yan wak'e wak'enta had'ida tambayan waye mai sallama.... Bud'e k'ofar da Gaje zatayi tayi idanu hud'u da Ahidjo wanda shakka babu taga bindiga a motarsa.... Ai a d'ari tayi wani irin juyi had'i da komawa cikin gida a guje tana rangad'awa Malam Ard'o kira tana fad'in "Malam ya biyo mu, wllhi ya biyomu ya karmu, nidai bazan tsaya ba na tabbata Deejoh ta sanar dashi komai...." Tana k'ok'arin cab'e garu take kururwan neman d'auki... Malam yayi kanta yana janyota daga saman garu.... Jin kururwar ya sanya Ahidjo kustowa cikin gidan shima... Kowa yasan rashin mutuncin Gaje shiyasama da take kururwan neman d'aukinta babu wanda yakai mata d'auki.. Da k'yar Malam ya samu ya sauk'o da Gaje daga saman garu, dukda haka bata daina b'oyewa bayan Malam tana rok'on Ahidjo kar ya harbeta ba sharrin Deejoh ne... Shikam yafi baiwa matar mai tab'in hankali, don bai tsamman wannan matar tanada sauran hankali ba.... Jiki har na rawa ta shige d'aki a guje had'i da kullo k'ofa.... Malam Ard'o girgiza kai kurum yayi kafin ya mik'awa Ahidjo hannu sukayi masabaha... Ga mamakin Malam Ard'o har k'asa matashin saurayin ya tsuguna yana gaidashi, ko ba'a ce masa ba zai iya shaida sirkinsa ne sabida ga kamannin Malam Sanda a tattaredashi... Cikin sauri Malam Ard'o shima ya shiga k'ok'arin durk'usawa yana amsa gaisuwar Ahidjo... Lokaci guda ya umarci Ahidjo da ya mik'e ya isa saman shimfid'a... Cikeda rusnawa Ahidjo ya k'arasa saman shimfid'ar ya zauna.... Nan suka soma sabon gaisuwa da Mahaifin Deejoh kana ya masa bayanin ko shi waye... Allah sarki, dad'i maras misaltuwa ne ya kama mahaifin Deejoh, shi kansa Ahidjon yaji dad'in yanda mahaifin Deejoh ya tarbesa, nan yake bayaniwa Malam Ard'o kan baisan dalilin da yasa matarsa take gudunsa ba tun ranar farko da suka soma had'uwa, nan dai Malam Ard'o yayita 'yan kame kamensa don shi kansa bai san mai zai ce ba.... Gaje kuwa tana daga k'ofa tana hangensu ta ramin k'ofa tana faman tab'e tab'en baki... Saida taga Ahidjo ya ciro kud'i cikin aljihunsa yana mik'awa mahaifin Deejoh ya sata sake baki tana duban damin kud'in... Babban abinda ya bata takaici shine yanda Malam Ard'o yak'i amsar kud'in yana cema Ahidjo "Wllhi D'ana ka bar kud'inka mun gode sosai...." Gaje kuwa daga yanda take lab'e take fad'in "Ard'o yau zamuyi daru muddin baka amshi kud'in nan ba...." Don ko fitowa ta kasa sabida wani irin tsoron Ahidjo da Allah ya d'aura mata... "Baba dan Allah ka karb'a idan ka d'aukeni D'a..." Ahidjo ya fad'i yana kuma damk'awa Malam Ard'o kud'in.... Da k'yar da sid'in goshi Malam Ard'o ya amshi kud'ad'en da Ahidjo ya basa.... Daga nan Ahidjo sallama ya masa kana ya fice daga gidan... Malam Ard'o ya bisa da kallo zuciyarsa na masa sanyi ko babu komai Deejoh d'an mutunci ta Aura ba kaman yanda mutanen gari suka d'auka ba..... Gaje kaman jira take yana ficewa ta k'araso ta wawashe kud'ad'en daga hannun Malam Ard'o tana faman washe baki... Malam Ard'o dai kallon mamaki ya bita dashi yana mamakin hali irin na Gaje.... Ahidjo na fitowa gidansu Deejoh wayar Lamid'o ya shigo masa, saida k'irjinsa yayi wani irin bugawa ba tareda sanin dalili ba, don harga Allah ya mancewa kowa cikinsu a 'yan kwanakin harta matarsa Nana H bai tunawa, duk abinda yake ciki Deejoh kawai yake tunawa.... "Hello Bro.... Kwana da yawa..." Ya fad'i yana rage girman idanunsa sabida hasken rana da ya fito.... Jin muryar Lamid'on cikin wani irin yanayi yasa Ahidjo nutsuwa sosai.. Daga d'aya b'angaren Lamid'o yaci gaba da fad'in "Heedj I really need your help..... Nasan babu wanda zai min sai kai...." Ahidjo yace "Ina jinka Lamid'o wai meke faruwa ne.... Just go straight please..." Lamid'o ya sauk'e ajiyan zuciya kana yace "Alright.... Heedj, kana jina....?" Gajeren tsaki Ahidjo yayi kana yace "Lamid'o wai menene dan Allah ka fad'a min...." "Heedj Nana K is alive.... She's alive...." Gaba d'aya Ahidjo yama rasa wacece Nana K, a hankali ya shiga nanata sunan *SameenaAleeyou📚**FUSKA UKU*🏮 *31* *©Sameena Aleeyou...✍🏽* "Nana Khadija 'yar uwar matarka data b'ace 20years back....." Lamid'o ya nanata cikin wata irin murya mai sanyin gaske.... Girgiza kai Ahidjo yayi kana yace "Lamid'o wace irin magana kake, lafiyarka kuwa, Nana K ta jima da rasuwa kowa yasan wannan da tayi surviving accident d'in da tuni an sani kuma da ta dawo wajen family d'inta, I'm pretty sure wata dai kawai ka gani mai kamadasu Nana H amma ba Nana K ba...." Girgiza kai Lamid'o yayi tamkar Ahidjo na ganinsa kana yace "Heedj ya kake magana haka, wllhi Nana K na gani da idanuna, dukda a hoto na ganta but wllhi tllhi na tabbata itace bazan zauna inai maka rantsuwa kan abinda banida tabbas akai ba...." Yayi maganar sounding serious... Sosai Ahidjo ya nutsu kana yace "Toh mai kayi, ka sanar da Siraj ne da familynsa ko kuwa....?" Kai Lamid'o ya kuma girgizawa kana yace "Banida wannan ikon Heedj da nayi..." "Kamar yaya....?" Ahidjo ya tambaya cikeda mamaki... Fuzar da iska Lamid'o yayi kana yace "Is a long story Heedj, babu time sannan bazai yuwu na sanar da kai a waya ba... Alfarma nake so ka min...." K'asar bishiya Ahidjo ya samu ya zauna kana yaci gaba da fad'in "Umhum ina saurarenka.... So kake na sanar da Siraj..?" Cikin sauri Lamid'o ya girgiza kai alamun a'a kana yace "Heedj ina cikin matsala yanzu haka mutumin da yayi kidnapping Nana K years back nima ya kamani ya tsareni da ya fahimci ina bincike akansa, ya fahimci nasan sirrinsa shiyasa ya kamani ya rufeni don kar na cimma burina na dawo da Nana K wajen real family d'inta...." Shafa kansa Ahidjo yayi kana yace "Now I get you, mutumin kake so a kama, zaka iya sanar dani location d'inka yanzu zamu tura mutanen ...." Saurin katsesa Lamid'o yayi da fad'in "No Heedj kai kafi kowa sanin case irin na kidnap haka ba'a saurin involving police, Heedj abinda yasa na kiraka so nake ka k'arasa abinda na fara kar ka damu dani I'll be fine I promise... Ahidjo Siraj is our brother koda ace baka auren niece d'insa Siraj d'an uwanmu ne na sani shekarun baya mun tab'a jefa rayukanmu cikin had'ari a sabida Siraj.... Nasan baka mance abinda ya faru 4years back ba.... Bana fatan irin wancan tragedy d'in ya kuma faruwa... But we need to do this Heedj, Nana K ta cancanci ta dawo cikin family d'inta, na tabbata zasuyi farin ciki maras misaltuwa,..." Fasali ya d'anja kana yaci gaba da fad'in "Idan na sanar da Siraj yanzu zai zargi wani abu shiyasa na soma sanar da kai and please kar ka sanar dashi har sai ka damk'a Nana K hannun family d'inta, Suna can garin Damaturu ta jihar Yobe..... Please Heedj nasan ka fahimceni a matsayinka na D'ansanda...." Sauk'e ajiyan zuciya Ahidjo yayi kana yace "Na fahimceka Lamid'o, insha Allah zan k'arasa aikin alkhairin daka soma, and da zaran na maido da Nana K gida insha Allah kaima zan fitar da kai and wancan mutumin will face justice...." A hankali Lamid'o ya saki murmushi kana yace "Alhamdulillah, na gode Heedj, Ubangiji ya baka nasara...." "Ka daina min godiya Lamid'o kar ka mance koda ace bana auren d'iyar Siraj hakki na ne kare Al'umma tinda nayi rantsuwa zan rik'e aikina bisa gaskiya da amana...." Jinjina kai Lamid'o yayi lokaci guda yaji hwaye na neman ciko idnunsa sabida cin amanan Ahidjo da sha yi a bayan idanunsa.... Wasu irin k'walla masu zafi suka zubo masa, lokaci guda yaji ya tsani kansa, bai tab'a jin nadama irinta yau ba.... Murya na rawa Lamid'o ke furta "Heedj... Please forgive me... Dan Allah ka yafe min brother...." Jikin Ahidjo yayi sanyi lokaci guda duk a tunaninsa sabida aikin da Lamid'o ya saka sa ne yake rok'onsa gafara tinda yasan dole akwai had'ari cikin aikin..... "Haba Lamid'o ka daina bani hak'ura and insha Allah kaima zaka fita daga wannan taskon just trust me bro....." Kasa furta komai Lamid'o yayi sabida wani irin kukan nadama da yaji na taso masa, tabbas Nana H ta cucesa, da ace bata persuading d'insa wajen suyita aikata masha'a ba da bai ci amanan abokinsa ba.... Kasa ci gaba da magana yayi lokaci guda ya kashe wayar had'i da durk'usawa saman gwiwoyinsa yana kuka sosai shar-shar da hawaye Wanda bai tab'a yin irinsa ba a rayuwarsa..... Yana durk'ushe wajen yana kuka yaji an banko k'ofa an shigo ana tafe hannaye..... "Bravo..! Bravo Smart boy....!!!" Muryar Alhaji Bulama ya daki dodon kunnuwansa.... A zabure Lamid'o ya mik'e yana goge hawayen fuskarsa lokaci guda yake hura hanci had'ida watsawa Bulama mugun kallo.... "You think you're smart right....?" Bulama yace yana mai murmusawa idanunsa kan Lamid'o, gurds d'insa majiya k'arfi sun saka sa a tsakiya.... A zuciye Lamid'o yayo kansa zai kai masa capka yake fad'in "I'm gonna kill you, you worthless....." Saidai kafin yakai aya K'artin nan sun kwantar dashi da duka.... D'aga masu hannu Bulama yayi alamun su k'yalesa kana ya k'arasa yana bubbuga wayar data tarwaste daga hannun Lamid'o a k'asa da sandarsa ta dogarawa.... Lokaci guda yake murmusawa yana fad'in "Lamid'o kenan.... Wato k'ok'arinka na matuk'ar birgeni.... Akwai ka da k'wazo da k'ok'ari, saidai kuma matsalan you such an idiot.... K'aton jiki gareka saidai kuma k'aramar kwanya gareka... Take a look of this....." Ya k'arashe yana k'ok'arin d'ago fuskar Lamid'o da sandar dake hannunsa, yayinda fuskar Lamid'on ke kife k'asa yana d'igan jini..... Wani d'an rami ya nuna masa jikin k'ofar d'akin wanda idan ba ka kula ba bazaka zaci camera bace 'yar k'arama mak'ale a wajen.... Bulama ya kuma murmusawa kana yace "You think I'm stupid, kana tunanin zan barka haka kurum ne bayan nasan kaida Nazir kunci amanata.... You're very much mistaken dear Son.... Na tsufa amma kwanyata bata tsufa ba, tafi ta matashi d'an shekaru talatin aiki.... Da sanina, ni da kaina na d'auki waya na baiwa Barde nace ya kawo maka don nasan dole Nazir ya sanar dakai wani abu.... Fine... Na sami information d'in da duk nake nema, and now kwanakin wancan traitor d'in k'irgaggu ne, tinda yaci amanata amfaninsa ya k'are.... Sannan ina welcoming sabon victim da ka jefosa cikin wannan mess d'in... Your good friend Ahidjo....." Girgiza kai Lamid'o yake yana wasu irin hawaye sanda ya isa har jikin k'afafun Bulama da rarrafe ya kamo k'afafun Bulama yana kuka sosai yake fad'in "Daddy please no.... Dan Allah Daddy na rok'eka kar ka kashe Nazir da Ahidjo..... Daddy please don't..... Dan Allah kada kayi komai ma Ahidjo.... He's innocent, wllhi ni na saka shi baisan komai ba, please Daddy ka kasheni kawai ka huta amma dan Allah banda Ahidjo.... Na jima ina zaluntarsa a baya idan ka kasheshi yanzu a dalilina bazan tab'a yafewa kaina ba.... Daddy Dan Allah no..... I beg of you please.....!" Ya k'arashe cikin tsananin kuka yana mai k'ank'ame k'afafun Bulama... Dariyar rainin hankali Bulama ya kece dashi kana ya sauk'ewa Lamid'o sandar hannunsa a gadon bayansa... Lokaci guda Lamid'o ya saki k'aran azaba yayinda Bulama yasa kai ya fice daga d'akin yana fad'in "Fool...!" Har Bulama ya fice Lamid'o bai daina kuka yana rok'onsa kada ya cutar da Ahidjo ba.... *** Daren ranar Deejoh rungume cikin jikinsa take yana mai ci gaba da lallashinta yana sanar da ita dole ya koma Abuja koda su Baffah basu amince ya tafi da ita ba sabida nemansa da ake cikin gaggawa a wajen aiki.... Deejoh ta kuma goge k'wallan da suka zubo mata cikin murya mai rawa sosai tace "Tafiya zakayi ka barni.... Dan Allah kada ka tafi ka barni kaji...." Ta k'arashe sabbin hawaye suna zubo mata.... Gaba d'aya Ahidjo ji yayi jikinsa ya masa sanyi sosai, bai tab'a tsammanin shak'uwarsu da Deejoh yakai haka ba.... Kasa furta mata komai yayi sai bin kyalkyawar fuskarta da hawaye ya wanke yake da kallo.... Zuciyarsa ta masa rauni sosai, ji yake kaman bazai iya tafiya ya bar Deejoh ba.... Shin ta yaya zai sanar da ita wani tafiya zaiyi mai tarin had'ari.... Wani b'angare na zuciyarsa can k'asa ji yake kaman idan ya tafi bazai dawo ba.... Lokaci guda ya janyota cikin jikinsa ya matseta sosai kaman mai tsoron kada a rabasu.... Yana jin kukanta har cikin k'irjinsa,.... "Dee I'll come back for you kinji.... Idan na dawo wannan karan zan d'aukeki mu tafi koda su Baffah bazasu amince ba.... You're my wife Dee, Shari'a ta yarjemin koda su Baffah basu yarjemin ba kinji koh....." Kasa cewa komai tayi sai hawayenta da suka k'aru, girgiza masa kai kurum take tana fad'in kada ya tafi ya barta cikin kuka.... Rungumota ya kumayi cikin jikinsa yana girgiza mata kai alamun ta daina kuka, lokaci guda yasa harahensa ya shiga lashe hawayen dake bisa fuskarta idanunsa a lumshe shima..... Daga nan al'amra suka soma canzawa tsakaninsu..... A wannan daren Ahidjo ya mance amaryar tasa k'aramar yarinya ce mai k'aramin shekaru.... A wannan dare Ahidjo ya maida Deejonsa cikakkiyar mace cikin lumana da tsananin nuna shauk'i dukda cewa su duka biyun sun wahala sosai.... Nitsuwa ya samu wanda ya jima bai sameta ba.... Tana kwance cikin jikinsa tana kukan da bai fita... Gani take ta tapka babban sab'on da Allah bazai tab'a yafe mata ba... Ita harga Allah batasan wannan itace rayuwar aure ba.... Shi kansa baiso hakan ta kasance ba amma babu yanda ya iya don ya kasa controlling kansa, ba a haka yaso yazowa Deejoh ba, shi kansa yasan ya apka mata da wuri, rayuwa mai cikeda jin dad'i ya tanadar masu saidai kana naka ne Allah na nasa, Na Allah shine dai-dai, tuni Allah ya k'addara faruwan hakan, tunawa da yayi Deejoh halal d'insa ne sai yaji hankalinsa ya kwanta ya sami nutsuwa sosai cikin zuciyarsa.... Lallashinta yaci gaba da yi yana sanar da ita halacin abinda suka aikata, da kuma matsayin mata da miji a addinance... Sosai yake fayyace mata komai yana sanar da ita wasu ilimi da bata sani ba... Tsananin kunyarsa ya hanata koda motsa d'an yatsanta ne, jin abinda sukayi ba haram bane sai ya sa hankalinta kwanciya, ta daina kukan sai ajiyan zuciya da take sauk'ewa... Albarka Ahidjo yaci gaba da saka mata had'i da masu addu'o'in samun zuri'a d'ayyiba... Gaban Deejoh ne yayi masifar fad'uwa sanda ta tuna yanda suke... Ta zabura zata mik'e taji azaban zafi ta k'asanta... Lokaci guda ta saki k'ara, saurin rik'ota yayi yana tambayarta mai take so..... Ai sabon kuka Deejoh ta fashe masa dashi tana nuna masa d'akin da suke ciki.... Sai sannan Ahidjoh ya fahimci d'akin Innah suke ciki, bazai tab'a son wani ya tadda halin da suke ciki ba shida iyalinsa..... Cikin sauri ya fice ya nufi kitchen yana k'ok'arin dafa ruwan d'umi, saidai kunna risho d'inma ya zame masa aiki.... A haka Innah ta jiyo karauniyarsa a kitchen, mamaki ya cikata ganinsa da tukunya yana k'ok'arin d'aura ruwa.... "Babana lafia dai koh...?" Innah ta tambaya tana dubansa, baima san ta shigo kitchen d'inba sai lokacin... 'Yan kame kame Ahidjo ya soma ya rasa mai zai ce mata gaba d'aya... Karb'an tukunyar tayi tana fad'in "Ai da ka kira Deejoh ta dafa maka ruwan .. Wai ina ta shiga ne ma....?" Ta k'arashe tana k'ok'arin d'aura tukunyar bisa madafi... Shafa k'eyarsa ya shigayi warily ba tareda ya furta komai ba don baisan mai zaicewa Innah ba, a hankali ya zame ya koma d'akin cikin sauri, ya soma kintsa wajen don wannan wani sirri ne nasu da ko mahaifansu bai kamata su gani ba, kaman yanda take a baya a Al'adan fulani.... Yana k'ok'arin taimakawa Deejoh ta mik'e suka jiyo sallaman Innah... Deejoh taji wasu sabbin hawaye suna gangaro mata, kallo d'aya Innah ta masu ta gane wani abu ya faru... Shafa kansa ya kumayi murya na sark'ewa yake sanar da Innah cewa Deejoh ce bataji dad'i ba... Innah da tuni ta gane meke wakana jinjina masa kai kurum tayi zuciyarta na mata wani irin dad'i kana tace "Jeka zan kula da ita...." Ya kuma shafa k'eyarsa yana satan kallon Deejoh dake faman hawaye murya can k'asa yace "Toh.... toh Innah..." Sihirtaccen annuri ne kwance saman fuskar Innah, fatanta Allah ya azirta yaran nata da zuri'a d'ayyiba.. A haka ta k'arasa ta kamo Deejoh tanai mata sannu har suka fice daga d'akin... Innah da kanta ta had'a wa Deejohnta ruwan d'umi ta kimtsa ta, daga bisani ta umarce Deejohn da tayi wankan tsarki irin wanda ta koya mata kwanakin baya lokacin data soma al'ada, dashike Deejoh batafi wata guda da soma Al'ada ba kafin zuwan Ahidjo.... Niya kawai Innah ta umarceta ta banbanta amma wankan iri guda ne.... Wajajen k'arfe goma da rabi na dare k'afafu sun soma d'aukewa garin ya soma yin shiru babu shaguna sosai a bud'e sai ka fice bakin babban kwalta.... K'aton super market dake gefen gidan mai yajesa yayo ma Deejoh sayayya, duk abinda ya d'aga sai yaga zataso, dangin kayan mak'ulashe da sauransu... Yana tafe a mota shi kad'ai yana sakin murmushin nishad'i, wani irin nutsuwa ya tsinci kansa ciki saikace ango mai auren fari.... Yana shigowa gidan ya iske Innah da Baffah basuyi bacci ba suna zaune parandar Baffahn tamkar shi suke jira... Gabansa ya yanke ya fad'i lokaci guda..... *SameenaAleeyou📚**FUSKA UKU*🏮 *32* *©Sameena Aleeyou...✍🏽* _God Bless Momma's_ Gabaki d'aya kasa shiga gidan yayi, ji yayi kaman an d'aure k'afafunsa, tamkar ya juya haka yaji saidai kafin ya ida wad'annan tunani nasa ya jiyo muryar Innah tana fad'in "Babana shigo mana ya ka tsaya daga wajen...." Da k'yar Ahidjo ya iya saita kansa kana ya soma takowa wata sallaman saman harshensa, gani yake tamkar Baffah zai masa d'add'aya.... Daga can gefe ya d'an zauna wacce tafi kama da durk'uso yana mai gaida iyayen nasa.... Innah dai sai wani sabon faran-faran take masa yayinda Baffah ya amsa babu yabo babu fallasa kaman kullum.... D'an sayayyan da yayo masu ya k'arasa ya aje gefen Innah yana mai fad'in "Innah ga wannan babu yawa...." "Kai madalla, toh Allah yayi albarka... Ka shiga ka duba Deejohn ne....?" D'an shafa kansa yayi kana yace "Dam yanzu.... Zan shiga ..." Ya k'arashe yana mik'ewa tsaye.... Har ya soma tafiya ya jiyo muryar Baffah ya ambaci sunansa cikin dakekkiyar murya... "Aliyu" "Na'am Baffah....!" Ya amsa cikeda rusunawa, lokaci guda ya dawo mazauninsa ya kuma zama Saida aka shafe kusan mintuna uku masu kyau Baffah baice komai ba, ba Ahidjo bane kawai ya damu da shirun Baffah harta Innah saida ta tsinci kanta cikin fad'uwar gaba da shirun mijin nata.... Bayan shud'ewan dak'ik'an Baffah yaci gaba da fad'in "Aliyu, ban aura maka Deejoh don kaci zarafinta ko ka wulak'anta ta, ko kayi mata wani abu mai kama da haka ba...." Maganganun Baffah sun saka k'irjin Ahidjo bugawa, innalillahi mai Baffah yake nufi, ba dai magana yake akan abinda ya faru tsakaninsa da Deejoh daren yau ba.... Muryar Baffah ya katse masa tunaninsa yanda yaci gaba da fad'in "Deejoh amanace a hannunmu kuma kaima amana ce a hannunka... Aliyu sam Deejoh bata kamace ka ba..." Ahidjo ya d'ago idanu yana duban Baffah, Innah ma Baffan take duba... Baffah yaci gaba da fad'in "K'warai Deejoh bata kamace ka ba, sabida ita yarinyace mai biyayya kai kuma D'ah ne maras biyayya,.." Sai sannan Innah tayi saurin katsesa da fad'in "Haba Malam, ya zaka dinga fad'in kalamai irin wad'annan akansa, baka gudun kalamanka suyi tasiri akansa....!" Wani kallo kurum Baffah ya mata ta kasa ci gaba da maganganun nata amma kam zuciyarta bata daina mata zafi ba... Baffah yaci gaba da fad'in "Kana saurare na.... Wllhi idan ka wulak'anta Deejoh bazan tab'a yafe maka ba..." Cikin sauri Ahidjo ya kuma d'ago kai yana duban Baffah kafin ya shiga girgiza kai yana mai fad'in "Haka bazata kasance ba insha Allah... Nasan na tapka kurakurai a baya amma insha Allah bazan sake tapka irin kuskuren dana tapka a baya ba.... Baffah koda ace bana son Deejoh ta zama wani b'angare na rayuwata a yanzu kuma the last thing da zanyi a rayuwata shine na wulak'anta ta.... Insha Allah bazaka sameni da wannan kuskuren ba na maka alk'awari..." Tausayin Ahidjo sosai ya kama Innah mai yasa mijinta bazai dinga kyakkyawan zato wa tilon d'ansu ba, meyasa yana mik'a wuyarsa ga shiriya mahaifin na pushing d'insa.... Tabbas wasu iyayen suke janyo wa yaransu fad'awa wata irin rayuwa, bazata gushe ba tana addu'an samun sauk'i da shiriya D'anta.... Har Ahidjo ya bar wajen Innah bata daina jimami da takaicin irin kakkausar harshe da mijinta ke amfani dashi kan d'an nasu ba.... Shiko Ahidjo gaba d'aya sanyi jikinsa ya masa musamman da ya lek'a d'akin Innah ya hangi Deejoh k'udundune a gado hawaye na sauk'owa daga idanunta, A hankali ya k'arasa shigowa d'akin had'i da zama gefe da ita, yana jin sanda sautin kukanta ya k'aru.... Zuciyarsa naci gaba da masa rauni... Baisan sanda ya kwanto ya rungumeta ta baya ba had'i da lumshe idanunsa.... Itama lumshe idanun nata tayi sabbin hawaye suna gangaro mata.... Sun d'an jima a haka kafin ya mirgino da ita suna fuskantar juna, lokaci guda Deejoh ta lumshe idanunta bata yarda sun had'a idanu ba... K'uri yayiwa fuskarta wanda siraran hawaye suke kwance bisa.... Murya can k'asan mak'oshi tamkar mai rad'a yace "Are you still crying...?" Jin bata amsa sa ba yakai 'yan yatsunsa saman fuskar nata yana bin hawayen yana shafasu a hankali yake fad'in "Dee kuka kike har yanzu.... Kiyi hak'uri kinji...." Ya k'arashe shima tamkar mai shirin kukan... Fuskarta ta juyar d'aya b'angaren sabon kuka na zuwa mata tace "Ni ka k'yaleni......" Ahidjo kuwa kwantar da kansa yayi a bayanta hannayensa na kewaye da ita gaba d'aya kana yace "Dee bazan iya k'yaleki ba, ke d'in b'angrene daga jikina..." Kukanta ne ya sassauta kana tace "Da gaske....?" Yanda tayi tambayar cikeda yarinta yasa Ahidjo dad'a rungumota jikinsa had'i da murmusawa kana yace "Sosai ma ko bakisan daga ribs d'ina aka cireki ba...." D'an d'ago idanu tayi tana dubansa kana tace "Ina ne ribs. ...?" Kamo hannunta yayi ya manna k'asan k'irjinsa kana yace "Daga nan d'ina aka cireki Dee sabida ke Matata ce..." Idanuwansu suka had'e waje guda, su duka kallon juna suke, kaman wacce ta tuna wani abu sai juyar da fuskarta tayi.... Murya can k'asa tace "Amma baka sona ai...." Mamaki maganan nata ya basa yanda ta fad'i har cikin ranta, shi bai mata kallon tama san meye soyayya sabida k'arancin shekarunta... Juyo da fuskarta ya kuma yi kana yace "Inji wa waye ya fad'a maki haka....?" "Ba najika kana ce ma Baffah koda baka sona ba.... Kenan wancan matar taka 'yar gayu kake so...." Ta k'arashe baki a ture Dariya taso basa amma ya d'an gimtse kana yace "Wato bakida daina lab'ewa kina sauraren maganan da ba'a aike ki ba koh? Ba na hanaki ba....." Ya k'arashe fuska babu walwala Girgiza masa kai tayi had'ida sadda idanunta k'asa kana tace "Kayi hak'uri bazan sake ba...." Wani irin dad'i ya mamaye masa zuciya, tunda yake baisan mace ta baiwa miji hak'uri don nashi matar batasan wannan ba a rayuwarta.... Murmusawa ya kumayi yana mai ci gaba da duban fuskarta.... A hankali ya gyara masu kwanciyar yana ayyana abubuwa da dama cikin zuciyarsa.... *** Kwance take saman k'irjinsa tana shafa fuskarsa lokaci guda tanai masa wasu salo masu rikita wanda ake masa.... Hannu yasa yana shafa fuskarta kana yace "Mai kike so ayi....." Murmusawa ta kumayi lokaci guda take yawo da 'yan yastunta saman fuskarsa kana tace "K'anwar matarka ce, kuma k'ark'ashinka take zaune, sannan ina hango soyayyarka cikin idanunta, so abinda nake so kaima zaka so, nasan you want her for yourself ni kuma I want her out of my Uncle's life.... Bana sonta kusan Uncle Siraj ko kad'an...." A hankali Nasaar ya jinjina kai kana yace "You're right.... I love her so much, kuma bazan tab'a barinta ma kowa ba is a promise...." Nana H ta kuma murmusawa had'i da gyara kwanciyarta sosai kana tace "Toh ka gani, so kaga I'm quite sure nida kai will make a great team..." ta tak'arashe tana kai masa sunba.... *** Yana fitowa daga sashen Innah bayan ya lallab'a Deejoh tayi bacci don saida ya bata paracetamol sabida d'an zafi da jikinta yayi... Wayarsa ya ciro ya shiga neman layin Sabi'u bugu biyu Sabi'u ya d'aga... "DT barka da dare..?" Cewar Sabi'u daga d'aya b'angaren "Barka Sabi'u, ya aiki...." "Mungode Allah, DT ya gida ya Family....?" Ahidjo ya amsa da "Alhamdulillah mun gode Allah..... Inaga nima zuwa gobe ko jibi zan shigo Abuja akwai wani aiki da nake dashi...." Sabi'u ya gyara tsayuwarsa kana yace "Toh, aiki kuma....? Harda kaine cikin wad'anda AIG zai tura Rivers, I thought hutunka bai k'are ba...." Shafa kansa Ahidjo ya d'anyi kana yace "No, ina so dama muyi magana dakai amma ba'a waya ba sai na dawo.... Insha Allah gobe ko jibin dai zan shigo....." Jinjina kai Sabi'u yayi kaman Ahidjo na kallonsa kana yace "Shikenan DT sai na jika...." Daga haka sallama sukayi da Ahidjo ya k'arasa sashensa yana neman layin matarsa Nana H..... *** *Damaturu* Gari na wayewa suka soma shirye-shiryen tafiya aiki, Daddah ta kad'a kai a karo na biyu sabida jiya akan idanunta Dakure ke rungume wasu maza, ta lura Hajiya Yagana tana fita Dakura ke maida wajen dandalin hira da samaruka marassa kamun kai gashi babu wanda ya isa ya mata magana sabida ta lura kowa tsoronta yake a cikin shagon.... Cikin zuciyarta take addu'an Allah sa ta tadda wani abu ba daidai ba a shagon..... Da wannan tunani su Mairo da Umma Marie suka k'araso suka isketa kafin suka d'auki hanyar masana'antar tasu..... Dakura kuwa sauk'arta kenan daga babur ta hangi Soji guda masu tsaron farkon layin yana k'arasowa dama samarukanta ne, wani sa'in idan ta tashi daga shagonsu k'arfe shida wajen Sojojin nan take tsayawa suyita rungume rungume suna abinda ba daidai ba..... Aiko yana k'arasowa ya soma washe baki yana gyara zanzaronsa ga uwar tumbinsa uwa randar burkutu. Yana tafe yana furta "Dakuura, ka sami isowa.." D'an yatsina fuska Dakura tayi tana kuma taunar chewing gum had'ida juya idanu.. Lokaci guda take furta "Shi wannan daga zuwata ya wani zo zai soma damuta....." Tana k'ok'arin biyan d'an mashin Sojin ya k'araso da sauri yana zaro kud'i cikin aljihunsa yake fad'in "A'a a'a wannan ai aiki na ne...." Ya k'arashe yana tambayar mai Mashin kud'insa... Lokaci guda Dakura ta soma murmusawa don ta yanda tafi k'arfi kenan, idonta idon kud'i ne.... "Haba officer ai daka barshi...." ta fad'i tana juya idanu had'ida yin k'araras da chewing gum.... Hannu ya mik'a yana rik'ota yake fad'in "A'a no don't worry, this is nothing.... Yau kunzo da wuri mu k'arasa tent d'inmu before your Madam come...." Murmushi Dakura tayi kana tace "A'a bazanje tantinku banga su ba...." Waigawa ya somayi yana dube -dube yake fad'in "Su waye kenan... Are you expecting someone...?" Dariya tayi irinta 'yan tasha kana tace "Money, kud'i nake nufi...." Dariya ya kuma yi kana yace "Ahh kudi is not a problem.... Muje..." Ya k'arashe yana kuma kamota Dai-dai lokacin su Daddah suka sharo kwana..... Mairo da Umma Marie sai labari suke Umma Marie na d'an mata bayanin yanayin unguwar, basu ankare ba sai jin Daddah sukayi tana rangad'a salati tanai masu nuni da Dakura da gardi ya rik'ota... Kasancewar bak'ar riga ce jikinsa bata kaki ba shiyasa Daddah bata fahimci ko waye bane.. A d'ari ta nufesu tana k'ok'arin ciro bulaliyarta da tayi sapiyanta cikin jakanta... Aiko tana cimmasu ba tareda tace dasu komai ba ta shiga zabga masu bulaliyar nan kace turota akayi.... Daga Umma Marie har Mairo kasa furta koda kalma sukayi sai kallon ikon Allah da suka tsaya yi.... Wandon jikin mutumin da boot d'in k'afarsa kurum Mairo ta hanga ta fahimci Soja ne *SameenaAleeyou📚**FUSKA UKU*🏮 *33* *©Sameena Aleeyou...✍🏽* *Gaisuwa tareda Fatan Alheri masoyan Mairo da Daddah sun gode matuk'a😅🤝🏼* "Tsinannun Allah farar safiya hantsi na kallonku kuna bad'ala ubanku zakuci....." Bata kai aya ba taji an rik'i bulaliyar gam.... Ta d'ago tana huci take duban mutumin wanda idanunsa suka koma tamkar garwashin wuta.... Dakura kuwa sai bala'i take tana tsinewa Daddah tana fad'in "Wllhi yau kashinki ya bushe tsohuwar kawai wllhi kaf danginki sai an kullesu, kuma babu uban da ya isa ya bud'eki...." "Ke dalla rufe min baki motar haya kurum, kina nan kutittiriya dake uwa gaban gado sai iya shege da iskanci koh, toh wllhi dake da samarukan naki duk idan dai ina nan ubanku zakuci...! Ta k'arashe tana k'ok'arin janye bulaliyarta hannun mutumin.... Karkatowa tayi tana fincikan bulalan take fad'in "Kai kuma ba tsoron pankan pankan nake ba kaji na fad'a maka.. Kaima....." Aya ta saka ma kalaman nata sanda idanunta suka sauk'a k'asa ta hangi wandon kakin dake jikin mutumin wanda ya tsaya mata tamkar gunki, take 'ya'yan hanjin Daddah suka shiga murd'awa... Bakinta ya shiga karkarwa tana girgiza kai lokaci guda ba tareda ta furta komai ba..... Mairo da Umma Marie da suka koma tamkar ruwa ya shanyesu sai sannan suka nufesu a d'ari.... Umma Marie ta shiga baiwa Dakura dake balbalin bala'i hak'uri yayinda Mairo ta isa ga mutumin tana k'ok'arin janye Daddah take fad'iwa Sojan "Yallab'ai kayi hak'uri bamu jima da dawowa daga jinyar tab'in hankali ba... Dan Allah kayi hak'uri Yallab'ai...." Banda jinjina kai babu abinda Daddah keyi tana fad'in "Shiyasa ma sam ban lura da wandon jikinka ba Yallab'ai...." Dakura kuwa sai kuruwa take tana fad'in "Wllhi Oga Bulus k'arya suke maka, tsaban iskanci ne ke damun wannan tsohuwar...." A duniya Mairo tak'i jinin abinda zai tab'a Daddarta balle a zageta... Karkatowa sosai tayi tana duban Dakura ta daina bada hak'urin da take kana tace "Idan kika sake zagi min uwa zan watsar zan shirya maki wad'annan wargazazzun hak'waran naki...." Dakura dake faman tsalle tana ruwan bala'i gata dududu bata wuce kafad'un Mairo ba, tsalle ta kuma dakawa had'i da cire d'ankwalinta ta sha d'amara tana fad'in "Woo wllhi ba'ayi shegiyar da zata zageni ba Dakura nake naci uban kowa na kwana lafiya...." Bata kai aya ba taji sauk'ar bulala a bayanta... Umma Marie salati kurum take jikinta sai rawa yake sam bata saba da tashin hankali ba... Daddah tana ganin haka don tayi trusting d'iyarta tasan tsaf zata iya da Dakura, ganin sojan nan ya manna waya a kunne Umma Marie na k'ok'arin rabiyar fad'ansu Mairo da Dakura , tasan hankalin kowa baya gareta, a hankali ta soma zame takalmanta cikin sand'a da dabara... Aiko tana kwab'esu ta wawace a guje tana fad'in "Mairo kar kika ragar mata, cimin uwarta da kyau ta yanda gobe idon gardi bazata gani ba...." Tana gudu take wannan maganganun takalma a hannu.... Ai Sojan nan a d'ari yabi bayanta saidai kafin ya cimmata Mairo ta watsar da Dakura cikin kwalbati kace k'ullin kayan wanki aka watsar, cikin sauri Mairo tasha gabansa tanai masa murmushi mai kashesa, lokaci guda ta shiga masa mad'e tana fad'in "Haba my Yallab'ai ba girmanka bane fad'a da mata kana Jarumin Soja..." Ai Oga Bulus yaga fara kyakkyawa wacce tafi Dakura tanai masa mad'e tuni ya shiga washe baki yana k'are wa Mairo kallo... Mairo ko cikin zuciyarta take addu'an Allah sa kar ya matso kusanta, k'irjinta sai faman bugu yake.... "Yarinya mai kyau....!" Oga Bulus ya fad'i yana kuma washe baki... Umma Marie kam tuni ta nufi hanyar da taga Daddah ta nufa don sanin halin da take ciki.... Dakura daga cikin kwalbati take faman nishi don ihu mai kyauma ta kasa..... Gashi layin ba mai yawan jama'a bane ya had'u kuma da safiya balle ta samu masu kawo mata d'auki.. Oga Bulus kuwa ganin Mairo ta soma tafiya ya shiga bin bayanta yana kiranta "Yarinya Mai kyau....!" Suna barin wajen Sojin da ya masu waya suka k'araso da hilux basu tadda kowa wajen ba sai Dakura dake faman nishi cikin kwalbati... Aiko nan suka zaci Dakura Oga Bulus ya turosu su kame.... Nan suka shiga janyota suna k'ok'arin watsa ta bayan Hilux take kururuwa tana fad'in wllhi ba ita bace su tausaya mata... Inaa ko kulata basuyi ba suka watsa ta bayan hilux da alama ko hausar ma basa ji..... *** A hankali Nazir ya soma bud'e idanunsa yana shafa gefen kansa da yake masa zafi da alama bugawa yayi.... Kallon yanda yake ya soma yi yana k'ok'arin recalling abinda ya faru dashi.... Idan bai manta ba he was at the airport yana k'ok'arin barin k'asar zuwa k'asar Ghana, wasu mutane biyu suna biye dashi a baya d'aya ya sha gabansa yayinda d'aya ya toshe hancinsa da farar tsumma.... Kallon d'akin da yake ya shiga yi kafin ya mik'e yana girgiza kai yake fad'in "Oh no no no.... Bulama you can't do this to me.... Where am I...?" Bulama dake zaune wata parlor ya d'ora k'afafu d'aya bisa d'aya cikin k'aramar computer d'insa dake hasko masa cameran da ya saka cikin d'akin da aka gark'ame Nazir murmushi yake yana duban Nazir d'in lokaci guda yake tuna cin amanarsa da Nazir yayi.... Yana kallo wasu k'arti suka bud'e d'akin suka shiga jin Nazir ya tashi... Tamkar wad'anda aka aiko nan suka shiga dukan Nazir ta ko ina babu magana sai jibgansa kurum suke.... Wani leda cikeda ruwan zafi suka dannan kan Nazir ciki suna basa wani nau'i na azaba.... Lokaci guda Nazir cikin tsananin jin jiki yake fad'in "Bulama I know you're watching this.... And you're enjoying it, amma ka sani bazaka tabbata kana yi ba... Lokacin ka zai k'are kaman yanda na Fir'auna ya k'are.... Zaka mutu and you'll rot in hell till eternity..." Bai kai aya ba suka kuma danna kansa cikin ruwan, sai faman wutsil wustil da k'afa yake sabida azaba... Daga yanda Bulama yake zaune hard'eda k'afufuwa dariya ya fashe dashi kafin ya mik'e ya nufi d'akin horon Nazir.... Yana shigowa suka dakata da azaban da suke gallazawa Nazir, Nazir ya d'ago kansa dake d'igan ruwan azaba yana aikawa Bulama mugun kallon da idanunsa da suka koma tamkar garwashin wuta kana yace "You rat.... You'll pay for this....." Bai kai aya ba Bulama ya sauk'e masa sandar hannunsa.... Nazir bai giving up ba ya kuma d'ago fuska kana yaci gaba da fad'in "I love her. .... I love Mairo, and I'm willing to give my life for her....." Dariya Bulama ya fashe dashi kana yace "You're so delusional young man.... Do you really know what I do to a Snitch like you....?" Ya kuma murmusawa kana yace "I won't end your life now, but believe me you're going to suffer here, wahalan da sai ka zab'i mutuwa fiyeda rayuwarka..." Yana ida fad'in haka ya kuma fashewa da dariya kana yace "Enjoy your company traitor..." Daga haka ficewa yayi yana bushewa da wata irin dariya.... Yana fitowa wayan Nasaar ya gani na shigo masa.... Wani d'akin ya nufa kafin ya d'aga wayan Nasaar, lokaci guda yake furta... "Alright, perfect mu had'u a can gida sai ka bani komai in details...." Daga haka katse wayar yayi yana cangwala sandarsa had'i da d'ingishi har ya isa mota... Wajajen k'arfe goma na safiya ya iso gidan, nan ya tadda Nasaar na jiransa.... Bulama na sauk'owa Nasaar da guards suka take masa baya..... A babban parlornsa suka yada zango shida Nasaar.... Bulama ya kurb'i ruwa kana yace "I'm all ears Attorney, give me good news...." Gyara zama Nasaar yayi kana ya soma fad'in "Boss about those Estates da na fad'a maka Siraj zai saya a nan Jabi... Yanzu maganar da nake maka ya sayesu, ni ya tura na had'u da client d'in akayi komai....." Wani dariyan jin dad'i Bulama ya fashe dashi kana yace "What a great news....! Yayi kyau Nasaar, you keep the good work...." Nasaar ya kuma murmusawa yana gyara zaman suit d'insa kana yace "Thank you Boss...." Bulama ya jinjina kai kana ya zaro wata check yayi rubutu bisa ya mik'awa Nasaar.... Cikeda rusunawa Nasaar ya karb'a, kafin yayi sallama wa Bulama... Jinjina kai Bulama yayi kana yace sai sunyi magana.... Har Nasaar yakai k'ofa ya jiyo muryar Bulama yana kiran sunan sa... Dawowa yayi da baya cikeda rusunawa yana mai amsawa... K'uri Bulama ya masa tamkar mai karantarsa kana ya soma fad'in "Nasaar I trust you hundred percent, don't ever try something that will break this trust I've for you...." Ya d'an murmusa kana yace "Bana yafewa maci amana... Be careful...." A hankali Nasaar ya jinjina kai kana yace "Never Sir, bazan tab'a cin amanka ba.. I promise..." Murmusawa Bulama yayi kafin yace "Good for you.... By the way ina jikokina, I hope suna lafiya kuma basu buk'atan komai.....?" Murmusawa Nasaar ya kuma yi kana yace "Suna lafiya, bazasu tab'a neman komai su rasa ba....." Murmusawa Bulama ya kuma yi had'i da jinjina kai kana yace "Kana iya tafiya...." Zama Bulama yayi bisa kujera kafin a hankali ya furta "Mas'ud..... Ka mutu ka bar baya da k'ura, I won't rest har sai naga k'arshen duk wani wanda ya fito daga tsatsonka, duk wani dukiyar da ka bari wa iyalanka sai naga bayanshi.... I'm sorry abokina...." Yana ida fad'in haka ya kuma d'aukan ruwa yana kwankwad'a.... *** Yauma tare suka fita lokacin lunch.... D'an yatsina fuska tayi tana dubansa kana tace "amma dai kasan ni sakatariyarka ce not your companion, stop taking me to places please.... And stop wasting your money on me please bana buk'ata..." Ta k'arashe tana jujjuya masa idanu cikeda tsiwa.... Idan steering wheel d'in motarsa ya amsa toh kuwa shakka babu shima zai amsa, tab'e baki ta d'anyi tana duban hannunsa dake rik'e da steering kaman ka tab'a jini ya fito sabida freshness... Siraj baiyi parking ba saida ya iso k'ofar Down Town..... Kallonsa tayi cikeda mamaki... Saidai kafin tayi magana Siraj yayi unlocking motar ba tareda ya kalleta ba yace "Shall we...." Yana fad'i yana gyara zaman business suit d'insa D'an fuzar da iska tayi kana tace "Do I have a choice...." Fitowa tayi tana take masa baya, d'an jiranta kad'an yayi suka shige ciki a tare... Aiko ma'aikatan wajen na hangosu suka k'araso suna gaishesa had'ida directing nasu special area don tuni Siraj ya biya reservation..... Azeeza tasha mamakin ganin yanda akayi k'awata wajen da kwalliya... Kasa zama tayi sai bin wajen da kallo take, Siraj kuwa na hankalce da ita baice komai ba sai zama da yayi yana duba menu d'in dake ajiye bisa table d'in.... Har Siraj yayi order Azeeza bata daina tab'e tab'en baki ba... Koda waitress ta tambayi order d'in Azeeza Siraj cewa yayi a kawo mata irin nasa.... Still ko kallonsa batayi ba, saima k'ok'arin ciro wayarta dake faman ringing cikin k'aramar side bag d'inta take..... Ganin lambar Nasaar ne yasa gabanta mugun fad'uwa kasa d'agawa tayi, cikin sauri ta saka wayar a silent.... Kusan sau uku tana yin haka dai-dai lokacin da aka k'awata gabansu da delicious.... Kafeta da idanu yayi ganin tak'i d'aga wayar..... Jin bazai daina kira ba ya sanyata kashe wayar gaba d'aya don sam bata so Siraj ya fahimci akwai wani abu tsakaninta da Nasaar.... Hankali kwance yake cakalan abincinsa lokaci guda ta stinkayo muryarsa yana fad'in "Was that your boyfriend... Meyasa kika kashe wayar...?" idanunsa naga plate yayi maganar... Saida ta kuma juya idanu kana tace "Nasan aikina kuma na san Boss d'ina ya hana kula samari lokacin aiki ko ka mance ne...." D'ago idanu yayi yana dubanta had'ida ajiye fork d'in hannunsa kana ya d'an murmusa lokaci guda yakai idanunsa kan plate d'inta wanda ko tab'awa batayi ba kana yace "Ki ci abinci 3 dot zamu bar wajen I've some clients to attend to..." Ya k'arashe yana mai ci gaba da cin abincinsa.... Girgiza masa kai tayi kana tace "I can't... Im not used to places like this.... Kawai idan ka gama mu tafi...." D'an murmusawa yayi kana yace "You should try this it's delicious... Ai na zaci yanda kike da tsiwa d'in nan cin abinci a wajaje irin nan bazai zame maki matsala ba..." Dubansa tayi fuska a tab'e kana tace "Whatever, and yes you don't know many things about me, do you?...." Murmusawa Siraj yayi kana yace "Don't worry, I can assure you that we will learn more of each other over the years we gonna spend together...." Da mamaki take dubansa kana tace "Did you say years...?" Ta kuma d'an murmusawa wanda yafi kama da yak'e kana tace "Kar ka mance shekara guda tak zamuyi a tare don next year by this time ina school insha Allah...." Murmusawa Siraj ya kuma yi kana yace "Kar ki damu zan barki kiyi school don ni a tsari na bazan hana Matata neman ilimi ba...." Ya k'arashe kyakkyawan murmushin da bata tab'a ganin yayi irinsa ba kwance saman fuskar sa... Gaba d'aya sai ji tayi jikinta yayi sanyi, abinda ta jima tana k'aryata ma zuciyarta gameda shi taji na kuma taso mata, bata kuma kallon idanunsa ba sai janyo plate d'in abincinta da tayi Da k'yar ta soma cakalan abincin don tasan daga nan wani meeting d'in nasa suka nufa... Suna fitowa daga restaurant d'in Hilton suka nufa yanda zai had'u da clients d'in nasa confidentially.... Duk wannan zirga zirga da suke Nazir na biye dasu a baya ba tareda saninsu ba... Ganin sun nufi Hilton ba k'aramin shiga tashin hankali yayi ba... Wasu irin tunani ne barkatai sukayita ziyartar kwanyarsa.... Abinka da wanda bai yarda da kansa ba sai yana ganin tamkar Siraj mugun nufi yakedashi akan Azeeza, wani irin tsanar Siraj ya kuma tasowa ya tokare masa mak'oshi.... Cikin sauri ya shiga neman layin Nana H Tana d'agawa Nasaar ya soma sanar da ita abinda ke faruwa.... Zuciyarta ya shiga mata wani irin k'una.. A d'ari ta fice ta suri motarta ta fice daga gidan, ... "You're death you little witch..."Ta furta cikin tsananin b'acin rai *** Nana A na fita daga office d'insa yayi saurin janyo wayarsa yana kuma neman layin Sabi'u... Bugu uku Sabi'u ya d'aga, cikeda k'osawa Junaid yake fad'in "Sabi'u, ina saurarenka.." Daga d'aya b'angaren Sabi'u yace "Ahidjo yana hanyar Abuja gobe.... So I'll get my boys ready, and don't forget to transfer the cash to my account.... I'll take care of everything ka gane..." Jinjina kai Junaid yayi kana yace "Perfect, sai kaji daga gareni...." *SameenaAleeyou📚**FUSKA UKU*🏮 *34* *©Sameena Aleeyou...✍🏽* Junaid yana katse kiran Sabi'u idanunsa suka kad'a sukayi jazir, fatarsa tayi jazir.... Cikin wata irin murya yake furta "I'm back, and I'll take my revenge on each and everyone of you... I'm gonna make you suffer much more than I suffered before...." a hankali ya lumshe idanunsa fuskar Zeenat na masa gizo cikin idanunsa, sautin k'aranta kafin ta mutu na kuma karad'a cikin kunnuwarsa da kwanyarsa.... *** Hold up ne sosai ya tareta, ko motsawa motocin basayi banda k'aran horns babu abinda kake saurare da alama ma wata k'atuwar motace ta b'aci ta tare hanyar, gaba d'aya wajen ya zama very congusted... Banda tsaki babu abinda Nana H ke bugawa, ji take tamkar tayi tsuntsuwa ta tashi sama sai buga steering wheel take tana huci, gashi ta shige tsakiya babu hali ta fice dolema ta jira ayi clearing cunk'oson.... Cikin sauri ta zaro wayarta ta soma kiran Nasaar, bugu biyu ya d'aga tamkar jira yake ta kira nan ya soma fad'in "Nana H what's taking you too long.... Ya kamata ki iso by now before that bastard uncle of yours does something to Zeeza... Wllhi ya mata wani abu zan iya kashesa...." Bai kai aya ba ta katsesa da fad'in "Shut up you idiot.. Mai ya hanaka binsu cikin hotel d'in, isn't she your responsibility..... you know you're such a jerk... And let me remind you this, wllhi wllhi wani abu ya samu Uncle d'ina you gonna hear it from me..." Cikin sauri ya katse kiran had'i da buga tsaki... Gyara zamansa yayi cikin mota don bai tunanin zai iya tafiya baiga fitowarsu ba.... Bayan shud'ewan awa guda ya hangi motar Siraj ya fito daga Hilton.... Cikin sauri ya tada motarsa shima ya shiga bin bayansu... Ga mamakin sa gidansu Siraj d'in yaga sun nufa.... Zuciyarsa taci gaba da masa zogi wato bai ishesu a hotel ba sai sun tafi har gida.... Da sauri ya kuma d'aukar wayarsa ya kira Nana H ya sanar da ita ta juyo gida sun nufi gidansu.... *** Kallon Siraj Azeeza tayi a karo na biyu kana tace "Nan kuma ina ka kawoni....?" Ba tareda ya dubeta ba yace "Gidan in-laws d'inki.... Fito muje....." Girgiza kai ta d'anyi kana tace "Sir nifa ba girlfriend d'inka bace, I'm your secretary don't forget...." D'an murmusawa yayi da gefen bakinsa kana yace "Nima bance ke budurwata bace, as far as I know this also part of your job.... So mu shiga kafin ki b'ata ran Boss d'inki...." Baki sake take dubansa, itakam bata tab'a ganin mutum irinsa ba, shi kuma nasa salon kenan, wai yafi k'arfin ya fito kai tsaye ya sanar da ita yana sonta ne saidai ta gani a actions d'insa ko mai... D'an tab'e baki tayi kana tasa kai ta bisa cikin gidan ganin zai tafi ya barta..... Ammah da Ayiya na parlor suna d'an tab'a hira kafin a shiga sallan la'asar su tashi don already anyi kira.... Lokaci guda suka tsinkayo sallaman Siraj... A tare suka amsa yayinda suka kuma jiyo sallaman wata budurwa dake biyeda Siraj d'in.... Ammah da Ayiya dai kallo suka shiga binsu dashi lokaci guda Ammah keyiwa Siraj barka da dawowa, had'ida yiwa budurwar sannu da zuwa, Ayiya kam baki sake take dubansu... "Ammah barka da gida.... Azeeza taho ki zauna..." Ya k'arashe yana nuni ma Azeeza data zauna bisa kujera... Azeeza kuwa kanta a k'asa ta k'arasa tana k'ok'arin zama bisa carpet take sannu wasu Ammah.... "A'ah a'a tashi ki zauna a sama please...." Ammah ta fad'i murmushi fal saman fuskarta... Azeeza ma murmushin take tana kuma sunne fuska had'i da gyara mayafinta, bata zauna saman kujeran ba sai cewa tayi "A'a nan ma yayi Ammah...." Kaman yanda taji Siraj ya ambaci sunan Ammah haka itama ta ambata.. Zama tayi suka soma gaisawa kafin Siraj ya mik'e yana duba agogon hannunsa don yaji ana shiga sallah masallacin k'ofar gida.... "Barinje sallah naji ana shiga.... Ammah ga Azeeza zata gaisheku.." Ya k'atashe yana ficewa cikin sauri Ammah baki har kunne take amsa Siraj d'in lokaci guda suka soma gaisawa, Ayiya ma da sakin fuska suka gaisa, lokaci guda Ayiya ta shiga rangad'a kira wa ma'aikatan kitchen kan kace mai an cika gaban Azeeza da kayan motsa baki..... Dai-dai nan Nana A ta sauk'o daga upstairs tana tambayar ko muryar Uncle ta jiyo don tana bayi tana alwala.... Ammah ta mik'e tana kuma murmusawa take fad'iwa Azeeza ta saki jikinta kana tace da Nana A "Eh shine ya fita sallah amma, maza kizo ku gaisa ga bak'uwa ya kawo...." Take annurin fuskar Nana A ya k'aru cikin d'an tafiyarta mai d'ingishi ta k'araso tanaiwa Azeeza sannu da zuwa.... Azeeza ta bita da kallon mamaki ganin tsananin kamannin da suke da Nana H saidai wannan fuskarta kalan saliha ce gata da faram-faram ba kaman Nana H ba.... Nan Nana A ta k'araso tana gaida Azeeza had'i da mata introducing kanta.... Ayiya ma mik'ewa tayi ta bar Nana A da Azeeza a parlorn..... Sosai Nana A ta sake da Azeeza lokaci guda Azeeza taji mutanen gidansu Siraj sun kwanta mata, sunada mutunci da karamci, wato dai Nana H ce kawai batayo hali irin nasu ba... Take ta soma kokonton anya Siraj zai iya kashe rai, anya Yayanta Junaid ba kuskure yayi ba..... Muryar Nana A ya katse ta sanda take fad'in "Mu haura sama kiyi sallah..." D'an murmusawa Azeeza tayi kana tace "Banayi ne...." Nana A tace "OK bara naje nayi yanzu zan sauk'o kinji... Dan Allah kici abinci kisha ruwa fa kinji, Uncle bazaiji dad'i ba idan yazo yaga bakici komai ba...." ta k'arashe cikeda raha.. Murmusawa Azeeza ma tayi kana tace "Kar ki damu zan sha....." Har Nana A ta haura sama Azeeza bata daina binta da kallo ba tana murmushi, itakam mutanen sun matuk'ar burgeta.... Tana nan zaune Siraj ya shigo yana gyara hannun rigarsa... Take ta tsuke fuska ba tareda ta dubesa ba.... Murmusawa yayi kana ya zauna gefenta ya d'auki fork yana shan yankakkiyar watermelon d'in da aka kawo mata, lokaci guda yake fad'in "Ya suka barki ke kad'ai ina Nana A..." Ba tareda ta dubesa ba tace "Sunje sallah...." Siraj ya kuma dubanta kana yace "Yaya baki bisu sallahn ba...." Harara ta galla masa ba tareda tace komai ba baki a ture.... Siraj ya kuma murmusawa da gefen bakinsa kana yace "Kodai bakiyi ne...." Ya k'arashe yana kuma d'aukan wani watermelon d'in had'i da kaiwa bakinsa... Cikeda masifa take dubansa kafin tace "Ai kasan ni arniya ce...." Wannan karan murmushi mai sauti ya d'anyi had'i da bud'e hannayensa yace "A'a ni bance ba, nasan yanayi ne yasa bakiyi ba.... So tell me kin sanar dasu Ammah wacece ke, kinsan ya kamata ku saba kafin ki shigo gidan... Oya bud'e bakin ki...." Ya k'arashe yana mik'a mata fruit d'in da fork d'in hannunsa.... Kallonsa kurum tayi had'i da girgiza kai don dariya ma yaso bata... Dai dai lokacin Nana H ta sako kai cikin parlorn... Wani irin bugu da k'irjinta yayi ganin yanda Siraj da Azeeza ke murmushi wa juna tamkar masoyan asali.... Cikin sauri ta katse su sanda ta bud'e murya tana fad'in "Uncle I didn't know you home already...." Ta k'arashe tana shigowa cikin parlorn... Murmushi Siraj ya sakar mata kana yace "Nana H sweetheart k'araso mana,..." Takowa take tana watsa wa Azeeza wani irin muguwar kallo yayinda Azeezar ma ta bita da kallon raini "What's this woman doing here...?" Ta fad'i tana k'arasowa kusan Siraj.... Mik'ewa Siraj yayi yana dubanta kana yace "Nana H, Azeeza is my guest..." Lokaci guda ta shiga hura hanci tana dubansa kana tace "I was at the company, naje nemanka aka ce min kun fita, sannan da na bi bayanka sai naga hotel kuka nufa Uncle... So uncle tell what is this woman dragging you into huh...?" Tayi tambayar tana zazzare idanu tamkar wacce zata rufesa da duka.... Duban mamaki kawai Siraj yake mata kana ya kasa yarda wai d'iyarsa ke masa irin wannan tuhumar.... Azeeza kam sabida tsaban mamaki ta kasa furta komai k'arara take hango soyayyar Siraj cikin idanun Nana H.... Lokaci guda Siraj ya kamo hannunta ya shiga janyota suka nufi k'ofa yana mai fad'in "You and I need to talk...." Harara ta watsa wa Azeeza tana biye dashi kana tace "Yes Uncle..." Suna fita haraban gidan ya kafeta da idanu cikin tsananin fushi da b'acin rai ya soma fad'in "Nana H what exactly is wrong with you... Just why are you like this.... Look I'm sick and tired of this attitude of yours kina jina.... Don na sake maki ba yana nufin na baki k'ofa bane ki raina ni, kisan irin kalaman da zasu ringa zuwa harshenki and especially a gaban mutane....!" Ya k'arashe idanuwansa sun firfito waje... Itama cikin tsananin fushi take fad'in "But Uncle can't you see that girl is chasing you.... She loves you Uncle... For crying out loud open your eyes and see....!" Girgiza kai kurum yake yana dubanta cikeda mamaki kana yace "And what's so wrong with that.... Laifi ne idan tana sona... How many times do I have to tell you this... Azeeza is my secretary she's my secretary nothing more nothing less, and yes we were at the hotel... I went there to attend to some clients...." Idanunta ne suka d'anyi rau-rau kana tace "But Uncle I'm.... I'm just trying to protect you, Uncle Nadiya bata jima da rasuwa ba, I'm afraid you might suddenly fall into a relationship with her.... Uncle ka san matsalanka and bana son ganinka cikin k'unci I love you with all my heart Uncle, It hurts seeing you broken..." Ta k'arashe tamkar mai shirin yin kuka.... K'arasowa yayi ya d'an rik'o hannunta kana yace "Na fahimceki sweetheart but you also need to understand me.... I can't live like this forever, I also need someone by my side..." Bai kai aya ba tayi saurin katsesa da fad'in "That someone is me Uncle... You have me and I'll always be here for you, I promise...." Ta k'arashe tana shafa fuskarsa hawaye na gangaro mata... Tinda Siraj yake da Nana H bai tab'a jin jikinsa yayi sanyi da lamarinta irin na yau ba... Gabansa sai dukan tara-tara yake.... Cikin sauri ya zame hannayenta daga fuskarsa kana yace "Muje ciki....." Cikin sauri ta rik'o hannunshi tana share fuskarta suka komo cikin parlorn.... Suna tafe wayar Siraj ta soma ruri cikin sauri ya cire hannunsa daga cikin hannun Nana H ya koma waje yana amsa wayar.... Aiko tana komowa cikin parlorn ta hangi 'yan gidan gaba d'aya sai nan nan da Azeeza suke babu kaman Ammah wacce tuni Azeeza ta shige zuciyarta, Nana A kuwa sai janta da fira take Ayiya na basu dariya, da alama suna jin dad'in firan nasu... Azeeza ko saurarensu kawai take amma hankalinta na wajen su Siraj da Nana H wanda har yanzu bataga shigowarsu ba tinda suka fice.... Itakam ta soma razana kardai Siraj neman niece d'insa yake.... Subhanallah bata fatan hakan ya tab'a kasancewa... "My Uncle is a wonderful man, ina mai tabbatar maki zai kula dake fiyeda tunaninki..." Nana A ta fad'i murmushi fal saman fuskarta.... Azeeza koh murmushin yak'e tayi ganin duk yanda suka zata Siraj masoyinta ne kana tace "Ah ai....." Isowan Nana H ya katse mata maganan nata.. "Ce maku tayi ita girlfriend d'in Uncle ne.... Well she's his secretary, and according to Uncle hanya ce ta biyo dasu ta nan shiyasa suka tsaya don naje office ban samesa ba shine ya biyo gida ya tadda meyasa nake nemansa bayan ya riski sak'ona..." Ta maido da dubanta ga Azeeza tanai mata murmushin na fiki iya bariki kana tace "Am I right....?" Murmusawa Azeeza tayi kana tana dubanta saidai kafin ta sami zarafin magana Ayiya ta katseta da fad'in "Sabida ke baki gane abubuwa ba.... Idan na miji na bada kulawa irin haka soyayya ce... D'iyata ki taimake mu ki korar mana aljanar data aure Sirajo kinji, mutum ya girma ya girme har yana neman zama tuzuru...." Kan Azeeza a k'asa tana kuma janyo mayafi tana rufe fuskarta take murmusawa kana tace "Ayiya bansan gidan nan zai kawoni ba don da ban yarda ba, mu Al'adanmu budurwa bata bin saurayi gidansu kafin aure koda gaisuwa ce sai ta kama dole...." Ayiya ta kuma murmusawa cikeda jin dad'i don taga irin kallon da Azeeza da Nana H ke watsa wa juna tasan tabbas wannan yarinya ita zata masu maganin Hafsatu kana tace "Kai amma Al'adanku abin burgewa ba kaman irinta wagga gida ba da aka ari Al'adan yahudu aka yafa....." Tamkar ta k'arasa ta shak'e Azeeza da Ayiya haka take ji, sai hura hanci take tana binsu da mugun kallo, kasa ci gaba da tsayuwa tayi a parlorn cikin tsananin k'una da k'irjinta ke mata ta fice.... Nana A kuwa dad'ine ya kuma cika zuciyarta jin Azeeza budurwar Uncle Siraj ne, tinda maganganun Azeeza hannunka mai sanda ne.... Nana H na fitowa ta hangi Ammah da Siraj suna magana can k'ofar bayan parlorn.... Cikin sauri ta lallab'a ta k'arasa kusan wajen had'i da kasa kunnuwa tana sauraro komai... Ammah taci gaba da fad'in "amma su waye iyayenta.....?" Siraj ya d'an murmusa kana yace "Marainiya ce Ammah, bata da kowa a nan sai mijin 'yar uwarta da take zaune da yaransa, ta rasa kowa nata a Maiduguri...." Cikeda tausayawa Ammah tace "Allah sarki gata yarinya ce sosai... Kuma da alama tanada hankali sosai...." Siraj ya kuma murmusawa yana jinjina kai kana yace "Azeeza nada hankali sosai Ammah, banso na bayyana abinda ke tsakaninmu ma jama'a tun yanzu kinsan matsalata...." Jinjina kai Ammah tayi kana tace "Gaskiya ne, kayi gaskiya Siraj, har yanzu mak'aryaci mayaudarin yaron nan bai bayyana ba koh...." Siraj ya D'angelo shafi kansa kana yace "Wai Lamid'o...." Ammah ta jinjina kai tace "Who else...." Siraj ya d'an fuzar da iska kana yace "He hasn't showed up Ammah, but we have no business to do with him anymore, don ko ya dawo bazan barshi yaci gaba da aiki da companyn mu ba.... hakan yafi mana, nasan Lamid'o bazai bayyana kansa nan kusa ba haka yake min ko a school ne muddin ya min laifi toh shi yake d'auke k'afa daga wajena, sannan Alhamdulillah Nana A ta watsar da sha'aninsa bata bari abin ya affecting d'inta sosai ba...." Ammah ta jinjina kai kana tace "Haka ne Siraj, barin k'arasa ciki mu gaisa sosai da sirkar tawa...." Siraj ya kuma murmusawa kana yace "Toh Ammah..." Lokaci guda Ammah ta shige ciki ta k'ofar bayan yayinda Siraj ya nufi sashen sa don canza kayan jikinsa zuwa masu sauk'i... Nana H dake matsan hawaye cikin sauri ta take masa baya.... Yana k'ok'arin zame rigar jikinsa Nana H ta banko k'ofar ta shigo.... Shaye da mamaki ya rik'e rigar a hannu yana dubanta... Cikeda tsananin mamaki yake furta "Ke...! Lafiyarki, wai meke damunki.... Wani kuka ya kuma taso mata jin irin kalaman da a yanzu Uncle ke mata wanda sam a baya baya mata irinsu.... Cikin kuka take fad'in "Uncle did you hear yourself now... Uncle kaji yanda kake min magana, tun kafin ka aureta ta rabamu dakai, and you know what hurts me the most...... You lied to me, kace min ba budurwarka bace and I over heard your conversation with Ammah... Uncle har ka fara b'oyemin abubuwa.....?" Ta k'arashe cikin tsananin muryar kuka... Zura rigarsa Siraj yayi kafin tako dab da ita, cikin muryar kwantar da hankali ya soma magana... "Were you eavesdropping again? Ba na hanaki sauraren maganar da babu ruwanki ba.... Well tinda kinji, eh ina son Azeeza, I love her with all my heart like I've never loved anyone before..... Kuma ina fatan ta zamto abokiyar rayuwata..." Girgiza kai Nana H take cikin rashin yarda da abinda kunnuwarta ke jiyo mata kana tace "Uncle you might put her life in danger.... If you really love her then don't marry her.... Uncle kar ka mance irin iftila'in da suka faru baya.... Uncle do you want that tragedy to repeat itself..." Ta k'arashe tana girgiza kai hawaye naci gaba da zubo mata Zeenat ne ta fad'o zuciyar Siraj da abinda suka aikata shekaru hud'u baya shida abokansa wanda sam baison tunowa, cikin sauri ya finciko hannun Nana H yana mata wani irin mugun kallo da idanunsa da suka sauya launi yake fad'in "Kar na sake jin magana makamanciyar haka daga bakinki, you have no right to decide for me... Just get out of here, get out of my room...." Ya k'arashe yana fitar da ita daga d'akin da k'arfinsa.... Mamaki ya kuma cika Nana H, da gaske ita Uncle ke treating this way akan mace... macen ma low class irin Azeeza lallai idan batayi da gaske ba tana gab da rasa Uncle Siraj d'inta.... Bata koma cikin gidan ba ta wuce garden zuciyarta naci gaba da mata k'una tana tunanin hanyar da zata b'ullawa lamarin... Siraj kuwa dafe kansa yayi yana tuno yanda ya tilasta wa Zeenat aurensa yayi amfani da k'arfin dukiyarsa da ikonsa ya tilastawa mahaifin Zeenat aura masa Zeenat.... Zeenat bata sonshi haka ya aureta.... Amma babu shakka saurayin da take so shi yayi ajalinta tinda shi suka tadda da ita, shi kuma saurayin sun kashe sa ba tareda bincike ba wannan dalili bazai tab'a barin Siraj ya huta ba idan ya tuna ran saurayin Zeenat da suka d'auka shida abokansa... But what if shi saurayin shine ya kashe Zeenat...? Take b'angare na zuciyarsa ta basa amsa da baku da laifi fansan ran matarka ka d'auka.... A hankali ya fuzar da iska kafin ya shirya cikin k'anan kaya ya nufi sashen Ammah yanda ya samu gaba d'aya sun saka Azeeza a tsakiya kowa na nan nan da ita, da alama itama tana jin dad'insu ta d'an saki jiki dasu... Murmushi Siraj ya saki soyayyar Azeeza na ratsa b'argo da tsokarsa... Jikinta ne ya bata Siraj yana bakin k'ofa aiko tana d'ago kai ta hangesa cikin shigar da bata tab'a ganinsa dashi ba, k'ananun kaya kyakkyawan murmushi saman kyakkyawan fuskarsa, kullum cikin suit take ganinsa yau da ya saka k'anun kaya sai ya mata kyau sosai k'uruciyarsa ta fito ba kaman yanda suit yake maidasa babban mutum responsible ba.... Waving ya mata had'i da kashe mata idanu.... Sam bata kulada Nana A dake faman zuba gefenta ba.... Sai sannan Nana A takai dubanta ga k'ofa nan taga Uncle Siraj tsaye yana sakarwa Azeeza murmushi, murmusawa Nana A tayi salon soyayyarsu na burgeta.... Sallama yayi ya shigo parlorn Ayiya na faman masa tsiya ya wani shasshanyewa... Wajajen biyar Siraj ya umarci Azeeza da ta tashi ya kaita gida, Nana A kam bata ma so tafiyar Azeeza ba don wani k'awancene ke shirin shiga tsakaninsu.... Ammah kuwa shopping bag babba ta sakawa Azeeza atampa super da leshi mai kyaun gaske had'ida turare Arab oud mai kyau da tsada... Sam Azeeza tak'i amsa saida Siraj ya amsa yace zai bata a mota.. Dole tayiwa Ammah godiya kafin ta masu sallama suka fice... Har bakin k'ofa Nana A da Ayiya suka raka Azeeza, Ayiya bata daina yiwa Siraj tsiya ba tana fad'in "Haka mijin naki yake kaman mai juju shi kad'ai yayita b'ata rai... Allah yaso ke ba irinsa bane...." Murmushi kawai Azeeza keyi yayinda Siraj ke raka Ayiya da mugun kallo, matar sosai ta tak'urawa rayuwarsa, shi baiso ma ta sake da Azeeza... Nana H daga yanda take zaune ta hangesu, lokaci guda taji kuka na kuma zuwa mata... Take ta soma baiwa kanta k'arfin gwiwa.. "You're strong and tough Nana H....." Bata kai aya ba kukan ya kuma zuwa mata ganin Siraj da kansa ya bud'ewa Azeeza k'ofa... Lokaci guda taci gaba da fad'in "But is okay to cry when you hurt... Azeeza you'll be next, I promise..." Tana ida fad'in haka tasa kai ta wuce cikin gida had'ida fad'awa d'akinta ta kulle gaba d'aya..... *** "So yaya kikaga in-laws d'in naki...." Ya fad'i sanda yake sharan kwana D'an kallonsa tayi had'i da kauda kanta ga duban window kana tace "Your are so kind.... Guda d'aya ce dai bata yo halinsu ba I guess halinka tayi, don itama ta iya wulak'anta mutane, and is like jealous of you...." D'an dubanta yayi gajeren murmushi saman fuskarsa had'ida girgiza kai kana ya maida dubansa ga kwalta yace "Hey am I that tyrant... C'mon don't be rude...." Tab'e baki ta kuma yi ba tareda tace komai ba... Siraj yaci gaba da fad'in "Haka Nana H take and especially akaina saboda basu san wani uba ba sai ni, shak'uwata da ita tun tana k'arama ya samo asali so sai take ganin kaman idan nayi aure matar will steal me from her kin gane... Amma tanada kirki sosai itama, and I'm pretty sure you'll soon get along with her too..." Cikin sauri ta shiga girgiza kai kana tace "No no I don't wanna get along with her.." Ba tareda ya dubeta ba murya cikeda umarni yace "You must cos she's your husband's fav...." Girgiza kai kurum Azeeza tayi kana tace "Stop fooling yourself I'm not your wife..." Murmushi ya kumayi kana yace "In the future..." Girgiza kai kurum tayi don ta soma sabo da halin Siraj Lokaci guda ta shiga Juya maganganunsa akanta, Nana H bata so yayi aure, bata son ganinsa da mace, tabbas akwai wani b'oyeyyen Al'amari da ya shige duhu... Tayi nisa duniyan tunanin sanda taji muryarsa yana fad'in "We are here..." Sai sannan ta kula har sun iso Siraj ya iya falfala gudu a mota sam bai ganin nisan unguwannin Abuja... Hannu tasa zata bud'e marfin motar kafin taji Siraj ya Kira sunanta Juyowa tayi tana dubansa yanda ya kafeta da madaidaitan idanunsa masu yalwan suma, gabanta yayi wani irin fad'uwa lokaci guda ta sauk'e idanunta k'asa Murmushi Siraj yayi don abinda yake son gani kenan if she feels something for him.... shopping bag d'in da Ammah ta bata ya mik'a hannu backseat ya d'auko kana ya mik'a mata D'an kallonsa tayi had'i da mak'e kafad'a "Why...?" Ya furta yana dubanta "Ka maida Ammah kayanta Barrister zaiyi fad'a Siraj ya d'an gyara zamansa kana yace "Bzaiyi fad'a ba cos soon zan fad'a masa about us, and idan baki karb'a ba Ammah zatayi fushi, ki karb'a kinji.... Shed'an ne mai maida kyauta..." D'ago idanu tayi tana dubansa taga murmushi saman fuskar sa, a hankali ta mik'a hannunta ta karb'a kana tace "Na gode Sir...." Har ta fice daga motar Siraj bai bar wajen ba saida ta isa k'ofar gida ta jiyo muryarsa yana fad'in "Banda latti, and my coffee should be ready before my arrival.." Murgud'a masa baki tayi kana tasa kai ta wuce... Ya rakata da kallo murmushi mai bayyan hak'wara saman fuskarsa kana ya d'an bud'e murya ganin ta bud'e gate zata shige yace "See you tomorrow...." Bata amsa sa ba sai waiving da ta masa had'i da sakar masa murmushin yak'e... A hankali ya furta "I love you...." Kafin ya tada motarsa ya bar wajen... Cak Azeeza ta tsaya jiyo sautinsu da tayi suna magana cikin fad'a.. Nasaar yaci gaba da fad'in "Because of your selfishness kana neman jefa rayuwar k'anwarka cikin garari, kan wani banzan revenge naka, you don't even care ko meye Siraj zai aikata da k'anwarka.....!" Cikin tsananin d'aga murya da huci Junaid yake fad'in "You shut up, and don't you dare raise your voice on me... Who the hell do you think you're, just because you helped me out, sai kayi tunanin zaka shiga rayuwar mu nida k'anwata and think you can decide for us... Azeeza is my sister she's my sister, and I know her well, nasan bazata tab'a yin abinda kake fad'i ba.... I raised her well nasanta nasan abinda zatayi nasan wanda bazatayi ba... Na fad'a maka ka ajiye kishinka a gefe don ni na saka Azeeza tayi playing idiot d'in I know she'll never fall for him....!" Ya k'arashe yana tsananin huci... Jinjina kai Nasaar yake shima d'in hucin yake kana yace "Fine... Naji, amma ka sani I love Azeeza I love with all my heart, and I can't sit back watching you ruining her life because of your stupid revenge, I'll protect her koda da rayuwana ne...." Yana ida fad'in haka yasa kai ya fice daga d'akin yana huci... Azeeza dake lab'e bakin k'ofar kuka ne yazo mata sosai, tabbas Siraj na tsananin buk'atarta ta lura wani ne mai laifi yake b'uya a bayansa, kafin Yayanta ya cimma burin fansarsa kan Siraj dole tayi iyaka k'ok'arinta wajen kub'utar dashi.... Lokaci guda ta wuce d'akinta batama bari suka san ta dawo gidan ba.... *** *Misau* Batasan ya shigoba sai hancinta da ya jiyo mata k'amshin turarensa, a hankali ta juyo da dubanta garesa... Murmushi ne kwance saman fuskarsa kana ya soma takowa ya shigo. a hankali ta d'an mik'e daga kwancen da take ta zauna.... Ahidjo ya k'araso gefenta ya zauna had'i da k'ura mata idanu.... Kallon da yake mata har saida ya bata tsoro don kallon yayi yawa har tayi tunanin ko wani abu ne a fuskarta.... Ganin tana shafa fuskarta alamun tana neman abinda yake kallo yasa Ahidjo d'an murmusawa kafin ya kamo hannayenta ya rik'e A hankali ya furta "Ki barni na kalli fuskarki ta yuwu kallon k'arshe kenan, gobe zan tafi Deejoh....." Gabaki d'aya yinin yau kalamansa karyar mata da zuciya suke, gaba d'aya ta koma sukuku... Girgiza masa kai tayi kana tace "Yaya zaka dawo, nasan zaka dawo ka tafi dani kamar yanda kace...." Ta k'arashe k'walla na ciko idanunta Murmushin k'arfin hali yake yana dubanta lokaci guda ya saka 'yan yatsunsa yana share mata hawayenta yake fad'in "You're so special here..." Yayi nuni da k'irjinsa kafin yaci gaba da fad'in "You're so special to me Dee, and last night was something special.... just unforgettable.... You're now part of me Dee..." Kuka kawai Deejoh take dukda ba gane abubuwan da yake fad'i take ba, lokaci guda take girgiza masa kai kana tace "Dan Allah ka min magana yanda zan gane, kace min zaka dawo kaji Yaya...." Matso da ita yayi ya rungume cikin jikinsa had'i da kwantar da kanta saman k'irjinsa tana jin bugun zuciyarsa yanda yake da sauri da sauri... A hankali ta lumshe idanu tsananin k'aunar mijinta na fuzgarta Saida yaji kukan nata ya lafa cikin k'irjin nasa kafin yaci gaba da fad'in "Dee promise me idan na tafi bazakiyi kuka ba, kinsan idan kikayi kuka daga duk yanda nike zanji...." Bata iya cewa komai ba sai jinjina masa kai da tayi Ahidjo yaci gaba da fad'in "I'll miss you Dee, so much.... Ki kula min da kanki kinji...." Nan ma kai kurum ta jinjina masa a hankali kafin tace "Toh yaushe zaka dawo...?" Tayi tambayar cikin sark'ewar murya "Just two weeks sati biyu kawai zanyi insha Allah..." Jinjina kai ta kuma tana goge ragowar hawayen idanunta, amma cikin zuciyarta kukan zuci take shid'inma da zai samu yayi kukan da wani abin ya ragu masa sabida yanda yake ji can k'asar zuciyarsa, a hankali ya gyara masu kwanciyarsu ya d'an kishingid'a yayinda Deejoh ta zamto samar k'irjinsa... A haka Innah ta lek'o da zummar shigowa saidai ganinsu a haka da tayi ya sata fasa shiga d'akin, a hankali ta koma sihirtaccen murmushi saman fuskarta.... *** *Damaturu* Baje-baje Daddah tayi tsakar gida tana basu labarin gudun data kwasa, idan taji an buga k'ofa sai ta soma dafe-dafen mik'ewa tana neman hanyar gudu saidai taji ashe almajirai ne masu bara sai ta koma ta zauna tana haki... Mairo na dariya take fad'in "Wllhi Daddah naji ina son auren mai saka uniform ko don saboda ke...." "Ya kawo min raini ubansa zanci ke nifa ba tsoro nikeji ba, shi sojan ma da nake shayi nasan ana masu alluran mahaukata ne shiyasa, kuma idan wannan allurar ta motsa toh fah basu sanin mi suke yi, wato rabona da irin wannan gudu tun ina matashiya 'yar shad'aya da na sayin fad'an wata k'awata ana ce mata Dumba, ta zubda wata yarinya tallanta ni daga zuwa aka saida min fad'ar sile guda don ni da saidai na sayi fad'a ba'a nemata, toh shine yayan yarinyar mafarauci ne ya kwance mana karnukansa na farauta nayi gudun famfalak'i.... " Umma Marie mai zatayi banda dariya... Mairo ma dariyar take kana tace "Aiko ni kika bari da tsaro zance ma k'aton arne wllhi har k'aryata ta k'are na rasa mai zance masa, gashi harda masa kwtancen k'arya don ce masa nayi ba shagon su Dakura muke aiki ba...." Daddah ta bud'e baki tana dariya kana tace "Ai wllhi gobe gobe zan nemi gidansu wancan kututturiyar don sai naga yaya jikinta ya kwana..." Gaban Umma Marie ya fad'i jin fad'an Daddah bamai k'arewa bane... Cikin lallama tace da Daddah "Ni kuwa Daddah da kin hak'ura ma had'u da ita dai a centre..." Daddah tace "Inaa ai bataci ta fitowa Santa (centre) ba yanda ta lallasu, gwara muje mu mata gaisuwan ban gajiya, ko ya kikace Mairo ta..." Lokaci guda Mairo ta jinjina kai tana fad'in "Haka ne Daddah ta..." Umma Marie dai tsoro lamarinsu ya soma bata ta soma tunanin idan zata iya ci gaba da zama da wad'annan mutane masu sayo fitina da kud'insu..... *** A ranar cikin jikin juna sukayi bacci shida Deejoh, wani irin bacci mai cikeda shauk'i da ni'ima ya had'u da sanyi maras cutarwa dake kad'awa a garin, Asubahin fari kafin ayi kiran farko Ahidjo ya farka yaji Deejoh cikin jikinsa, wayarsa ya lalumo ya haske fuskar Deejoh dake bacci da ita, a hankali ya saki murmushi kafin yakaiwa lips d'inta sunba, ganin ta d'an soma motsawa ya sanyasa saurin gyara mata kwanciyarta kafin ya mik'e a hankali ya nufi d'akinsa... Cikin sauri ya shiga kimtsa kayayyakinsa.... Ya jima yana duban Deejoh rik'eda jakarsa kafin ya k'araso ya shafi fuskarta a hankali, turarensa da yake amfani dashi ya ajiye mata gefenta kafin a hankali ya furta "I'm sorry Dee... I'm sorry, Allah yaso saduwarmu...." Ya k'arashe muryarsa na tsananin rawa, a hankali ya mik e bayan ya kuma gyara mata bargonta kafin ya rataya jakkarsa ya fice.... *SameenaAleeyou📚**FUSKA UKU*🏮 *35* *©Sameena Aleeyou...✍🏽* A hankali Deejoh ta bud'e idanunta, nan taga haske ya haske labulen d'akin alamun ta makara sallan asuba.... Waigawa gefe da gefenta tayi taga bataga Ahidjo ba, k'irjinta yayi wani irin yankewa ya fad'i.... A firgice ta mik'e k'irjinta naci gaba da bugawa ta nufi sashen Ahidjo, cikin sauri ta dad's d'akinsa gabanta naci gaba da fad'uwa tana addu'an Allah sa mafarki take bai tafi ba.... Gwiwoyinta ne sukayi wani irin sanyi sanda ta tura k'ofar d'akin taga babu shi.. Babban abinda yafi d'aga mata hankali shine bata ga kayansa ba... Take wasu irin hawaye suka shiga zarya a idanunta.... Da gaske ya tafi, da gaske Yayanta ya tafi... Kuka sosai take sanda ta nufi waje k'ofar gida ta hangi k'asar bishiyar da yake paka motarsa babu motar..... Bata san sanda ta tsuguna a wajen ba ta shiga rusa kuka mai dalili.... Baffah da Innah da sukayi jigum-jigum a k'ofar Baffan, don tunda zai fita sallan asuba yaga bai ga motarsa ba sannan bai gansa a sahu a masallaci ba yasan akwai wani abun, koda ya dawo gida ma saida ya duba d'akinsa ya tarar baya nan... Tun daga nan yasan Ahidjo tafiya yayi.... Jiyo kukan Deejoh da Innah tayi ya sakata kamo bakin zaninta wani sabon kuka na taso mata.... Baffah baice komai ba sai girgiza kai da yayi tausayin Deejoh na shiga cikin zuciyarsa, shi dama yasan za'a rina, don mai hali baya canza hali, Aliyu bazai canza halinsa ba, tabbas yayi kuskuren aura masa Deejoh.... *** Zaune yake a office yana duba takardun Estates d'in da ya saya recently a Jabi, wayarsa ya ciro cikin suit pocket d'insa kafin ya shiga neman layin Nasaar.... Nasaar dake zaune office d'insa idanunsa sunyi jazir ya k'urama waje guda idanu ba sai ance maka tunanin wani babban abin yake ba, lokaci zuwa lokaci yake huci shi kad'ansa yana murza pen d'in dake hannunsa da iyaka k'arfinsa, tsanin matse pen d'in da yake har saida pen d'in ta fashe a hannun sa lokaci guda yaji masa ciwo a hannunsa, sai sannan ya kula da wayarsa dake faman ruri.... D'an matse hannunsa mai d'igan jini yayi kafin ya d'aga wayarsa nasa, ganin Siraj ne mai kira ya dad'a bak'anta ran Nasaar, kaman bazai d'aga ba don kira na uku kenan.... A hankali ya furta "Imbecile..." Kafin ya d'aga wayar... Daga d'aya b'angaren Siraj ya sanar dashi yana nemansa ba tareda ya kawo komai cikin zuciyarsa ba... Azeeza na zaune gaban table d'inta tana wasu 'yan danne-dannenta cikin computer Nasaar yazo wucewa zai shige office d'in Siraj.... Cak ya tsaya yana duban Azeeza idanunsa sun kad'a sunyi jazir, shi kad'ai yasan irin k'unan da zuciyarsa ke masa, musamman idan ya tuna jiya hotel ya gansu itada Siraj.. Jikinta ne ya bata ana kallonta aiko tana d'ago kai sukayi idanu hud'u, fuskar nan nasa tamkar bai tab'a dariya ba.... Gaban Azeeza ya yanke ya fad'i, takai dubanta ga hannunsa dake d'aure da tissure paper da alama ciwo yaji, k'irjinta ya kuma bugawa, tama kasa cewa komai gaba d'aya, bata tab'a ganin Nasaar cikin irin wannan yanayi ba.... Ta yunk'ura zata mik'e cikeda kulawa, saidai kafin ta k'arasa mik'ewa Nasaar ya shige office d'in Siraj.... Ganin Nasaar ne ya shigo yasa Siraj mik'ewa yana kuma bubbud'e documents d'in dake hannunsa yake fad'in "Nasaar are you sure takardun nan sun cika, banso daga baya azo ana samun matsala kaga ba k'aramin kud'i aka zuba....." Aya yayima kalamansa jin sam Nasaar d'in bai tareda shi... D'ago idanu Siraj yayi yana dubansa kafin yace "Lafiya? Is everything alright....?" Bai kai aya ba Nasaar ya katsesa da fad'in "Nothing is alright Siraj...." Ajiye takardun hannunsa yayi yana duban Nasaar d'in cikeda mamaki kana ya d'an girgiza kai yace "Sorry ban gane ba... Mai kake nufi, badai kan Estates d'in bane koh...." Ya k'arashe yana duban Nasaar d'in dake faman huci tamkar mai shirin kai masa naushi... Nasaar yaci gaba da fad'in "Siraj, don't you try that with Azeeza....." Cikeda gargad'i yayi maganar.... "Wait what did you say... What do you mean Nasaar, meye kake fad'i....?" Cewar Siraj dake duban Nasaar d'in cikeda mamaki.... Matsowa Nasaar yayi dab da Siraj yana bud'e idanunsa yake ci gaba da fad'in "Nasan ka san abinda nake nufi Siraj, don't try it with Azeeza...." Girgiza kai Siraj yayi lokaci guda fuskarsa ta sauya kafin ya soma fad'in "I've no idea what you're talking about, yes I admit I love your sister in-law, amma bansan mai kake nufi da kar nayi trying da Azeeza ba... What the hell was that...?" Murmusawa Nasaar yayi da gefen bakinsa kana yace "Come on Mr President, you know I know you well, and I know all of your secrets cos I'm your lawyer,...." Cikin sauri Siraj dake faman huci ya katse Nasaar da fad'in "You shut up already! get out of here... Get the hell out of my office, now!!!" Ya k'arashe yana nuni da k'ofa wa Nasaar.... Girgiza kai Nasaar yayi had'i da murmushi da gefen bakinsa kana yace "You can't boss me when it comes to our little secret you know.... So tell me itama abinda kayi da sauran matan kake shirin yi da ita,...?" Ya kuma murmusawa kafin yaci gaba da fad'in "You've always been a womanizer, ko k'arya ne...? Kowa na ganinka sallah sallah while on the contrary kai ba mutumin da ake zato bane.... Duk 'yan matan da kake nema kafin ka kai ga aurensu kake lalata masu rayuwa, bansan mai ya kashe sauran but zaka k'aryata akan Zeenat...? Zaka k'aryata cewa baka aikata hakan da Zeenat ba, nida kai munsan Zeenat committed suicide because she never loved you and you forced her tayi zina dakai kafin aurenku, you even threatened her idan bata amince ba zaka kashe saurayinta da take so take mafarkin aura.... A dalilin haka ta kashe kanta ko ba haka bane..." Girgiza kai Siraj yake kana yace "No Nasaar Zeenatu was murdered, bata kashe kanta ba.... Tsohon saurayinta ya kasheta...." Murmushi Nasaar ya kumayi kana yace "Siraj kenan, meyasa ka dage tsohon saurayinta shi ya kasheta, sabida baka so ka rayu with the guiltiness ya ringa eating d'inka alive.... Sabida kai da abokan ka kunyi tarayya wajen murk'ushe rayuwar tsohon saurayin Zeenat wanda bashida laifin komai.... Sannan da mahaifin Zeenat ya shigar da k'ara ni ne lauyan da na tsaya tsayi da fata har aka kori shari'ar akayi watsi da ita aka kuma rufe maganar harta family d'inka basu san da zancen ba.... Siraj ni ne nan na rufe sirrin FUSKA UKU ya rufu babu wanda ya kuma ji har rana mai kaman ta yau... Zeenat ta rasa rayuwarta because of you Siraj, sannan kaida abokan ka kuka kashe JUNAID tsohon saurayin Zeenat...." Siraj dake zuban hawaye sabida laifuka da dama da ya aikata a baya cikin sauri ya rik'o hannun Nasaar kana ya soma fad'in "Nasaar you know I've changed completely and wllhi ni ba Siraj d'in da ka sani a baya bane... I love Azeeza with my heart, kuma itama wllhi tana sona.... Nasaar dan Allah kar ka zama sanadiyan rasa farin cikin da nake shirin samu....." Fincike hannunsa Nasaar yayi kana yace "No Siraj, ai laifukan daka aikata zaiyi wuya Ubangijinka ya barka ka sami farin ciki a wannan rayuwar taka, har sai ka biya laifukan da kayi a baya, shin banza Allah yake d'auke rayuwar duk 'yan matan da kake nema.... Idan baka sani ba ka sani, hakkin Zeenat da Junaid sune suke binka.... Siraj I'm sorry bazan iya baka Azeeza ba, baka auren Azeeza sanin ko kai waye tamkar cin amana ne, na sani mu dukanmu masu laifi ne... Bazan iya ba sabida kai ba tsarkakke bane....." Ya k'arashe cikin tsananin rawar murya idanunsa sunyi rau-rau tsananin soyayyar Azeeza na fizgarsa, b'angare na zuciyarsa yana tuna Bulama shi ya tsunduma sa cikin rayuwar Siraj... Cikin sauri ya fice daga office d'in yana mai k'ok'arin saita kansa.... Gijif Siraj ya zauna cikin kujeransa numfashinsa na fita da k'yar, dafe kansa ya kumayi wasu hawaye na kuma zubo masa, Nasaar ya d'aga masa mik'in da ya kasa warkewa cikin zuciyarsa.... *** Da k'arfin gaske Junaid ya bugi wheelchair d'insa yana wani irin huci yake fad'in "Sabi'u why... Yaya akayi hakan ta kasance, saida ka tabbatarmin baza'a sami failure ba gashin an samu.... Na rasa chance d'ina..." Shafa kansa Sabi'u yayi kana yace "Junaid, wllhi canza hanya yayi, duk a tunani na ta Jos zaibi ashe ta Kano yabi.... Amma kar ka damu friend idan ya tsallake wannan bazai tsallake gaba ba I promise you....." Huci kawai Junaid keyi kafin ya kashe wayar ba tareda ya kuma furta koda kalma ba.... Shi kad'ai yake faman tururi yana hura hanci, idan ka tsaya gefensa zaka iya jiyo turirin da yakeyi.... Da k'arfin gaske yayi jifa da wayar yana furta "Damn it...! You damn imbecile da hannuna ya kamata na kashe ka..... Kayi escaping wannan amma gaba I promise you bazaka sha ba.... I'll face you man to man even if I'm on this damn chair...." Ya k'arashe yana duban kujeran nasa da hannayensa... Nana A da Aunty Larai dake tafe suna zaga foundation d'in suka jiyo kaman sauti daga office d'in Junaid... Nana A ta dubi Aunty Larai tace "Kina ji kuwa....?" Ta k'arashe tana nuni da office d'in Junaid... Cikin sauri Aunty Larai ta jinjina kai kana tace "Naji Asma'u, sauri muje mu duba shi...." "Yeah sure, let's go....!" Nana A ta fad'i cikin sauri sanda suka nufi office d'in Junaid..... Junaid yana jiyo sautin takalmansu yayi saurin saita kansa tamkar yana aiki.... K'wank'awasa k'ofar sukayi suna masu neman izinin shiga.... Take yayi saurin tura kekensa ya k'arasa ya d'au tarwatsttsen wayarsa ya had'a kafin ya basu izinin shigowa... Kallon kallo Aunty Larai da Nana A suka shiga yima juna ganin lafiya suka tadda Junaid... Da sakin fuskarsa suka gaisa, kafin Aunty Larai ta fice ganin babu abinda ke faruwa... Nana A kuwa k'uri ta masa tana karantarsa bayan Aunty Larai ta fice... D'an dubanta yayi had'i da d'aura murmushi saman fuskarsa kafin yace "Are you alright Gorgeous.... Akwai wani abu ne.....?" D'an girgiza kai tayi had'i da tab'e baki kana tace "I know you're not well, I can see it from your eyes... Meke faruwa...?" Kauda fuska Junaid yayi fuskar Kawunta Siraj na masa gizo cikin idanunsa, a kullum idan ya kalli Nana A fuskar Siraj yake gani k'arara a tattareda ita sai yaji tamkar ya murk'usheta ko tsananin hatred d'in da yake cinsa ciki zai ragu.... Girgiza mata kai yayi kafin a hankali ya furta "Babu komai Asmah, I'm.... Just fine..." Murmushi Nana A ta kumayi kana tace "Ba gaskiya kake fad'i ba, ni na tabbata akwai wani abu...." Take ya k'ura mata dogayen idanunsa masu cikeda k'warjini yana kuma tuno abubuwan da suka faru dashi.... A hankali kuma ya kauda kansa gefe kana yace "Fad'a maki bashida amfani sabida babu abinda zaki iya min....." Nana A tayi jigum tana dubansa cikeda tausayawa kafin ta k'araso ta zauna kujeran gefe dashi kad'an kana tace "Dan Allah ka fad'a min abinda ke damunka maybe I can help...." Karkatowa sosai Junaid yayi yana dubanta kafin ya kuma girgiza kai yace "Asmah there's nothing you can do about it.... Just don't insist please, ki tafi office d'inki dan Allah I want to be alone..." Cikin sauri ta katse sa da fad'in "Bazan tafi ba sai ka sanar dani abinda ke damunka, a koda yaushe idan ina cikin k'unci ko damuwa nakan yi sharing dakai, kana d'ebe min kewa kana bani shawarwari wanda suka sakani naji relief, so don me ni zan kasa yi maka irin abubuwan da kake min..... Dan Allah ka sanar dani meke damunka kaji..." Tsareta da idanu yayi yana dubanta kafin ya soma fad'in "Na fad'a soyayyar wacce batasan inayi ba kuma koda tasan inayi tafi k'arfina nida ita are from different world... Bazata tab'a sona back ba...." Ya k'arashe yana mai kafeta da idanunsa... Tunda ya soma magana gabanta ke fad'uwa.... A hankali ta sadda kanta k'asa kafin ta d'ago tana dubansa kana tace "Kana nufin kanada nakasa ita batada nakasa,...? Meyasa baka sanar da ita ba....?" Shiru ya d'anyi na giftawan lokaci kafin yaci gaba da fad'in "Ba wannan nake nufi ba,..." Cikin sauri ta taresa da fad'in "Toh mai kake nufi...?" Saida ya kuma zuba mata idanu kafin yaci gaba da fad'in "Ina nufin ita 'yar masu kud'i ne, ni kuma talaka ne wanda bashida komai kuma bashida kowa..." Gaban Nana A yaci gaba da bugawa cikin sauri, zuciyarta na fad'a mata wasu abubuwa... K'ok'arin saita kanta tayi kana ta soma fad'in "Ka gwada fad'a mata koda zatayi rejecting d'inka, shi soyayya duk babu ruwansa da wannan, kar kayi giving up so easily, ka sanar da ita what you really feel about her... Kar mu dinga saurin cire tsammani daga rahamar ubangijinmu... Ka fad'a mata please...." A hankali ya saki murmushi kana yace "Haka ne Asmah, na gode da shawarwarinki kuma insha Allah zan fad'a mata... Tak'aitaccen murmushi ta kuma sakar masa kafin tace "I'll get back to work, see you later..." Jinjina mata kai yayi yana binta da kallo murmushi saman fuskarsa, har ta kai k'ofa ta jiyo muryarsa ya ambato sunanta cikin wata irin siga.... Karkatowa tayi tana dubansa kafin Junaid yaci gaba da fad'in "What if you are my problem... What if you are the one, will you accept me....?" Ya k'arashe baya ko k'yafta idanu daga duban nata... Kasa furta komai tayi sai kallon data bisa dashi, take kuma ta sadda kanta k'asa, a hankali ta furta "Excuse me...." Daga haka ficewa tayi ba tareda ta kuma cewa komai ba... Office d'inta ta fad'a kalaman Junaid suna kuma mata yawo a kwanya.... Batayi shirin soma sabon relationship ba, after what happened to her recently, ko warkewa daga mikin da Lamid'o ya haifarwa zuciyarta batayi ba, bata tunanin zata kuma afkawa soyayya nan kusa, sannan bazataso tayi hurting Junaid ba, bai cancanci haka ba, he went through a lot in life... A hankali take shafe idanunta da duka hannayenta biyu had'i da kumshesu, lokaci guda take furta "Ya Allah gani gareka....." *** Ammah kawai Ahidjo ya samu a parlor tana kallon tashan Discovery Family, nan suka gaisa cikeda kulawa Ammah na tambayarsa yaya aiki.... Ahidjo ya amsa da "Lafiya lou Ammah, mun sameku lafiya...?" "Lafiya lou.... Ai wannan aiki naku akwai wahala ace mutum yau yana can gobe yana nan...." Murmusawa Ahidjo ya kuma yi kana yace "Wllhi fah Ammah, aikin d'ansanda babu sauk'i..." "Toh Allah shi taimaka, ka shiga ciki ka sami matar taka tana nan d'akinta, ince tasan da dawowar taka.." Girgiza kai Ahidjo yayi alamun a'a kana yace "Surprising d'inta nake so nayi...." Ammah ta kuma murmusawa kana tace "Yayi kyau, wayaga masoya.. Maza haura sama ka sameta...." Fuska cikeda murmushi ya mik'e kana yace "Toh Ammah..." Kai tsaye ya nufi benen yana mai marmarin ganin fuskar matarsa.... A hankali ya kama handle d'in k'ofar ya murd'a, can ya hangeta kwance tana sharan baccin data saba babu sallah balle salati.... Murmushi Ahidjo ya saki yana shak'an k'anshin Nana H da yayi missing... A hankali ya k'arasa shigowa d'akin kafin ya nufi jikin gadon... Hankali kwance take baccinta sanda ya zauna gefenta yana mai shafa kyakkyawar fuskarta.... *SameenaAleeyou📚**FUSKA UKU*🏮 *40* *©Sameena Aleeyou...✍🏽* Jigum Azeeza tayi a d'aki tana tunanin rayuwa hawaye na ci gaba da kwaranyo mata, su kuma wace irin rayuwa suka tsinci kawunansu ciki, ace mutum baida buri sai na d'aukan fansa.... Kuka mai k'arfi ya kuma kufce mata hoton iyayensu ta janyo cikin kayanta ta shiga kalla tana shafawa hawaye naci gaba da kwaranya mata, a hankali take furta "Meyasa kuka tafi kuka barmu a wannan duniyar mai cikeda son zuciya da tsananin mugunta.... Meyasa kuka barmu... Why....?" Ta k'arashe kuka sosai na kuma kufce mata, da sauri ta rungume hoton a k'irjinta tana mai ci gaba da cizgan kuka... A halin yanzu batasan mai takeji gameda Siraj ba saidai iyakacin abinda ta sani shine bazata tab'a cutar dashi kuma bazata bari a cutar dashi ba muddin tana raye kuma tanada halin yin hakan, lokaci guda ta tuna yau a office da kansa ya fita ya kawo mata abinci k'arewa ma barin office d'insa yayi ya dawo nata dukda ba gwananin hira bane amma tana enjoying company d'insa yanda wasu qualities na maza wanda ba ko wani namijin bane ke dashi, sannan she can't deny he's special and unique in his own ways.... A hankali ta kuma sakin murmushi tana tuna kalan murmushinsa wanda yakeyi da gefen bakinsa had'ida d'aga gira d'aya sama.... A hankali ta lumshe idanunta kana ta gyara kwanciyarta don ta tabbata tunanin Siraj zai taimaka mata tayi bacci.. *** Washe gari koda Nasaar ya buk'aci su tafi office tare k'in aminta tayi domin ji take a halin yanzu sam ko k'aunar kasancewa dashi batayi, a ganinta shike dad'a tunzura Junaid kan k'udirinsa instead ya nusar dashi hanya a matsayinsa na lauya, sai yanzu take ganin sam Nasaar bai cancanci aikinsa ba, cin amanar k'asa ne sannan wulak'anta karatu ne.... Bai tilasta mata binsa ba saidai har k'asan zuciyarsa yaji zogin abinda ta masa, ta gwammaci ta shiga motar haya ta tafi office akan ta shiga motarsa, bayan Siraj da kansa yake dawo da ita, sosai wannan abu yayiwa Nasaar ciwo.... *** Isowarsa gidan kenan ya hangi Siraj na k'ok'arin shiga mota cikin shigarsa ta zuwa aiki, fasa shiga motar Siraj yayi had'i da tsayawa yana duban motar Ahidjo har ya k'araci paka motar, domin sam Siraj baisan Ahidjo ya dawo gari ba... Cikin takunsa mai cikeda aji ya nufi yanda Ahidjo ya ajiye motarsa dai-dai sanda Ahidjon ma ya fito daga nasa motar, handshake sukayi kafin Siraj yake tambayarsa yaushe ya dawo... Dubansa kawai Ahidjo keyi yana mamakin Siraj bazai tab'a canzawa ba yasan abu sai yayi kaman bai sani ba bacin haka ai gidan nan ya soma sauka dawowarsa yasan ko Nana H bata sanar dashi ba Ammah zata sanar dashi.... Nan ya sanar dashi kwana biyu kenan da dawowarsa, sam Siraj bai sani d'inba da gaske don yanzu abubuwa sun masa yawa a office sannan uwa uba soyayyar Azeeza da ke neman d'auke hankalinsa gaba d'aya.... Gaisawa suka d'anyi sama-sama don already yanada appointment da wasu clients da suka iso Nigeria a daren jiya... Sallama yake k'okarin yiwa Ahidjon kafin Ahidjo ya kamo hannunsa sosai kana yace "Siraj ina so muyi magana dakai and it's about Lamid'o our bro..." Karkatowa sosai Siraj yayi yana dubansa kana yace "Banida lokacinsa Heedj kuma banson jin komai gamedashi, now will you excuse me...." Ya k'arashe yana k'ok'arin rab'awa ta gefensa Mamaki ne ya cika Ahidjo, toh meye Lamid'o ya masa, meke faruwa...? Toh kodai ya sanar dashi halinda Lamid'o ke ciki ne...? Amma kuma Lamid'o ya rok'i alfarmarsa kada ya sanar da kowa iyakacin sak'on da ya bada a fad'iwa Nana A shine yana tsananin k'aunarta da duka zuciyarsa.... Har Siraj ya soma tafiya Ahidjo yayi saurin taresa da fad'in "Siraj what's all this, meye Lamid'o ya maka, kar ka mance we're brothers...." "Enough Ahidjo, na fad'a maka babu abinda ya had'ani dashi kuma banson jin komai about him...." "Even if he was kidnapped....?" Cewar Ahidjo cikin dakatar da Siraj d'in "I don't bloody care, k'aryar nasa ta nan ya fito kenan, ban fatan sake ganinsa balle a cikin gidan nan... kuma ban yarda kayi maganar Lamid'o wa niece d'ita Nana A ba, are we clear....?" Girgiza kai kawai Ahidjo yake cikin rashin yarda da kalaman Siraj lokaci guda yake huci dukda baisan abinda ya had'asu ba, a hankali ya kad'a kai kana yace "Very well, nima da yuwar bazaka sake gani na ba, but ko meye Lamid'o ya maka kar ka mance sadaukarwar da ya maka a baya.... Na barka lafia Siraj Laushi, sannan ka sanar da Nana A Lamid'o loves her, with all his heart.... Excuse me....!" Yana ida fad'in haka ya nufi motarsa ba tareda ya shige gidan ba yayi ficewarsa, Siraj ya bisa da mugun kallo kafin yayi gajeren tsaki ya shige motarsa shima..... Ahidjo na ficewa daga gidan ya nufi gida domin shiryawa gwara yayi maza ya k'arasa aikinsa don yasan idan Siraj yaga abinda Lamid'o ke shirin yi zai tabbatar Lamid'o worth his friendship kuma ya cancanci a basa auren Nana A, da haka ne kurum zai taimaka wa abokan nasa.... Sauri sauri yake shirin Nana H na biyedashi duk yanda yayi.... Ta kuma kamo bayan rigarsa tana hawaye kana tace "Are you really leaving.... Heedj kar ka tafi ka barni please, yaushe yaushe ka dawo dan Allah ace har zaka sake tafiya....?" Ta k'arashe cikin tsananin rawar murya... K'uri ya mata yana dubanta kafin ya rungumota cikin jikinsa, lallashinta yake yana mai ci gaba da fad'in "Sweetheart I thought you're used to this already, haba Nana ta ki bani k'arfin gwiwa please, kin rigada kinsan abinda zan tafi nema..." Jinjina masa kai tayi tana mai share hawayenta take fad'in "Hakane Heedj, you're the best Allah ya taimakeka ka dawo mana da Nana K safe and sound...." Hannayenta ya kama kana yace "Ameen sweetheart, don't ever forget how much I love you okay...." Jinjina masa kai tayi tana murmushi take masa addu'an kariya kana tace "You take care okay..." Shima jinjina mata kai d'in yayi had'i da manna mata peck gefen chick d'inta kana ya rataya jakkarsa.... Har mota ta masa rakiya tanai masa waving kafin yana wucewa ta komo cikin gida tamkar zata kifa da k'asa ta d'auki wayarta ta shiga dialing layin Nasaar..... Nasaar na ganin kiranta yayi saurin d'agawa dama ita d'in yake jira... "Kana jina, he just left the house get ready and don't you failed me, zan turo maka brand d'in motar in short kawai zan turo maka hoton motar right a way...." Bata ko jira cewarsa ba tayi saurin katse kiran tana k'ok'arin tura hoton motar Ahidjo... Da shike a speaker ya saka masu wayan shida Bulama suna gama saurare Bulama ya kece da wata iriyar dariya kana yace "Nana Hafsatu kenan ba don ke jinjin Mas'ud bane sai nace musanyenki akayi da nawa jinin, koda baki kashe shashashan mijin naki ba ni nan zan kashe maki shi, sannan zan kuma d'aura alhakin mutuwarsa a wuyarki tareda dalilai masu k'wari...." Ya kuma duban Nasaar kana yace "Aikinka yana kyau sosai...." Lokaci guda Bulama ya mik'e yana mai kiran yaransa.... Nasaar kuwa dafe kansa yayi yana tambayar kansa shin mai ya aikata.... *** "Sabi'u ban yarda Nana H tasan inada wata mata ba acan gida, na yarda da kai kuma nasan ko ban dawo ba zaka kular min da family na, akwai rayuwa akwai mutuwa shiyasa na sanar dakai gameda Deejoh...." Jinjina kai Sabi'u yake yana dubansa kana yace "Kar ka damu DT you can always count on my support, insha Allah...." Jinjina kai Ahdijo yayi had'ida masa godiya kana yace "Ni zan wuce yanzu Allah ya k'addara saduwarmu....." Jinjina masa kai kawai Sabi'u yayi kafin ya masa rakiya har wajen motarsa ya shige had'ida barin wajen.... jikin wandon Sabi'u 'yar k'aramar abin sauraren magana ne wanda daga can yanda Junaid yake ya saurari komai yanda duk Sabi'u da Ahidjo sukayi, a hankali Junaid ya shiga matse hannunsa yana tunanin harbi uku ya jiyo sanda yaje ceton Zeenat, wanda ya tabbata cikin FUSKA UKU ko wannensu harbi guda yayi mata... A hankali ya furta "Zaka mutu yau kaman yanda ka kasheta...." Tunda ya soma driving yake tsintar kansa da wani irin fad'uwar gaba, ga wani irin gudu da bai tab'a yin irinta ba shi yake falfalawa bisa hanyar, tafiya tsakanin Abuja da Yobe ba tafiya bane mai sauk'i kasancewar shid'in d'ansanda ne yasa duk checkpoint d'in da ya iso suna ganin ID d'insa suke sara masa su basa hannu, yawan checkpoints dake tsakanin Jos to Bauchi yasa basu cimmasa ba sabida tashin tashin na hankula da ake yawan samu bisa hanyar, sannan Bauchi to Damaturu shima akwai checkpoints sosai sabida Al'amarin tsaro dake bisa yankin.... Duk wannan tafiya da Ahidjo keyi baisan ana biye dashi ana farautar rayuwarsa ba, gari ya soma duhu sanda ya shiga garin Damaturu baisan ina ya nufa ba first saidai yasan hoton Nana H da Nana A dake tafe dashi zaisa ya samu nasaran abinda ya kawosa cikin yardar Allah tunda su duka ukun are identicals.... Basu cimmasa ba sai a garin ta Damaturu A dai-dai wani duhuwa ya hangi wata mota ta sha gabansa yayinda wasu k'artai suka nufo motarsa suna masa nuni da bingogi suke fad'in kada ya motsa.... D'aga hannayensa sama kurum yayi yana tambayarsu su fad'i mai suke nema daga garesa..... Fad'i suke idan yayi motsi zasu harbesa, lokaci guda d'aya daga cikinsu ya shige k'asar motar, Ahidjo yanaji suna k'ok'arin fasa wajen wucewar man fetur baida halin motsawa don sun pointing bindiga saitin kansa yana motsawa zasu harba.... Lokaci guda fuel ya soma kwarara, tabbas yaji warin fetur amma baiji k'aran zubanta ba sai wuta da ya kama lokaci guda.... Yanaji yana gani wuta na k'ok'arin had'awa dashi don har ya soma galabaita sanda ya soma k'ok'arin ceton kansa.... A dai-dai lokacin wasu mutane sanye da kayan Soji suka iso wajen don basa d'auki yayinda wad'ancan 'yan ta'addan suka gudu.... Sanda Sojin nan suka cirosa haki kawai yake yana k'ok'arin k'arasa cire rigarsa da wuta ya kama, farin fatarsa duk yayi bak'i sabida azaba... Suna cirosa kuwa motar ta kama gadan-gadan kan kace mai tai exploding.... Can gefe suka matsa suna kallon yanda motar ta kama da wuta... Sai sannan Ahidjo ya sami zarafin d'ago kai yana dubansu da zummar masu godiya saidai babban abinda yafi basa mamaki hango wani mutumi da yayi tsakiyar sojojin shi kad'ai ne sanye da jampa sannan mutumin dattijo ne sosai, lokaci guda kansa ya kuma d'aurewa yana mai ci gaba da tarin hayak'i daya turnuk'esa.... Bai ankara ba yaji sauk'an k'otar bindiga a wuyarsa... Dukansa suka shiga yi sanda wannan mutumin ya masu alama, jina jina sukayiwa Ahidjo kafin Dattijon ya k'araso kansa yana dubansa.... Cikin murya mai fita da k'yar Ahidjo ke tambayarsa "Wanene kai, me kake nema daga gareni, waye yasa ka min wannan aikin...." Yayi maganar tamkar mai koyon magana sabida tsananin azaba da ya sha.... Sandar hanunsa tsohon ya kuma kwad'a masa mari da ita wanda saida ya gautar masa da fuska... Lokaci guda yasa k'artan suka d'ago masa Ahidjo da ko tsayuwa bai iyayi sabida azaba kana ya saka hannu ya d'ago fuskar Ahidjon dake nishi da k'yar kana yace "Matarka, matarka Nana Hafsatu ita ta biyani na kashe ka, sabida bataso ka dawo da 'yaruwarta gida, sannan she never loved you, sabida kawunta ta aureka ba soyayya ba.... And now zaka mutu...." Ya k'arashe yana kuma kai masa naushi a ciki Da k'yar Ahidjo ke girgiza kai yana fad'in Nana H bazata tab'a masa haka ba don tana k'aunarsa... Dariya mutumin yayi kana yace "Shiyasa nace you're fool, Ka fad'a trap d'inta..." Lokaci guda ya janyo dutsen dake gefensa kafin ya bugama Ahidjo a k'eyarsa nan wani sabon jini ya kece..... Da k'arfin gaske ya kuma tokarinsa ya fad'i gefe babu alamun numfashi a jikinsa.... Bulama ya kece da dariya kana ya furta "Babu wanda ya isa ya bayyana Mairo sai lokacin dana so yayi....." Daga haka shida yaransa suka bar wajen cikin motocinsu, suka bar Ahidjo mace a wajen.... *** Murmushi take daga saman benen tana mak'ale da wayar a kunnenta a hankali ta furta "Very well, ka tabbata motar ta k'one k'urumus....?" Daga d'aya b'angaren Nasaar yace "I promise you Ahidjo ya zama tarihi tokarsa ma baza'a samu ba....." Nana H ta kuma murmusawa cikeda jin dad'i kana tace "You know this calls for celebration ya kamata kazo muyi murna a gida...." Daga haka katse wayar tayi dai-dai sanda ta sauk'o parlor ta zauna bisa kujera tana mai fashewa da wani irin dariya "Heedj heedj heedj you such an idiot, Oh my dear husband I'm truly sorry but you've to die, wannan shine kawai hanyar da zai hana Nana K dawowa garemu, nayi imani idan ina numfashi Ammah da Uncle kai da duk wani dangi namu babu wanda zaisan Nana Khadija na raye balle ta dawo garemu, yanzu na soma toshe duk wata k'ofa da zai sadata da asalin danginta...." Wani dariyar ta kuma fashewa dashi kafin ta soma k'wak'ulo kuka tana fad'in "Yeah yeah, I've to cry for you Heedj, I must cry for you....." Ta k'arashe tana dariya amma hawaye ne ke sauk'owa daga idanunta.... *** Sanda Sabi'u ya sanar da Junaid cewa Ahidjo ya mutu sakamakon tabbatar masa da yaransa sukayi cewa sun k'onesa cikin mota, maimakon yayi farin ciki yaji dad'i sai akasin haka, gaba d'aya sai ji yayi zafin da zuciyarsa ke masa babu abinda ya ragu saima wanda ya k'aru, d'aki ya k'ume yana kuka sosai tamkar k'aramin yaro yana mai tuna Zeenat da alk'awarin da yayi mata na d'aukan fansa akan FUSKA UKU..... *** *Damaturu* Wajajen k'arfe biyar suka isa gidan Baba Malam, shashen su Yaya Azumi suka fara biyawa suka gaisa kafin suka k'araso wajen Baba Malam, gaisawa sukayi sosai kafin Baba Malam ya tambayi Mairo ko ta kama addu'an da ya koya mata, tiryan-tiryan kuwa ta soma karanto masa, sosai Baba Malam yaji dad'i ya lura Mairo nada saurin kama karatu, gashi karatun da ya bata shekaran jiya har ta kama... Baba Malam ya kuma gyara zama yana dubansu kana yace "Maryama inaso ki sanar dani matakin karatunki...." Mairo tayi shiru tana tuna yaushe rabonta da makaranta na boko ma balle na islama wanda da yawan iyaye muke sakaci dashi mubada k'arfi ma karatun boko bayan wannan karatun addini shine zai taimakemu ranar gobe domin da zaran bawa ya mutu ayyukansa sun tsaya cak, ba hujja bace a yanzu yanda ilimi ya shiga lungu da sak'o kajewa ubangijinka a matsayin rashin sani, kar mu mance tabi'ai da wad'anda suka rigayemu sun sha wahala sosai wajen neman ilimi, mu a yanzu ilimi ya wanzu mana ko ina ya ratsa ko ina, zama babu neman ilimin addini ba k'aramin kuskure bane, don Allah mu gyara mu baiwa lahirarmu himma domin itace rayuwa dawammemiya Girgiza kai Mairo ta d'anyi kana tace "Malam rabona da makaranta inaga tun muna wata gari mai Rafin zurfi a can ta k'asashen yamma, shid'inma a aji uku na tsaya a sakandare lokacin da muka bar garin ban kuma shiga wata makaranta ba, sannan islamiya kuma nasan a baya mukanje ta allo shima tunda muka baro garin Kazaure na daina zuwa...." Ga mamakin Mairo k'walla ta hango idanun Baba Malam, tabbas tana cikin duhu na jahilci ace mace budurwa haka batada ilimin fiqhu toh da meye zata gyara addininta, yaya take wanka, yaya take tsarki, yaya take alwala balle aje maganar sallah, shi bautan Allah sam ba'ayinsa daka, komai da ka gani muddin addini ne toh sai kanada hujjan yinsa ba kawai kai tsaye zakayi ba kace kaga anayi ne... Wllhi wllhi muje mu nemi ilimi, yanda ake bautan kanta kafin ta ta zama karb'ebb'iya, wllhi ubangijinmu zai tambayemu, musamman mu mata masu yin jini na al'ada, mata don Allah mu farga mu fita mu nemi ilimi mu gyara addininmu don wllhi ba'ayin addini daka... Allah ya mana muwafaqa ameen... Tambayoyi da dama Malam yayiwa Mairo sai ya kula rayuwarta gaba d'aya an ginasa ne wajen dambe da sunan k'watan 'yanci wanda dambe sam ba Al'adan 'ya mace bace, namijin ma ba'a koyar dashi dambe ba balle Mace, ita mace wace halitta ce mai tsananin kima da daraja saidai idan ita ta watsar da darajanta amma 'yar uwa ko yaya kike ki sani Allah ya maki kima da daraja, musulunci ta gama maki komai saidai idan kece kika watsar da kanki toh sai ki nemi wad'an nan kima da daraja naki ki rasa, muyi hattara mata.... Tabbas daga Mairo har mahaifiyarta Daddah sunada buk'atar koyarwa ta addini tun daga littafan fiqhu da tauhidi yanda zasu san Mahaliccinsu su kuma san yaya ake bauta masa, Baba Malam ya yanke shawarin Hafizu ya dinga zuwa har gida yana koyar dasu addini dukda cewa sunsan za'a sha fama sosai da Daddah don har yanzu batasan ina Mairo da Umma Marie ke zuwa ba.... *** Washe gari Nana H ta dawo gida sabida tafiyar da Ahidjo yayi, Siraj d'in kansa baiji dad'in dawowar nata ba, shikam yafi so ta natsu a d'akinta, Ayiya kuwa haka tayita yab'a mata maganganu marassa dad'i wanda sam Nana A batajin dad'in hakan tana matsuk'ar son 'yar uwarta sosai... Saidai ga tsananin mamakinsu Nana H wannan karan a saliha tazo gidan, don tunda tazo bakaji hayaniyarta ma 'yan aiki ba balle 'yan ahalin gidan... Haurowa sama tayi bayan sun gama hira da Ammah ta baro Amman tana kallon tashan labaru, tana hango k'ofar d'akin Nana A ta saki murmushi kafin ta soma kwaikwayon yanayin tafiyar Nana A har ta isa k'ofar d'akin.... Tana isa ta soma knocking a hankali, daga yanda Nana A ke zaune saman gado tana waya da sabon chwing gum d'inta Junaid ta bada izinin shigowa a tunaninta ma Ayiya ce... Ganin Nana H ce ya sanya Nana A sakin murmushi, daga bakin k'ofar murmushin ne kwance saman fuskar Nana H kafin tace "May I... ?" Jinjina mata kai Nana A tayi kafin tayi saurin yin sallama da Junaid, ta maido da hankalinta ga Nana H tana mai fad'in "Sis shigowa mana..." Murmusawa Nana H ta kumayi kana tace "Gani nayi kaman 'yar uwar tawa soyayya take na katse mata...." Nana A ta murmusa cikeda kunya kana tace "Kai Nanatu c'mon, ba soyayya bane, maganar da ya shafi foundation muke...." K'arasowa take murmushin bai bar saman fuskarta ba had'i da rungume kafad'un Nana A kana tace "I can see it from your eyes Sis, I'm pretty sure you're in love with that guy from the foundation, and you know what wllhi kun dace, he's super handsome although yanada deficiency, amma it doesn't matter idan dai kina sonshi, hankali kwance don nasan bazai tab'a hurting d'inki ba tunda shima yana fama da lalura makamanciyar taki ...." Ta d'an kuma marairaice fuska kafin ta dafa Nana A tace "Sister I really want to see you happy, please give that guy a chance wllhi na hango tsan-tsan soyayyarki a idanunsa sanda naje d'aukoki a foundation, Nana A kar kiyi wasa da damarki bakisan mai rayuwa ta tanadar maki ba, karma kiyi tunanin Lamid'o da abinda ya maki, maza suna suka tara kowa da halinsa, kiga dai yanda muke zaune da Heedj shekara biyu babu yaji balle saki, in fact ba'a tab'a jin kanmu ba sai wanda ba'a rasa ba..." Ta k'arashe murmushi saman fuskarta Murmushi Nana A keyi tana mai jin dad'in shawarwarin 'yar uwar tata kafin ta rungumeta cikin sauri tana fad'in "Nana H thank you, thank you sister, bansan mai zanyi ba idan babu ke...." Juya idanu kawai Nana H keyi tana yayyamutsa fuska lokaci guda take bubbuga bayan Nana A kana tace "I love you sister, everything for my only sister...." Ayiya ce ta shigo tanai magana wa Ammah saidai labarun da ake nunawa ya tafi da hankalin Ammah, k'onenniyar motar Ahidjo aka nuna ana sanarwa an sami motar tasa a k'one k'urumus sannan ba'a sami gangar jikinsa ba, jami'an tsaro sun tabbatar cewa jikin DT Aliyu ta k'one k'urumus cikin motar wanda yasa ba'a samesa ba.... Wani irin k'ara Ammah ta saki a dai-dai lokacin da Siraj yayi sallama parlorn, Nana H da Nana A a gigice suka nufo downstairs... . *Toh fah masu karatu ga Ahidjo dai anyi ajalinsa, ga Deejoh a gida batasan cewa da takaba akanta ba, shin yaya Deejoh zataji idan wannan labari na rashin mijinta ya risketa, Shin Junaid zai cimma burinsa akan FUSKA UKU, shin yaya rayuwa zata kasancewa Siraj babu abokansa, shin Lamid'o zai kub'uta daga hannun Bulama? Shin auren Siraj da Azeeza mai yuwa ne,? Yaya zata kasance tsakanin Junaid da Nasaar idan yasan cewa ya danne shari'ar Zeenat, Shin Mairo zata dawo gida....?* *Uwar gayya Nana H😂 one word for her please guys....* #FU #SameenaAleeyou #Nagode *SameenaAleeyou📚**FUSKA UKU*🏮 *41* *©Sameena Aleeyou...✍🏽* *ZBI Zauren kara Zauren mutunci Zauren sharhi fatan alheri gareku gaba d'aya😍🤝🏼* *Wai haka Heedj keda masoya, yau harda wad'anda bansan suna bin labarin ba sun zuba sharhi kan mutuwar Heedj😂, kar ku damu insha Allah he's in better place.... Na gode da k'aunarku gaba d'aya♥* Girgiza kai Siraj yake yana kallon abin tamkar almara, no badai Heedj d'insa ba.... He was here,.... Suna tare d'azu'dazun nan... No it can't be him, they must be mistaken, it can't be Heedj... Baisan sanda k'afafuwarsa suka kasa d'aukansa ba yayi wani irin silalewa a wajen zuwa k'asa... Ammah cikin sauri tana k'ok'arin maida kukanta ta nufi Nana H ta rungumeta sosai yayinda Nana H d'in ke fad'in "Ammah no.... Not my Heedj, Ammah I can't lose him, I already lost a lot of people, Ammah I lost my parents and my Sister, and I.. I just can't lose my husband in such a tragic way like that..... Ammah I just can't...." Ta k'arashe cikin wani irin kuka mai firgitarwa... Cikin rawar murya Ammah ke sanar da ita tayita karanto innalillahi wa inna'ilaihiraji'un Dai-dai lokacin Nana A ma ta fasheda wani irin kuka yayinda Ayiya ta k'arasa da sauri ta rungumeta, Allah sarki idan ka gansu dole su baka tausayi.... Zaune kawai Siraj yake dirshan a wajen yana tuno sa'insan da sukayi a safiyar yau, ashe tafiyar kenan, ashe Heedj sallama yazo masa, Innalillahi wa Inna'ilaihi raji'un, meyasa bai saurari Heedj ba da abinda zai fad'a masa, meyasa ya gaggaya masa magana anyhow, meyasa basuyi rabuwa ta dad'i ba.... Meyasa ya rasa abokanansa aminansa.... Why his friends why..... Kuka mai k'arfi wanda Siraj bai tab'a irinta ba a girmansa ita ta kufce masa..... Kuka yake bilhakk'i da gaskiya yana fad'in "Dan Allah ku fad'a min ba Heedj bane, ni nasan bashine, wllhi kuskure sukayi amma ba Heedj d'insa bane... A guje Nana H ta tafi ta fad'a jikinsa tana wani irin kuka mai tsuma zuciyar mai sauraro, sosai Siraj ya rungumeta suna cazgan kuka tare... Da k'yar Ammah ta iya k'arasawa garesu tana basu baki dukda dai kanaji kasan k'arfin hali kawai take, Allah sarki ta tuna dududu baifi kwana uku da zuwa nan ba har tana masa tsiya asubahin fari daga sauk'arsa ya biyo matarsa sai gashi kwatsam wai yau babu shi tabbas d'an Adam shi ba komai bane idan ya fahimci hakan, yanzu-yanzu ana taredakai anjima mala'ikan mutuwa zai zare ranka, Al'amari na Allah _Kun fayakun_ ne, Sarkin da baida fadawa sai bayi, sarkinda baida mashawarci, sarkin da mulkinsa take dawamemmiya... Allah ka bamu k'arshe mai kyau... Ameen...! A wannan dare iyalan marigayi Mas'ud Laushi sunga tashin hankali wanda suka jima basuga irinta ba, Siraj dole ya baka tausayi sabida yanda abin yayi affecting d'insa, gashi yayi neman duniya wayan Lamid'o bai shiga, shi kansa yasan a yanzu suna buk'atar juna daga shi har Lamid'o sabida rashin d'anuwansu da sukayi, saidai rashin shigar wayar Lamid'on sosai ya d'aga masa hankali, duk wani layi da yasan zai iya samun Lamid'o ya kira bai samu ba, tunanin maganganun Ahidjo a safiyar ranar ta shiga yawo a kwanyarsa, da gaske kenan Lamid'o kidnapping d'insa akayi.... Wani sabon jiri ya kuma tasowa Siraj da k'yar ya iya k'arasawa sashensa.... Nana H ta tashi zata bi bayansa Ammah ta kamota tana tambayarta ina zata tayi hak'uri... Girgiza kai Nana H keyi tana mai ci gaba da hawaye take fad'in "Ammah Uncle Siraj needs me, bazan iya jure ganinsa cikin tashin hankali ba.... Baki sake Ayiya ke duban ikon Allah, wai matar da mijinta ya mutu kenan amma tashin hankalin da Siraj ke ciki yafi na mutuwar mijinta, abun sosai ya baiwa Ayiya tsoro ya kuma d'aure mata kai... Ammah na girgiza kai take fad'in "Nana Hafsat Siraj will be okay kinji koh, ke a yanzu kin shiga takaba maza mu wuce sama ki canza wad'annan tufafi don sunyi kwalliya da yawa sannan ki cire duk wani sark'a da 'yan kunne, ki nutsu waje guda kiyiwa mijinki addu'an dacewa, tabbas mutuwar Ahidjo dole ya tab'aki sosai sabida ganin gawarsa kawai zai iya kwantar maki da hankali saidai muyi hak'uri haka Allah ya k'addara bazamu bisne Ahidjo ba, Allah ya masa rahama ya kuma toni asirin duk wanda keda hannu a mutuwarsa.." Rungume take da Ammah tana ci gaba da matsan hawaye b'angare na zuciyarta ji take kaman ta shak'e Ammah sabida ta haneta zuwa wajen Uncle, shegen shisshigi ina ruwanta idan ma batayi takaban ba ai mijinta ne, harda wani addu'an Allah tona asiri irin taji dad'in nan.... Ta kumayin tsuka cikin zuciyarta kafin a fili ta kuma fashewa da sabon kuka, da k'yar Ammah ta janyota suka nufi sama.... Ayiya da Asma'u zaune sukayi bisa kujera Asma'u na hawaye take fad'in "Ayiya da gaske Uncle Heedj ya tafi, Ayiya rabona dashi tun kafin yayi tafiyar can da ya d'an jima, Ayiya Uncle nada kirki shikad'aine zai iya zama da 'yar uwata sabida hak'urinsa da kirkinsa.... Ayiya ina tausayin 'yar uwata, ta rasa mijinta a k'aramin shekaru... A kullum ina hangosu zasu hayayyafa su kuma tsufa tare ashe kana naka Allah yana nashi.... Na Allah shine dai-dai.... Allah yajik'anka Uncle Heedj kyawawan d'abi'unka su bika.... Tabbas ka barmu da kewa na rashinka....." Ta k'arashe cikin kuka sosai... Ayiya ta rungumota tana lallashinta cikin daurewa zuciyarta cikeda damuwar sam bata kyautawa Ahidjo ba sanda yake raye sabida rashin jituwa da Nana H dake tsakaninsu saida ya shafi Ahidjo sanda ya soma neman auren Nana H ta d'auki kulawarta ta maida kan Lamid'o wanda batasan shine zaici amanar d'iyarta Nana A ba, Allah sarki Ahidjo tabbas yafi matarsa kirki, zata jima tanajin zafin abubuwan data masa a baya.... Siraj kuwa yana fad'awa d'aki hotonsu da suka d'auka su uku tare a makaranta can United States ya d'auka yana gani, sun dafe juna su duka FUSKA UKUN, Siraj na tsakiya yayinda Ahidjo da Lamid'o ke gefe-gefe.... K'ura ma hoton idanu yayi wasu irin sabbin kuka suna taso masa, a hankali ya zauna had'ida rungume hoton cikin k'irjinsa, lokaci guda ya janyo wayarsa ya shiga neman layin Azeeza, bugu ta d'aga don ita yanzu har firgita take idan taga wayar Siraj tunda tasan Yayanta na farautar rayuwarsa.. Saidai kafin ta sami zarafin magana tajiyo sautin kukansa, sosai hankalinta ya tashi tabbas ba k'aramin abu bane zai saka namiji kaman Siraj kuka, take kawai taji kuka na zuwa mata itama gashi ya kasa fad'in komai sai kuka... Cikin kuka itama take fad'in "Sir... Siraj lafiya, meke faruwa ne dan Allah ka sanar dani...." Ta k'arashe tana k'ok'arin mik'ewa had'ida neman takalmi zata fice bata damu da duhu da gari yayi damuwarta kawai Siraj ya zama safe.. Junaid daga balcony ya hangeta cikin sauri ya turo kekensa ya fito had'ida shan gabanta.... Sosai Azeeza ke kuka tana tambayar Siraj ya sanar da ita abinda ke faruwa... "Dan Allah sir ka sanar dani yanda kake wllhi yanzu zanzo, please ka sanar dani...." Ta k'arashe cikin shesshek'a... Cikin rawar murya Siraj dake tak'ure waje guda yake fad'in "Azeeza ABOKAINA abokaina Azeeza, na rasa su gaba d'aya.... Azeeza na rasasu... Heedj ya tafi ya tafi Azeeza tafiya ta har abada, dan Allah kice min zasu dawo zamu kuma rayuwa tare A DUNIYAR MU kice min zasu dawo kinji...." Ya k'arashe cikin wata irin sanyin murya... Wani irin sanyi jikin Azeeza yayi don tasan k'udirin Yayanta akan FUSKA UKU. A hankali ta silale saman tile tana mai watsawa Yayanta Junaid wani irin duba da rianannun idanunta... *** Washe gari kan kace mai labari ya riske ko ina, Sabi'u shi yayi duk wani cuku-cuku aka bada report na boge cewa tsagerun boko haram su suka k'ona Agent Aliyu cikin motarsa kasancewar da yawan mutane sun kwana da sanin rayuwar duk wani force a yankin arewa maso gabas yana cikin had'ari babba.... Da wannan k'akk'waran dalili yasa Siraj basu tsananta binkice ba sannan Nana H ma ta nuna batason binciken don bazata juri wasu unnecessary stupid interrogations daga jami'an tsaro ba sabida tana fama da jimamin mutuwar mijinta... A b'angaren Azeeza sosai halinda Siraj ke ciki ya dameta, a ranar kwana na biyu ta fito cikin shiri zata tafi gidansu Siraj ta'aziya don koda ace basu jituwa da Nana H tasan matsayin Ahidjo a wajen Siraj, sannan su Ammah sunada mutunci sun cancanci gaisuwa, lokaci guda kuma ta tuna toh waima ta yaya zata soma gaisar da Siraj, ta shiga gidan ta gansu cikin k'unci da kuka tace mai? Yayanta ne silan komai kokuwa mai zatace....? Lokaci guda wasu sabbin hawaye suka shiga gangaro mata tausayin Siraj na ratsa b'argo da tsokarta... D'ago kan da zatayi sukayi idanu hud'u da Junaid yana dubanta babu alamun wasa a fuskarsa.... "Zeeza kukan mai kikeyi....?" Ya tambaya yana dubanta Kauda kai gefe tayi wasu hawayen na kuma zubo mata lokaci guda taji bazata iya zuwa ta'aziyan ba don koda taje kuka zatayitayi.... Har cikin ransa Junaid kejin kukanta a hankali ya k'arasa gareta yana mai tura kekensa, ganin k'anwarsa cikin tashin hankali sai ya kuma jefa zuciyarsa cikin k'unci.... "Zeeza ki daina kukan nan kina jina....." Jiyowa tayi cikin tsananin kuka tana dubansa had'i da girgiza kai take fad'in "Yaya vengeance has turned you into something else... Yaya this is not you.... Why why meyasa ka zab'i zama maras yafiya, shin kaji dad'i a ranka sanda ka riski labarin mutuwar Ahidjo.... Meyasa ka kasheshi...?" Cikin daka tsawa idanunsa na fitar da wani irin ruwa ya katseta da fad'in "Because he killed her, that imbecile killed my Zeenah, and look at me Zeeza, Zeeza rayuwata saman keken guragu batada wani amfani, have I ever told you sabida d'aukan fansan Zeenah akan FUSKA UKU nake rayuwa, ban tab'a fad'a maki ba koh toh yau ki sani, randa burina ya cika nima zan tafi Zeeza, zan tafi na sami Ammi da Baaba.... And Zeenah zamu kasance tare har abada..." Ya k'arashe hawaye masu zafi naci gaba da kwaranya masa... Lokaci guda Azeeza ta soma jada baya tana tunanin tabbas Yayanta Junaid ya sami tab'in kwanya... Da k'yar Nasaar dake tsaye bakin k'ofa ya gama saurarensu tsaf ya iya juyawa kansa na masa wani irin nauyi, sam ji yake zuciyarsa tamkar zata fito waje ta fashe, soyayyar Azeeza na neman tarwatsa masa rayuwa, shin Azeeza kukan mai take irin haka, shin kukan kauce hanya da Yayanta yayi take ko kuwa ma Siraj take wannan kukan..? Mutum d'aya ce tak zata iya amsa masa wannan tambayar kuma ba kowa bace face ita Azeezar... Cikin sauri ya fice daga gidan ya nufi motarsa ba tareda sanin yanda ya nufa ba, tambayar kansa yake maiyasa yake zama looser a kullum, mai yasa yake tura mota ta tafi ta barsa da k'ura a kullum.... Gefen hanya Nasaar ya samu ya paka motarsa had'ida kifa kansa jikin steering wheel k'irjinsa naci gaba da masa wani irin zogi, tabbas wannan karan kam bai shirya barin Azeeza ma kowa ba, he'll fight for her love even if it will cost him his life..... *** Bayan sati biyu da faruwan wannan Al'amari jigum Ayiya tayi tana kallon irin rayuwar da ake a gidan marigayi Mas'ud Laushi wai da sunan musulmai, ace Ahidjo ya mutu amma su kasa neman iyayensa da danginsa su sanar dasu, basu san ko iyayensa na raye ba, ko suna mace, Nana H dake lab'e jikin staircase tana sauraren Ayiya da Ammah cikin sauri ta nufo downstairs tana mai matso hawaye ta fad'a jikin Ammah a guje tana fad'in "Ammah yanzu shikenan daga mutuwar mijina an soma zancen a nemo danginsa ko wata mijina baiyi ba za'a soma d'aga min hankali da nemo danginsa, Ammah da wanne zanji da zafin mutuwar mijina koda nemo danginsa Ammah dan Allah kada ki biye wannan matar ko kuma wllhi nima mutuwa zanyi idan aka tak'urani....." Ta k'arashe tana kuka sosai.. Lallashinta Ammah ta shigayi tana sanar da ita bazata kuma jin maganar ba har sai ta dawo cikin hayyacinta.... Nana H kuwa jin haka ta d'ago idanunta ba tareda Ammah ta kula ba tana mai watsawa Ayiya mugun kallo had'ida sakar mata makirin murmushi... Girgiza kai kurum Ayiya tayi tana mamakin yanda son zuciya yayi tasiri tsakanin Al'umma a wannan duniya tamu, tabbas akwai gyara sosai cikin rayuwan gidan Mas'ud Laushi, sabida tsananin takaici Ayiya bata iya furta komai ba sai mik'ewa da tayi ta bar parlorn, Nana Hafsatu ita ke juya gidan yanda taso, kuma babu mai taka mata birki... Wannan abu sosai yake k'ona zuciyar Ayiya, tasha attempting barin gidan amma sabida Nana A sai ta fasa, tasan idan ta tafi Hafsatu zata iya cutar da ita sannan sam su iyayen basa ganin hakan, fatanta Allah ya wankar masu da idanu su soma ganin wacece d'iyar tasu.... *** Yau kusan kwanaki kenan daga Deejoh har Innah suna wasu irin mafarkai barkatai gameda Ahidjo, Innah kullum cikin addu'a take tana rok'on Allah ya tsare mata d'anta a duk yanda yake, ita kuwa Deejoh k'uryar d'aki shine wajen yinyinta don tinda Yayanta kuma mijinta Ahidjo ya tafi walwalarta ya tsaya a gidan, kullum rungume da kwalban turaren da ya bata take bacci ko fesawa batayi tsaban taltala turaren da take tana kallon mijinta a jiki, a kullum zuciyarta bai tab'a karaya cewa Yaya Ahidjo bazai dawo ba tasan tinda ya mata alk'awari tabbas zai dawo d'in, wannan take tunawa taji ta sami natsuwa sosai cikin zuciyarta... A can Abuja kuwa Sabi'u gaba d'aya ya rasa wanne zaiyi, shin ya tafi can gida Misau ya sanar masu ne ko kuwa, wata zuciya tace cin amanar taka zaiyi yawa idan bakaje ka duba mahaifansa da kuma iyalinsa da ya barta, take Sabi'u yaji zuciyarsa na raya masa washe gari yayi asubanci zuwa garin Misau ta jihar Bauchi **** A garin Damaturu kuwa da k'yar da sid'in goshi aka shawo kan Daddah ta yarda Hafizu yake zuwa yana basu karatu, duk bayan lisha suke karatun a farfajiyan gidan Umma Marie, tuni Daddah ta tilastawasu Dakura suma suka soma zuwa karatun, idan ka zauna a majalisin karatun ko ka k'i sai kayi dariya, Malam Hafizu kam nashan fama, gashi da alama idanunsa sun sauk'a kan Mairo saidai kunya irin tasa ta kasa barinsa ya nuna, shiko baisan wacce idanunta ta sauk'a kansa Dakura bace, abun har mamaki yake baiwa Balaji mahaifin Dakura yanda ta rik'e karatun bilhak'k'i bayan a baya babu kalan yak'in da baiyi da ita ba kan zuwa islamiya, amma yanzu lisha nayi ta janyo Falmata sun tafi, har alla alla take tajeta taga Malam Hafizu, su Dakura harda d'inka hijabai ta raba masu gaba d'ayansu, ga wani sabon k'awancen da ya shiga tsakaninsu da Mairo... Malam Hafizu yana gama parking Babur d'insa wayan mahaifinsa Baba Malam ya shigo masa... Da sallama ya amsa saidai jin muryar mahaifin nasa wani iri ya sanyasa dakatawa... Lokaci guda Hafizu ke furta "Baba kana nufin yau ya farka....?" Daga d'aya b'angaren Baba Malam yace "Hafizu maza kazo gida ina nemanka, ina tsammanin Allah ya masa cikawa...." Take Hafizu yaji jikinsa yayi sanyi k'alau lokaci guda ya jinjina kai yana mai amsawa da "Toh Baba..." Kafin ya isa Babur d'insa.. Bai ida hawa ba ya hangi Mairo tana fitowa da abin shimfid'a wanda suke zama bisa suyi karatun, tana sanye cikin dark blue hijab wanda ya fito da haskenta sosai.... *SameenaAleeyou📚**FUSKA UKU*🏮 *42* *©Sameena Aleeyou...✍🏽* Cak Hafiz ya tsaya yana duban Mairo ba tareda ya iya burka babur d'in ba, zuciyarsa tana mai ci gaba da bugu bai tab'a tsintar kansa cikin matsananciyar soyayyar wata mace ba sai akan Mairo, dama shid'in tun can mutum ne da bai shiga sabgan mutane, haka nan Allah yayisa da tsananin kunya kaman mace kai har yafi wasu matan ma, inama zai iya sanar da ita gyambon datajiwa zuciyarsa ko zai sami sassauci... Muryarta ne ya dawo dashi daga duniyar tunanin da ya tafi... "Malam badai tafiya zakayi ba, kayi hak'uri dan Allah abin hawa ne su Dakura basu samu da wuri ba kuma gasu nan tafe don yanzu haka da mukayi waya tace min sun samu, kayi hak'uri Malam bara na kawo maka ruwa..." Ta k'arashe tana shimfid'a darduman dake a hannunta Tunda ta soma magana Hafiz ke dubanta, cikin sauri ya kauda idanunsa daga kanta gudun kada ta d'ago su had'a idanu ta fahimci mai yake ciki, take kuma ya tuna Baba ke kiransa da kuma abinda ya fad'i masa a waya.... D'an k'ak'aro murmushi yayi kana yace "Maryama baiwar Allah (Haka nan yake kiranta) kuyi hak'uri wllhi wani uziri ne mai girma ya taso daga gida, Baba yana buk'atata cikin gaggauwa kar ku damu yau kowa ya huta..." Ya k'arashe yana k'ok'arin yin key wa Babur d'insa... Daddah da fitowarta kenan dama da k'yar ta mik'e donma Mairo ta b'oye tuwo tace babu mai ci sai an dawo daga karatu shiyasa ta mik'e ta fito karatun bai wai don taso ba... Ai jin Malam Hafiz yace yau babu karatu sai ta shiga washe baki tana fad'in "Yauwa Malam d'angari, wllhi yaron nan shiyasa fah kake burgeni, yo kwanya ma ai tana son hutu, jeka abinka zo na bud'e maka k'ofa..." Ta k'arashe tana tattare hijabinta had'i da hangame masa k'ofa... Mairo dai duban Daddah kurum take tama hanata ta tambayi Hafiz ko lafiya Baba yake don taji yace wani babban uzuri ne ya taso... Kai Daddah bazata tab'a canzawa ba dai..... Yo Daddah kam ina ruwanta dad'i ya samu babu karatu harda taka rawarta... Hafiz dai sadda kai kurum yayi ya fice cikin sauri yana mai addu'an Allah ya tashi kafad'un wannan bawa nasa.... Malam Hafiz na ficewa su Dakura suka iso, aiko ta hangi wulk'awan Babur d'insa cikin sauri ta k'araso haraban gidan ta baro Falmata na biyan mai adaidaita, nan ta tadda Mairo na linke dardumarsu ta zama... "A'a Mairo ina Malam d'in ya tafi, kardai shid'in na gani na ficewa daga layin nan...." Mairo ta jinjina kai sanda Daddah ke rangad'a mata kira daga cikin gida tana fad'in tazo ta basu tuwonsu idan ba horon yunwa zata masu ba... D'an girgiza kai kurum tayi kana ta dubi Dakura tace "Wllhi wai wani uzuri ya taso masa daga gida, kinga mafa Malam na k'ok'ari k'ila d'an lokacin da yake zuwa hirarsa muke amfani da ita, wllhi yana mana k'ok'ari sosai..." Dakura ta d'anyi jim kana tace "Amma kinaga Malam Hafiz anya nada budurwa kingafa ko kallon mata bai iyawa...." Tak'aitaccen dariya Mairo tayi tana buge darduman bayan ta linke kana tace "Toh kodai kina ciki ne kam da har kika iya gano hakan...." Murmusawa Dakura tayi tana mai bin Mairo da kallo kana tace "Kyaji dai dashi ni bara na k'arasa wajen Daddah ta tace min kutittiriya muyi fad'a..." Isowar Falmata kenan take fad'in "Wllhi kuwa Mairo idan tayi tsami zamuji, kullum ko a gida zancen kenan Malam Hafiz, kinsan ma ranar ashe har recording karatunsa tayi sanda yake mana k'ari...." Mairo mai zatayi banda dariya... Tafewa sukayi itada Falmata suna dariya suke fad'in "Ashe dai ustaz yayi kasuwa...." "Kanku dai akeji...." Cewar Dakura kana ta shige ta barsu suna ci gaba da kwasan dariya... *** Hafiz na shigowa d'akin ya hangi Mamarsa Yaya Azumi da kuma mahaifinsa Baba Malam kan mutumin da ya tsinta cikin kwalbati sati biyu da suka shud'e a hanyarsa ta dawowa gida... Yaya Azumi tanakan murza wani ganye a hannunta Baba Malam na shafe goshin maras lafiyar dashi, dashike Yaya Azumi likitan gargajiya ce, Allah ya mata baiwan sanin magunguna da dama.... Cikin sauri ya k'arasa shigowa d'akin yana kai hannu jikin maras lafiyan yake fad'in "Baba da gaske ya cika....?" Girgiza kai Baba Malam yayi kana yace "A zatona ya cika sanda naga jikinsa na mimmik'ewa amma sanda mahaifiyarka tazo ta tabbatar min da sauran ransa bai cika ba.... Hafizu idan muka bar wannan bawan Allah a nan ba tareda kulawan asibiti ba zai iya mutuwa, tabbas mahaifiyarka na iyaka k'ok'arinta amma jikin nasa tsanani yake kumayi, ace yau sati biyu idanunsa na rufe baisan yanda yake ba, inaga gwara mu nemi taimakon asibiti..." Jinjina kai Yaya Azumi tayi kana tace "Mahaifinka yayi gaskiya Hafizu asibiti shine kawai taimakon da zamu k'arasa masa....." Girgiza kai Hafiz yayi cikeda tashin hankali kana yace "Baba ku gane, yanzu lokacine da muke ciki na tsananin tsaro, haka kurum baza'a karb'i mutumin nan a asibiti ba sai da rahoto daga jami'an tsaro, idan muka kaisa mu kuma zamu jefa kawunanmu ne cikin had'ari don za'ace dole mu fad'i waye ya masa haka, kundai san yanda yanayin garin yake ....." Ya k'arashe damuwa fal fuskarsa... Jinjina kai Baba Malam yayi kana yace "Kuma fah tabbas ka fad'i gaskiya Hafiz musamman idan akayi la'akari da kamala ta addini da mukedashi, tabbas wani ma ya samu hanyar mana cune.... Amma Hafizu bazamu barsa haka nan ba, wannan bawan Allah ban zaci zai kawo war haka a raye ba, tabbas Allah shi yasan dalilin da yasa ya bar wannan bawa nasa a raye.... Hafizu dole muyi wani abun, Allah kad'ai yasan dalilin da yasa mutumin nan ya fad'o hannunmu...." Jinjina kai Hafiz yayi kana yace "Haka ne Baba...!" Shiru ya d'an ratsa tsakani ko wannensu yana tunanin mafita, lokaci guda Hafiz ya tuna da abokinsa Sahal wanda sukayi collage tare kafin Sahal ya tafi jami'ar Maiduguri ya karanti likitanci, a halin yanzu Sahal babban likita ne a babban asibitin Damaturu..... Cikin sauri Hafiz ya soma murmushi yana hamdala yayinda Baba Malam da Yaya Azumi suka bisa da kallo suna jiran suji menene ya tuna.... "Baba Mama mun samu mafita da yardar Allah, ai kun tuna Sahal abokina da muka fara Kwaleji tare...." A tare suka jinjina kai Mama Azumi tana fad'in "Tabbas aiko kwanaki ma yazo nan ya gaisheni...." Hafiz yaci gaba da fad'in "Yanzu ai babban likita ne, zan kirasa yazo har gida mu tattauna matsalar idan ma shi zai kaisa asibitin kunga babu wanda zai zargemu... Ko ba haka ba...." Ya k'arashe yana dubansu gaba d'aya.. Murmusawa Baba Malam yayi had'ida bubbuga kafad'un Hafiz kana yace "Allah ya maka albarka Hafiz, hak'ika kai D'A NAGARI ne burin ko wasu iyaye, har kullum ina alfahari dakai, Allah ya maka albarka, Allah yasa ko bayan raina ka rayu akan wannan turba da kake bisa....." Gaba d'aya murmusawa suke harda Yaya Azumi, har k'asar zuciyarta take jin dad'i idan taga tilon d'an nata da mijinta yanda mu'amala keda kyau da tsafta a tsakaninsu, tabbas iyaye masu kausasa harshe akan 'ya'ayansu suke jefa 'ya'yan nasu cikin fitintinu na rayuwa wani sa'in... Allah ka ganar damu iyaye mu zamto masu saka albarka cikin rayuwar d'iyoyinmu sabida su d'in kiwo ne Allah ya bamu kuma zaya tambayemu gameda yanda muka tarbiyantar dasu..... Washe gari kuwa Dr Sahal ya amsa kiran Baba Malam cikeda girmamawa, Baba Malam ya masa bayanin komai da alfarmar da suke nema daga garesa.... Cikeda girmamawa Sahal yace "Haba Baba wllhi kun wuce ku nemi alfarma daga gareni, abubuwan alkhairi da kukayimin a baya a dalilin Hafiz bazan tab'a mantawa ba... Baba zanyi insha Allah, bayan haka taimako kukayi nidai d'aurawa kawai zanyi akai, Allah ya waita irinku a Al'umma...." Ameen Baba ya amsa dashi yana murmusawa cikeda jin dad'i kana yace "Kaima Allah k'aro likitoci irinka Malam Sahal, mu shiga ka gansa....." Ya k'arashe yana k'ok'arin mik'ewa Sahal yayi saurin taimaka masa kafin suka shiga d'akin a tare yanda wannan bawan Allah ke kwance tamkar gawa idanunsa a rufe ruf..... Cikin sauri Sahal ya k'arasa ya shiga 'yan dube-dubensa da wasu 'yan kayan aiki da yazo dasu.... Ya d'an jima yana dube duben kafin ya fito parlor ya taddasu gaba d'aya suka mik'e suna jiran ta cewar Dr Sahal... D'an shafa goshinsa yayi kana yace "Zuciyarsa bata daina bugawa ba saidai yaji raunuka masu tsananin muni, ba iyaka wad'anda kuke gani a fili ba harda ciki wanda a turance muke kira internal injuries, sabida haka dole mu tafi asibiti sabida idan ba wani ikon Allah ba zuciyarsa tana gab da daina bugawa, zamu tafi asibiti yanzu, kar ku damu ni zanyi komai insha Allah...." Ya k'arashe yana mai kiran wani abokin aikin nasa yana mai sanar dashi a shirya d'akin tiyata..... Godiya sosai su Baba suka dinga yima Dr Sahal, kafin Sahal da Hafiz suka ciccib'i mutumin suka fita dashi zuwa motar Sahal dake pake bakin lungun..... *** Da sallama ya turo k'ofar office d'in nata murshi saman fuskarsa kafin ya d'an bubbuga k'ofar a hankali da zoben dake yatsar sa yana mai fad'in "May I...?" Gyara zamanta tayi murmushi saman kyakkyawar fuskarta kana tace "Sure, please come in..." Har ya shigo cikin office d'in murmushi bai bar saman fuskarsa ba, d'an gefe da ita ya paka wheelchair d'in nasa kana yace "Are you still working.... Haba Gorgeous ki daina stressing kanki da yawa please, ke duk wanda ya jima yana aiki kina biyansa overtime ke kuma babu mai biyanki fah, besides banson ganinki kina wahala sai naji kaman banida wani amfani....." Ya k'arashe yana mai kasheta da wani irin duba.... D'an murmusawa tayi had'ida girgiza kai kana tace "Babu wani stress fah, kawai wani sa'in zaman office d'in yakan d'an rage min damuwa ne shiyasa nake zama bayan lokacin tashi..... What about you, meyasa baka tafi ba...." K'uri ya mata yana karantarta damuwa sosai saman fuskarsa kana yace "Damuwa kuma Gorgeous, kyakkyawa kamarki bata kamaci damuwa ba, please ki sanar dani meke damunki ko zan iya yin wani abu akai..." Ya k'arashe cikin tsananin nuna kulawa..... D'an jim tayi tana mai k'ok'arin maida k'wallan dake neman zuwa idanunta lokaci guda ta saka d'an yatsanta tana gogewa kana ta d'an saita kanta, cikin sanyin muryarta ta soma fad'in "I couldn't help but.... But keep worrying about my Uncle and my Sister, you see, this isn't easy for the both of them, they're going through a tough situation, if only.... if only I could take all their burdens away from them.... Nana H ta rasa mijinta and Uncle ya rasa abokinsa Ahidjo sannan wani sabon tashin hankalin har yanzu babu labari gameda Lamid'o, koda ace ya mana Lauri in the most horrible way ya kamata musan wani hali yake ciki, amma har yanzu shiru.... Junaid family na suna cikin k'unci da damuwa and it breaks my heart seeing them suffering.... Uncle yaga iftila'i kala-kala a rayuwarsa ina fata watarana komai ya zama labari ya kasance cikin farin ciki...." Ta k'arashe cikin tsananin rawar murya had'da sunkuyar dakai sabida kuka da yazo mata gadan-gadan..... Idanun Junaid sukayi ja sosai, jijiyoyinsa suka kuma mimmik'ewa ganin yanda Nana A ta damu da damuwar so called Uncle d'inta Siraj, batasan cewa Siraj deserve all this, shine wandama yafi tsana cikin FUSKA UKU shine silan komai, kuma bazai tab'a hutawa ba sai yayi hurting d'insa in the most terrible way sannan ya kashesa, ya rabasa da rayuwarsa kaman yanda ya raba Zeenat da nata...... K'ok'arin saita kansa ya d'anyi kafin ya ciro handkerchief gefen aljihunsa ya mik'a mata, saida ta d'ago idanu tana dubansa kafin ta karb'i handkerchief d'in bayan ta hango d'inbin damuwa a k'wayar idanunsa.... Jikinta yayi sanyi sosai ganin yanda damuwarta ke zamtowa damuwar Junaid, tabbas Junaid yana nuna mata kulawa mai tsananin wanda shakka babu tasan ba komai bane illa SO..... K'ak'aro murmushi tayi ta sakar masa had'ida masa godiya..... Shid'inma murmushin ya k'ak'aro wacce iyakacinta fatan baki kana yace "Ki daina min godiya gorgeous, I love you and I care for you, I'm willing to do everything in this world to make you happy, I love seeing you happy, murmushi a koda yaushe shine ya kamaci kyakkyawar fuskarki, ki ci gaba da masu addu'a kar ki mance kullum kece kike sanar dani halin da muka tsinci kawunanmu ciki is a trial daga Allah, so ki saka ma zuciyarki haka, insha Allahu komai zai wuce watarana ya zamto labari sannan gaskiya zata bayyana....." Kalamansa na k'arshe shi ya sanyata dubansa tana mai maimaita kalmar cikin zuciyarta, ba tareda ta kawo komai ba ta shiga jinjina kai tana murmusawa wata b'angare na zuciyarta tana jin Junaid nada babban matsayi wanda bata tab'a baiwa wani namiji ba..... Kallonsa ta d'anyi had'i da sakin murmushi don shakka babu taji sanyi cikin zuciyarta sanar dashi da tayi, a hankali ta soma furta "Kanada zuciya mai kyau, na gode sosai for always being here, and please idan bazaka damu ba I'll like to introduce you to my family, and especially to my Uncle......" Wani irin d'agowa Junaid yayi yana dubanta kafin k'irjinsa ya buga da k'arfin gaske uwa an sauk'e guduma, zata b'ata masa plans d'insa baiyi niyyan confronting Siraj yanzu ba tabbas ba haka ya tsara ba..... Muryarta ne ya katse masa tunanin nasa... "Dan Allah kar kace a'a wllhi family na zasuyi farin cikin had'uwa dakai especially Uncle Siraj da Ayiya, kaji please...." Ta k'arashe cikin siga na kashe murya wanda batama san tayi hakan ba.... Shiru kaman bazaice komai ba sai kuma ya sakar mata murmushi yace "Shikenan zan had'u da Family d'inki hakan na nuna min kin accepting d'ina...." Ya k'arashe cikeda zolaya Tak'aitaccen dariya tayi itama had'i da d'an sunkuyar dakai ba tareda ta iya furta komai ba.... Lokaci guda kuma ta d'an d'ago murmushin bai bar saman fuskarta ba tace "Zamuje gobe insha Allah sai kazo da shirinka....." Ta k'arashe tana mai tattara takardun dake bisa table d'inta alamun ta tashi itama Murmushin shima yake cikin sauri ya turo wheelchair d'insa yana mai k'ok'arin tayata tattara takardun yake fad'in "No no let me do this please princess....." Murmushi kawai take tana dubansa zuciyarta nai mata wani irin sanyi, a haka suka fito tare har waje, idan ka gansu sai kace masoyan asali.... *** Lokaci zuwa lokaci take duban k'ofan office d'insa, tinda ya shige ya sanar da ita baida buk'atan ganin kowa,.... A hankali ta d'an fuzar da iska had'ida rintse idanu, ta kasa tab'uka komai gaba d'aya sai tunanin halin da Siraj ka iya kasancewa ciki, tausayinsa na kuma ratsa zuciyarta, can k'asar zuciyarta take ji anya bazata sanar da Siraj komai ba, zuciyarta ta kasa natsuwa gaba d'aya, gwara ta sanar dashi koda hakan zai rabata da Yayanta Junaid,......A hankali ta mik'e had'ida gyara mayafin kanta had'ida furta "I'll tell him everything, everything I know....." Lokaci guda ta nufi k'ofar office d'in nasa had'i da yin knocking k'irjinta naci gaba da bugawa.... "Who's there...? Didn't I say........" aya ya dasa ma kalamun nasa hango fuskarta da yayi ta turo k'ofar fuskarta cikeda damuwa..... *SameenaAleeyou📚**FUSKA UKU*🏮 *43* *©Sameena Aleeyou...✍🏽* Saita kansa ya d'anyi had'i da k'ak'aro murmushin k'arfin hali kana yace "K'araso mana...." Azeeza da tayi tsaye a wajen tamkar wacce ruwa ya shanye da k'yar ta iya jan k'afafunta ta soma tafiya tamkar kazar da k'wai ya fashema.... Kujeran dake gaban table d'insa ya nuna mata kana yace "Zauna...." Babu musu ta zauna kaman yanda ya umarta d'in.... K'irjinta sai wani irin bugu yake tamkar zai fito waje, k'warjinin Siraj gaba d'aya ya cika wajen., sunan Allah kurum take ambata cikin zuciyarta don batasan da wanne zata soma ba.... K'uri Siraj ya mata yana karantar ta ganin yanayin nata, tamkar ba Azeezar da ya sani mai tsiwa da confidence ba.... Yanayin nata sosai ya d'aga masa hankali domin kuwa damuwa ya hango k'arara saman fuskar sa.... "Azeeza lafiya, meke faruwa...?" Ya tambaya cikeda kulawa bai janye idanunsa daga dubanta ba Banda murza 'yan yatsun hannunta babu abinda take, da k'yar ta d'an iya k'ok'arin saita kanta kana tace "Sir.... Dama.... Dama.....!" Shiru tayi ta kasa ci gaba da magana sabida girman abinda take shirin fad'in Siraj ya matsar da fuskar computer d'in dake gabansa yana dubanta sosai kana yace "Ina saurarenki wani abu ne ya faru, ko wani abin aka maki a nan, fad'a min ko wanene...." Ya k'arashe cikin d'an d'aga murya wannan karan... Muskutawa ta kumayi kukan da take mak'alewa lokaci guda ya shiga zuwa bakinta.... Cikin sauri Siraj ya shiga girgiza kai yana fad'in "Oh no no please Azeeza, if there's one thing I hate in this life shine naga mace na kuka, please ki daina kukan nan kinji...." Ya k'arashe murya cikeda kulawa.... Bata daina kukan ba saima k'aruwa da yayi, Siraj ya mata k'uri kawai don baisan yaya zaiyi ya lallasheta tayi shiru ba.... Hannayensa yake k'ok'arin kaiwa saman nata, har saida yakai hannayensa kusan nata kaman wanda ya tuna wani abu sai kuma ya fasa rik'o hannayen nata, wani irin zogi kukan nata ke masa can k'asar zuciyarsa, Azeeza kuwa kaman cewa ake ta k'ara.... Dafe kansa kurum yayi had'ida tattare naman goshinsa lokaci guda ya d'an matso da fuskar sa kusan nata.... A hankali ya soma furta "Azeeza... Zeeza look up, ki kalleni please....!" Yayi maganar cikin tsananin sanyin murya.... Cak kukan nata ya tsaya, lokaci guda ta d'ago idanu tana dubansa, chocolate face d'inta ya zamto very pale, fuskar Siraj dab nata ta gani, k'wayan idanuwansu ne suka had'e waje guda.... Su duka d'in basu san suna kallon juna haka ba.... Lokaci guda Azeeza tayi saurin sadda nata idanun k'asa k'irjinta naci gaba da bugu cikin sauri, sai faman shan zuciya da take alamun taci kuka... K'ok'arin saita kansa shima yayi had'ida d'an yin gyaran murya kana ya soma fad'in "Azeeza ever since I met you, I become allergic to your tears...." Kallonsa tayi da kod'add'un idanunta... Siraj ya jinjina kai sihirtaccen murmushi saman fuskarsa kafin yaci gaba da fad'in "Yeah, idan na ganki kina kuka toh shakka babu I'll fall sick.... Dan Allah kar ki sake kuka irin haka kinji idan ba so kike nayi ciwo ba...." Ya k'arashe idanunsa a kanta.... Lokaci guda ta d'anyi murmushi sabida harga Allah ya bata dariya da yace he's allergic to her tears.... Ganin tayi murmushi yasa Siraj jin dad'i shid'inma murmushi saman fuskarsa kafin yaci gaba da fad'in "Ina saurarenki, ki kwantar da hankalinki ki fad'a min meke faruwa...." K'irjin Azeeza ya kuma bugawa but she has to do this batada wani zab'i muddin tana son kub'utar da Siraj.... A hankali ta soma fad'in "Sir there's something you need to know......!" Batakai aya ba wayan salulan Siraj ta soma ringing, ganin Nasaar ne mai kira ya sanyasa d'agawa had'ida d'an d'aga mata yatsa yana fad'in "Excuse me I've to take this..." Don yasan it must be something about business "Yes Nasaar ina jinka...... Whattt....!!?" Ya fad'i yana mai mik'ewa tsaye..... Lokaci guda Azeeza ma ta mik'e tana mai ci gaba da dubansa ga k'irjinta dake wani irin bugu don ita kam sam bata k'aunar tarayyan Nasaar da Siraj tinda tasan cin dunduniyarsa yake da sunan taimakawa Yayanta wajen d'aukan fansa.... Girgiza kai kurum Siraj yake yana karanto innalillahi kafin yace "Nasaar kar ka bar wajen ka kira duk wani kampani na kashe gobara daka sani, gani nan tafe..." Daga haka katse wayar yayi cikin sauri ya nufi ma'ajiyan suit d'insa ya d'auka yana k'ok'arin saka suit d'in Azeeza ke tambayarsa meke faruwa, damuwar dake bisa fuskarta sosai ya k'aru.... Yana mai daidaita zaman suit d'in jikinsa yake fad'in "Wllhi Estates d'in da bamu jima da saya bane wuta ya kamasu, yanzu haka fire service sunata iya k'ok'arinsu wutan tak'i cinyewa, Allah yasa babu kowa cikin gidajen.... Zan tafi yanzu, and please office d'ina na hannunki don bansan yaushe zan dawo ba..." Daga haka ficewa yayi cikin sauri wani wayar na shigo masa.... Komawa kurum Azeeza tayi ta zauna cikin kujera had'ida dafe kanta, itakam anya zata iya zama tanaji tana gani ana cutar da Siraj, gaskiya bazata iya ba, gwara ta tattara ta koma Damaturu k'ila can tafi samun kwanciyar hankali.... Kafin ta bar office d'in saida ta tattara masa duk wasu takardunsa dake bisa table tayi ta maidasu cikin folder a gefe, gaba d'aya Azeeza wani iri take jinta, zuciyarta ta cika da damuwa sosai.. Daga office gida ta wuce straight.... Tindaga bakin gate ta hango yayanta Junaid zaune a farfajiyan gidan da alama dawowarta yake jira, take wasu sabbin k'walla suka ciko idanunta, tausayin yayanta ya shiga ratsa zuciyarta, take zuciyarta ta soma tuhumarta da laifin cin amanar Yayanta d'an uwanta d'aya tak da ya rage mata.... Babu yanda ta iya dole ta tafi ta barsu daga shi har Siraj muddin tana so ta sami nutsuwa cikin zuciyarta Hannu tasa tana share hawayen da suka zubo mata kafin ta k'arasa gaban Yayan nata tana mai ci gaba da share hawayen dake zubo mata d'aya bayan d'aya Bai iya ce mata komai ba sai k'ura mata idanu da yayi.... Cikin kuka Azeeza ta soma fad'in "Yaya I'm sorry, I'm sorry Yaya Junaid, but I can not do this anymore.... Yaya kayi hak'uri I failed you...." Kuka ya hanata ci gaba da magana.... Girgiza kai Junaid yake yana mai ci gaba da dubanta kana yace "I don't get you Zeeza, what exactly do you mean... Mai kike nufi....?" Kallonsa ta kumayi wani kukan na zuwa mata kana tacI gaba da fad'in "Yaya you see, I was about to tell Siraj the whole truth... But then something came up.. And....." Bata kai aya ba Junaid dake faman hura hanci cikin bugun k'irji ya turo wheelchair d'insa gabanta had'i da kamo hannayenta duka biyu, cikin tsananin d'aga murya yake fad'in "Zeeza and what....? Tell me Zeeza did you tell that imbecile about my plans... Did you....?" Ya k'arashe idanunsa na tsarto da wani irin ruwa.... Girgiza kai take ba tareda ta iya furta koda kalma ba.... Shima Junaid d'in hawaye ke fitowa daga idanunsa sanda yaci gaba da fad'in "Zeeza you're so reckless, baki san cewa idan Siraj yasan gaskiya ba harda ke abin zai shafa sannan zakiyiwa Nasaar asarar aikinsa, idan kikayi haka baki kyautawa Nasaar ba...." Cikin d'aga murya tace "That's exactly why I want to leave, that's why I want to disappear.... Yaya wllhi bazan iya ba, I'm leaving to Damaturu right this moment...." Ta k'arashe tana mai shigewa cikin gida cikin sassarfa tana mai share hawayen da suka wanke mata fuska... Cikin sauri Junaid ya take mata baya yana ambato sunanta, k'ok'arin tattara kayanta take sanda Junaid ya paka daga gefe yana dubanta, hawaye masu zafi basu daina fitowa daga idanunsa ba.... A hankali ya soma fad'in "Are you really leaving me Azeeza, da gaske zaki tafi ki barni, kar ki manta bakida kowa saini sannan banida kowa sai ke.... Azee don't leave me..." Ya k'arashe yana kamo hannayenta Girgiza kai take tana dubansa kafin taci gaba da fad'in "Yaya learn to love yourself please.... Matsalarka shine ka kasa son kanka, ka kasa accepting k'addarar da mahalaiccinka ya d'auro maka, shin Yaya baka tab'a sanin idan mutum bai mutu ba Allah bai gama masa halitta ba, bayan wannan Zeenah bazata tab'a wuce tata k'addarar ba itama.... Haba haba saikace babu zuciya cikin k'irjinka, karfa ka mance mun rasa iyayen mu, waye zamu kuma rasawa kamarsu a duniyar nan... Yaya don Allah open your eyes and see, kar ka bari shed'anin dake jikin ka yayi nasara akanka..." Ta k'arashe cikin kwantar da murya had'ida tausasa harshe.... Gefe guda yake duba lokaci guda maganganun Azeeza ke yawo a kwanyarsa.... Juyowa yayi yana dubanta fuskar sa tayi ja gaba d'aya sanda ya soma fad'in "No Azeeza, I won't back down, not, never.... Until I get justice for my self and my Zeenah..... Those three most pay for what they did... And you've to help me finish what we've already started..... If not zaki rasani for good, your only brother, your only family left....." Kallonsa kurum take tana girgiza kai kafin ta silale k'asa tana mai ci gaba da kuka... Ko takanta Junaid bai kuma bi ba yayi ficewarsa daga d'akin, can k'asar zuciyarsa yana jin babu abinda zai hanasa k'arasa abinda ya fara only then zai zama free daga alk'awarin da yayima Zeenah..... *** *Damaturu* Bayan shud'ewar wasu awasu awanni Dr Sahal ya fito daga d'in tiyatar yana mai share zufan dake bisa goshinsa da farin handkerchief... Cikin sauri suka mik'e gaba d'aya suka nufi Dr Sahal, take ya buk'aci yayi magana da Baba Malam, ya kuma umarcesu dasu kwantar da hankulansu domin anyi aikin cikin nasara kuma da ikon Allah zai sami lafiya, ... Da wannan batu na Dr Sahal Hafiz da mahaifiyarsa suka sami natsuwar zuciya, shi kuwa Baba Malam takewa Dr Sahal baya yayi suka nufi office d'insa... Bayan ko wannensu ya daidaita saman kujera Sahal yayi gyaran murya kana ya soma fad'in "Baba anyi aiki cikin nasara da yardar Allah, mun godewa Allah don ban zaci abin zai zo mana da sauk'i kaman haka ba, abinda yasa bamu kaisa can babban asibitin gwamnati ba shi sai anyi wasu cike-cike sannan zai d'auki lokaci kafin ayi aikin tunda asibiti ne na gwamnati kuma kaga ga yanayin case d'in nasa wannan dalili yasa muka kawo majinyacin asibitin abokin aikina wanda ba na gwamnati ba, da kuma taimakonsa muka gudanar da aikin...." Baba Malam ya jinjina kai kana yace "Haka ne Likita, ai babu abinda zamu iya biyanku dashi saidai muce Allah ya biyaku da mafificin alkhairi..." D'an girgiza Kai Sahal yayi kana yace "Babu komai Baba amfanin likita kenan cikin Al'umma, abinda nake son sanar dakai shine wannan mutumi ya sami raunuka cikin jikinsa kaman yanda na sanar daku daga farko,.." Baba Malam ya jinjina kai yana mai fad'in "Haka ne likita.." Sahal ya kuma jinjina kai had'ida d'an fuzar da iska kana yaci gaba da fad'in "Baba a zahirin gaskiya jini ya zuba sosai a jikinsa, sannan jini ya d'an tab'a kwanyarsa kad'an wanda mukayi nasarar cirewa cikin yardar Allah... Amma kuma wani hanzari ba gudu ba... A gaskiya Baba koda wannan majinyaci ya sami lafiya dole ya iya rasa d'aya ko fiyeda d'aya cikin abubuwan da zan lissafo maka, kodai ya rasa hankalinsa ma'ana ya sami tab'in hankali ko kuma ya rasa jinsa ko ganinsa ko ya rasa tunaninsa ma'ana tunaninsa ka iya shafewa sabida ikon Allah ne kurum zai raya mutumin nan, don tunda nake aikin likitanci ban tab'a gamuwa da mutumin da ya sami mummunar had'ari irin na wannan mutumin ba.... Sannan abu na k'arshe munada buk'atar jini cikin gaggawa a k'ara masa, don cikin mu biyu dagani har abokin aikina babu wanda jininsa ya dace da nasa, kai Baba girma ta sauk'o maka balle mu auna naka idan ya dace mu d'iba amma...." Cikin sauri Baba Malam ya katse sa da fad'in "A'a likita ceton rai ne, ka auna nawa idan baiyi ba ka auna na iyalai na, fatanmu Ubangiji ya tada kafad'un wannan bawa nasa, kar kaji komai likita...." Jinjina kai Dr Sahal yayi kana yace "shikenan Baba zamuyi yanda kace zamu auna...." Daga haka mik'ewa sukayi a tare suka fice daga office d'in... Koda aka auna jininsu babu wanda nasa ya dace da na wannan mutumin, ana haka su Umma Marie suka iso hankali tashe, Mairo da Daddah sai dannan Umma Marie suke suna fad'in insha Allah babu abinda zai sami Kawunta Baba Malam.... Sosai Hafizu yayi mamakin hangosu Umma Marie suna k'ok'arin shigowa reception sai sannan ya tuna sanda sukayi waya Umma Marie ta tambayeshi asibitin da suke kuma bai sanar da ita wani mutumin suka kawo ba, tabbas dole hankulansu ya tashi don jiya ce masu yayi Baba Malam na nemansa cikin gaggawa dole suyi zaton k'ila Baba Malam d'in ne babu lafiya ko Mamansa Yaya Azumi.... A hankali ya dafe kansa don tun jiya d'in basu sami natsuwa ba daga shi har iyayensa... Turus su Umma Marie sukayi ganin su duka ukun a reception... Baba Malam ya mik'e yana tambayarsu lafiya yaya ya gansu haka....? Daddah baki sake tace "Yo ai ku zamu tambaya bawan Allah, jiya Malam Hafizu bai mana karatu ba ya tafi afujajan cikin tsananin tashin hankali yana mai sanar damu kana neman sa cikin gaggawa.... A daren hankalin Mariya ya tashi taso zuwa muka danneta mukace ta bari gari ya waye, haka dai muka kwana muna dannarta don ta sanar damu jikinta na bata wani abin ne ya sami kawunta, toh safiyar yau d'in nan muka nufi can gidanka bamu taddaku ba, shine muka yanke shawarin ta kirawo Hafizu ta tambaya, Hafizu ko yace kuna asibiti kaji dalilin da yasa muka taho...." Ta k'arashe koro bayanin tana mai zama saman kujera.... Baba Malam ya girgiza kai kurum yana mamakin shirirta irinta Hafizu bacin haka yaya zai sanar dasu suna asibiti gashi tun jiya basuji daga garesu ba ga halin da ya barosu ciki ai dole hankali ya tashi.... D'an girgiza kai Baba Malam yayi kana yace "Ku kwantar da hankulanku babu abinda ya samemu lafiya lou muke...." Umma Marie na share ragowar hawayen idanunta take fad'in" Amma Kawu wajen wa kuka zo asibiti gaba d'ayanku tun safe tinda nasan danginmu gaba d'aya basa garin nan suna Taraba...." Gaba d'aya suka dubi juna, Baba Malam Hafiz da kuma Yaya Azumi... Kafin su sami zarafin magana Dr Madi abokin aikin Dr Sahal ya k'araso yana tambayar "Kuma kunzo a auna jinin naku ne ko za'a sami wanda yayi....?" A'a aiko Dr ya kuma shigar dasu duhu.. Daddah na zaro idanu tace "Auna jini ni Bintu... Ke Marie ina ne nan anya ba wajen 'yan shan jini ba yaya daga zuwa zasuce a auna jinin mu... Mairo matso daga kutiri na...." Ta k'arashe tana janyo Mairo gam jikinta... Gaba d'aya kallo sukabi Daddah dashi itako ko a jikinta batama san tayi ba. Umma Marie dai abin mamaki ya bata, ta shiga binsu da kallo d'aya bayan d'aya... Hafiz ya dubi Iyayensa kafin yace "Baba inaga Umma Marie ya kamata ta sani tinda ita kad'aice danginmu a garin nan, sannan ko bamu sanar da ita ba nan gaba zata sani..." Yaya Azumi ta jinjina kai kana tace "Hakane Hafiz..." Take Hafiz ya sanar dasu komai duk abinda ke faruwa... Sosai su Umma Marie suka tausaya ma wannan mutumi sannan suka buk'aci likita da ya auna jininsu idan yayi a d'iba tunda ceton rai ne... Nan fah Daddah tace bataji ba bata gani ba babu mayen da zai d'ibi jininta dana d'iyarta, saida Mairo ta nuna mata b'acin ranta sosai kafin ta amince... Wani ikon Allah kuwa cikinsu gaba d'aya jinin Mairo ce yayi dai-dai dana wannan mutumi, take aka kuwa d'iba aka k'ara masa, saidai ba'a barsu sun shiga sun gansa ba don har lokacin bai farka sannan zai iya d'iban kwanaki kafin ya farfad'o.... *SameenaAleeyou📚**FUSKA UKU*🏮 *44* *©Sameena Aleeyou...✍🏽* Mairo na kwance saman gadon da aka d'ibi jininta su Daddah suka shigo, dan Likitocin sun buk'aci karta tashi har sai ta sami hutu sosai domin kuwa ba k'ank'anin jini aka d'iba a jikinta ba, Daddah tana shigowa ta fad'a kan Mairo tana tambayarta yaya takeji.... D'an murmusawa kurum Mairo tayi kana tace "Banjin komai Daddah sai rashin k'arfin jiki ki kwantar da hankalinki kinji, banso ki damu lafiyata lou...." Daddah na rik'eda hannunta take fad'in "Dole hankalina ya tashi d'iyata, duk abinda zai sameki a duniyar nan zanyi fatan ta sameni amaimakon ke...." Murmushi Mairo take tana duban yanda Daddah ta d'aga hankalinta kuma ta damu, tabbas Daddanta tana sonta shiyasa wani sa'in koda tayi wani abin takan mata uzuri duba da yanayin halinta da kuma shekaru da suka soma sauk'o mata... Su Umma Marie su Yaya Azumi da Baba Malam duk suma sun shigo sun mata sannu tareda k'ara mata godiyan jihadin da tayi domin wannan dangin jihadi ne, gata mace mai rauni da kuma fitar da jini duk wata hakan baisa tak'i baida jininta ga wannan bawan Allahn ba domin ceto rayuwarsa... Hafiz ne yayi sallama ya shigo d'akin hannunsa d'auke da bak'ar leda, gaisar da Mairo shima yayi kana ya isa gefen Daddah ya mik'a mata bak'ar ledar yana mai fad'in "Likita yace ta shanye duka biyu domin ta sami k'arfin jikinta..." Daddah ta jinjina kai tanai masa sannu kafin ta shiga bud'e ledar ta ciro gwangwanin maltinar guda biyu.... Wasu 'yan awanni Mairo tayi a kwance kafin Dr Sahal yace zata iya tafiya saidai zuwa dare ma idan son samu ta sake shan Maltina koda gwabgwani guda ne, sannan ake mata pate ko miyan ganyen inyamurai ta Singapore ci har na tsawon sati guda... Kota kan wannan bawan Allah su Daddah basubiba suka nufi gida da Mairo domin ita kanta tana buk'atar jinya.... Hafiz ma bai iya zaman asibitin ba dole yabi sawunsu don hankalinsa sam bazai kwanta ba sai yaga halin da Maironsa ke ciki.... *** *Tambuwal* Kwance ta hangi Zaliha har lokacin bata mik'e ba kaman ta mance yau d'in nan zasu tafi, saida Umman Zaliha ta shigo d'akin sosai idanunta suka sauk'a kan sark'an bead wanda tasan shakka babu Mairo ce ta bata.... D'an murmusawa Umma tayi kafin ta k'arasa ga Zaliha ta d'an dafata "Zali ki tashi ki shirya kinga Babanki yace motar k'arfe biyu zamubi yanzu kuwa d'aya ma ta gauta...." Ta k'arashe tana mai janyo akwatin Zalin... Share k'wallan da suka zubo mata Zaliha tayi kana tace "Umma wllhi ji nake kaman kar na tafi kaman nayita zama k'ila wata rana su Mairo zasu dawo, zamu sake ganin juna.... Ga Nazir ma tunda ya tafi shiru bai kuma waiwayomu ba, wai shin haka rayuwar take, kana sanin mutane kuma suna barin rayuwarka, Umma wllhi yanzu har tsoron sabo da mutane nake, wai Umma Abbah bazai iya canza aikin nan nasa ba kawai ba sai mun bar garin nan ba, kinga bamu tab'a zaman wani gari bafa sai nan..." Ta k'arashe tana mai jefa sark'ar cikin jakan kayanta.... Umma ta kuma murmusawa kana ta kamo hannun Zaliha tace "Ki kwantar da hankalinki Zaliha idan da rabo wataran zaki kuma had'uwa da Mairo sannan wajen aiki su suka zab'i su canzawa mahaifinki kuma kinga bazaice ya ajiye aikinsa ba kawai dan iyalansa basa son barin garinsu, wannan aiki dashi yake nema mana abinda zamuci, ki kwantar da hankalinki kinji koh...." Jinjina kai Zaliha tayi kana ta rungume Ummanta tana addu'an Allah ya amshi bakin Umma watarana ta sake had'uwa da k'awarta Mairo.... Mahaifin Zaliha Gandiroba ne yanda aka masa transfer daga garinsa zuwa garin Suleja ta jihar Niger domin ci gaba da aikin kulada fursunoni a can prison na garin Suleja.. *** *Abuja* Kaman yanda suka tsara yau ce ranar da Junaid zai fuskanci family d'inta, dan already ta sanar da kowa yau d'in tanada bak'o daga foundation d'insu wanda a wajenta ya wuce abokin aiki kurum, yanada matsayi babba cikin zuciyarta, kowa a gidan saida ya fahimci hakan.... Daga saman bene Nana H ke hangosu sanda Malam Sile ya ida parking motar kana ya k'araso da sauri yana bud'ewa Junaid front seat yayinda Nana A ta fito daga bayan motar tana mai k'ok'arin janyo wheelchair d'insa da aka nad'e a gefenta sabida shiga mota da zaiyi, cikin sauri Malam Sile ya k'araso ya amshi wheelchair d'in yana mai fad'in "Haba Hajiya ai da kin bari zan d'auko masa..." Nana A na murmushi take fad'in "A'a babu komai Malam Sile ai zan iya...." Batakai aya ba suka jiyo muryar Nana H daga saman bene ta window tana fad'in "Kai Malam Sile bakaji mai tace bane, zata iya... Besides Sister gwara ki soma koyon taimakon gurgun mijin naki kafin kuyi auren... Gaskiya kin burgeni Nana A...." Ta k'arashe tana mai tafe hannaye had'ida furta "Bravo...!" Malam Sile dai girgiza kai kurum yayi kafin ya ware kujeran Junaid ya saka masa yayinda Nana A ta d'an girgiza kai had'ida fuzar da iska, wani sa'in idan Nana H tayi wani abin sai suga kaman mutuwar mijin nata bai dameta ba, bacin haka yaya za'ace mata mai takaba ce wannan... Shiko Junaid k'uri ya mata daga saman benen kafin ya dawo da dubansa ga Nana A wacce ke k'ok'arin had'o kalma domin basa hak'uri garin irin ta na farko da ya samu a gidansu... Cikin sauri ya shiga girgiza mata kai kyakkyawan murmushi saman fuskar sa kana yace "It's okay, kar ki damu na ganeta tun ranar da muka had'u a foundation, dole a gida a samu irin haka wani sa'in, kar ki damu kinji..." D'an langab'ar dakai tayi kana tace "But dole na damu, ai ni na kawo ka...." Girgiza mata kai ya kumayi kana yace "Ban damu ba gorgeous and idan kina son ganin damuwata shine ki shiga damuwa nan ne zakiga hankalina ya tashi..." D'an murmusawa tayi cikeda jin dad'i kafin ta soma turasa a wheelchair d'in suka nufi cikin gida.... Aiko suna shiga ta shiga rangad'awasu Ammah da Ayiya kira, Rabbeca ce ta fito daga hanyar da zai sadaka da kitchen tanai masu sannu da zuwa... Lokaci guda Nana ta nufi upstairs tana mai sanar da Junaid she'll be right back... Jinjina mata kai yayi yana mai k'arewa gidan kallo yanda aka kashe Naira tamkar a turai.... Yana cikin kalle-kallen ne Nana H ta sauk'o cikin takunta na isa, ko mayafi babu jikinta wai sunan mai takaba..... "Hello cripple.... Barka da zuwa, naga alama 'yar uwata ta aminta dakai although ni ban yarda dakai ba I'm quite sure you're after her money, you don't love her... I'm sure of it...." Ta fad'i tana mai murmusawa had'i da k'arasa shigowa cikin parlorn, lokaci guda take jinjina kai alamun tana tabbatar da abinda ta fad'i.... Kallo Junaid ya bita dashi kana shima ya murmusa yace "Barkanki, kinyi kama sosai da Nana A saidai FUSKARKU ne kurum iri guda amma kowa da halinsa, a zahiri Nana A itakeda nakasa amma a b'angaren hallaya taki halin ne nakashasshiya don na tabbata da za'a baki hoton d'abi'arki kiga yanda yake looking tabbas bazakiso ba, bayan gurgu ne haka nan yake da muni ba kaman yanda fuskarki keda kyau ba, and yes na saye zuciyar 'yar uwarki kaman yanda kika gani, and there's absolutely nothing you can do about it..." ya k'arashe yana mai d'aga mata gira guda Mutuwar tsaye kurum Nana H tayi tana kallon wannan shegen gurgun yanda yake watsa mata bak'ak'en maganganu... Bata ida shan mamaki ba ta jiyo muryarsa yana fad'in "Oh by the way, I heard that you lost your husband...." Ya d'an tab'e fuska kana yaci gaba da fad'in "What a pity..." Lokaci guda kuma ya saki murmushi ganin looks d'in da takedashi a fuskarta kana yaci gaba da fad'in "Kodayake kaman mutuwar bai dameki ba balle na mik'a maki ta'aziyata k'ila mutuwarsa ke kanki ya fiye maki rayuwarsa ne.... Am o right...?" Ya k'arashe murmushi saman fuskar sa... Huci Nana H kurum take don tama rasa mai zata fad'i, isowan su Ayiya da Nana A ya sanya Junaid tura kekensa ya nufesu, cikeda rusunawa yake gaida Ayiya, Cikeda jin dad'i Ayiya tayi hanyar kitchen don kawo ma Junaid abin tab'awa, lokaci guda take umartansa da ya saki jikinsa.... Nana A takai dubanta ga Nana H da ko juyowa ta kasa yi domin bata ida had'iyan maganganun da Junaid ya gama watsa mata ba... Lokaci guda Nana A ta maido da dubanta ga Junaid d'in kana tace "Lafiya dai ko...?" Ta tambaya ta mai dubansa daga shi har Nana H d'in... Murmusawa Junaid yayi kana yace "Lafiya lou, nayima 'yar uwarki ta'aziya ne na babban rashi da tayi, hak'ik'a rasa masoyi babban rashi da bai misaltuwa, na tausaya mata sosai...." Ya k'arashe damuwa fal fuskar sa... D'an murmusawa Nana A tayi kafin ta k'arasa ta rungumo 'yar uwarta Nana H tana mai lallashinta a zatonta abinda Junaid d'in ya fad'i haka ne.... Lokaci guda Nana H ta b'anb'are hannun Nana A daga rik'on data mata tana mai ci gaba da huci had'ida watsawa Junaid mugun kallo kafin ta maido da dubanta ga Nana taci gaba da fad'in "Ke kuma I just hope shima wannan d'in ba yaudarar ki zaiyi ba, you're so naive Nana A, you can easily be fooled by everybody.... You seems so desperate, well gaki ga wannan musakin randa yayi breaking d'inki sai ki ci gaba da kukan ki like a crybaby...." Tana ida fad'in haka ta watsa masu harara ta wuce... Zama tayi cikin kujera zuciyarta na mata zafin abinda 'yar uwarta ta mata gaban bak'onta... Cikin sauri ya turo wheelchair d'insa ya matso kusanta cikin muryar kwantar da hankali ya soma lallashinta.. Nana A ta d'ago cikin muryar kuka take fad'in "Haba Junaid, 'yar uwata ce fah take min haka gaban kowa, wllhi I'm tired of putting up with her attitudes towards me.... Haba haba, this is so unfair...." Kuka ya hanata ci gaba da magana... Cikin kwantar da murya yaci gaba da fad'in "She's your sister, Asmah, kici gaba da hak'uri da ita I'm sure watarana zata daina...." Baikai aya ba ta kuma d'agowa tana fad'in "Tun ina yarinya Ayiya ke fad'a min wata rana zata daina, yaushe ne watarana zaiyi, yaushene please,... " Ta k'arashe tana mai goge fuskarta da tissue paper.... Junaid na murmushi yake fad'in "Randa na d'aukeki gaba d'aya sweetheart, randa kika koma gidana da zama, zatayi kewarki sannan bazata kuma b'ata maki rai ba domin I'll not allow that.... Kinji koh...." Ya k'arashe murmushi saman fuskar sa gefen kumatunsa guda na lostawa.... Murmushin itama tayi kafin ta kuma karb'an tissue paper d'in dake mik'a mata ta share fuskarta.... Nana H dake mak'ale staircase tana hangosu, k'atutun bak'in ciki ne ya tokareta ganin yanda wannan gurgun ke ririta Nana A, bata kuma iya ci gaba da kallonsu ba sai haurawa d'akinta da tayi ta fad'a kan gado, lokaci guda tunanin Heedj ya fad'o mata, da kalan soyayya da kulawa da yake bata, for the first time dataji hawayen gaskiya suna zuba mata dalilin Heedj... A hankali ta rungumo pillow tana mai furta "Heedj I miss you, and I hope you'll understand me....... I miss you Heedj, I miss every single thing about you...." Lokaci guda ta janyo wayarta ta nemo hotonsa wanda ya d'auka sanye da kakinsa ta police tamkar ka kirasa ya amsa, yayi matuk'ar yin kyau... Shafa hoton ta shigayi tana mai ci gaba da furta.... "Nasan baka cancanceni ba, amma nasan zaka fahimci mutuwarka zai fiye maka rayuwarka akan abinda zaka iya gani nan gaba.... I hope you rest in peace....." Ta k'arashe tana mai d'aura wayan saman k'irjinta hotonsa bai bar saman screen ba.... A can parlor kuwa Ammah da Ayiya tarban mutunci sukayiwa Junaid, koda Ammah ta buk'aci Nana A ta kirawo 'yar uwarta su gaisa da Junaid d'in sai cewa tayi sun riga sun gaisa.... Uncle Siraj kuma an masa waya bazai sami dawowa gida kan lokaci ba sabida sabgogin dake gabansa don ko sanar dasu abinda ya faru da estates d'insu baiyi ba Allah yasa bai cinye k'urumus ba kuma an hana 'yan jarida d'auka... Da wannan batu na rashin dawowar Siraj akan lokaci Junaid ya samu kwanciyar hankali yasan bazasu had'u yau da Siraj ba.... Malam Sile shi ya maidasa har gida bayan Nana A ta masa rakiya har farfajiyan gidan nasu ta kuma sanar da Malam Sile ya tafi dashi a hankali... Su Ammah da Ayiya kuwa sai yaba hankalin yaron suke sunsan tabbas Siraj zaiyi Na'am dashi shima idan ya gansa, fatansu Alla ya tabbatar da akahrinsa don ko kad'an naksan sa bai damesu ba tunda suka lura Asma'un tana so..... *** Washe gari k'uri ya mata yana karantar ta gaba d'aya batada walwala, d'an gyara zamansa yayi kana yace "Azeeza I'm listening to you, you were about to tell me something yesterday, right....?" D'ago kod'edd'en idanunta tayi tana dubansa kana ta kuma sunkuyar da kanta, i zuwa lokacin Siraj ya soma shakkun abindake damunta ko kuma take son sanar dashi, Baijin zai iya rabuwa da ita a halin yanzu... Muryarta ya jiyo cikin kuka tana fad'in "Sir I'm sorry... I'm sorry,.... Bazan iya ba, I'm resigning sabida zan bar garin....." Girgiza kai Siraj yake cikin tsananin tashin hankali ya mik'e daga saman kujeransa ya dawo dab da ita had'i da durk'usawa gaban kujeranta lokaci guda ya soma fad'in "Azeeza no, no please.... Don't do this to me, please..... I'm not asking you to love me Back but please give it a try.... I.... I know inada matsala when it comes to love but I assure I feel different with you..." Lokaci guda Azeeza ta mik'e ganin Siraj durk'ushe a gabanta tana mai share hawayen idanunta take fad'in "Sir I'm sorry, but I've already made up my mind, I'm leaving, I can't stay here anymore... I just can't...." Ganin ta nufi k'ofa ya sanya Siraj mik'ewa da sauri ya kuma shan gabanta yana tsananin huci yake dubanta yanda take kuka, datasan zafin da kukanta ke masa da ta daina.... Yana huci yake furta "Why? Tell me why, why did you make me believe that you feel something for me, why Azeeza, is it because of money or what.... Why the sudden change of mind, just tell me why.. I need to know...." Cikin tsananin daka tsawa yake maganar... Sosai take kuka ganin tashin hankalin data hango saman fuskar Siraj lokaci guda taci gaba da fad'in "Siraj ban tab'a sonka ba, sannan banaso zaman mu yayi tsayi kayi tunanin I feel the same for you.... I don't want to end up breaking you.... Please understand me....." Girgiza kai yake yana dubanta cikin tsananin tashin hankali lokaci guda yaci gaba da fad'in "No Azeeza I could feel your heart vibrating towards mine saying you love me too, I know you does, your eyes said it.... Azeeza wllhi ban tab'a son wata mace kaman ke ba before.... Kar ki cutar da soyayyarmu sabida wani dalili naki daban...." Hannu tasa tana goge fuskarta kana tace "Thanks for everything Sir... Goodbye...." Tana ida fad'in haka ta rab'a ta gefensa ta fice... Ko motsi mai kyau Siraj ya kasa sai kallon da ya bita dashi har ta fice... meyasa Al'amra suke faruwa dashi haka, shikenan kowa nasa rasawa yakeyi, ya rasa Ahidjo, ya rasa Lamid'o yanzu ga Azeeza itama yana neman rasata, wai meke faruwa dashi ne....? Da k'yar ya iya komawa saman kujera ya zauna yana tuna tun farkon had'uwarsu da Azeeza... A ranar da k'yar Siraj yes iya komawa gida, tunda Ammah ta gansa haka tasan akwai matsala... K'arasawa garesa Ammah tayi ganin yanda ya rik'o suit d'insa kaman ruwa ya shanyesa, tambayarsa take meke faruwa bai iya amsata ba sai rungumeta da yayi kukan da bai k'aunar ya fito ya shiga kwararowa daga idanunsa, Ammah hankali tashe cikin rawar murya itama irinta mai kuka take fad'in "Siraj lafiya, meke faruwa Son, please talk to me..." Sosai Siraj ke kuka wanda kana jin kukan tarin k'uncin dake cikin zuciyarsa ne ke fitarwa... Nana H da sauk'owarta kenan ta hangi Uncle rungume da Ammah yana kuka tamkar k'aramin yaro, take taji itama kuka na zuwa mata domin a duniya idan kanaso kaga tashin hankalinta shine Siraj ya shiga tashin hankali... Tasye tayi tana dubansu hawaye na zubo mata itama... "Siraj ka min magana na rok'i arzikin ka, wani ne ya kuma mutuwa....?" cewar Ammah cikin tsananin tashin hankali... Da k'yar ya iya saita kansa kafin ya soma fad'in "Ammah kowa barina yake, Ammah meyasa mutanen da nakeso suke tafiya su barni, Ammah ni haka zan k'araci rayuwata, Lamido ya tafi ya barni, Ahidjo ya tafi ya barni and now Azeeza...." Cikeda tashin hankali Ammah ke fad'in "Mai ya sami Azeeza Siraj, ka fad'a min dan Allah..." Jin haka yasa Nana H dake zuban hawaye ta soma murmusawa don a tunaninta Azeeza ma tabi sahun sauran matan Uncle ne... Girgiza kai Siraj yayi kana yace "Tace bata sona Ammah, and she's leaving for good..... Ni kuma kalan tawa k'addarar kenan Ammah..." Cikin sauri Ammah ta kuma rungumesa tana basa baki... Sai sannan Nana H ta k'araso cikeda kulawa ta rungumesa tana fad'in "Uncle let her be, ita tayiwa kanta asara don wllhi nasan kafi k'arfin wancan trap d'in, dama kai ba class d'inta bane, Uncle I assure you zaka sami mata daidai da kai, and Lamido za'a samesa soon, Ahidjo kuma insha Allah he's in better place, we love him all..." Ta k'arashe murmushin kwantar da hankali saman fuskarta,.. K'ak'aro murmushin shima yayi kafin ya rik'o hannunta suka zauna saman kujera yana mai fad'in "Thank you sweetheart..." Murmushi Ammah ta d'an saki had'ida binsu da kallon tausayi domin tasan su duka d'in dauriya suke, a kullum fatanta Al'amra su daidaita a family d'inta.. A b'angaren Azeeza kuwa koda ta koma gida kuka ta dingayi tamkar wacce aka mata mutuwa, kotakan Junaid batabi ba ta shiga tattare kayanta zata gudu... Lallab'awa tayi ta fice daga gidan ba tareda kowa ya ganta ba.. Saidai tana fita Yayanta Junaid ya shigo d'akin yaga wayam, ya hangi wardrobe d'inta wayam, a d'ari ya shiga neman layin Nasaar, take ya sanar dashi yayi saurin bin bayan Azeeza yana tunanin guduwa tayi... Nasaar cikin tsananin tashin hankali ya bar site d'in da yake can Jabi yanda ake renovating gidajen da suka k'one... A d'ari ya karyo layin unguwar tasu nan kuwa ya hangeta tana k'ok'arin taran taxi, cikin sauri ya danna burki ya fice daga motar ya nufeta, aiko Azeeza na hangosa ta soma gudu... Saidai gudun namiji da mace ba d'aya ba... Lokaci guda ya cimmata.. Duk k'ok'arin k'watan kanta da take ta kasa, da k'arfi take fincika tana kuka sosai take fad'in "Let go of me, you monster, let me go..." Ta k'arashe tana mai kwad'a masa jakkan hannunta, saidai inaa Nasaar bai saketa ba ya jefata a mota had'i da saka ma motar key yana fad'in "You shut up, bakisan danger d'in da kike neman jefa rayuwarki ciki ba..." Cikin kuka take fad'in "Babu ruwanka dani koma mutuwa nayi, you've no idea how much I hate you..." Ta k'arashe tana kuka sosai.. Koda suka iso gida ma da kansa ya sureta ya jefata a d'aki suka kulleta shida Junaid... Kuka Azeeza take daga cikin d'akin tana rok'on Yayanta Junaid ya bud'eta... Cikin b'acin rai yake fad'in "This is the consequences of your actions Azeeza, a cikin d'akin nan zaki zauna har sai na gama d'aukan fansata kan Siraj, na tabbata rashinki zai jefasa cikin musiba da k'unci yanzu zai d'and'ani zafin ka rasa masoyi kafin ya bak'unci lahira... Cikin Kuka Azeeza take fad'in "Yaya Junaid don't hurt him please, I beg you kar ka cutar dashi, hurt me instead, dan Allah kar ka cutar da Siraj...." Duk kalaman da take a kunnen Nasaar ji yake kaman yaje ya shak'e Siraj Azeeza ta daina tunaninsa... Cikin sauri ya fice daga parlorn don bazai iya ci gaba da sauraron kukan da take akan Siraj ba.... Haka suka kulle Azeeza saidai su dinga mik'a mata abinci babu fita A haka aka kuma kwashe sati biyu, a dai-dai wannan lokaci Sabi'u yayi shirin tunk'aran iyayen Ahidjo domin ya sanar dasu mutuwar d'ansu.... Gidan Mai unguwa Sabi'u ya soma zuwa ya kuma sanar da abinda ya kawosa cewa sak'o yazo badawa ga mahaifan Aliyu, Mai Unguwa ya buk'aci a kirawo Malam Sanda saidai Sabi'u ya nuna yafiso idan da hali a kaisa can gidan Malam Sandan ya fad'i masu sak'om domin kaman hakan zaifi... Mai Unguwa ya jinjina kai kana ya kirawo d'aya daga cikin 'yan fadansa yace suyiwa bak'om rakiya zuwa gidan Malam Sanda... Tafiyace mai d'an rata kad'an dashike gidan ba'a cikin gari yake ba kafin suka isa.... Sank'ira yayi sallama k'ofar gidan Malam Sanda, baki na biyu aka amsa daga ciki kafin Malam Sanda ya fito suna gaisawa da Sankira... Nan Sankira yake masa nuni da bak'on da yazo nemansa daga can birnin tarayya Malam Sanda ya maido da dubansa ga Sabi'u kafin ya mik'a masa hannu sukayi masabaha, cikeda rusunawa Sabi'u ke gaida Malam Sanda kafin Sankira ya masu sallama yace ya barsu lafiya... Malam Sanda ya dubi Sabi'u kana yace "Toh bawan Allah gashi ban wayeka ba, lafiya dai koh...?" Sabi'u ya d'an gyara tsayuwarsa kana yace "Toh wato Baba wani Al'amari ke tafe dani, kuma akan D'anka Ahidjo ne, amma idan bazaka damu ba zanso mu shiga daga ciki sai na sanar dakai komai gaban sauran iyalan naka domin Ahidjo ya sanar dani yanada iyali a nan gida..." Baffah ya jinjina kai kana yace "Haka ne, amma abinda ban gane ba shine wani sak'o ne zai baka dashi bazai iya zuwa ba, wato abin nasa har ya kai ya daina zuwa saidai yayo aike, toh idanma wani abin ya baka ka kawo mana ka maida masa kayansa don dagani har iyalaina bamuda buk'ata...." Shiru Sabi'u yayi yana duban Malam sanda had'i da karantarsa kana ya d'anyi gyaran murya yace "Baba wato wannan Al'amari da zan sanar daku Al'amari ne mai girma, kayi hak'uri mu shiga daga ciki, ka zauna kaima domin sak'o na magana zan sanar daku ba ta dukiya ko na wani abu makamancin haka ba... Dan Allah Baba..." Ya k'arashe cikin k'ank'an dakai... Shiru tamkar Malam Sanda bazaice komai ba sai kuma yace "Shikenan mu shiga daga ciki... Baffah da kansa yayiwa Sabi'u shimfid'a kafin ya kirawo Innah, ganin Baffah da bak'o matashi ya sanya jikin Innah yin sanyi don ba kowa ya fad'o mata ba face tilon d'anta, gaisawa Innah sukayi da Sabi'u kafin Baffah ya buk'aci ta kirawo Deejoh su taho tare... Nan Innah ke sanar da Baffan Deejohn bataji dad'i ba tun safe zazzab'i ya rufeta, bata gane jikin ba.... Baffah yace "Subhanallah yaya baki sanar dani ba...?". Naga zazzab'in ya d'an sauk'a ne shiyasa ban sanar dakai ba amma yanzu haka ma bacci take..." Baffah ya jinjina kai kana yace "Ki zauna toh wannan bawan Allah sak'o yaron nan ya basa ya kawo mana..." Jin haka yasa k'irjin Innah bugawa da k'arfin gaske domin kuwa tabbas tasan Ahidjo Baffah ke nufi, lokaci guda ta nemi waje ta zauna k'irjinta naci gaba da bugu, don haka kurum ta tsinci kanta da tsoron jin sak'on da za'a isar masun *** *A garin Damaturu* Yau yake cika sati biyu cif a asibitin, a hankali ya soma motsa d'an yatsansa, yana mai k'ok'arin bud'e idanunsa da suka masa nauyi tamkar an d'aura masa manyan duwatsu, da kad'an kad'an idanun nasa suka bud'e gaba d'aya... Nurse dake k'ok'arin d'aura drip mamakine ya cikata taga abinda batayi zato ba.... A guje ta fice kiran Dr Sahal hakan yayi dai-dai da shigowarsu Baba Malam da kuma Hafiz, ganin Nurse d'in ta fito daga d'akin a guje ya sanyasu nufan d'akin cikin sauri... *Toh fah mai karatu wasan zai soma... Just stay tuned guys* *SameenaAleeyou📚*

Post a comment

0 Comments